Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Mustapha Musa Kaita da Awwal Ahmad Janyau

time_stated_uk

  1. Rufewa

    A nan za mu dakata da kawo labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu.

    Da fatan za ku ci gaba da kasancewa da shafin bbchausa.com domin samun labarai da dumi duminsu da hotuna har ma da bidiyo.

    Ku ci gaba da bibiyarmu a Facebook da Twitter da Instagram

  2. Mutum 76 suka rage masu ɗauke da korona a Kaduna

    Gwamnatin jihar Kaduna ta ce yanzu mutum 76 suka rage masu ɗauke da cutar korona a jihar.

    Sanarwar da gwamnatin jihar ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce an sallami mutum 149 daga cikin 232 da aka tabbatar da suna ɗauke da cutar, yayin da cutar ta kashe mutum bakwai.

    Gwamnatin ta ce za a a iya kara samun yawan masu ɗauke da cutar saboda gwaji da ake gudanarwa a wurare da dama.

    Sanarwar ta ce kuma an gudanar da gwaji kusan 2000 a jihar.

    View more on twitter
  3. Ana ce-ce-ku-ce a Ghana kan ƴan majalisar da ke dauke da korona

    Tsohon shugaban Ghana John Dramani Mahama ya bi sahun wasu ƴan Ghana da ke yin kiran sanin makomar wasu daga cikin ƴan majalisa da ake tunanin suna ɗauke da cutar korona.

    John Mahama ya yi kiran ne a shafinsa na Twitter a ranar Juma’a, inda ya ce rahotannin da ke cewa cutar korona ta yadu a majalisa abin damuwa ne, yana mai cewa ya kamata ƴan kasa su san halin da ake ciki.

    View more on twitter

    John Mahama ya yi kiran ne a shafinsa na Twitter a ranar Juma’a, inda ya ce rahotannin da ke cewa cutar korona ta yaɗu a majalisa abin damuwa ne, yana mai cewa ya kamata ƴan kasa su san halin da ake ciki.

    Kiran tsohon shugaban na zuwa yayin da al’ummar Ghana ke zargin shugabannin majalisar ƙasar da ɓoye gaskiyar bayanai kan rahotannin da ke cewa wasu daga cikin ƴan majalisar guda biyu da wasu ma’aikata 13 sun kamu da cutar korona.

    Shugabannin majalisar dai sun ce sun gudanar da gwaji kan dukkanin ƴan majalisar da kuma ma’aikatan majalisar makwanni biyu da suka gabata.

    Amma bayan mako biyu ne aka fara ce-ce-ku-ce kan cewa wasu daga cikin ƴan majalisar da ma’aikata sun kamu da cutar, kamar yadda jaridar Citi Newsroom ta ruwaito.

    Ta kuma ce ƴan kasar da dama da suka haɗa har da ƴan majalisar sun yi kiran a bayyana sakamakon gwajin da aka yi wa dukkanin ƴan majalisar da kuma ma’aikata a majalisar.

  4. Ga tsofaffin da suka ci korona da yaƙi

    Masana kimiya sun ce cutar korona ta fi yi wa tsofaffi illa fiye da duk wani rukuni na shekaru.

    Amma duk da labarai kan girman ɓarnar cutar, amma kuma akwai na kyakkyawan fata inda wasu da suka haura shekara 100 a Birtaniya suka tsira daga cutar korona.

    Vera Beeley
    Image caption: Vera Beeley

    Bayan ta warke daga cutar korona a asibiti, wata tsohuwa ƴar shekara 102 Vera Beeley ta yi tambaya cikin raha: " Ko yaushe za a sake buɗe mashaya?"

    "Ba wai don za ta tafi ba," kamar yadda jikanta Ian Whitehead ya yi dariya.

    "Duk da shekarunta (ya nuna kamar) komi ya ƙare. Mun yi tunanin wannan zai iya samunta, amma kuma hakan bai yiwu ba."

    Jane Collins
    Image caption: Jane Collins

    Jane Collins, mai shekara 104 ta samu tsira daga yaƙe-yaƙen duniya guda biyu, da tabarbarewar tattalin arziki da dama kuma har yanzu tana gwagwarmaya yayin da ta warke daga cutar korona, a cewar jikanyarta Sarah Balmforth.

    Pat Aldridge
    Image caption: Pat Aldridge

    Lokacin da Pat Aldridge, 'yar shekara 105 daga Somerset aka kai ta asibiti tana fama da matsalar numfashi, iyalinta sun yi tunanin da wuya ta rayu.

