Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail, Nasidi Adamu Yahaya da Awwal Ahmad Janyau

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Nan za mu dakata da kawo labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faru a Najeriya da sassan duniya.

    Sai ku kasance da mu gobe idan Allah ya kai mu domin ci gaba da samun labarai da sanin halin da duniya take ciki.

  2. Sojoji sun tsaurara tsaro a Myanmar bayan kwace mulki

    Sojoji a Myanmar

    Sojoji a Bama sun tsaurara matakan tsaroa ƙasar bayan da suka kwace iko a juyin mulki.

    Sojojin na sintiri a kan titunan Naypyidaw babban birnin ƙasar da Yangon wanda shi ne gari mafi girma.

    An kuma sanya dokar hana fita a kasar.

    Wata kafar talibin ta sojoji ta sanar da sabbin ministoci da aka naɗa wadanda zasu maye gurbin wadanda aka cire daga kan mulki.

    An tsare shugabannin farar hula na ƙasar ciki harAung San Suu Kyi .

    A sanarwar da ake ganin ta rubuta kafin a kamata, Aung San Suu Kyita yi kira ga jama’a akan su bijirewa juyin mulkin.

  3. Ƙungiyar Miyetti Allah na son a yi ƙidayar dabbobi a Najeriya

    Ƙungiyar fulani makiyaya a Najeriya ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gudanar da kiɗayar makiyaya da dabbobinsu a kasar.

    Fulanin makiyayan sun ce yin hakan zai taimaka musu wajen tantance yawan dabbobin da ke cikin garken, wanda zai ba su damar kamo sabbin shiga ba bisa ka'ida ba.

    Shugabannin sun nuna cewa tun a shekarar 1991, ba a sake wata kiɗayar dabbobi ba.

    Wakilin BBC a Legas Umar Shehu Elleman ya tattauna da sakatare janar na kungiyar Miyetti Allah na kasa, Alhaji Baba Usman Galzarma.

    Video content

    Video caption: Hirar Umar Shehu Elleman da sakataren Miyetti Allah na kasa
  4. Mutum 6 a Najeriya sun harbu da nau'in korona da ta ɓulla Birtaniya

    Hukumar da ke hana yaɗuwar cutaka a Najeriya NCDC ta ce wata nau'in cutar korona da ta fara ɓulla a Birtaniya ta harbi mutum shida a Najeriya.

    Hukumar ta ce dole a ci gaba da bin matakan kariya domin rage yaɗuwar cutar

    View more on twitter
  5. Shin Barcelona ta koma kan ganiyarta ne?

    Messi
    Image caption: Lionel Messi shi ne dan wasan da ya fi zura kwallo a tarihin Barcelona da La Liga

    Ranar Lahadi Barcelona ta doke Athletic Bilbao da ci 2-1 a wasan mako 21 a gasar La Liga da suka fafata a Camp Nou.

    Lionel Messi ne ya fara ci wa Barcelona kwallo kuma na 650 da ya ci a kungiyar sannan na 49 da ya zura a raga a bugun tazara.

    Wannan sakamakon ya kai Barcelona ta koma ta biyu a kan teburin La Liga da maki 40 iri daya da wanda Real Madrid ta uku a teburi take da shi.

    Kuma Barcelona ta yi wasa 10 a jere a gasar La Liga ba ta tare da an doke ta ba, wadda ta ci karawa takwas da canjaras biyu.

    Karanta cikakken labarin a nan.

  6. Labaran BBC cikin minti ɗaya

    Video content

    Video caption: Minti Ɗaya da BBC
  7. Afrika Ta Kudu ta karɓi kason farko na rigakafin korona

    Rigakafin korona

    Kasar Afrika ta kudu ta karɓi kaso na farko na alurar rigakafin cutar korona kuma tana gab da ƙaddamar da wani shirin rigakafi wanda za ta fara da ma’aikatan kiwon lafiya.

    Shugaba Cyril Ramophosa ya je babban filin jirgin sama na Johanesbourg domin karbar alurar rigakafin miliyan daya na kamfani Oxford Astrazeneca da wata cibiyar magunguna a Indiya ta hada.

