Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Buhari Muhammad Fagge

time_stated_uk

  1. Rundunar Ƴan sandan Najeriya ta zargi ƴan Biafra da kashe jami’anta biyu

    Rundunar ‘yan sandan jihar Kuros Ribas ta ce ‘yan kungiyar IPOB masu fafutikar kafa ƙasar Biafra da ke neman ballewa daga Najeriya sun kashe 'yan sanda biyu a bakin shingayen binciken ababen hawa a karamar hukumar Obubra da ke tsakiyar jihar ta Kuros Riba.

    Gwamnatin jihar ta gano cewa akwai hannun ‘yan kungiyar Biafra da kai wa jami’an tsaron farmaki.

    Ku saurari rahoton Wakilin BBC na Legas Umar Shehu Elleman

    Video content

    Video caption: Rundunar Ƴan sandan Najeriya ta zargi ƴan Biafra da kashe jami’anta biyu
  2. An yi hatsaniya a Jangebe bayan miƙa ƴan matan da aka sako ga iyayensu

    Yan matan Jangebe
    Image caption: Lokacin da iyaye ke tarbar ƴaƴansu da aka sako daga hannun ƴan bindiga

    Rahotanni daga Zamfara a arewacin Najeriya sun ce an samu hatsaniya a garin Jangebe lokacin da gwamnatin jihar ke mika ƴan matan da aka sako ga iyayensu.

    Wasu mazauna garin sun shaida wa BBC cewa hatsaniyar ta faru ne bayan da wasu mutanen garin na Jangebe suka kama jifar sojoji bayan jami’an gwamnati da suka yi rakiyar ɗaliban sun miƙa su ga iyayensu.

    “Sojoji sun yi harbi bayan da mutane suka kama jifansu,” in ji wani mazauni garin Jangebe.

    Sai dai kwamishinan tsaro na jihar Abubakar Dauran ya ce lafiya lau suka miƙa ɗaliban ga iyayensu, ba ya da masaniya da abin da ya biyo baya.

    Garin Jangebe
    Garin Jangebe
  3. ICC ta bude bincike kan zargin aikata laifukan yaki a yankunan Palasdinawa

    Kotun ICC
    Image caption: Kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta kasa da kasa ICC

    Babbar mai gabatar da kara ta kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta kasa da kasa ICC ta bude bincike kan aikata laifukan yaki a yankunan Palasdinawa.

    Fatou Bensouda ta ce binciken zai duba abubuwan da suka faru a yankunan da Isra'ila ta mamaye a Gabar Yamma ti Kogin Jordan, da Gabashin birnin Kudus, da kuma Zirin Gaza tun a ranar 13 ga watan Yunin shekarar 2024.

    A watan da ya gabata ne, kotun wacce ke da mazauni a birnin ta yanke hukuncin cewa za ta dauki matakan bin diddigin aikata manyan laifuka kan yankunan.

    Isra'ila ta yi watsi da matakin na Ms Bensouda, yayin da jami'an Palasdinawa ke yabawa da shi.

    Kotun ta ICC na da karfin ikon gurfanar da wadanda ake zargi da aikata kisan kare-dangi, da laifukan yaki da kuma laifukan cin zarafin bil adama a yankunan a bisa abinda yarjejeniyar birnin Rome ta shekarar 2015 ta tanada.

  4. Faransa ta amince ita ta kashe Ali Boumendjel na Algeria

    AFP

    Faransa ta amsa cewa ita ta kashe fitaccen dan kishin kasar nan na Algeria bayan azabtar da shi da sojojinta suka yi shekara 60 baya.

    An kama Ali Boumendjel yayin yakin neman 'yancin algeria a 1957, aka kuma sanar da mutuwarsa jim kadan bayan bacewarsa in da aka ce kashe kansa ya yi.

    Amma a wata tattaunawa da aka yi da jikokin Ali Boumendjel a ranar Talata Shugaba Emmanuel Macros na Faransa ya jaddada batun mutuwarsa.

    "Bai kashe kansa ba. An azabtar da shi ne sannan ya mutu daga baya," in ji Macron.

    Algeria ta samu 'yan cin kai daga Faransa a 1962 bayan kwashe shekara bakwai ana yaki.

  5. Labarai da dumi-dumiKungiyar masu kai kayayyaki kuduncin Najeriya ta janye yajin aiki

    Shugaban kasuwar alaba a Legas
    Image caption: Shugaban kasuwar Alaba Rago a Legas

    Haɗaɗɗiyar Kungiyar masu kayan gwari da cimaka dabbobi ta ƙasa ta janye aikin aikin da take yi na haramta kai kaya a kudancin Najeriya.

    Ƙungiyar ta janye yajin aikin ne bayan tattaunawa da tawagar gwamnatin tarayya karkahin jagorancin gwamnan jihar Kogi.

