Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Awwal Ahmad Janyau da Buhari Muhammad Fagge

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Nan muka kawo karshen labarai da rahotannin da muke kawo muku a wannan shafi.

    Buhari Fagge ke cewa mu kwana lafiya.

  2. EU na nuna halin ko in kula kan bukatar Firaministan India Nerandra Modi

    Nerandra Modi

    Shugabannin Tarayyar Turai sun ki cewa uffan game da bukatar firanministan India Nerandra Modi na cire hakkin mallakar rigakafin Korona.

    A wani taron da Mr Modi yayi da su ya ce yin hakan zai baiwa kasashe damar mallakar rigakafin cikin lokaci ba tare da wata matsala ba.

    To amma sanarwar hadin gwiwa da EU ta fitar ta ki cewa eh ko kuma a'a game da bukatar Nerandra Modi, sun dai ce suna jinjinawa kasashen duniya kan fadi tashin da suke yi wurin shawo kan annobar.

    Sai dai a gefe guda Fafaroma Francis da shugaba Biden na Amurka da kuma takwaransa Emmanuel Macron na Faransa duk sun goyi bayan bukatar Mr Modi.

    Fafaroma Francis kenan yake cewa yakamata kasashe su duba halin da al'umma su ke ciki game da wannan annoba, ba su fifita ikon mallakar rigakafi ba akan ceton rayuwa.

  3. A karon farko an zabi mace bakar fata a majalisar dokokin Scotland

    Kaukab Stewart

    A karon farko an zabi mace bakar fata a majalisar dokokin Scotland.

    Wannan shine karo na biyar da Kaukab Stewart ta jam'iyyar Scotish National Party na takara kuma sai a bana ta samu nasara.

    Malamar makarantar mai shekaru 53 ta kada abokiyar takararta Sandra White daga Green Party da yawan kuri'u sama da dubu biyar.

    Shugabar gwamnatin Scotland kuma jagorar jam'iyar SNP Nicola Sturgeon ta ce bata da kalaman da za ta bayyana irin farin cikin da ta ji da nasarar Kaukab Stewart.

  4. Sama da mutum 30 mafi yawa yara sun mutu a wani harin bam a Afghanistan

    Hari

    Hukumomi a Afghanistan sun tabbatar da mutuwar mutun talatin mafi yawansu kananan yara a wani harin bam da aka kai kusa da wata makaranta da ke Kabul.

    Hakama harin ya jikkata karin wasu mutun fiye da talatin.

    Rahotanni sun ce an tada bam din a daidai lokacin da yan makaranta ke tasowa.

    Hotunan da aka rika yadawa a shafukan sada zumunta sun nuna jikunkunan yan makaranta yashe akan titi ga kuma motoci na ci da wuta..

    Mafi yawan mazauna yankin na Sayeedul Shuhada da ke arewacin Kabul mabiya addinin Shi'a ne, da ke fuskantar hare-hare daga Kungiyar IS.

    Wakilin BBC yace harin na zuwa a daidai lokacin da dakarun Amurka da Nato suka fara kwashe komatsansu daga Afghanistan kamar yadda aka yi alkawari tsakaninsu da kungiyar Taliban.

    Asibti
  5. Babban malamin cocinnan Habasha ya soki gwamnatin kasar

    Abune Mathias

    Babban malamin cocinnan na Habasha Abune Mathias ya zargi gwamnati da aikata kisan kiyashi a yankin Tigray da ke arewaci.

    Wannan ne karon farko da jagoran na mabiya addinin kirista ya yi magana tun bayan fara yakin watanni shida da suka wuce.

    Abune Mathias ya ce ya so yayi magana tuntuni amma aka kwabe shi.

    Wakiliyar BBC tace a wani hoton bidiyo na tsawon minti sha huduAmma yace an rika yiwa kisan gilla a yankin Tigray har a cikin coci.

    Sai dai gwamnati ta ce wadanda ta hara shugabannin yankin ne ba fararen hula ba.

  6. 'Yan bingida sun kashe 'yan sanda bakwai a Fatakwal

    Yan sanda

    Yan bindiga sun kashe akalla jami'an 'yan sanda bakwai a Fatakwal da ke kudancin Najeriya.

    An kai hari ofishin 'yan sanda biyu da kuma wajen duba ababan hawa a daren ranar Juma'a.

    Yan sanda sun a jihar Rivers sun ce an kashe biyu daga cikin maharan.

    A wani hari da aka kai wani ofishin 'yan sanda yayi sanadiyyar mutuwar jami'ai uku.

    Wannan na zuwa ne kasa da wata guda da 'yan bindiga suka kashe wasu jami'an hukumar kwastam uku, da sojoji biyar tare da tarwatsa wasu yan sanda a wurare daban na jihar Rivers din.

    Hare-haren sun janyo gwamnan Jihar ya sanya dokar hana fita da daddare da kuma haka kai wa da kawowa daga karfe 10 na yamma zuwa 6 na safe.

    Jami'an gwamnati da wuraren aikinsu na kara zama inda 'yan bindiga ke yawan kai wa hari musamman a kudancin Najeriya.

  7. Bayern Munich ta lashe Bundesliga na 9 a jere

    BBC

    Gwarzuwar gasar Bayern Munich ta kara lashe gasar karo na tara a jere.

    Wannan na zuwa ne bayan rashin nasarar da RB Leipzig da ke biye mata ta yi a hannun Borussia Dortmund da ke neman tikitin zuwa Champions a badi.

    Leipzig, wadda ta fara jan ragamar gasar da maki bakwai akan Munich an doketa 3-2.

    Dan wasan Ingila Jadon Sancho ne ya ci kwalo biyu bayan Marco Reus ya fara jefa daya.

    Da kwallayen Luka Klostermann da Dani Olmo wasan ya zama 2-2 kafin daga bisani kwallon Sancho ta karshe ta bai wa Munich damar cin gasar gabanin wasanta da Borussia Monchengladbach.

  8. Kalli hotunan yadda Norwich City ta yi murnar lashe Championship

    Norwich ta kara dawo wa gasar Premier bayan samun nasarar da suka yi ta lashe gasar Championship.

    A 2019 ma ita ce ta lashe gasar inda ta buga Premier, amma ta koma Championship saboda gaza katabus da ta yi.

    Ga shi a wannan lokacin ma ta kara dawo wa, kalli wasu daga cikin hotunan yadda suka yi murna:

    @NorwichCityFC
    @NorwichCityFC
    @NorwichCityFC
    @NorwichCityFC
    Pukki
  9. An shiga ranar ta 8 ta dokar kulle a Pakistan

    EPA

    A Pakistan, yau ne ake shiga ranar ta 8 da kafa dokar kulle, yayin da kwanaki kadan suka rage a gudanar da bikin karamar salla.

    Mahukunta sun dakatar da harkokin da ba su wajabta ba, kana an dakatar da yin balaguro zuwa wuraren yawon bude ido.

    A halin da ake ciki dai Pakistan na fuskantar zagaye na uku na annobar korona, abin da ya haifar da matsaloli masu tsanani ga yan kasar.

  10. Kotu a Kenya ta janye haramcin kasuwancin naman Jaki

    Jaki

    Wata kotu a Kenya ta sake yanke hukunci kan haramcin da aka sanya na yankawa tare da sayar da naman Jaki a Kenya.

    A watan Fabrairu bara ne ma'aikatar gona ta kasar ta bayyana haramcin domin kare yunkurin karewar jinsin da kuma biyan muradun masu rajin kare namun daji.

    Kasar da ke gabashin Afrika ta halasta kasuwancin naman jaki wanda ya buya a 2012 saboda karuwar bukatarsa daga China.

    Ministan noma na kasar ya ce wannan ba karamin kuskure ba ne, saboda hakan zai iya kawo karshen jakuna a kasar.

    Kenya na da kimanin jakuna miliyan 1.2 a yanzu, wani koma baya da aka samu idan aka kwatanta da shekara 10 baya da suke da jakuna miliyan 1.8, kamar yadda bayanan gwamnati suka bayyana.

  11. Neymar ya tsawaita kwangilarsa da PSG

    Neymar na Brazil
    Image caption: Neymar ya amince ya ci gaba da taka leda a PSG har 2025

    Neymar na Brazil ya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya da Paris St Germain inda ya amince ya ci gaba da taka leda har zuwa 2025, kamar yadda PSG ta sanar.

