Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Awwal Ahmad Janyau da Umar Mikail

time_stated_uk

  1. An harbe wani damisa bayan ya tsere daga kejinsa a Indonesia

    Damisa

    Hukumomi a Indonesia sun harbe wani damisa na jinsin Sumatran bayan ya tsere daga kejinsa a wani gidan ajiyar namun daji.

    Mahukunta sun ce sun ɗauki matakin ne saboda sun kasa yi masa allurar sumarwa kuma yana shirin yin ɓarna.

    Wani damisan da ke cikin kejin, shi ma ya tsallake kuma ya shiga wani daji da ke kusa.

    Ma'aikatan gidan zoo ɗin na Senka da ke Kalimantan sun ce an ga gawar wani ma'aikaci wadda aka yi imanin cewa damisan da ya gudu ne ya halaka shi.

    Ana tunanin dabbobin sun samu damar tserewa ne saboda ruwan saman da aka tafka a yankin, wanda ya lalata wasu sassan gidan namun dajin.

  2. Egypt ta saki ɗan jaridar Aljazeera Mahmud Hussein

    Hukumomi a Egypt sun saki dan jaridar Aljazeera da ya shafe shekara hudu a gidan yari.

    Tun a watan Disamban 2016 ne ake tsare da Mahmoud Hussein ba tare da an gurfanar da shi a gaban kotu ba.

    Hukumomin sun zarge shi da yaɗa labaran karya da kuma shiga wata haramtacciyar kungiya.

    Shugaban riko na Aljazeera Mostefa Souag ya yi maraba da sakin Mr hussein, inda ya ce ba ya jin dadin wani dan jarida ya shiga uɓuba a kan gaskiyarsa ba, kamar yadda Mahmud Hussein ya samu kansa a hannun Egypt.

    Ba wannan ne karon farko ba da gwamnatin Egypt ta kama ma'ikatan Aljazeera, a baya wasu ma'aikata uku sun shafe shekaru a gidan kaso.

  3. Varane ya ceci Real Madrid a hannun Huesca

    Raphael Varane

    Raphael Varane ya ci wa Real Madrid ƙwallo biyu, inda ta doke Huesca da ke ƙasan teburin La Liga a wasan mako na 22.

    Nasarar ta taimaka wurin sauƙaƙa matsin lambar da ke kan mai horarwa Zinedine Zidane bayan Levente ta casa tawagar tasa har gida a makon da ya gabata.

    Zidane ya buƙaci 'yan jarida da su "tsahirta masa" kafin wasan na yammacin Asabar, yana mai cewa ƙungiyarsa na kan hanyar lashe La Liga.

    Javi Galan ne ya fara zira ƙwallo a ragar Madrid minti takwas da dawowa daga hutun rabin lokaci, kafin ɗan bayan Faransa Varane ya farke a minti na 55.

    Ɗan wasan mai shekara 27 ya ƙara ta biyun ne bayan an bugo bugun tazara, inda ya buga ta zaren da yake kusa da shi.

    Real, wadda ke matsayi na biyu a teburi, tana bin bayan Atletico Madrid ne da tazarar maki bakwai, sai dai Atletico na da kwantan wasa biyu.

    Wasa ɗaya kacal Real ta ci daga cikin biyar na baya-bayan nan da ta buga, abin da ya sa 'yan jarida suka yi wa ɗan ƙasar Faransan ca.

  4. Baki ɗayan 'yan Afirka na murna da zaɓar Okonjo-Iweala - Buhari

    Buhari da Ngozi

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gode wa gwamnatin Amurka bisa goyon bayan da ta nuna wa Ngozi Okonjo Iweala don jagorancin ƙungiyar kasuwanci ta duniya WTO.

    A ranar Juma'a ne Ngozi Okonjo-Iweala ta samu goyon bayan Amurka bayan abokiyar takararta Yoo Mhung-Hee ta Koriya ta Kudu ta janye.

    "Mun yi murna da matakin da sabuwar gwamnatin Amurka ta ɗauka na cire shingen da aka saka kafin a samu mace kuma 'yar Afirka ta farko da za ta jagoranci ƙungiyar WTO," in ji Buhari cikin wani saƙon Twitter.

    "'Yan Najeriya da 'yan Afirka baki ɗaya na murna da wannan sabon mataki na Amurka, wanda ke nuna sabon babi mai amfani game da alaƙar Afirka da Amurka ƙarƙashin jagorancin Joe Biden."

    Buhari ya ƙara da cewa "mun shaida cewa Amurka ta nuna goyon baya ga 'yar ƙasarmu Okonjo-Iweala wadda ake matuƙar girmamawa".

