Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Awwal Ahmad Janyau

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Karshen labarai da rahotanni namu ke nan na yau.

    Ku kasance da mu a gobe idan Allah ya kaimu domin domin wallafa muku wasu sabbin labaran.

    Buhari Muhammad Fagge ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Brazil ya mutu a hadrin jirgi

    Getty

    Wani karamin jirgi dauke da yan wasa hudu da kuma shugaban hukumar kwallon kafa ta Brazil ya yi haradi a Jahar Tocantins.

    Rahotanni sun ce babu wanda ya tsira da ransa a jirgin.

    Yan wasan na kungiyar kwallon kafa ta Palmas na shirin buga wasan kalubale ne da kungiyar Vila Nova a gobe Litinin.

    Shedun gani da ido sun bayyana cewa jirgin ya kama da wuta jim kadan bayan tashinsa.

    A yanzu Hukumar Kwallon kafa ta Brazil ta sanar da dage wasan da aka shirya yi a gobe.

  3. Isra'ila za ta buɗe ofishin jakadanci a Hadaddiyar Daular Larabawa

    Reuters/GettyImage

    Israila ta sanar da bude ofishin jekadancinta a Hadaddiyar daular Larabawa, yayin da itama kasar ta ta sanar da bude makamancinsa a birnin Tel Aviv na Israila.

    Kasashen biyu sun amince da maido da huldar diflomasiyya tsakaninsu bayan kwashe shekaru ana zaman doya da manja.

    Dama watannin da suka gabata Israila ta gyara dangantaka da kasashen Bahrain da Sudan da Morocco.

    To sai dai gyaran dangantakar bai yi wa Palesdiwa dadi ba, kuma suna kallansa a matsayin cin amana.

  4. An saka ranar komawa makarantun gaba da sakandire a Kaduna

    Ma'aikatar Ilimin Jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta sanar da ranar Litinin 25 ga watan Janairu 2021, a matsayin ranar da za a koma karatu a manyan makarantun jihar.

    Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na intanet ma'aikatar ta ce sai da ta tabbatar da shirye-shiryen makarantun kan ka'idojin dokar korona da hukumomin lafiya lafiya suka zayyana.

    Akwai tabbatar da sanya takunkumi da dalibai za su rika yi da malamansu da kuma sauran ma'aikatan makarantun, samar da na'urar gwada zafin jiki, da ba da tazara da dai sauran ka'idoji.

    Sanarwar ta ce dole ne kuma wannan doka ta ci gaba dan haka za a rika kai ziyarar ba zata a ko wanne lokaci domin tabbatar da hakan.

    Haka kuma ana ci gaba da bibiyar yadda sauran makarantun sakandire da masu zaman kansu ke shiri domin su ma a bude su anan gaba.

    View more on twitter
  5. An kashe sojojin Mali shida a kan iyakarta da Burkina Faso

    BBC

    Akalla sojojin Mali shida sun mutu a tagwayen hare hare da aka kai a kan iyakar kasar da Burkina Faso.

    To amma rundunar sojin Mali ta ce ta mayar da zazzafan martani da sanyin safiyar yau.

    Ta kuma sanar da cewa luguden wutar da tayi wa maharan ya bata nasarar kashe talatin daga maharan. Kan iyakar ta Burkina Faso ya zama wani yanki da mayaka suka addaba.

    Don ko a ranar Alhamis an kashe sojoji uku a wani harin bam da aka kai.

  6. Saraki ya bai wa Buhari shawara kan rikicin makiyaya da Yarbawa

    Bukola Twitter

    Tsohon shuagaban majalisar dattawan Najeriya Abubakar Bukola Saraki ya shawarci shugaba Buhari kan rikicin da ke kara ruruwa tsakanin makiyayay da Yarbawa a yankin kudancin kasar.

    Cikin wasu jerin sakonnin da ya wallafa a shafinsa na Twitter Saraki ya ce yana bibiyar duka abubuwan da ke faruwa game da wa'adin da aka bai wa Fulani makiyaya a Jihohin Oyo da Ondo, wanda ya kai da kona duniyoyinsu a jihar Oyo.

    Ya shawarci Shugaba Buhari da ya kira dukkan masu ruwa da tsaki daga bangarorin biyu da kuma bangaren tsaro domin yi wa tufakar hanci tun kafin ta yi kamari.

    Ya kara da cewa wannan ba lokacin da za a tsaya ana maganar jam'iyyar APC ko PDP ba ne, lokaci ne da za a ceto Najeriya daga duhun da take neman fadawa.