    Amma sallamar ta daga asibiti bayan ta yi kwanaki biyar, Ms Aldridge ta ce ta yi sa'a la'akari da shekarunta.

  5. Ƴan ƙauye sun yi fito na fito da ƴan bindiga a Katsina

    ƴan bindiga a Najeriya

    Rundunar ƴan sanda a jihar Katsina a ce aƙalla mutum 13 suka mutu bayan fito na fito da suka yi da masu satar shanu a ƙaramar hukumar Faskari.

    Kakakin rundunar ƴan sandan jihar ta Katsina Gambo Isah ya shaida wa BBC cewa a daren Juma'a ne wasu ƴan bindiga masu satar shanu suka abka ƙauyen Unguwar Gizo cikin ƙaramar hukumar Faskari domin satar shanu, daga nan kuma mutanen ƙauyen suka far masu domin kare dukiyoyinsu.

    Ya ce mutanen ƙauyen 13 aka kashe, yayin da kuma bakwai suka ji rauni.

    Kakakin rundunar ƴan sandan ta Katsina ya yi kira ga mutane su ƙauracewa yin fito na fito da barayi waɗanda ya ce suna ɗauke da manyan makamai da suka haɗa da bindiga AK47.

    Ya ce babban hatsari ne mutane su tari ɓarayi da bindiga harba ka ruga ko duwatsu su fito suna gaba da gaba da ƴan bindiga inda ya yi kira ga mutane su dinga sanar da jami'an tsaro.

    Harin na zuwa ne a yayin da sojojin Najeriya suka kaddamar da sabon farmaki kan masu fashin daji a Katsina, jihar da shugaba Muhammadu Buhari ya fito da ke makwabtaka da Zamfara da ɓarayi suka addaba.

    An shafe shekaru yankin arewa maso yammaci na fama da hare-haren ƴan bindiga masu satar shanu da garkuwa da mutane inda wata ƙungiya ta ICG ta ce kimanin mutum 8,000 aka kashe a yankin.

  6. An killace ƴan Najeriya da aka kwaso daga China

    Gwamnatin Najeriya ta ce ta kwaso ƴan kasarsa 286 da suka maƙale a China saboda dokar kulle da aka kafa a ƙasar sakamakon annobar cutar korona.

    A saƙon da ta wallafa a Twitter, Hukumar da ke kula da ƴan Najeriya a ƙasashen waje ta ce ƴan Najeriyar sun iso a Abuja da misalin ƙarfe 2:30 na ranar Asabar.

    Amma hukumar ta ce za a killace su na tsawon mako biyu kamar yadda hukumar daƙile cutuka a ƙasar da ma'aikatar lafiya ta Najeriya suka ɓuƙata.

    View more on twitter
  7. Likitoci sun yi barazanar 'shiga yajin aiki' a Najeriya

    Likitocin Najeriya

    Likitoci masu neman ƙwarewa a asbitocin gwamnatin tarayya da ake kira Resident Doctors sun ba gwamnati wa'adin mako biyu ta biya wasu bukatunsu da suka hada da rashin biyansu kudaden alawus da suka kira na cutar korona ko kuma su tsunduma cikin yajin aiki.

    Ƙungiyar likitocin ta ƙasa ta ce idan har ba a biya hakkokinsu ba kafin cikar wa'adin da suka bayar za su tsunduma cikin yajin aikin, kamar yadda kafar talabijin ta Channels ta ruwaito.

    Kafar ta ce likitocin sun yi gargaɗin ne a wani taron manema labarai da suka gudanar a Bauchi yayin babban taron ƙungiyarsu karo na 40.

    An ambato shugaban ƙungiyar likitocin Aliyu Sokomba, na cewa daga cikin buƙatun da suke son a biya masu sun haɗa da kuɗaɗen alawus na yaƙi da annobar korona, bayan sun ji labarin cewa an biya wasu likitoci da ma'aikatan lafiya.

    Sun kuma buƙaci a dawo da abokan aikinsu da aka kora a asibitin koyarwa ta Jami'ar Jos tare da biyansu albashi.

  8. Ƴan bindiga sun kashe mutum 15 a Burkina Faso

    Ƴan bindiga sun kashe a kalla mutum 15 yayin wani hari a arewacin Burkina Faso, kusa da iyakar ƙasar da Mali.

