29 ga watan Mayu ranar bakin ciki ce da jimami – Kwankwaso

Kwankwaso Tsohon gwamnan Kano ne
Bayanan hoto,

Kwankwaso ya ce ba sa farin ciki da ranar 29 ga Mayu

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce su ba sa murna da ranar rantsar da sabbin gwamnoni ta 29 ga watan Mayu saboda a cewarsa "fashin mulki aka yi masu".

Ya ce a jihar Kano ranar ta 29 ga watan Mayu ranar bakin ciki ce.

Sanata Rabi'u Kwankwaso ya kara da cewa abin da ya faru a lokacin zaben ranar 21 ga watan Maris da ya bai wa gwamna Abdullahi Umar Ganduje nasara ya zo masu da ba-zata.

Zaben Kano dai ya ja hankali bayan sanar da cewa zaben bai kammalu ba a ranar Asabar 9 ga watan Fabrairu.

A zaben 9 ga watan Maris da aka gudanar PDP ce kan gaba da tazarar kuri'a sama da dubu 26.

An sake gudanar da zaben Kano ne a wasu mazabun kananan hukumomi 28.

Jam'iyyar APC ta lashe zaben a rumfunan kananan hukumomi 27 da aka sake zaben, yayin da PDP ta lashe karamar hukumar Dala.

Gwamna Ganduje
Bayanan hoto,

Gwamna Ganduje lokacin da ya yi nasara

Waiwaye

Rabi'u Musa Kwankwaso shi ne uban gidan Abba Kabir Yusuf a siyasance, kuma akwai takun saka sosai tsakaninsa da Gwamna Ganduje, wanda a baya ya yi masa mataimakin gwamna har sau biyu.

A lokacin da PDP ta tsayar da Abba a matsayin dan takararta, Kwankwaso ya sha suka a ciki da wajen jihar, inda ake zarginsa da cewa ya tsayar da surukinsa a matsayin dan takara.

Da dama dai sun so Kwankwason ya mara wa tsohon mataimakin Ganduje Farfesa Hafiz Abubukar, mutumin da ya yi murabus daga gwamnatin Ganduje wanda kuma daga bisani hakan ya haddasa ficewarsa daga jam'iyyar PDP.

Sai dai Kwankwason ya ce Abba ba mijin 'yarsa ta cikinsa ba ne, mijin 'yar dan uwansa ce, kuma bai tsayar da shi don radin kansa ba sai don ganin mutum ne da zai yi wa jihar Kano aiki bisa kishin kasa da jajircewa, sannan kuma "ba zai yi masa butulci ba."

Abba Kabir Yusuf

Asalin hoton, @RM_kwankwaso

Bayanan hoto,

A zaben 9 ga watan Maris da aka gudanar PDP ce kan gaba da tazarar kuri'a sama da dubu 26

Yawan masu kada kuri'a a Kano

Kano dai ita ce ta biyu a yawan wadanda suka yi rajistar zabe a Najeriya bayan Legas, inda mutum miliyan 5,457,747 suka yi rajista.

Sai dai mutum 4,696,747 daga ciki ne suka karbi katunansu na zabe.

Sannan kuma a jihar ba a samu raguwar masu kada kuri'a sosai ba idan aka kwatanta da na zaben shugaban kasa, ba kamar wasu jihohin ba da raguwar masu kada kuri'ar ya yi kasa sosai idan aka kwatanta da na zaben shugaban kasar.

taswirar inec

Asalin hoton, InEC