    Ya kuma ambato shugaban Majalisa Ahmed Lawal da mataimakinsa Femi Gbajabiamila da su tabbatar majalsia ta shiga cikin wannan lamari.

    Ya ce halin da ake ciki na tsaro a Najeriya kowa na da ta cewa domin neman mafita.

    View more on twitter
  7. Korona ta kashe tsohon ministan Buhari

    Google

    Tsohon Antoni Janar kuma Ministan shari'a na Najeriya Abdullahi Ibrahim ya rasu a ranar Lahadi bayan kamuwa da cutar korona kamar yadda jaridun kasar ke rawaito wa.

    Tsohon ministan shari'ar wanda ya rike ministan sufuri da na sojin sama lokacin mulkin shugaba Buhari na farko karkashin mulkin soji, ana rawaito cewa ya mutu ne a cibiyar killace masu fama da korona da ke Abuja a ranar Lahadi.

    Jaridun kasar na cewa wani wanda bai son a bayyana sunansa ne ya sanar musu da mutuwar Abdullahi Ibrahim.

    An wallafa mutuwar tsohon ministan a shafinsa na intanet.

    Marigayin ya rike ministan shari'a a karkahsin Gwamnatin Abdussalam Abubakar wadda ta mika shugabanci ga gwamnatin farar hula a 1999.

    Gabanin a nada shi ministan shari'ar, ya rike ministan ilimi da kimiyya da fasaha.

    Marigayin shi ne na baya-bayan nan daga cikin manyan jami'an gwamnati da wannan annoba ta kashe.

  8. Gwamnatin Buhari ta bai wa 'yan Najeriya kunya - Jega

    BBC

    Tsohon shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Attahiru Jega ya ce Gwamnatin Buhari ta watsa wa 'yan kasar kasa a ido saboda gaza yin abin da aka zabe ta ta yi.

    A wata tattauanwa da ya yi ta musamman da gidan jaridar Daily Trust, an tambayi Jega kan lamura daban-daban da suka hada da sake fasalin kasar, da kuma ra'ayinsa kan ta ina kuma ya kamata a fara.

    An tambayi Jega ko maki nawa zai iya bai wa Shugaba Buhari kan rikon kamu ludayinsa.

    Jega sai ya ce "Gwamnatin Buhari kwata-kwata ba ta yi abin kirki ba. Ya kamata ya yi abin da ya fi haka.

    "Abin bai yi dadi ba, ya bai wa 'yan Najeriya da yawa kunya. Amma har yanzu yana da lokacin gyara wasu abubuwan, amma idan zai iya kenan.

    "Babu wani boye-boye, Gwamnatinsa ta ba da kunya. Mutane da dama sun yi ta yi masa fatan nasara amma yanzu suna nuna damuwa kan yadda kasar take tafiya," in ji Jega.

    Ya kuma ce "An yi wasu kura-kurai na sakaci wadanda bai kamata su faru ba, kuma akwai bukatar gyara su cikin gaggawa," Jega ya kara da cewa.

  9. Najeriya da Chadi sun tattauna kan Boko Haram

    Shugaban Chadi Idriss Deby da jekadan Najeriya

    Shugaban Chadi Idris Deby ya gana da tawagar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

    Shafin jaridar Alwihda ta ce shugaban Najeriya ya aika tawagar ne ƙarƙashin jagorancin jekadan Najeriya Ambasada Ahmed Rufa’i inda suka tattauna kan hulɗar ƙasashen biyu musamman matsalar tsaro.

    Sai dai babu wani cikakken bayani kan saƙon da tawagar Najeriya ta tafi da shi ga shugaban Chadi.

    Gwamnan Borno Farfesa Babagana Umara Zulum mai fama da rikicin Boko Haram ya taɓa kai ziyara Chadi inda ya gana da shugaba Deby.

  10. Jirgin ƙasa ya kashe matashin da ya je ɗaukar bidiyon TikTok

    Jirgin ƙasa

    Jirgin ƙasa ya kashe wani matashi mai shekara 18 a Pakistan.

    Jirgin ƙasa ya take matashin ne a yayin da abokinsa ke ɗaukarsa hoton bidiyo kan titinin jirgin domin ya yaɗa a kafar TikTok, kamar yadda abokinsa ya bayyana.

    Lamarin ya faru ne a ranar Juma'a a yankin Rawalpindi kusa da Islmababad.

