Abin da ya sa ba za a saki faya-fayen fim din Mansoor yanzu ba- Ali Nuhu

Mansoor

Asalin hoton, @realalinuhu

Bayanan hoto, A cewar Ali Nuhu tsoron masu satar fasaha ya sa ba za a saki fim ɗin a kasuwa ba yanzu sai bayan an kammala nunawa a sinima

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa Ali Nuhu ya bayyana dalilin da ya sa ba za a fara sayar da faya-fayen sabon fim din Masoor a kasuwa ba.

Dan wasan ya ce za a ci gaba da nuna fim din a sinima ne har sai mai fim din ya samu yadda yake so domin "gudun masu satan fasaha su far ma fim din."

Fim ɗin Mansoor, wanda jarumin ne ya shirya kuma ya ba da umarni, labari ne na wani matashi ɗan gaba da fatiha.

Mahaifiyar Manoor ta yi ƙoƙarin ɓoye masa wani sirri game da asalinsa, sai dai soyayya ta sanya shi neman sanin gaskiyar al'amari.

Iyayen wata yarinyar da soyayya ta hada su a sakandare ne suka yi masa gorin asali, inda hakan ya tilasta masa katse karatu, ya bazama duniya don gano mahaifinsa.

An ƙaddamar da fim ɗin Mansoor ranar Alhamis ta hanyar nunin farko, a wani gawurtaccen biki cikin wata sinima da ke birnin Kano.

Kuma sai a nan gaba ne za a fitar da faya-fayensa na bidiyo a kasuwa.

Fiye da shekara 10 da fara tunanin wannan fim, wanda aka shafe fiye da shekara biyu ana tsarawa.

Daraktan fim ɗin, Ali Nuhu ya ce jigon Mansoor shi ne juriya da tawakkali don samun waraka ga wani halin alhini da ɗan'adam ka iya fuskanta a rayuwa.

"Akwai soyayya a cikinsa, amma jigonsa ba soyayya ba ce. Darasin da yake ƙoƙarin isar wa al'umma shi ne duk abin da ka ga ya samu mutum a rayuwa...kar ka yi masa gori."

Ya ci gaba da cewa "kar ka tsangwame shi a kan wannan abu. Domin mai yiwuwa hanyar da Allah Ya jarabce shi ke nan, kamar yadda kai ma a matsayinka na ɗan Adam akwai hanyar da Allah Ya jarabce ka."

Saɓanin yadda aka saba ganin fitattun jarumai a fina-finan Kannywood, a wannan karon an yi amfani da wasu sabbin fuskoki a matsayin manyan jarumai, da suka haɗar da Umar M Sharif da Maryam Yahaya.

Sama da shekara 20 ke nan da fara harkar fina-finan Hausa (Kannywood), amma masu sharhi na sukar cewa ba a sanya fasahar zamani sosai a cikin fina-fianan.

Sai dai masu fim ɗin Mansoor sun ce sun yi ƙoƙarin tunkarar wannan ƙalubale wajen haɗa shi, don haka ne ma a cewarsu, fim ɗin ya kasance mafi tsada a duniyar Kannywood, don kuwa an kashe kusan naira miliyan takwas wajen hadawa da tallata shi.