Tsohon shugaban NNPC Maikanti Baru ya rasu

Maikanti Kachalla Baru

Asalin hoton, NNPC

Tsohon Shugaban Kamfanin Mai na Kasa a Najeriya, NNPC Maikanti Kacalla Baru ya rasu.

Wata majiya daga iyalinsa ta tabbatar wa BBC rasuwar tsohon shugaban na NNPC.

Shi ma shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari, ya tabbatar da rasuwar mutumin da ya gada, a wani sakon ta'aziyya da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Kauce wa Twitter
Ya kamata a bar bayanan Twitter?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a Twitter

Kyari ya ce: "Dan uwana, abokina kuma gwanina, Dr Maikanti Kachalla Baru, tsohon shugaban NNPC ya rasu a daren jiya. Mutum ne abin koyi. Allah Ya yafe kura kuransa sannan ya yi rahama a gare shi".

An haifi marigayin a garin Misau na jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya a 1959 kuma ya halarci Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria 1982 inda ya yi karatu a fannin Injiniya.

Ya soma aiki a babban kamfanin man na Najeriya a 1991 inda ya yi ta samu karin girma har ya kai ga zama shugaban na NNPC.

Maikanti Kacalla Baru ya rike mukamin shugaban NNPC daga 2016 zuwa 2019 bayan ya yi aiki a sassa daban-daban na bangaren mai a Najeriya.

Shi ne shugaban NNPC na goma sha takwas.

Ya bar mata biyu da 'ya'ya da dama.

Shugaban BBC Hausa Aliyu Tanko da Maikanti Baru
Bayanan hoto, Marigayin ya kai ziyara hedikwatar BBC da ke London a watan Nuwamba 2017