    Ƙungiyar ta ce ta mika bukatu guda biyar ga gwamnan domin gabatar da su ga shugaban ƙasa da take son a biya mata.

    Ta amince ta janye yajin aikin bayan gwamnati ta yi alkawalin diba bukatun, amma kungiyar ta yi barazanar komawa yajin aikin idan har gwamnati ba biya bukatun ba.

  6. Korona ta kashe mabiyan cocin Katolika 85 a Tanzaniya

    BBC

    Cocin Roman Katolika a Tanzania ta ce mata 60 da suka sadaukar da rayuwarsu wajen bauta da malaman coci 25 sun mutu a cikin watanni biyu da suka gabata bayan nuna alamun kamuwa da cutar korona.

    Sai dai cocin ta ce bai gudanar da gwaji ba domin tabbatar ko korona ce ta yi ajalinsu saboda akwai karanci samun damar gwajin a Tanzania.

    Cocin ta gargadi yan kasar kan daukan matakan kariya da muhimmanci.

    Shugaban Tanzania John Magafuli ya raina girman tasirin annobar, yana mai cewa addua ta isa kariya.

  7. Kun iya maganar kurame? Wata likita ta ce yana da kyau ku koya

    An ware ranar 3 ga watan Maris din kowace shekara a matsayin Ranar Kurame Ta Duniya, ranar da aka ware don fadakar da mutane yadda za su kaucewa abin da zai iya haifar da kurumta ko matasalar ji.

    A cikin wannan bidiyon, wata likita Dakta Ameera Aliyu Aminu ta ja hankalin mutane kan amfanin maganar kurame.

    Ku latsa hoton da ke kasa don kallon bidiyon:

    Video content

    Video caption: Kun iya maganar kurame? Ga abin da wata likita ke cewa
  8. 'Yan kasuwar da ke kai kaya kudancin Najeriya sun janye yajin aikin da suke

    Getty Images

    Shugabannin kungiyar masu kai shanu da kayan abinci a Najeriya karkashin hadaddiyar kungiyarsu ta AUFCDN sun amince su janye yajin aikin kai kaya kudancin kasar.

    Sun cinma wannan matsayar ne a wata tattaunawa da suke yi da gwamnonin a birnin tarayyar Abuja a ranar Laraba.

    Jaridar Daily Trust ta ce ta tattauna da shugaban matasan da suke kai shanu kudancin Abdullahi Tomda ke Legas, ya shaida mata cewa Gwamnan Kogi Yahaya Bello na cikin wadanda suka halarci taron, wanda ya nemi su dakatar da wannan yajin aikin.

  9. Masu hakar ma’adanai sun yi martani kan matakin gwamnati na dakatar da shawagin jirage a Zamfara

    Video content

    Video caption: Hirar Jabir Sambo da mai kamfanin hakar gwal Alhaji Nazir Muhammad

    Masu hakar ma’adanai a jihar Zamfara sun fara martani kan matakin gwamnatin Najeriya na dakatar da shawagin jiragen sama a jihar.

    A jiya Talata ne hukumomi suka sanar da matakin, a wani yunkuri na dakile safarar makamai da ta ke zargin ana amfani da jiragen ana yi.

    Kuma dama kusan shekaru biyu kenan da hukumomin suka dakatar da hakar ma’adanai a jihar bisa dalilan tsaro.

    Abokin aikinmu, Jabir Mustapha Sambo ya tattauna da shugaban wani kamfanin gwal a zamfara Alhaji Nazir Muhammad, don jin ra’ayinsa game da wannan sabon matakin.

    Ku latsa hoton da ke kasa don sauraron hirar:

  10. An kashe mutum 11 a zanga-zanga a Myanmar

    Myanmar

    An kashe mutum a kalla 11 a Myanmar a wasu jerin kazamin rikici tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zangar neman a dawo musu da zababbiyar gwamnatin da aka hambarar.

    Sannan har yanzu ba a samu rahotan mutane da aka kashe a yankunan Mandalay da Monyawa da Myingyan ba, inda shaidu suka ce sojoji sun bude wuta babu gargadi.

    An kuma bayar da rahoton mutuwar mutum guda a birnin mafi girma na kasar, Yangon, ko da yake an tarwatsa masu zanga-zanga ta hanyar amfani da hayaki mai sa kwalla.

    Sojoji na kuma cafke jami'an lafiya da ke kai wa wadanda aka jikkata agaji.

    Rikicin na zuwa ne kwana guda bayan kungiyar kasashen nahiyar Asiya sun ja hankali kowane bangare kan kiyayewa.

  11. An nada sabon Sarki 'Mai Tangale' a Gombe

    Mai Tangale

    Gwamnatin jihar gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya ta naɗa sabon sarki Mai Tangale na ƙaramar hukumar Ɓilliri.