    An ruga da shi asibiti amma matashin ya yi nisan kwana.

  11. SERAP ta ɓukaci Sadiya ta yi bayani kan yadda za ta raba kuɗi ga talakawa

    Kungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya ta buƙaci gwamnatin Najeriya ta yi bayani kan tsarin biyan kuɗaɗen da take raba wa talakawa.

    Ƙungiyar ta ba ministar ma’aikatar kula da ayyukan jin-ƙai da kare Afkuwar Bala'i wa’adin mako ɗaya ta bayyana yadda ake shirin raba naira biliyan 729 ga ƴan Najeriya sama da miliyan 24.

    Ƙungiyar ta ce tana son a yi mata bayani kan hanyoyin da za a bi wajen biyan kuɗin da sunayen waɗanda za su ci gajiyar shirin da kuma tsarin zaɓen mutanen da za a raba wa kuɗaɗen.

    Kuma ko za a miƙa kuɗaɗen ne kai-tsaye ga mutane ko ta asusun banki.

    SERAP kuma na son gwamnatin Najeriya ta yi bayani kan dalilin biyan N5,000 ga ƴan Najeriya miliyan 24.3, wanda ta ce ya yi daidai da kashi biyar cikin 100 na kasafin kuɗin Najeriya na 2021 na tiriliyan 13.6.

    Zuwa yanzu babu wani martani da ya fito daga ministar ko ma’aikatarta da ke kula da raba kuɗaɗen ko kuma daga gwamnatin Najeriya.

    SERAP ta yi gargadin cewa idan har ba ta ji komi daga gwamnati ba za ta ɗauki matakin shari’a ƙarƙashin dokar ƴancin samun bayanai don tilasta wa gwamnati yin abin da ta nema.

    View more on twitter
  12. An bukaci Pantami ya ɓullo da tsarin toshe layi idan an sace saboda NIN

    Yayin da gwamnatin Najeriya ta ɓullo da sabon tilastawa ƴan ƙasar haɗa layukansu na salula da kuma lambobinsu na katin shedar ɗan ƙasa, wani ɗan ƙasar ya bayyana damuwa kan makomar layin mutum idan ɓarayi sun sace.

    Gambo Muhammad a sahafinsa na Twitter @gambomuhammad6 ya ba ministan sadarwar ƙasar Sheikh Pantami shawara ya ɓullo da tsarin yadda mutum zai toshe layinsa idan har an sace layin.

    Ya buƙaci a samar da wasu lambobi da mutum zai iya aikawa ya toshe layinsa idan an sace.

    Ministan kuma ya amsa cewa ya karɓi shawarar tare da gode masa, sai dai bai bayyana ko shawarar da aka ba shi ba za ta samu ga ƴan Najeriya.

    View more on twitter
  13. An kashe kaji kusan miliyan a Iran saboda cuta

    Shugaban ƙungiyar masu kiyon kaji na Iran Nasser Nabipour, ya ce kaji 900,000 aka kashe saboda cutar murar tsuntsaye.

    Ya ce an kashe kajin ne bayan sun kamu da babbar cutar murar tsuntsaye.

    Ya ce cutar ta yaɗu tsakanin kaji da tsuntsaye a lardin Khorasan da wasu sassan Iran.

    Mr Nabipour ya ce tsaikun yin rigakafi shi ya haddasa yaɗuwar cutar tsakanin kajin.

    Kaji
  14. Ƴan bindiga sun sace mutum 15 a jirgin ruwan Turkiya a Najeriya

    Wasu ƴan bindiga a tekun Najeriya sun kashe wani matuƙin jirgin ruwa tare da yin awon gaba da wasu 15 da ke cikin jirgin ruwa mai dakon kaya na Turkiya, kamar yadda kamfanin dillacin labarai Anadolu na Turkiya ya ruwaito a ranar Lahadi.

    Kamfanin dillacin labaran ya ce wanda aka kashe ɗan asalin ƙasar Azerbaijan ne.

    Kafar yaɗa labarai ta NTV a Turkiya ta yi magana da ɗaya daga cikin matuƙa jirgin ruwan da ke ciki wanda ya ce wasu da dama sun ji rauni.

    Jirgin mai suna Mozart na kan hanyarsa ce daga Legas a Najeriya zuwa birnin Cape Town na Afirka ta Kudu wanda ya taso a ranar Asabar.

    An bayyana cewa yanzu ya kamo hanya yana kusa da Gabon.