    Ita ce kasar da cutar korona ta fi ƙamari a nahiyar Afrika kuma mutun dubu 44 sun rasa rayukansu sanadin cutar

  8. Jigo a jam'iyyar APC Tony Momoh ya rasu

    Tony Momoh

    Daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulkin Najeriya Prince Tony Momoh ya mutu.

    Ya rasu yana da shekara 81.

    Momoh shi ne tsohon shugaban jam'iyyar Congress for Progressive Change (CPC), daya daga cikin jam'iyyun da suka dunkule suka kafa APC.

    Momoh dan jarida ne da ya zama ministan watsa labarai tsakanin 1986 zuwa 1990 lokacin mulkin sojin Janar Ibrahim Babangida.

    Tuni manyan 'yan siyasa da masu fada a ji a kasar suka soma bayyana ta'aziyyarsu ga rasuwar dan siyasar.

    Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya bayyana marigayin a matsayin mai yin siyasa "ba da gaba ba."

    View more on twitter
  9. An yanke wa mutum 100 hukunci a Abuja kan ƙin sanya takunkumi

    Ƴan sandan Najeriya

    Wata kotun tafi da gidanka a Najeriya ta yankewa mutum fiye da 100 waɗanda suka karya ka’idojin kariya daga cutar korona hukuncin biyan tara a Abuja.

    Kotun ta yankewa mutanen ne hukunci bayan ta same su da laifin ƙin sanya takunkumi a cikin jama’a.

    Ku saurari rahoton Zahraddeen Lawan.

    Video content

    Video caption: An yanke wa mutum 100 hukunci a Abuja kan ƙin sanya takunkumi
  10. An umarci 'yan sandan Najeriya su tursasa wa mutane sanya takunkumi

    'Yan sandan Najeriya

    Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya Mohammed Adamu ya umarci manyan jami'ansa da su tabbatar an tursasa wa 'yan kasar sanya takunkumi domin kare su daga kamuwa da cutar korona.

    Ya bayyana haka ne a sakon da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan kasar Mr Frank Mba ya aike wa manema labarai ranar Litinin.

    "Babban Sufeton 'yan sanda M.A Adamu ya baayr da umarni ga mataimakansa 17 da ke rundunonin 'yan sanda da ke shiyyoyi da Kwamishinonin 'yan sanda na jihohi 36 da Abuja, su tursasa bin dokar kare kai daga kamuwa da COVID-19," a cewar sanarwar.

    Ta kara da cewa a yayin da 'yan sandan za su tabbatar da bin wannan doka, za kuma su yi hakan ne cikin da'a da mutunta jama'ar da ake so a kare su daga kamuwa da cutar.

    Shugaba Muhammadu Buhari ne ya sanya hannu kan umarnin ranar 26 ga watan Janairu yana mai amincewa da daurin wata shida kan duk wanda aka kama ba sanye da takunkumi ba a banar jama'a.

  11. Kosovo ta ƙulla hulɗa da Isra’ila

    Kosovo ta zama kasar Musulmai ta baya-bayan nan da ta kulla huldar diflomasiyya da Isra’ila.

    Ta kuma amince da birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra’ila, abin da ya sa ta yi hannun riga da sauran kasashen musulmin duniya.

    A cikin 'yan watannin da suka gabata wasu jerin kasashen Larabawa da suka haɗa da Daular Larabawa da Bahrain sun daidaita alaƙarsu da Isra'ila.

    Amma saɓanin Kosovo ba, ba za su kafa ofisoshin jakadancinsu a birnin Kudus ba.

    Mallakar birnin wani ɓangare ne na takaddama tsakanin Isra’ila da Falasɗinawa, waɗanda ke son gabashin Kudus da aka mamaye a matsayin babban birnin ƙasarsu.

  12. Darajar naira na ci gaba da faɗuwa

    naira

    Darajar naira ta ƙara faɗuwa kan dalar Amurka a kasuwar bayan fage a ranar Litinin.

    Ƴan kasuwa sun ce darajar kuɗin na yi mugunyar faɗuwa inda ake sayar da dala ɗaya kan naira 480 a kasuwar bayan fage.

    Ƙarin kashi 20 fiye da farashin da Babban Bankin Najeriya ya ƙayyade kan naira 381.

    Buƙatar dala na ci gaba da ƙaruwa, kuma wannan ke sanya matsin lamba a kan

    naira.