    A 2017 PSG ta ɗauko Neymar daga Barcelona kan makudan kudi yuro miliyan 222.

    Tun zuwansa PSG, dan wasan mai shekara 29 ya ci kwallo 85 a wasa 112, kuma ya bayar an ci sau 51.

    Neymar kuma ya lashe wa PSG kofuna 9 tare da taimakawa kulub din zuwa wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai a karon farko.

  12. Atiku da Saraki sun yi alhinin rasuwar Aisha Alhassan

    Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya jajantawa iyalan tsohuwar ministar mata Aisha Alhassan da ake kira Mama Taraba da Allah Ya yi wa rasuwa.

    A ranar Juma’a aka sanar da rasuwar ƴar siyasar ƴar asalin jihar Taraba.

    Atiku ya ce rasuwarsa Aisha Alhassan ta matukar girgiza shi yana mai cewa, “na yi ƙoƙarin jin halin da take ciki da yamma bayan na kira lambarta ba a ɗauka ba! Inna lillahi wainna Ilaihi Rajiun!”

    View more on twitter

    Haka ma tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya Sana Bukola Saraki ya jajantawa iyalan Aisha Alhassan da abokai da kuma magoya bayanta.

    Ya ce za a ci gaba da tunawa da iya saboda jajircewarta wajen yi wa jama'a aiki.

    View more on twitter

    Marigayiyar ta wakilci Taraba ta Arewa a matsayin sanata, ta kuma rike mukamin ministar mata a gwamnatin Buhari.

    A ranar Lahadi ake sa ran yin jana’izarta a garin Jalingo jihar Taraba.

  13. Ƴan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a Chadi

    Ƴan sanda a Chadi sun harba hayaki mai sa ƙwalla domin tarwatsa masu zanga-zanga, wadanda suka bijerewa dokar da gwamnatin sojin ƙasar ta sanya ta hana zanga-zanga.

    A ranar Juma’a ne sojojin da suka karɓe mulki bayan mutuwar shugaba Idriss Deby suka haramta zanga-zangar da gamayyar ƴan adawa da ƙungiyoyin fararen hula suka kira.

    Rahotanni sun ce ƴan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar a N'Djamena.

    Masu zanga-zangar sun fito saman tituwa wasunsu suna ƙone tutar Faransa da ta yi wa Chadi mulkin mallaka kuma mai goyon bayan gwamnatin Idriss Deby kuma wadda suke zargin tana goyon bayan sojojin da suka ƙwace mulki bayan mutuwar shugaban.

    A ranar 20 ga Afrilu sojojin Chadi suka sanar da mutuwar Idriss Deby tare da naɗa ɗansa Mahamar Deby a matsayin wanda ya gaje shi.

    Tun lokacin zanga-zanga ta ɓarke, kuma bayanai sun ce sama da mutum 600 aka kama.

    Mahamat Idriss Deby ya yi alƙawalin gudanar da zaɓe cikin watanni 18.

  14. Super League: Real Madrid da Barcelona da Juventus na kan bakansu

    Super League

    Real Madrid, Barcelona da Juventus sun kare matakinsu na kafa sabuwar gasa da suka kira European Super Leaguebisa ga abin da suka kira ‘barazana’daga Uefa.

    Su ne ƙungiyoyin da suka rage ba su janye matakin kafa sabuwar gasar ba daga cikin 12, kuma yanzu suna fuskantar barazanar hukuncin mai tsauri daga hukumar ƙwallon Turai

    Duk da sauran ƙungiyoyi Tara sun janye, da suka ƙunshi har da ƙungiyoyin gasar Premier shida, amma kuma hukumar Uefa ta ci tararsuta maƙudan kuɗi.

    A ranar Juma’a Uefa ta ce ƙungiyoyin uku za su fuskanci hukunci mai tsauri.

    Sanarwar haɗin guiwa da Real da Barca da Juve suka fitar ta ce “Ƙungiyoyin da suka ƙungiyoyin sun sha wahala suka suna ci gaba da shan wahala daga matsin lamba da barazana domin watsi da matakin.

