Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga A'isha Babangida, Habiba Adamu, Usman Minjibir da Nabeela Mukhtar Uba

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Duka-duka a nan muka kawo karshen kawo muku labaran kai tsaye. Da fatan za ku sake kasancewa da mu da safiyar ranar Alhamis idan Allah ya kai mu. Kafin nan za ku ku iya ci gaba da bibiyarmu a shafinmu na bbchausa.com da ma sauran shafukanmu na soshiyal midiya domin samun labaran abubuwan da suka faru a yau din nan. A madadin dukkan ma'aikatan sashen Hausa na BBC, Abdullahi Bello Diginza da Usman Minjibir ke fatan an sha ruwa.

  2. Kotu ta haramta wa jagorar adawar Rwandan tsayawa takara

    .

    Wata kotu a Rwanda ta yi watsi da buƙatar fitacciyar jigon hamayyar ƙasar, Victoire Ingabire na cire mata takunkumin tsayawa takarar shugabancin ƙasar da ke tafe cikin watan Yuli.

    A shekarar 2018 ne aka saketa daga gidan yari bayan shafe shekara takwas a gidan yari saboda laifin barazana ga tsaron ƙasa da batun kisan kare dangin ƙasar na 1994.

    A ƙarƙashin dokokin Rwanda, mutanen da aka ɗaure a gidajen yari na fiye da wata shida ba za su tsaya takara ba.

    sai dai misis ingabire ta ce hukuncin bi-ta-da-ƙullin siyasa ne kawai.

    yayin da take jawabi a wajen harabar kotun a Kigali babban birnin kasar, matar mai shekara 55 ta ce ba ta amince da abin da alƙalin kotun ya faɗa ba, sai dai matsalar ita ce ba za ka iya ɗaukaka ƙara ƙasa da shekara biyu da hukuncin kotu ba.

    "Haƙiƙa ƙasar ba ta cikin ƙasashen da ke bin doka," in ji 'yar siyasar.

    Misis Ingabire fitacciyar mai sukar manufofin gwamnatin shugaba Paul Kagame ce - wadda ta kasance jigo a ɓangaren hamayyar ƙasar cikin kusan shekara 30.

  3. Ba za mu biya kuɗi don sakin ɗaliban Kuriga ba - Gwamnatin Najeriya

    ..

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sake jaddada umarninsa ga jami'an taron ƙasar da su yi duk mai yiwuwa don kuɓutar da ɗaliban makarantar Kuriga da 'yan bindiga suka sace a makon da ya gabata.

    Cikin wani jawabi da ministan yaɗa labaran ƙasar, Mohammed Idris ya yi wa manema labarai, jim kaɗan bayan taron majalisar zartarwar ƙasar da aka gudanar a fadar gwamnati, ministan ya ce gwamnati ba za ta biya ko sisin kobo ba a matsayin fansa ga maharan don sakin ɗaliban.

    Ministan ya ce gwamnatin ƙasar ba za ta lamunci ci gaba da sace ɗalibai don yin garkuwa da su ba, don haka ya ce gwamnati ke kira ga jami'an tsaron da su yi duk abin da ya kamata don tabbatar da sakin ɗaliban da sauran mutanen da hannun 'yan bindiga a faɗin ƙasar.

    ''Idan ta kama gwamnati za ta yi amfani da ƙarfin tuwo wajen kuɓutar da ɗaliban nan, saboda hukumomin tsaronmu a shirye suke ko me za a yi a dawo da waɗanna ɗaliban'', in ji shi.

    A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne wasu 'yan bindiga suka kai hari makarantar furamare da ƙaramar makarantar sakandiren Kuriga, inda suka sace ɗalibai fiye da 280, kodayake gwamnan jihar Uba sani ya ce daga baya wasu 28 sun kuɓuta.

  4. Sanatocin kudancin Najeriya sun farfaɗo da ƙungiyarsu

    ..