    View more on twitter
  5. Da gaske WHO ta fasa bai wa Najeriya rigakafin korona?

    Rigakafin korona

    Gwamnatin Najeriya ta ce ba gaskiya ba ne cewa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta cire ƙasar da wasu ƙasashe daga shirin samun rigakafin cutar korona na COVAX.

    Wannan ya biyo bayan wasu rahotanni ne da wasu jaridun ƙasar suka wallafa cewa Najeriya da wasu ƙasashe guda takwas sun gaza shiga jerin waɗanda za a bai wa allurar rigakafin.

    "Hukumar Lafiya ta Duniya ba ta cire kowace ƙasa ba daga Afirka daga cikin shirin samun rigakafin korona na COVAX," in ji W. Kazadi Mulombo, wani wakilin hukumar ta WHO.

    "Hasali ma, tana taimaka wa dukkanin ƙasashe ne domin su samu rigakafin cikin gaggawa," in ji shi.

    Ita ma hukumar lafiya a matakin farko ta Najeriya NPHCDA ta musanta rahoton tana cewa "na ƙanzon kurege ne:"

    Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa tana jiran karɓar rigakafin guda 100,000 ta hanyar shirin na COVAX, wanda aka ƙirƙira domin a tabbatar cewa ƙananan ƙasashe sun mallaki allurar.

    View more on twitter
  6. Ba za mu lamunci take haƙƙin da China ke yi ba - Amurka

    Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya fada wa takwaransa na China cewa kasarsa ba za ta lamunci keta hakkin bil'adama a Xianjiang da Tibet da Hong Kong ba.

    Mr Blinken ya kuma bukaci China da ta yi Allah-wadai da juyin mulkin da aka yi a Myanmar.

    Ya ce matsawar ba ta yi hakan ba za su zarge ta da haddasa rikici.

    Sai dai har yanzu gwamnati a China ta ki ta yi tir da juyin mulkin da sojojin Myanmar din suka yi.

  7. Gwamna Rabiu Kwankwaso ne ya ba ni filin da aka rushe - Sheikh Abduljabbar

    Sheik Abduljabbar

    Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya faɗa wa BBC cewa ce gwamnatin Kano ce ƙarƙashin jagorancin Rabiu Musa Kwankwaso ta mallaka masa filin, wanda gwamnati ta rushe.

    Gwamnatin Kano ta rushe ginin makarantar ta Abduljabbar mai suna Jauful Fara a unguwar Filin Mushe a ƙwaryar birnin na Kano.

    An ɗauki lokaci ana rikici kan filin tsakanin malamin da mutane, sai dai shehin malamin ya yi iƙirarin cewa gwamnati ce ta mallaka masa shi.

    "Tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ne ya kira ni da kansa ya shaida mani cewa an ba ni filin amma sai dai har gwamnatin ta sauka ba a ba ni takardar mallakarsa ba," in ji Sheikh Abduljabbar.

    Gwamnatin Kano ta yanzu ta ƙwace filin ne sakamakon koke da ta ce ta samu daga mutanen yankin, kan cewa filin mallakinsu ne.

    Kimanin wata biyu kenan gwamnati ta fitar da filaye a wajen ciki har da na Malam Abduljabbar da ya yi iƙirarin gwamnatin da ta shuɗe ce ta ba shi.

  8. An sake cinye Arsenal a Premier League

    Arsenal

    Minti biyu kacal da take wasa Aston Villa ta cilla wa Arsenal ƙwallo a zare a wasan mako na 23 na Premier League.

    Tsohon mai tsaron ragar Arsenal ɗin ne, Emiliano Martinez, ya fara bugo ƙwallon wadda Bertrand Traore ya tsinta bayan Soares ya yi kuskure, inda shi kuma Ollie Watkins ya cilla ta zaren Mat Ryan.

    Wannan ne karon farko da Villa ta yi nasara kan Arsenal a wasa biyu a jere cikin shekara 28.

    Ranar 8 ga watan Nuwamban 2020 Villa ta casa Arsenal da 0-3 har gida a gasar Premier.

    Tsohon golan na Arsenal ya hana Granit Xhaka farke ƙwallon ɗaya tilo a lokacin da ya ɗaɗa masa wani bugun tazara.

    Da wannan sakamako, Villa ta zama ta takwas a teburi, yayin da Arsenal ke mataki na 10.

  9. An zaɓi Musulmi shugaban mujallar shari’a ta Jami’ar Harvard

    Hassaan Shahawy
    Image caption: Hassaan Shahawy ne shugaba Musulmi na farko a tarihin mujallar na shekara 134

    Mujallar shari’a ta The Harvard Law ta sanar da Ba’amurke ɗan asalin Masar kuma Musulmi a matsayin shugabanta.