    Malam Danladi Sanusi Maiyamba shi ne ya zama sabon Mai Tangalen kamar yadda wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na gwamnatin jihar Isma'ila Uba Misilli ya fitar a ranar Laraba.

    Sanarwar ta ce Gwamna Inuwa Yahaya ya yanke wannan hukunci ne bisa ikon da dokar masarautu ta Gombe ta 2020 ta ba shi.

    Ta kuma ce an naɗa Malam Sanusi ne saboda kyawawan halayensa da kuma cancantarsa, kamar yadda kwamishinan ƙananan hukumomi da masarutu Ibrahim Dasuki Jalo ya fada a yayin da yake miƙawa sabon Mai Tangalen takardar ba shi sarautar.

    A makon da ya gaba ne aka tafka rikicin addini a ƙaramar hukumar Ɓilliri kan batun wanda za a naɗa a matsayin sabon Mai Tangale, bayan mutuwar tsohon sarkin Dr Abdu Buba Maisharu II.

  12. Za a bude cibiyoyin sabunta layikan waya (Swapping) a duka kananan hukumomin Najeriya

    Other

    Gwamnatin Najeriya ta amince da samar da cibiyoyin domin sauya layikan wayar da suka bata ko aka sace (Swap) a kananan hukumomin kasar 774.

    Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa tsakanin NCC da NIMC da aka fitar a ranar Laraba.

    An cimma wannan matsaya ne a zama na hudu na kwamitin ministoci kan rijistar NIN-SIM.

    Kamar yadda sanarwar ta bayyana rijistar NIN da akan iya yi a kan waya an kara tsawaita ta daga shekara daya zuwa shekara biyar.

  13. An harba makamin roka 10 kan wani sansanin soji a Iraƙi

    GETTY IMAGES

    A kalla makamin roka 10 ne ya sauka a sansanin sojojin Iraƙi da take saukar sojin Amurka da ke da kawancen dakarun Iraƙi.

    Wata majiyar dakarun tsaro ta ce an kashe fararen hula da ke aikin lokacin harin da aka kai wa sansanin Ain al-Assad.

    It's the fourth such attack on Western installations in Iraq in less than three weeks.They have been blamed on factions backed by Iran.

    Wannan ne karo na hudu da aka kai irin wadannan hari kan sansanin sojin yamma da ke Iraq cikin kasa da mako uku. Ana zargin wasu da ke samun goyon bayan Iran ne ke kai harin.

    Ko a makon jiya sai da Amurka ta kai wani harin sama kan dakarun da ke goyon bayan Iran a Syria.

    Fafaroma Francis ya ce ziyararsa da ya shirya kai wa Iraƙi a ranar Juma'a tana nan.

  14. Mace mai juna biyu ta mutu a motar da ta taka nakiya a Burkina Faso

    Tashin hankali na masu ikirarin jihadi a arewa da gabashin Burkina Faso ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutum 1000
    Image caption: Tashin hankali na masu ikirarin jihadi a arewa da gabashin Burkina Faso ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutum 1000

    A ƙalla mutum biyar ne suka mutu, ciki har da wata mace mai juna biyu, a Burkina Faso a lokacin da wata motar ɗaukar marasa lafiya ta bi ta kan wani abun fashewa.

    Motar na ɗauke da matar ne da mijinta da wata yarinya da wasu mata biyu.

    Hukumomi sun ce lamarin ya faru ne a Gaskinde, kusa da iyakar ƙasar da Mali - wani yanki da ake yawan kai hare-haren ƴan bindiga da ke da alaƙa da ƙungiyoyin al-Qaeda da IS.

    Tashin hankali na masu ikirarin jihadi a arewa da gabashin Burkina Faso ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutum 1000 kuma ya tursasa wa mutane miliyan daya barin muhallansu a shekarun baya-bayan nan.

  15. Bankin Duniya zai gina makarantu 159 ya kuma gyara 69 a Kaduna

    Getty Images

    Shirin Bankin Duniya na samar da ilimi ga 'yan mata zai gina makarantun sakandire daga aji daya zuwa uku guda 90, zai kuma gina daga aji hudu zuwa shida guda 69, ya kuma gyara 69 da suka lalace a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.

    Shugaban shirin AGILE a jihar, Habibu Alhassan ne ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya hakan a Kaduna a ranar Laraba.

    Yace shirin na tsawon shekara biyar an kirkiro shi ne domin tabbatar da cewa yara mata daga tsakanin shekara 10 zuwa 20 sun samu karatun sakandire.

    Yaka kara da cewa gina sabbin makarantun da kuma gyara wadanda suka lalacen wani yunkuri ne na samar da wani tsarin da zai kara ba su damar koyo a rayuwarsu.