    Kwana guda bayan zazzafar muhawara a majalisar dattawan Najeriya - da ta haddasa dakatar da sanata Abdul Ningi, wanda shi ne shugaban ƙungiyar sanatocin arewacin Najeriya - sanatocin kudancin kasar sun farfaɗo da ƙungiyarsu tare da zaɓar shugabanni.

    Ƙungiyar sanatocin kudancin ƙasar ta zaɓi sanata, Adetokunbo Abiru mai wakiltar Legas ta gabas a matsayin sabon shugaban ƙungiyar.

    A baya dai shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan ƙasar, Senator Opeyemi Bamidele ne ke jagorantar ƙungiyar.

    Sanatoci 51 ne daga jihohin kudancin ƙasar 17 suka taro domin farfado da ƙungiyar, wata tara bayan ƙaddamar da majalisar ta 10.

    Sanata Bamidele ya ce ƙungiyar ba sabuwa ba ce domin kuwa tana nan tun lokacin majalisa ta tara, yana mai cewa ayyukan ƙungiyar sun dakata ne sakamakon samun sabon muƙamin shugaban masu rinjaye na majalisar da ya samu.

    Hakan na zuwa ne kwana guda da Majalisar Dattijan Najeriya ta dakatar da Sanata Abdul Ningi daga majalisar na tsawon wata uku bayan zargin shi da furta kalaman da ake ganin sun 'zubar da ƙimar majalisar.'

    A wani zama mai cike da hatsaniya, majalisar ta bai wa sanatocin damar yin bayani ɗaya bayan ɗaya, inda kusan dukkanin su suka nuna rashin jin daɗi kan kalaman sanata Ningi a wata tattaunawa da ya yi da sashen Hausa na BBC.

    Kalaman na sanata Ningi dai da ya yi a BBC Hausa da ma ba su yi wa fadar shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu daɗi ba, inda mai magana da yawunsa ya fitar da sanarwa, inda a ciki ya musanta kalaman sanatan.

    Haka nan lamarin ya janyo cece-ku-ce a faɗin ƙasar, saboda ana ganin hakan a matsayin wata fallasa ta badaƙala da ke gudana a ƙarƙashin ƙasa.

    Wata takarda mai dauke da sa-hannun sanata Abdul Ningi wanda shi ne shugaban kungiyar sanatocin arewacin Najeriya ta 'Northern Senators Forum', ta nuna yadda sanata Ningi ya yi murabus daga shugabancin kungiyar.

    "Na ajiye aikin shugabancin kungiyar sakamakon abubuwan da suka biyo bayan takaddamar da ta wakana a zauren majalisar dattawa."

  5. MDD ta ce dakarun Isra'ila sun kai hari cibiyar raba tallafi ta Rafah

    .

    Hukumar kula da 'yan gudun jihirar Falasɗinawa ta Majalisar Dinkin Duniya UNRWA ta ce an kashe ɗaya daga cikin ma'aikan hukumar tare da raunata wasu mutum 22 a lokacin da dakarun Isra'ila suka kai hari cibiyar raba tallafin abinci a Rafah, da ke kudancin Zirin Gaza.

    Shugaban hukumar ta UNRWA, Philippe Lazzarini ya ce hare-hare kan cibiyoyin hukumar, ya ''zama saɓo dokokin ayyukan jinƙai na duniya ne''.

    A wani labarin kuma ma'aikatar lafiyar Hamas da ke Gaza ta ce hare-haren dakarun Isra'ila ta sama sun kashe mutum biyar

    Kawo yanzu dai rundunar sojin Isra'ila ba su ce komai ba game da batun.

    Yankin Rafah dai na cike da Falasɗinawan da aka ƙiyasta cewa sun kai miliyan 1.4, da ke neman mafaka daga hare-haren dakarun Isra'ila ta ƙasa daga wasu wurare a Gaza.

  6. Na ji takaicin dakatar da Sanata Abdul Ningi - Bala Mohammed

    .

    Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammad ya nuna damuwarsa kan matakin da majalisar dattawan Najeriya ta ɗauka na dakatar da sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawan ƙasar, Sanata Abdul Ahmed Ningi tsawon wata uku.