    Ministan watsa labarai na ƙasar ya bayyana cewa an kai harin ne ga wasu jerin motoci da ke ɗauke da ƴan kasuwa a lardin Loroum a ranar Juma'a.

    Wani wanda ya shaida lamarin ya bayyana cewa wasu ƴan banga ne da ke taimaka wa sojoji wajen yaƙi ke rakiyar motocin 'yan kasuwar yayin da aka kai harin .

    A farkon shekarar nan, yawan waɗanda 'yan bindiga suka raba da muhallansu a ƙasar ya ƙaru daga dubu 90 zuwa sama da dubu 800.

    Tun a 2017, rikici a ƙasar ya tilasta wa makarantu su rufe a arewacin ƙasar.

  9. Yadda farashin kayayyakin abinci ya ƙaru a Najeriya – NBS

    Shinkafa

    Farashin kayayyakin abinci ya karu a a Najeriya a watan Afrilun 2020 a cewar wani rahoto da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta wallafa kan farashin kayayyakin abinci a ƙasar.

    Rahoton hukumar wanda aka fitar a watan Mayu, ya ce matsakaicin farashin 1kg na shinkafa na karuwa shekara shekara da kashi 31.97 kuma wata wata da kashi 7.56 zuwa N471.84 a watan Afrilun 2020 daga N438.66 a watan Maris na 2020.

    Sannan shinkafar gida da aka noma aka sarrafa ta fi sauƙi a jihohin Kebbi da Sokoto, yayin da ake sayar da 1kg na shinkafa a Kebbi kan farashin N267.17, a Sokoto kuma kan N232.65.

    Shinkafar kuma ta fi tsada a jihar Bayelsa inda ake sayar da 1kg N591.17, a cewar rahoton.

    Haka ma rahoton ya ce farashin ƙwai na gidan gona ya karu da kashi 2.04 a shekara shekara da 3.338 a wata wata inda ake sayar da dozen guda 12 kan 476.72 a wata Afrilu daga N461.15 a Maris din 2020.

    Hukumar NBS ta ce ta tattara rahoton farashin kayayyakin abincin ne daga kananan hukumomi 774 na sassan jihohin Najeriya hadi da Abuja tare da tattaunawa da mutane sama da 10,000 domin tantance farashin kayayyakin.

  10. Yadda aka gyara cikin Masallacin Madinah kafin buɗe shi gobe

    .
    .
  11. Trump na shan suka kan ficewar Amurka daga WHO

    Shugaba Trump

    Shugaba Donald Trump na shan suka ciki da wajen Amurka bayan ya sanar da ficewa daga Hukumar Lafiya ta Duniya WHO a ranar Juma'a.

    Shugaban kwamitin lafiya a majalisar dattijai ta Amurka Lamar Alexander ya yi gargaɗin cewa wannan na iya kawo cikas ga aikin samar da riga-kafin cutar korona.

    Mista Alexander wanda ɗan jam'iyyar Republican ne, ya ce matakin na Trump zai iya hana haɗin kan kasashe na daƙile yaɗuwar cutar a Amurka.

    Tarayyar Turai ta buƙaci Trump ya sauya tunani. Jamus ta ce matakin shugaban koma baya ne ga kiwon lafiya a duniya.

    Shugaba Trump ya jaddada cewa China ce ta mamaye hukumar Lafiya ta duniya WHO, kuma hukumar ta kasa samar da sauye-sauyen da Amurka ke buƙata.

  12. Nijar za ta fara tatsar bayanan mutane a wayoyin salula

    Mohamadou Issoufou na Nijar

    A Jamhuriyar Nijar, majalisar dokokin ƙasar ta amince da wata dokar da za ta bai wa hukumomi damar sauraren maganganun 'yan kasar ta wayoyi ko kafofin sadarwar zamani.

    A halin yanzu, za a iya amfani da muryoyin mutane da aka naɗa yayin da suke yin waya wurin gudanar da bincike.

    Nijar na ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka da ke fama da hare-haren masu iƙirarin jihadi.

    Ƙudurin dokar ya samu amincewa da ƙuri'a 104 cikin 'yan majalisa 171 na ƙasar. 'Yan majalisa na ɓangaren adawa sun fice daga zauren majalisar lokacin kaɗa ƙuri'ar don nuna rashin amincewarsu da wannan doka.