    An bayyana cewa shi ne shugaba musulmi na farko a tarihin mujallar na shekara 134.

    Hassaan Shahawy ɗalibin shari’a a jami’ar Harvard ya ce yana fatan zaɓensa ya wakilci “ci gaban ilimin shari’a da kuma inganta muhimmancin bambance-bambance da kuma girmama ga sauran ɓangararori na shari’a.

    Manyan fitattun mutanen da suka riƙe mukamin sun haɗa da tsohon shugaban Amurka Barack Obama, wanda shi ne shugaban mujallar baƙar fata na farko da aka zaɓa a 1990.

    Shahawy ya kammala digirinsa na farko a ɓangaren tarihi a Jami’ar Harvard a 2016, daga nan ya tafi jami’ar inda ya yi digiri na uku kan shari’ar musulunci.

  10. Idriss Deby zai sake yin tazarce wa’adi na shida a Chadi

    Tun 1990 Idriss Deby ke shugabanci a Chadi

    Jam’iyya mai mulki a Chadi ta amince shugaba Idriss Deby a matsayin ɗan takararta inda zai nemi wa’adi na shida a zaɓen shugaban ƙasar da za a yi a bana.

    Deby mai shekara 68 ya shafe shekara 30 kan mulki a Chadi, kuma yanzu ana sa ran zai sake neman ƙarin shekarun a zaɓen watan Afrilu.

    Matakin ya haifar da zanga-zanga a ƙasar, inda wakilin BBC a Ndjaména ya ce matasa da mata sun fito saman titi suna zanga-zanga domin adawa da takarar Deby da ke saman mulki tun 1990.

    Jami’an tsaro kuma na ci gaba da farautar masu zanga-zanga kuma zuwa yanzu ba za a iya tantance yawan waɗanda aka kama ba ko suka ji rauni.

    Duk da daɗewa kan mulki da kuma salon mulkinsa, amma Deby na samun goyon bayan ƙasashen duniya musamman saboda tasirinsa ga yaƙi da ta’addanci a yankin Sahel.

  11. Gwamnati ta kama mabarata 500 a Kano

    Masu bara kan titi

    Gwamnatin Kano ta kama masu yin bara kan titi 500 da suka ƙunshi har da mata da yara.

    Kwamishinan mata da walwalar yara Malama Zara’u Muhammad ta tabbatar wa BBC da kamen ƙarƙashin dokar haramta bara a faɗin jihar.

    Waɗanda aka kama kuma sun haɗa da Maza da yawa almajirai da ke bara kan titi.

    Gwamnatin Kano ta ce za ta shafe tsawon watanni uku tana kamen domin tsabtace birnin daga gudanar da ayyukan ashsha.

  12. Tarayyar Afrika na babban taronta a intanet

    Tarayyar Afrika ta gudanar da taronta na 34 ta intanet saboda annobar korona.

    Shafin Twitter na gwamnatin Najeriya ya wallafa hotunan shugaba Buhari a fadarsa a taron na AU tare da shugabannin Afrika.

    A taron za a ƙaddamar da sabon shugaban ƙungiyar shugaban Congo Felix Antoine Tshisekedi

    A taron na kwanaki biyu, shugabannin Afrika kuma za su zaɓi shugaban da zai jagoranci ƙungiyar a shekarar 2022.

    View more on twitter
  13. Tattaunawa da Gwamna Maimala Buni kan zawarcin Jonathan

    Video content

    Video caption: Hirar Ibrahim Isa da Gwamna Maimala Buni
  14. Yadda manoma ke zanga-zanga a Indiya

    Yadda manoma ke zanga-zanga a Indiya

    Dubun-dubatar manoman Indiya sun toshe manyan hanyoyi a faɗin ƙasar yayin da suke ci gaba da zanga-zangar adawa da sabbin dokokin ayyukan noma.

    Toshe hanyoyin na tsawon sa’o’I uku ya katse zirga-zirga a yankuna da dama na Indiya amma ana barin zirga-zirgar motocin daukar marasa lafiya da muhimman ayyuka.

    ‘Yan sanda sun kama masu zanga-zanga da dama.

    Yadda manoma ke zanga-zanga a Indiya

    Mahukunta sun girke jami’an tsaro sama da 50,000 a cikin babban birnin kasar, Delhi da kewaye, don hana duk wani tashin hankali.

    Amma shugabannin manoman sun ce ba za a toshe hanyoyin cikin gari ba.