  15. Iran ta buƙaci Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi Allah wadai da matakin Isra’ila Masallacin Kudus

    Iran ta ce ya kamata Majalisar Ɗinkin Duniya ta fito ta yi Allah wadai da abin da Isra’ila ta yi wa Falasdinawa masallacin Kudus.

    Kamfanin dillacin labaran ƙasar IRNA ta ambato kakakin ma’aikatar harakokin waje Saeed Khatibzadeh na yin Allah wadai da hari kan abin da ya kira hari a Masallacin al Aqsa da Falasdinawa masu ibadah da jami’an tsaron Isra’ila suka kai a ranar Juma’a.

    “Jamhuriyyar musuluncin Iran na kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da duk wata hukuma ta ƙasa da ƙasa da su yi abin da ya dace bisa haƙƙin da ya rataya a wuyansu domin ɗaukar mataki kan wannan laifukan yaƙin,” in ji Khatibzadeh.

    Aƙalla Falasdinawa 205 suka ji rauni a arangamar da suka yi da jami’an tsaron Isra’ila a harabar masallacin al Aqsa a yayin da suke sallah da daren Juma’ar ƙarshe a watan Ramadan.

  16. Korona ta kashe sama da mutum 4,000 a Indiya a rana ɗaya

    A karon farko, fiye da mutum 4,000 cutar korona ta kashe a rana ɗaya a Indiya.

    Akwai fargabar cewa ainihin adadin mace-macen ya fi haka yawa da kuma yawan waɗanda suka kamu da cutar inda ake samun sama da mutum dubu ɗari huɗu a rana.

    Masu aiko da rahotanni sun nuna cewa mace-mace na iya karuwa kamar yadda kwayar ta bazu a yankunan karkara wadanda ke da karancin kiwon lafiya.

    A ranar Asabar, babban ministan jihar Tamil Nadu a kudancin ƙasar ya sanar da dokar kulle ta tsawon mako biyu kamar yadda jihohi makwabta, Karnataka da Kerala suka ɗauki matakin.

    India Covid
  17. Yadda Falasdinawa ke arangama da ƴan sandan Isra’ila a Masallacin Kudus

    Kungiyar Hamas ta Falasdinawa ta gargadi ga Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu kan abin ta kira kada ya yi wasa da wuta bayan da Falasdinawa kusan 200 sun ji rauni a arangamar da suka yi da ƴan sandan Isra'ila a Kudus ranar Juma'a.

    Falasdinawa a Kudus

    Shugaban Hamas, Ismail Haniyeh ya ce, Falasdinawa za su ci gaba da ba da kariya ga unguwar Shaikh Jarrah da ke gabashin Kudus da aka mamaye, inda Isra’ilawa ƴan kama wuri zauna ke ikirarin filayensu.

    Ana ci gaba da samun tashin hankali kan yiwuwar korar Falasdinawa daga yankin.

    Falasdinawa da jami'an tsaron Isra'ila a Kudus

    Mafi yawan wadanda suka ji rauni a arangamar sun ji rauni ne a harabar masallacin al-Aqsa lokacin da ƴan sanda suka buɗe wuta da harsasan roba bayan jifarsu da duwatsu da kwalabe.

    Gwamnatin Biden tana matsa wa Isra’ila lamba kada ta aiwatar da matakin.

    Falasdinawa da jami'an tsaron Isra'ila a Kudus
  18. Ƴan Nijar na fama da tsananin zafi da ƙarancin lantarki

    Ƴan Nijar na ci gaba da fama da matsanancin zafi, inda wasu ƴan kasar ke kokawa musamman a wannan lokaci da ake fama da matsalar wuta da ƙarancin ruwa a wasu yankunan ƙasar.

    Masana a ɓangaren yanayi sun fara gargaɗin mahukunta da ma jama'a, kan cewa lamarin zafin na iya ci gaba da ƙaruwa.

    Katiellou Lawan Gaptia, darakta ma’aikatar kulla da yanayi ta kasa a jumhuriyar ta Nijar ya yi wa BBC ƙarin bayani

    Video content

    Video caption: Ƴan Nijar na fama da zafi da ƙarancin lantarki
  19. Maraba

    Muna maku maraba da kasancewa da mu a wannan shafin inda za mu kawo labarai kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance da mu.