    Yan fashin teku a Najeriya sun yi kaurin suna wajen sace matuka jirgin ruwa inda ko a 2019 an taba sace matuka jirgin Turkiya kafin aka sake su a watan Agustan 2019.

  15. Shugaban Iraƙi ya amince a zartar da hukuncin kisa kan fursunoni 340

    Shugaba Barham Salih

    Shugaban Iraƙi Barham Salih ya amince da zartar da hukuncin kisa kan fursunoni sama da 340 da kotu ta yanke wa hukunci kan laifukan ta’addanci da sauran tuhume-tuhume.

    Sai dai ba a bayar da cikakken bayani ba kan laifukan ko wannensu, amma akwai mayaƙan IS da dama a gidajen yarin Iraƙi.

    Masu sharhi sun ce tabbatar da hukuncin kisa ga mutane da dama zai dami ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam, waɗandake sukar tsarin shari’ar Iraƙi.

    Sun ce ana amfani da ƙarfi ta hanyar azabtarwa don mutum ya amsa laifi, kuma ana yin gaggawa wajen shari’a.

  16. Najeriya za ta ba Ecowas dala miliyan 20 na yaƙi da ta’addanci

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
    Image caption: Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a taron Ecowas da aka gudanar ta intanet

    Gwamnatin Najeriya ta ce ta ware dala miliyan 20 zuwa ga ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka Ecowas domin yaƙi da ta’addanci a yankin.

    Ministan harakokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ne ya shaida wa taron shugabannin ƙasashen karo na 58 da aka gudanar a ranar Asabar.

    Ministan ya ce tuni Najeriya ta bayar da umurnin fitar da kuɗaɗen zuwa ga asusun Ecowas.

    Ya kuma ce gwamnati ta ware dala miliyan 80 domin yaƙi da ƴan ta’adda a arewa maso gabashin Najeriya da kuma ƴan fashin daji a arewa maso yammacin ƙasar.

    Matsalar tsaro musamman ta’addancin Boko Haram da IS a yankin ƙasashen na yammacin Afirka ne ya mamaye taron shugabannin.

    Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou ya faɗa wa taron shugabannin na Ecowas cewa ta’addanci ne babbar barazanar da yankin sahel ke fuskanta.

  17. Ta’addanci ne babbar barazanar yankin Sahel – Issoufou

    Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou

    Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou ya faɗa wa taron shugabannin Ecowas da aka gudanar ta intanet a ranar Asabar cewa ta’addanci ne babbar barazanar da yankin sahel ke fuskanta.

    Jaridar Niamey et les 2 jours ta ce a cikin jawabin shugaban ya jaddada girman barazanar tsaro da yankin ke fuskanta.

    Ya kuma yi kiran ƙara haɗin kai tsakanin ƙasashen domin magance abin ya ƙira matsalar tsaro da ke ƙara taɓarɓarewa.

    Shugabannin na Ecowas sun tattauna ne a taronsu karo na 58.

  18. Ƙarin mutum 1,633 sun kamu da korona a Najeriya

    Alƙalumman hukumar ɗakile cutuka masu yaduwa ta Najeriya NCDC sun nuna cewa mutum 1,633 suka kamu da korona cikin sa'a 24 a ƙasar.

    Cutar na ƙara yaduwa a Najeriya inda a ranar Juma'a mutum sama da 2,000 NCDC ta ce sun kamu da korona adadi mafi girma tun ɓullar cutar a ƙasar.

    View more on twitter
  19. An fara ceto masu hakar ma’adinai da suka makale a rami tsawon mako biyu a China

    Kafofin yada labaran gwamnatin China sun ce masu aikin ceto a gabashin kasar sun ceto bakwai daga cikin gungun masu hakar ma'adanai da suka makale a karkashin kasa tsawon makonni biyu.

    An nuna hotunan masu aikin ceton na murna a yayin da suka fara fito da mutum na farko.

    Yanzu an tafi da su asibiti domin diba lafiyarsu.

    Makeken ramin ya rufta ne sakamakon fashewar wani abu, wanda har yanzu ba a san musabbabinsa ba.

    Masu hakar ma'adinai 11 ne aka gano cewa na raye tun da farko, amma daga baya daya ya mutu.

    An sami damar yin magana da su ta waya, har ma da aika musu abinci da magani.

    Aikin ceto masu hakar ma'adinai a China
  20. Budewa

    Muna maku maraba da kasancewa da mu a wannan shafin da za mu kawo maku labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya