INEC ta dage zaben Kogi da Bayelsa da mako biyu

Farfesa Mahmoud
Bayanan hoto, Tun da fari INEC ta sanya biyu ga watan Nuwamba mai zuwa a matsayin lokacin zaben gwamnonin jihohin Kogi da Bayelsa, amma yanzu ta maida shi 16 ga watan.

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, INEC ta dage lokacin gudanar da zaben gwamna a jihohin Kogi da Bayelsa zuwa 16 ga watan Nuwamba.

A watan Afirilu da ya wuce ne INEC ta fitar da sanya ranar biyu ga watan Nuwamba mai zuwa a matsayin ranar gudanar da zaben, wanda yanzu kuma ta sauya ranar.

A wata sanarwa da INEC din ta fitar ranar Alhamis, ta ce ta yi ta samun kiraye-kiraye daga gwamnati, da majalisu da shugabannin al'umma har da na addinai daga jihar Bayelsa kan a sauya lokacin, saboda ya zo dai-dai da ranar addu'ar shekara-shekara da ake gudanarwa tun daga shekarar 2012.

Hukumar ta ce dage zaben ya shafi sauran ranakun da aka sanya don gudanar da duk wasu al'amura da suka shafi zaben na jihohin Kogi da Bayelsa.

Mako biyu ne hukumar zaben ta kara kan ranar da ta sanya domin gudanar da zaben tun da farko.