  13. 'Babu wanda ke ɗauke da cutar korona a Kebbi'

    Hukumomin lafiya a jihar Kebbi sun sanar cewa a halin yanzu babu ko mutum guda da aka sani mai cutar korona a jihar.

    Wannan na zuwa ne bayan sallamar mutum biyu da suka rage a cibiyar killace masu cutar.

    Alƙaluman NCDC na cewa mutum 33 ne suka kamu da korona a Kebbi, tun bayan bullarta a jihar.

    Kwamishinan lafiya, Honorabul Jafar Mohamed Kilin, kuma shugaban kwamitin yaƙi da korona a Kebbi. ya shaida wa BBC cewa an sallami mutum biyu da suka rage bayan gwaji ya dawo kuma ya nuna ba su ɗauke da cutar korona.

    "Hakan ya nuna yanzu babu wanda ke ɗauke da cutar da aka killace," in ji shi.

    Amma ya ce suna jiran dawowar samfurin wasu da suka aika domin tabbatar da ko suna ɗauke da cutar.

    Video content

    Video caption: Hirar BBC da kwamishinan lafiya na Kebbi
  14. Amurka na zargin Rasha da rura wutar rikicin Libiya

    .

    Rundunar sojojin Amurka na zargin ƙasar Rasha da rura wutar rikicin da ke faruwa a Libiya.

    A wata sanarwa da rundunar sojin da ke reshen Afirka ta fitar ta bayyana cewa lamarin ya zama babban abin damuwa ga nahiyar Afirka.

    A farkon makon nan ne dai Amurka ta bayyana cewa Rasha ta kai jiragen yaƙi zuwa ga Janar Khalifa Haftar a Libiya, wanda ke rikici da gwamnatin ƙasar.

    Sai dai Rasha ta musanta kai jiragen 'yaƙin ga Libya.

  15. Labarai da dumi-dumiMutum 365,437 cutar korona ta kashe a halin yanzu

    A yau Asabar da mislain karfe 1:00 na rana agogon Najeriya, taswirar da ke nuna alƙaluma kan cutar korona ta Jami'ar Johns Hopkins ta bayyana cewa mutum 365,437 cutar korona ta kashe a faɗin duniya.

    Amurka ce kan gaba inda mutum 102,836 suka mutu, sai kuma Birtaniya ce ta biyu inda mutum 38,243 suka mutu.

    Alƙaluman sun bayyana cewa ƙasar Italiya ce ta uku inda mutum 33,229 suka mutu a ƙasar.

  16. Sanarwa

    Ku kasance da mu anjima, inda za mu kawo muku tattaunawa da shahararren mawakin Hausa Hamisu Breaker.

    .
  17. Buhari ya yi ta'aziyya bisa rasuwar Maikanti Baru

    ..

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi ta'aziyya ga iyalai da 'yan uwa da abokan arziƙin Tsohon Daraktan Kamfanin NNPC Marigayi Maikanti Kachalla Baru.

    A wata sanarwa da sakataren watsa labarai na shugaban ƙasar Femi Adesina ya fitar ya bayyana cewa shugaba Buhari ya yaba da irin gudunmawar da marigayin ya bayar wajen ganin cewa an samu ci gaba a ɓangaren man fetur.

    A safiyar yau Asabar ne dai aka sanar da rasuwar marigayin inda aka bayyana cewa ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.

    An haifi marigayin a garin Misau na jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya a 1959 kuma ya halarci Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria 1982 inda ya yi karatu a fannin Injiniya.

    Ya soma aiki a babban kamfanin man na Najeriya a 1991 inda ya yi ta samu karin girma har ya kai ga zama shugaban na NNPC.

    Maikanti Kacalla Baru ya rike mukamin shugaban NNPC daga 2016 zuwa 2019 bayan ya yi aiki a sassa daban-daban na bangaren mai a Najeriya.

  18. Gobe Lahadi za a buɗe Masallacin Madinah

    .

    Gwamnatin Saudiyya ta bayar da umarnin buɗe masallacin Manzon (SAW) da ke a garin Madinah a gobe Lahadi.

    Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito cewa tuni hukumar da ke kula da manyan masallatan ƙasar biyu ta gama shirye-shiryen buɗe masallacin tare da sharuɗɗa masu tsauri.

    An bayyana cewa kashi 40 cikin 100 na yawan mutanen da masallacin zai iya ɗauka kaɗai za a iya bari su yi sallah a lokaci guda.