  16. Mutum 10 sun mutu a hadarin jirgin sama a Sudan ta Kudu

    BBC

    Hukumomi a Sudan ta Kudu sun tabbatar da mutuwar mutum 10 a wani hadarin karamin jirgin sama a yammacin ranar Talata a gabashin jihar Jonglei.

    Hatsarin ya faru ne jim kadan bayan tashin jirgin daga filin jirgin sama na Pieri inda ya nufi Juba babban birnin kasar.

    Tuni aka tashi wata tawaga domin gudanar da bincike kan hadari, kamar yadda Ministan surufi Madut Biar Yel ya bayyana.

    Jirgin na wani kamfani ne na cikin gida, wanda ake kira South Supreme. kuma har yanzu kamfanin bai ce komi ba kan hadarin.

  17. An saki wakilin BBC da aka kama a Ethiopia

    BBC

    An saki wakilin BBC da aka kama a yankin Tigray da ake rikici a cikinsa a Habasha.

    An sako Girmay Gebru ne wanda aka tsare a sansanin sojoji da ke babban birnin kasar Mekelle.

    BBC dai ba ta san dalilin kama wakilin nata ba, kuma har aka sako shi ba a bayyana dalilin tsare shi ba.

    Haka kuma ta samu tabbacin sakin wasu 'yan jarida na cikin gida da aka kama, wadanda suke aiki da jaridun Financial Times da kmanin dillancin labarai na AFP.

  18. Yan bindiga sun sace sama da mutum 50 a Neja

    AFP

    'Yan bindiga sun sace sama da fasinjoji 50 akan titin Tegina zuwa Minna a cikin karamar hukumar Rafi da ke jihar Neja a arewacin Najeriya a jiya Talata.

    Rahotanni sun ce 'yan bindigar sun yi wa wasu motocin fasinja kwantan ɓauna da ke dauke da mutum tara a ko wacce, a kusa da garin Kundu mai tazara kadan zuwa Zungeru.

    Rahotannin sun kara da cewa an shiga da fasinjojin daji, an kuma bar motocin nasu a inda aka sace su.

    Haka kuma 'yan fashin dajin sun kara kwashe wasu 'yan kauyen Gidigori a karamar hukumar Rafi, tare da kona wasu motoci biyar da kwashe wasu abubuwa masu daraja.

    Wani jami'in gwamnatin ya ce har yanzu 'yan bindiga basu ce komai ba game da mutanen.

    A ranar Litinin kuma 'yan bindigar sun kashe mutum daya sun kuma sace mutane da dama a Manta a karamar hukumar Shiroro.

  19. APC ba za ta iya ceto Najeriya daga matsalolin da take ciki ba - Bukola Saraki

    @BUKOLASARAKI
    Image caption: A jiya ne Bukola Saraki ya kai wa tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ziyara

    Tsohon shugaban majalisar dattawan Najariya Bukola Saraki ya ce, bai kamaata a barwa jam'iyyar APC mai mulki matsalar Najeriya ba ita kadai.

    Saraki wanda shi ne ke jan ragamar kwamitin sasantawa na jam'iyyar PDP, ya nuna cewa a kwai bukatar hada hannu da 'yan hamayya domin lalubo mafitar da za a yi maganin matsalolin Najeriya baki daya, musammam a yankunan da ke fama da matsalar tsaro.

    Saraki ya bayyana hakan ne bayan wata tattaunawa da tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo a dakin karatunsa na Abeokuta da ke jihar Ogun.

    Tsohon shugaban Majalisar ya ce, "Idan muna maganar akan garkuwa da mutane, abin da ake bukata shi ne gwamnati da samar da shugabancin da zai kira wo duka masu ruwa da tsaki. mu zo a tattauna muga yadda za a shawo kan wannan matsaloli."

  20. An kashe masu zanga-zanga hudu a Myanmar

    Getty Images

    An kashe mutum hudu cikin masu zanga-zangar nuna kin jinin juyin mulkin sojoji a Myanmar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

    An dai kwashe makonni ana gudanar da zanga-zangar sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar, suna cewa akwai magudi da aka yi a yayin zaben kasar da aka gudanar.

    A gefe daya kuma, jakadan Myanmar a Majalisar Ɗinkin Duniya ya jaddada cewa har yanzu shi ne halastaccen wakilin ƙsar duk da ƙoƙarin sojin da ke mulkar ƙasar na maye gurbinsa.

    Kyaw Moe Tun ya faɗa wa Majalisar Ɗinkin Duniya cewa waɗanda suka yi juyin mulki a watan da ya gabata ba su da ikon soke naɗin da aka yi masa.

    Sojojin Myanmar da ke mulki sun ce sun kore shi saboda cin amanar ƙasarsa.