    A ranar Talata ne majalisar ta dakatar da sanatan bayan zarginsa da zubar wa majalisar kima, a wata hira da ya yi da sashen Hausa na BBC, inda ya yi zargin cewa majalisar ba ta gano inda wasu kuɗi har tiriliyan uku suka shiga ba a kasafin kuɗin kasar.

    Bayan dakatar da shi ne kuma, sanatan ya ajiye muƙaminsa na shugaban ƙungiyar sanatocin arewacin ƙasar.

    Yayin da yake jawabi a taron majalisar zartaswar jihar a fadar gwamnati, gwamna Bola Mohammed ya ce ya ji takaicin dakatar da Sanata Ningi da majalisar dattawan ta yi.

    '' Haƙiƙa, jiya na ji bakin cikin dakatarwar da majalisar dattawan ƙasar nan ta yi wa ɗaya daga cikin jajirtattun sanatocin da muke da su a Bauchi, saboda faɗar gaskiya, saboda kawai ya tsaya a kan gaskiya,'' in ji gwamnan na jihar Bauchin.

    Gwamman Bala Mohammed - wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP, ya kuma ce “Tabbas ban san abin da za mu yi ba, amma za mu tattauna da shi don ganin abin da ya kamata mu yi don taimaka masa, saboda ina goyon bayan duk abin da yake yi, kuma wannan shi

    Dalilin da ya sa majalisa ta dakatar da Sanata Abdul Ningi

    Wane ne Bala Muhammad Kauran Bauchi?

  7. Ana ci gaba da fafatawa a Khartoum duk da watan Ramadan

    ..

    Alamu sun nuna cewa tsagaita wuta a watan Ramadan a Sudan zai yi wahala bayan sojojin ƙasar sun sanar da cewa sun sake ƙwato shelkwatar gidan labarai na kasar da ke Omdurman.

    Wani shafin intanet ya rawaito cewa babban hafsan sojoji Janar Abdel Fattah al Burhan yayi alkawarin fatattakar dakarun-RSF daga koina har sai "nasara ta samu".

    Yayi maganar ne yayin ziyarar sojoji a birnin wanda yake a tsallaken kogin maliya daga babban birnin Khartoum.

    Dakarun na RSF sun ƙwace ginin gidan talabijin da rediyo na ƙasa bayan ɓarkewar faɗa a watan Afrilun shekarar da ta gabata sannan har yanzu ba su wallafa komai ba kan kwace shelkwatar daga hannunsu a shafukansu na sada zumunta.

    Amma Shafin intanet da ke goyon bayan dakarun RSF ya rawaito cewa babban jami'in RSF ya sha alwashin "mai da martani mai zafi" yayin da ya ce har yanzu babban birnin Khartoum na hannun mayaƙansu.

    Yaƙin da aka kai watanni sha ɗaya ana gwabzawa kan kwatar ikon babban birnin na ci gaba duk da kiran da majalisar dinkin duniya tayi kan samar da yarjejeniyar da za ta bari a shigar da kayan agaji da ake bukata cikin Sudan yayin azumin watan Ramadan.

    Ƙwace shelkwatar gidan labaran gagarumar nasara ce ga sojojin abin da ya dade yana ci wa sojojin tuwo a ƙwarya.

    Wannan na nufin cewa kusan duka birnin Omdurman ya koma ƙarkashin ikon sojojin kuma hakan alama ce ta ƙokarinsu na sake mayar da babban birnin karkashin ikon gwamnati daga hannun RSF.

  8. Najeriya ta samu bashin kammala layin dogo daga Kano zuwa Maraɗi

    ..

    Najeriya ta samu bashin dala biliyan 1.3 domin kammala aikin titin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Maraɗi da ke jamhuriyar Nijar, kamar yadda ma'aikatar sufurin klasar ta sanar ranar Laraba.

    Layin na dogon dai zai kara dankon zumunci tsakanin kasashen guda biyu ta fuskar zamantakewa da tattalin arziki.

    Ma'aikatar sufurin ta Najeriya ta ce kamfanin gine-gine na kasar China, CCECC, shi ne zai samar da kaso 85 na yawan kudaden.

    Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin Najeriya da hadin gwiwar bankin Africa Export-Import Bank da bankin habaka tattalin arzikin Afirka na Africa Development Bank.

    "Samun bashin na dala biliyan 1.3 na nuni da irin nasarar da za a samu wajen kammala layin dogon," in ji sanarwar.

    Wannan dai na daya daga cikin shirye-shiryen gwamnatin Najeriya na inganta harkar sufuri a fadin kasar domin bunkasa tattalin arzikin kasar.T

  9. DR Kongo ta soke lasisin kamfanonin haƙar ma'adinai na Rasha

    ...

    Jamhuriyyar Dimokraɗɗiyar Kongo ta soke lasisin kamfanin haƙar ma'adinan Kazakh ERG na kasar Rasha saboda gaza cika sharuddan ƙasar game da hannun jarin cikin gida na wasu 'yan kwangila na kamfanonin haƙar ma'adinai na ƙasashen waje a cewar gidan radiyon Faransa RFI.

    Hukumar da ke kula da harkokin kwangila (ARSP) na DR Congo, ta ce ta gano yadda kamfanin hakar ma'adinan Kazakh ERG da ke aiki da ma'adinan tagulla guda huɗu da na Cobalt, ya ɓoye mallakin kamfanoni tara na kasashen duniya.

    Shugaban ARSP, Miguel Katemb Kashal ya bayyana cewa, waɗannan kamfanoni masu zaman kansu, waɗanda ke da alaka da masu hannun jarin Rasha na kamfanin Kazakh ERG Group, sun ƙulla kwangiloli na daruruwan miliyoyin daloli, tare da kashi 98 cikin 100 na kwangilar Kazakh ERG.

    An ɗauki irin wannan mataki a kan Barrick Gold na Canada da haɗin gwiwar Sicomines na China yayin da hukumomi suka tilasta bin ƙa'idodin kwangilar gida.

    Wannan ci gaban dai ya biyo bayan kin amincewa da ƙulla yarjejeniyar soji da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo a baya-bayan nan da ta yi da Rasha.

  10. Kenya ta jinkirta aika 'yan sanda zuwa Haiti bayan murabus ɗin firaministan ƙasar

    Ƙasar Kenya ta ce za ta jinkirta aika jami'an 'yan sandanta zuwa Haiti bayan da Firaministan yankin Caribbean Ariel Henry ya sanar da murabus dinsa a ranar 11 ga watan Maris, kamar yadda shafin intanet na Nation mai zaman kansa ya ruwaito.

    Babban sakataren harkokin wajen Kenya Korir Sing’oei ya ce jinkirin babu makawa saboda murabus din Henry ya sa Haiti ba ta da wata gwamnati da za ta hada kai.

    Ya ƙara da cewa har yanzu kasar Kenya na kan bakan ta na cewa za ta tura jami'an 'yan sandan kasarta 1,000 zuwa yankin Caribbean karkashin tawagar Majalisar Dinkin Duniya mai suna MSS.

    Kafofin yaɗa labarai na kasar Kenya da al'ummar kasar sun nuna shakku kan yadda rundunar 'yan sandan kasar ta Gabashin Afirka za ta iya magance tashe-tashen hankula a kasar Haiti, duba da tashe-tashen hankulan da ke faruwa a cikin gida, ciki har da 'yan fashi da makamai a yankin arewa maso yammacin kasar Kenya.

  11. An kashe waliyyan addinin Kirista uku a Afrika ta Kudu

    ...

    An kashe wasu waliyan addinin kirista uku 'yan kasar Masar a cikin wani coci ko gidan bauta a Afirka ta Kudu, in ji Cocin.

    Kisan ya haifar da matukar bacin rai da firgici ga al'ummar Coptic Orthodox a Afirka ta Kudu da ma wajenta.

    Archbishop Angaelos na Cocin 'a bayyana kisan a matsayin "abin bakin ciki da ban tsoro".

