An gudanar da jana'izar Marigayi Sarkin Zazzau Shehu Idris
Wannan shafi na kawo muku bayanai kai-tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi sakamakon zaɓen gwaman jihar Edo da ke Najeriya da ƙarin labarai.
Rahoto kai-tsaye
Daga Nabeela Mukhtar Uba da Mustapha Musa Kaita
time_stated_uk
Rufewa
Mustapha Musa Kaita
Multi-Media Broadcast Journalist
Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu Litinin za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.
Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan shafin a yau:
Za ku iya duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da ma wasu muhimmai.
Birtaniya ta jinjina wa Najeriya kan zaɓen Edo
Gwamnatin Birtaniya ta jinjina wa Najeriya kan zaben Edo da aka gudanar a ranar Asabar.
Jakadiyar ƙasar a Najeriya Catriona Laing ce ta wallafa hakan a shafinta na Twitter, inda ta ce an gudanar da sahihin zaɓe, kuma duka 'yan takarar na kira da a rungumi zaman lafiya.
Ta kuma gode wa ƙungiyoyi masu zaman kansu dangane da irin gudunmawar da suka bayar a lokacin zaɓen.
A yau ne dai hukumar INEC a ƙasar ta sake tabbatar da Godwin Obaseki na Jam'iyyar PDP a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Edo a karo na biyu, bayan ya doke abokin hamayarsa na Jam'iyyar APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu.
Sudan za ta tattauna da Amurka a Daular Larabawa
Sudan ta ce tawagar wakilanta ta tafi Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa domin tattaunawa da jami’an Amurka a yayin da take ƙoƙarin ganin an cire ta daga cikin jerin sunayen ƙasashen da Amurka ta zayyana suna tallafa wa yan ta’adda.
Janar Abdel Fattah al-Burhan ne ke jagorantar tawagar wakilan na Sudan.
A 1993, Amurka ta saka sunan Sudan cikin masu taimaka wa ta’addanci saboda goyon bayanta ga mayaƙan da ke iƙirarin jihadi, ciki har da Osama bin Laden wanda ya shafe shekara 5 a ƙasar.
A tattaunawar, Amurka ta buƙaci Sudan ta biya sama da miliyan 300 a matsayin diyya ga iyalan waɗanda aka kashe a hare-haren ta’ddanci.
Sannan Amurka za ta yi amfani da damar domin janyo ra’ayin Sudan ta sasanta da Isra’ila
Tattaunawa da Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore
Yadda jama'ar Edo ke murnar lashe zaɓen da Obaseki ya yi
Shugaban Majalisar Dattawa ya yi ta'aziyya bisa rasuwar Sarkin Zazzau
Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan, ya aika saƙon ta'aziyyarsa ga jama'ar Zazzau bisa rasuwar sarkin a yau Lahadi.
A wani saƙo da shugaban ya wallafa a shafinsa na Twitter, Lawan ya kuma miƙa ta'aziyyarsa ga jama'ar jihar Kaduna kan rasuwar Alhaji Shehu Idris, ɗaya daga cikin manyan sarakunan Najeriya.
"A lokacin mulkinsa, marigayin ya yi amfani da basira da kuma darajarsa wajen kawo zaman lafiya da kuma ci gaban Masarautar Zazzau.
"Za a ci gaba da tunawa da shi saboda matsayinsa da gaskiyarsa da kuma soyayyar da ya yi wa mutanensa da son ci gabansu a lokacin da yake raye," in ji Lawan.
An gudanar da jana'izar Marigayi Sarkin Zazzau Shehu Idris
An gudanar da jana'izar Marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris a fadarsa da ke Zaria.
Dubban jama'a ne suka halarci jana'izar sarkin, ciki har da sarakuna da manyan malamai da manyan ma'aikatan gwamnati.
An gudanar da jana'izar ne a cikin gida sakamakon dubban jama'a da suka cika wajen fadar maƙil.
Sarkin dai ya rasu yana da shekara 84, ya kuma shafe shekara 45 kan karagar mulki.
Yadda mutane suka cika Fadar Sarkin Zazzau
Janai'zar Sarkin Zazzau Kai-Tsaye
Hotuna: Jama'a sun cika maƙil wajen jana'izar Sarkin Zazzau
Buhari ya yi wa Obaseki na PDP murnar lashe zaɓe
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yaba wa tsarin zaɓen jihar Edo, wanda Godwin Obaseki na PDP ya yi nasara.
A wata sanarwa da mai ba magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya fitar, shugaban ya taya wanda ya samu nasara murna sannan ya buƙace shi da ya nuna halin sanin yakamata da tawali’u a nasarar tasa.
Ya kuma ce alwashin da ya sha kan batun gudanar da zaɓe mai gaskiya da adalci na nan daram.
Buhari ya jajanta wa mutanen Kaduna kan rasuwar Sarkin Zazzau
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana kaɗuwarsa da alhinin rasuwar mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, kamar yadda wani saƙon ta'aziyya da mai taimaka wa shugaban kan harkokin watsa labarai Garba Shehu ya fitar.
