Tunisia: Za a daidaita rabon gado tsakanin maza da mata

Shugaba Essebsi

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Shugaba Essebsi ya ce Tunisia kasa ce mai sassaucin ra'ayi.

Shugaban Tunisia zai bayyana wata sabuwar doka da za ta daidaita rabon gado tsakanin maza da mata.

Shugaba Beji Caid Essebsi ya ce zai gabatar da kudurin dokar ga Majalisar dokokin kasar.

A adinin musulunci maza sun fi mata samun kaso mai yawa , sai dai shugaba Essebsi ya nanata cewa Tunisia kasa ce mai sassaucin ra'ayi.

Ana sa ran zai sanar da kudurin daidaita rabon gado tsakanin maza da mata a ranar mata ta duniya .

Haka kuma ana ganin shugaban zai sanar da kudurin kare hakkin yan luwadi da madugo, sai dai ya ce zai kafa wani kwamiti da zai yi nazari kan shirin nasa kafin ya wallafa shi domin kaucewa fushin yan kasar, ko kuma a bayyana shi a matsayin wanda ya yi ridda.