    Dubban manoman sun yi sansani a wajen Delhi tsawon watanni biyu da rabi

    Yadda manoma ke zanga-zanga a Indiya
  15. Ya kamata Najeriya ta sake nazari kan haramta kuɗin intanet - Atiku

    Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya buƙaci gawamnati ta sake nazari kan matakin Babban Bankin ƙasar (CBN) na rufe asusun 'yan kasuwa da kamfanoni masu amfani da kuɗin intanet na cryptocurrency yana mai cewa yanzu lokaci ne da ya kamata a faɗaɗa tattalin arzikin Najeriya.

    Ya kuma ce rashin ayyukan yi ga matasa ne babban ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta.

    "A zahiri, ya ma wuce ƙalubale, buƙata ce ta gaggawa. Yana shafar tattalin arzikinmu da ƙara taɓarɓarewar matsalar tsaro a ƙasa," in ji Atiku.

    View more on twitter
  16. Issoufou ya buɗe sabuwar kwalejin horar da sojoji a Nijar

    Shugaba Issoufou na Nijar

    Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou ya ƙaddamar da sabuwar kwalejin horar da manyan sojoji a Yamai a yayin da ƙasar ke son ninka yawan sojojinta zuwa 2025.

    Kafar talabijin ɗin ƙasar ta Tele Sahel ta ambato shugaban na cewa an ɗauki sojoji da ba su horon da ya dace.

    Ta kuma ambato ministan tsaron Nijar Issoufou Katambe yana cewa kwalejin za ta horar da manyan sojoji ne da za su riƙe muƙamai da ke buƙatar ƙwarewa ta zamani.

    Kwalejin na cikin wani shiri na shekara biyar na ninka yawan sojojin Nijar daga 25,000 zuwa 50,000 a 2025.

  17. Biden ya soke matakin Trump na ayyana Houthi matsayin ƴan ta’adda

    Houthi a Yemen

    Sabuwar gwamnatin Amurka ta soke ɗaya daga cikin matakin ƙarshe da tsohon shugaban kasar, Donald Trump ya ɗauka, wato ayyana ƴan tawayen Houthi a Yemen a matsayin ƴan ta'adda.

    Wani jami’in ma’aikatar harakokin wajen Amurka ya ce matakin da ya ƙara kazancewar mawuyacin halin rikicin jin-ƙai da duniya ke fuskanta.

    A ranar Alhamis Shugaba Biden ya sanar da cewa ya dakatar da tallafin soja ga ƙawancen da Saudiyya ke jagoranta da ke fada da ƴan Houthi.

    Sakataren harkokin wajensa Antony Blinken ya yi tattaunawar farko ta wayar tarho da takwaransa Ministan harkokin wajen Saudiyya.

    A ranar Juma'a, Fadar White House ta ce tana fatan Masarautar Saudiyya za ta inganta matsayinta kan ƴancin ɗan adam.

  18. Ra'ayi Riga: Cutar kansa da hanyoyin magance ta

    Filin Ra'ayi Riga ya tattauna da masana game da cutar kansa, da irin matsalolin da ake fuskanta wajen maganinta da kuma hanyoyin magance ta.

    Shirin ya kuma ji irin matakan da gwamnatoci ke dauka na yaki da cutar.

    Video content

    Video caption: Filin Ra'ayi Riga
  19. Korona ta sake kashe mutum 9 a Najeriya

    Alƙalumman da hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta fitar a ranar Juma'a sun nuna cewa cutar korona ta ƙara kashe mutum tara cikin sa'a 24.

    Yanzu jimillar mutum 1,641 cutar ta kashe a Najeriya.

    Alƙalumman sun kuma nuna cewa ƙarin mutum 1,624 suka kamu da korona a ƙasar, inda yanzu yawan waɗanda cutar ta shafa suka kai 137, 654, daga cikinsu 111,639 sun warke.

    View more on twitter
  20. Okonjo-Iweala ta gode wa Buhari da ƴan Najeriya

    Ngozi Okonjo-Iweala ta nuna matukar godiyarta ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma ‘yan Najeriya kan goyon baya da suka nuna mata a ƙoƙarin da take yi na zama shugabar ƙungiyar kasuwanci ta duniya (WTO).

    A ranar Juma'a ne Ngozi Okonjo-Iweala ta samu goyon bayan Amurka bayan abokiyar takararta Yoo Mhung-Hee ta Koriya ta Kudu ta janye.

    A shafinta na Twitter Okonjo-Iweala ta gode wa Amurka da kuma Yoo Mhung-Hee bayan ta yi godiya ga shugaban ƙasarta Muhammadu Buhari da kuma ƴan Najeriya.

    Ngozi Okonjo-Iweala yanzu za ta zama mace ta farko kuma ƴar Afrika da za ta jagoranci ƙungiyar.

    View more on twitter