    Kisan ya faru ne a cocin Saint Mark da Saint Samuel the Confessor da ke Cullinan, mai tazarar kilomita 30 gabas da Pretoria.

    An gano dukkan mutanen uku da raunukan wuka in ji kakakin rundunar ‘yan sandan lardin Col Dimakatso Nevuhulwi kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

    Col Nevuhulwi, ya ƙara da cewa ƴan sanda na ci gaba da ƙoƙarin gano musabbabin kisan inda ya ce an ba da rahoton maharan sun bar wurin ba tare da daukar wani abu mai muhimmanci ba".

    Yawan laifuka na tashin hankali ya yi yawa a Afirka ta Kudu kuma kasar tana daya daga cikin kasashen da aka fi kashe mutane a duniya.

    Waliyan cikin Cocin Orthodox, ɗaya daga cikin tsoffin majami'u a duniya, suna sadaukar da rayuwarsu ne ga addu'o'i da Ibada.

  12. Hisbah ta kama musulman da ba sa azumi a Ramadan a Kano

    ...

    Hukumar Hisbah ta kama wasu musulmai 11 a ranar Talata waɗanda aka ga suna cin abinci a lokacin azumin watan Ramadan a jihar Kano.

    Jihar Kano - da ke da mafi rinjayen musulmi - ta kasance mai aiki da dokokin shari'a da tsarin addinin musulunci.

    Hukumar ta hisbah kan gudanar da bincike a wuraren cin abinci da kasuwanni duk shekara a cikin watan Ramadan.

    Kakakin hukumar, Lawal Fagge ya shaida wa BBC cewa an kama mutum 11, maza 10 da na mace ɗaya da ba sa azumi.

    "Mun kama mutane 11 a ranar Talata ciki har da wata mata da ke sayar da gyaɗa da aka ga tana cin kayanta inda wasu kuma suka sanar da mu," .

    “Sauran mutum 10 maza ne, kuma an kama su a fadin birnin musamman kusa da kasuwannin da ake tafka ta’asa.

    Amma ya ce daga bisani an sake waɗanda aka kama bayan sun yi rantsuwar cewa ba za su sake shan azumi da gangan ba.

    Ya kara da cewa za a ci gaba da gudanar da bincike amma ya ce an keɓe waɗanda ba musulmai ba.

    "Ba mu kama waɗanda ba musulmai ba saboda wannan bai shafe su ba kuma kawai lokacin da za su iya yin laifi shi ne idan muka gano suna dafa abinci don sayar wa musulmi da ya kamata yana azumi."

    Kimanin shekaru 20 da suka gabata ne aka ɓullo da shari’ar Musulunci domin ta dace da dokokin da ba ruwansu da addini a jihohi 12 na arewacin Najeriya, waɗanda galibinsu Musulmi ne.

    Watan Ramadan na da matukar muhimmanci a Musulunci.

  13. Hukumomin Tigray na ƙasar Habasha sun ce an kori tsofaffin 'yan tawaye 100,000

    ...

    Hukumomi a yankin Tigray na arewacin ƙasar Habasha sun sanar da korar tsoffafin mayaƙan sa kai 100,000 bisa yarjejeniyar zaman lafiyar Pretoria ta shekarar 2022 a cewar wani rahoto da jaridar Addis Standard mai zaman kanta ta fitar.

    Shugaban rikon kwarya na yankin na Tigray, Getachew Reda, ya jaddada kudirin gwamnatin ta Tigray na aiwatar da yarjejeniyar Pretoria, duk kuwa da kalubalen da ake fuskanta kamar rashin isassun kayan aiki na gyarawa da kuma mayar da mutanen da aka kora.

    A baya dai Getachew Reda ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta kori tsofaffin mayakan sa kai sama da 270,000 ba har sai an kammala aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya a watan Nuwamban 2022 tsakanin gwamnatin tarayya da tsohuwar ‘yan tawayen Tigray People’s Liberation Front (TPLF).