    Masu shigo da kaya na fuskantar ƙalubale yayin da kuma masu saka jari a kasuwar canji wasu suka fice.

    Ƴan kasuwa sun ce har yanzu Babban Bankin Najeriya bai ci gaba da sayar da dala ba a wannan shekarar ga masu saka jari na ƙasashen waje, kuma bai sayar da kuɗaden waje ba ka kamfanonin canji a makon da ya gabata.

  13. Hezbollah ta ce ta harbo jirgin Isra'ila da ya ratsa Lebanon

    Ƙungiyar Hezbollah ta sanar da harbo wani jirgin Isra'ila da ya ratsa sararin samaniyar Lebanon a kudancin ƙasar.

    A cikin wata sanarwa, Hezbollah ta ce," Mayakanmu da safiyar Litinin sun harbo jirgi marar matuƙi mallakin maƙiya Isra'ila bayan ya ratsa ta sararin samaniya a yankin birnin Blida."

    A nata ɓangaren, Isra'ila ta ce an harbo jirginta a lokacin wani ran gadi a kan iyaka da Lebanon, kamar yadda sanarwar da ma'aikatar tsaron Isra'ila ta bayyana.

  14. Amurka ta ce Iran ta kusan kammala shirin haɗa makamin nukiliya

    Shugaba Biden

    Amurka ta ce makwanni suka rage wa Iran ta kammala samar da kayayyakin haɗa makamin nukiliya.

    Sabon Sakataren harakokin wajen Amurka ne Antony Bilken ya bayyana haka a wata hira da kafar NBC.

    Iran ta jingine shirinta na nukiliya ƙarƙashin yarjejeniyar da aka ƙulla da manyan ƙasashen duniya a 2015. Amma Gwamnatin Donald Trump ya rusa yarjejeniyar, kuma domin mayar da martani Iran ta saɓa alƙawalin da ta ɗauka a yarjejeniyar.

    Gwamnatin Biden ta nuna cewa a shirye take ta sake tattaunawa yarjejeniyar.

  15. Birtaniya ta sanya takunkumi kan manyan jami'an gwamnatin Zimbabwe

    Gwamnatin Birtaniya ta sanar da sanya jerin takunkumai kan hudu daga cikin manyan jami'an hukomomin tsaron Zimbabwea, tana mai zarginsu da keta hakkin dan adam, ciki har da kashe masu zanga-zanga.

    Kasar za ta rufe asusan bankin Ministan Tsaro Owen Ncube da shugaban 'yan sanda da shugaban hukumar leken asiri da kuma tsohon shugaban dogaran shugaban kasar.

    Kazalika an hana su ziyartar Birtaniya.

    Birtaniya ta bayyana su a matsayin masu hannu a kashe masu zanga-zangar da ta biyo bayan zaben kasar na 2018, da kuma hargitsin da ya faru a watan Janairun sekarar 2019.

    A sakon da ya wallafa a Tuwita, kakakin gwamnatin Zimbabwe Nick Mangwana ya ce dukkan jami'an da ake magana a kansu ba su da kaddarori a Birtaniya kuma ba su da niyyar yin tafiya zuwa kasar.

  16. Jonathan ya yi kira a saki Aung San Suu Kyi

    Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi kira ga sojojin da suka yi juyin mulki a Myanmar da su saki jagorar kasar Aung San Suu Kyi.

    Mr Jonathan ya yi kiran ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Tuwita ranar Litinin.

    "Ina kira da a saki zababbiyar shugabar Myanmar Aung San Suu Kyi ba tare da sharadi ba," in ji Mr Jonathan.

    View more on twitter

    Ya kara da cewa yana goyon bayan mulkin dimokradiyya a duk fadin duniya "kuma ina kira da a maido da tsari mulkin a Myanmar."

    A safiyar Litinin ne sojojin kasar suka yi wa gwamnatin farar hula juyin mulki sannan suka yi awon gaba da Aung San Suu Kyi da wasu manyan jami'an gwamnatinta.

    Kazalika sun sanya dokar ta-baci a kasar tsawon shekara guda.

  17. An kama masu sayar da ruwan gishiri a matsayin riga-kafin korona

    Rigakafin korona

    Hukumomi a China sun kama mutum 80 bisa zargin sayar da riga-kafin cutar korona na boge.