Saƙon ta’aziyyar, wanda shugaban ya aika wa Gwamna El-Rufa’i da kuma mutanen jihar Kaduna, Buhari ya ce Najeriya ta yi babban rashin ɗaya daga cikin sarakunan gargajiya da suka daɗe.
Ya kuma ce ba za a taɓa mantawa da gudunmuwar da Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ya bayar wajen tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya tsakanin ƴan Najeriya ba a shekaru masu zuwa.
Shugaban ya kuma yi roƙon Allah ya gafarta wa marigayin, Ya kuma ba iyalansa da waɗanda suke ƙarƙashinsa juriyar babban rashin da suka yi.
Hotuna: Yadda jama'a suka fara taruwa a Masarautar Zazzau kafin jana'izar sarki
Gawar Marigayi Sarkin Zazzau Shehu Idris ta isa Zaria
Da yammacin yau ne Gawar Marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ta isa Zaria, inda ake sa ran za a gudanar da jana'izar sarkin da misalin ƙarfe biyar na yammaci.
Sarkin ya rasu ne a yau Lahadi, a asibitin sojoji na 44 da ke birnin Kaduna.
Sarkin ya rasu yana da shekaru 84, ya kuma shafe shekaru 45 kan karagar mulki.
Hotuna: Yadda ƙafa ta ɗauke a gidan Ize Iyamu
Obaseki ya yi jawabi bayan lashe zaɓe
Godwin Obaseki wanda hukumar INEC ta sanar a matsayin wanda ya ci zaɓen gwamna na Edo ya gabatar da jawabi inda ya godewa al'umar jihar bisa zaɓensa domin ya sake jagorantar jihar a zango na biyu.
"Al'umar Edo sun bayyana zaɓinsu" a cewar Obaseki.
Obaseki ya kuma gode wa Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari bisa kare dimukraɗiyya tare da bai wa INEC da hukumomin tsaro damar gudanar da aikinsu ba tare da yi musu katsalandan ba.
Obasekin ya bayyana haka ne cikin wani jawabin kai-tsaye da ya yi wanda aka nuna ta shafin PDP da ke Tuwita
Obaseki ya lashe zaɓen Edo
Baturen zaɓen gwamna na jihar Edo, Farfesa Rim-Rukeh ya sanar da gwamna Godwin Obaseki na Jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen da aka gudanar bayan da ya samu ƙuri'u 307,955.
An kammala tattara sakamakon zaɓen Edo
Baturen zaɓe na hukumar INEC Farfesa Rim-Rukeh ya bayyana taƙaitaccen bayani kan zaɓen gwamna na jihar Edo.
A cewarsa, yawan mutanen da aka tantance a zaɓen sun kai 557,443 sai halastattun ƙuri'u da suka kai 537,407.
A cewarsa, ƙuri'un da suka lalace sun kai 12,835 inda a jumulla ake da 550,242 a matsayin yawan ƙuri'un da aka kaɗa.
Ya kuma bayyana yawan ƙuri'un da APC da PDP da SDP da kuma LP suka samu a zaɓen.
APC: 223,619
LP: 267
PDP: 307,955
SDP:323
Ana dakon sanarwar INEC kan wanda ya lashe zaɓen gwamna na Edo
A halin da ake ciki, an bayyana dukkanin sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi 18 da ke jihar ta Edo.
Ana dakon sanarwar baturen zaben hukumar INEC kan wanda ya lashe zaben gwmana na jihar Edo wanda aka gudanar jiya Asabar.
Ga yadda sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin yake:
Karamar Hukumar EGOR
APC: 10202
PDP: 27621
Karamar Hukumar OWAN EAST
APC: 19295
PDP:14762
Karamar Hukumar OVIA NORTH EAST
APC: 9,907
PDP: 16,987
Karamar Hukumar ETSAKO WEST
APC: 26,140
PDP: 17,959
Karamar Hukumar ESAN WEST
APC: 7,189
PDP: 17,434
Ƙaramar Hukumar ESAN SOUTH EAST
APC: 9237
PDP: 10563
Ƙaramar Hukumar OREDO
APC: 1836
PDP: 43498
Ƙaramar Hukumar IKPOBA OKHA
APC: 18218
PDP: 41030
Ƙaramar Hukumar IGUEBEN
APC: 5199
PDP: 7870
Ƙaramar Hukumar OWAN WEST
APC: 11193
PDP: 11485
Ƙaramar Hukumar ESAN CENTRAL
APC: 6719
PDP: 10794
Ƙaramar Hukumar ESAN NORTH EAST
APC: 6556
PDP: 13579
Ƙaramar Hukumar UHUNMWODE
APC: 5972
PDP: 10022
Ƙaramar Hukumar AKOKO EDO
APC: 22963
PDP: 20101
Ƙaramar Hukumar ETSAKO EAST
APC: 17011
PDP: 10668
Ƙaramar Hukumar ETSAKO CENTRAL
APC: 8359
PDP: 7478
Ƙaramar Hukumar ORHIONMWON
APC: 10458
PDP: 13445
Ƙaramar Hukumar OVIA SOUTH WEST
APC: 10636
PDP: 12659
Sakamakon zaɓen Ƙaramar Hukumar Ovia South West
APC: 10636
PDP: 12659