  14. Yadda na sulale daga hannun ƴan fashin daji - Ɗalibi

    Video content

    Video caption: Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

    A ranar Alhamis 7 ga watan Maris ne ƴan fashin daji suka shiga wata makarantar gwamnati a garin Kuriga da ke ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna, suka sace ɗalibai zama da mata fiye da 280.

    Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ɗaliban suka kammala taron safe, inda ƴan bindigar suka yi wa makarantar ƙawanya tare da kora ɗaliban zuwa cikin daji.

    Wannan ɗalibin wanda ya kuɓuta ya shaida wa BBC cewa ya kwanta ne a cikin ciyawa, inda ya riƙa jan ciki kafin ya samu wurin buya.

    A cikin wannan bidiyo ɗalibin ya bayyana irin wahalar da ya sha kafin samun kuɓuta da kuma halin da sauran ɗalibai suka kasance a ciki.

    Sannan ya bayyana yadda ya samu komawa cikin gari bayan yin tafiya mai tsawo a cikin daji.

  15. Dakarun Djibouti sun fice daga tsakiyar Somaliya saboda rikicin cikin gida

    ....

    A jiya ne dakarun ƙasar Djibouti da ke aiki ƙarkashin rundunar wanzar da zaman lafiya ta Tarayyar Afirka a Somaliya (Atmis) suka fice daga wani babban sansanin soji da ke tsakiyar garin Beledweyne a yankin Hiiraan saboda kasancewar dakarun yankin da ke gaba da juna.

    Sama da shekaru 10 ne sojojin ke jibge a garin kafin janyewar.

    Rahotanni sun ce dakarun yankin na da rikicin siyasa ne kasancewar daya sansani mai goyon bayan gwamnatin yankin na Hirshabelle ne yayin da daya kuma ke da alaka da bangaren ‘yan adawa masu ɗauke da makamai da aka fi sani da jihar Hiiraan.

    Gwamnatin tarayyar Somaliya da jami'an na Hiiraan ba su ce komai ba game da janyewar.

    Rahotanni sun ce sojojin Djibouti sun fice daga sansanoninsu ne bayan tattaunawa tsakanin shugaban Atmis Souf Mohamed El-Amine da mataimakin wakilin Majalisar Dinkin Duniya Raisedon Zenenga.

    Janyewar na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar al-Shabab ta kwace wasu yankuna a jihar Galmudug mai makwabtaka da ita, inda sojojin gwamnatin Somaliya suka yi watsi da sansanoni da dama.

  16. MDD ta yi amfani da sabuwar hanya daga Isra'ila don isar da agaji a arewacin Gaza

    ...

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce an yi amfani da wata sabuwar hanya ta ƙasa wajen kai abinci zuwa arewacin Gaza a karon farko cikin makonni uku.

    Sojojin Isra'ila sun ce wasu motocin yaƙi shida na hukumar samar da abinci ta duniya WFP sun tsallaka ta wata kofa da ke shingen iyakar Gaza.

    Isar da kayan abincin zuwa Gaza da daddare na ranar Talata "wani bangare ne na hana Hamas karbar kayan abincin", in ji MDD.

    Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen duniya ke matsin lamba ga Isra'ila ta ba da damar shiga yankin Falasɗinawa domin isar da kayan agaji a daidai lokacin da ake fama da yunwa yayin da take ci gaba da yaki da ƙungiyar Hamas.

    A ranar Talata kuma wani jirgin ruwa ɗauke da tan 200 na kayan agajin abinci daga wata kungiyar agaji ya tashi daga ƙasar Cyprus a ranar Talata, inda ya ƙaddamar da wani sabon hanyar ruwa zuwa yankin Falasdinawa.

    Ana sa ran isar jirgin kusa da Gaza ranar Alhamis.

    Koyaya, an yi nuni da cewa shiga ta hanya ita ce hanya mafi sauri don samun kayan da ake buƙata cikin gaggawa.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce ayarin motocin WFP sun sami damar yin amfani da titin sojojin Isra'ila da ke kan shingen kan iyakar Gaza don isa arewa tare da kai isassun abinci ga mutum 25,000.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutum 576,000 a Gaza na fama da matsanaciyar yunwa.