    Kamfanin dillancin labarai na ƙasar mai suna Xinhua ya ruwaito cewa mutanen na sayar da ruwan gishiri ne a matsayin rigakafin tun a watan Satumba.

    An ƙwace aƙalla kwalba 3,000 na maganin a sassa daban-daban na ƙasar.

    Gwamnatin China ta ƙudiri aniyar yi wa mutum miliyan 50 rigakafin cutar korona nan da tsakiyar watan Fabarairu.

  18. Ƙasashen duniya na ci gaba da Allah-wadai da juyin mulki a Mymmar

    Mymmar

    Gomnatoci na ƙasashen duniya na ci gaba yin Allah-wadai da juyin mulki da sojoji suka yi a Mymmar.

    Amurka da Japan da Indiya da Tarrayar Turai sun yi kira ga mahukunta a ƙasar kamn su mutunta mulkin Dimokuradiyya.

    Kakakin gwamnatin Japan ya ce kasarsa ta nemi ɓangarorin da lamarin ya shafa da su zauna da juna a teburin shawara kamar yadda dimokuradiyya ya tanada.

    Shi ma Firaminista Boris Johnson na Bitanitya ya nemi sakin shugabannin farar hula.

    Ita ma China - babbar abokiyar kasuwancin Myammanr - ta nemi dukkanin ɓangorin kan su mutunta kundin tsarin mulki tare da kiyaye zaman lafiya.

    Sai dai maƙobta irinsu Cambodia da Thailand sun ce juyin mulkin sojoji lamari ne na cikin gida.

  19. Bobi Wine na ƙalubalantar nasarar Shugaba Museveni a kotu

    Uganda

    Ɗan takarar adawa a zaɓen shugaban ƙasar Uganda, Bobi Wine, ya shigar da ƙara a kotu yana mai ƙalubalantar sakamakon nasarar Shugaba mai-ci Yoweri Museveni.

    Lauyan mawaƙin wanda ya zama ɗan siyasa da kuma jam'iyyarsa ta National Unity Platform, ya ce suna buƙatar a je zagaye na biyu a zaɓen.

    Shugaba Museveni - wanda ya hau mulki tun shekarar 1986 - ya lashe zaɓen ne da kashi 58 cikin 100 na ƙuri'un.

    Bobi Wine, wanda sunansa na gaskiya shi ne Robert Kyagulanyi, ya samu kashi 35.

    Jam'iyyar Museveni mai suna NRM ta bayyana a ƙarshen mako cewa ta tattara tawagar lauyoyi domin kare nasararta a gaban kotun, wadda aka sanar a watan Janairu.

  20. Buhari bai karya dokar yaƙi da korona ba – Fadar Shugaban Ƙasa

    Muhammadu Buhari a Daura

    Fadar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta ce shugaban bai karya dokar yaƙi da annobar cutar korona ba a garin Daura mahaifarsa a ƙarshen mako.

    Jam'iyyar PDP mai adawa da sauran 'yan Najeriya sun soki Buhari bayan ɓullar wasu hotuna da ke nuna shugaban a cikin jama'a ba tare da takunkumi ba yayin da yake magana da su a lokacin sabunta rajistarsa ta jam'iyyar APC.

    A makon da ya gabata ne Buhari ya sanya hannu kan dokar daƙile yaɗuwar annobar cutar korona, wadda ta tanadi ɗaurin wata shida ko tara a kan waɗanda aka kama ba tare da takunkumi ba a bainar jama'a.

    Da yake magana ta kafar Channels TV a cikin shirin Surise Daily, mai magana da yawun shugaba Buhari, Garba Shehu, ya ce Buhari na sanye da takunkuminsa a lokacin aikin rajistar kuma ya cire ne kawai a lokacin da yake magana da mutane.

    "Mutane ba su fahimta ba, shugaban ƙasa na sanye da takunkuminsa tun farko. Ya cire ne a lokacin da yake magana a makirfo. Wannan kawai wasan yara ne da PDP take yi," in ji Garba Shehu.

    Buhari na ziyarar aiki ta kwana huɗu a garin Daura mahaifarsa da ke Jihar Katsina, inda daga cikin ayyukan da zai gudanar har da sabunta rajistarsa ta jam'iyya mai mulki, wada ya yi ranar Asabar.