Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail da Buhari Muhammad Fagge

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Nan muka kawo karshen labarai da rahotannin namu na yau.

    Buhari Fagge ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Fasinjoji 14 sun kone a wani hadarin mota akan hanyar Legas - Ibadan

    Fasinjoji 14 ne suka kone ciki har da yara uku a wani hadari da ya rutsa da su akan babban tinin Legas zuwa Ibadan.

    Rahotannin sun ce motoci uku ne da suka hada da Toyota samfurin RAV 4 da Camry da wata Mazda ta haya ne suka yi hadarin da misalin karfe 10 na dare Alhamis.

    Wata motar haya ce aka ce ta wuce Toyata RAV 4 dake tsakiyar titin.

    Sai motar ta kasa rikuwa wanda hakan ya janyo ta yi ta juya wa kafin daga bisani ta kama da wuta.

    Kakakin hukumar kula da hadura Babatunde Akinbiyi ya tabbatar da faruwar lamarin da safiyar Juma'a.

  3. Japan ta kara tsawaita dokar ta baci daf da fara gasar Olympics

    Olympics

    Hukumomin Japan sun kara tsawaita dokar ta tabaci da aka sanya domin yaki da cutar korona, kasa da watanni biyu kafin fara gasar wasannin Olympics.

    Tilas aka dauki wannan mataki saboda kasar ta gagara shawo kan cutar korona da ke ci gaba da yaduwa kamar wutar daji.

    Wakilin BBC ya ce a lokacin da firai minista Yoshihide Suga ya sanya dokar ta baci a karo na uku ranar 25 ga watan Afirilu, yawancin kwararru a Japan sun ce sanya dokar kulle ta kasar baki daya na kwanaki 17, ba za su magance matsalar karuwar masu kamuwa da cutar ba.

    A wasu asibitocin gadaje sun yi karanci, da magunguna da sauran kayan aiki. Dokar kullen za ta ci gaba da aiki a biranen Osaka da Tokyo har zuwa karshen watan nan.

    A watan Yuli ake sa ran fara gasar Olympics, kwanaki biyu da suka gabata aka bude shafin korafi, tare da kiran a soke yin wasannin a Japan, kuma tuni sama da mutum 2000 suka sanya hannu akai.

  4. Sojojin da ke marawa 'yan adawa baya a Somaliya na koma wa sansani

    Reuters

    Sojojin kasar Somaliya da ke marawa 'yan adawa baya, sun fara janyewa daga wuraren da sukai tsaguwar kwari a birnin Mogadishu, bayan samun ci gaba a kokarin da ake yi na ceto siyasar kasar daga durkushewa.

    An ga yawancin jami'an tsaron dauke da makamai na tafiya da kafa, wasu a cikin motocin yaki su na komawa sansanin soji da ke Mogadishu.

    Janyewar su dai za ta sassauta tsoron da farar hula ke yi na barkewar tashin hankali tsakanin jami'an tsaron da kansu ya rabu gida biyu, kan gaza yin zabuka a kasar.

    A makon da ya wuce shugaba Mohamed Abdullahi Farmajo, ya soke aniyarsa ta kara tsawaita wa'adin mulkinsa da shekaru biyu, tare da kira ga firai minista Mohammed Hussein Roble ya shirya gudanar da zabe.

    EPA
  5. An ceto wasu 'yan cirani a kan iyakar Katsina ciki har da jaririya 'yar wata 11

    'Yan cirani

    Hukumar kula da shige da fice ta Najeriya ta ce ta ceto wasu mutum 10 da ake zargin an yi fatauncinsu a kan haryar Babban Mutum da ke Jihar Katsina.

    Rahotanni sun bayyana cewa cikin wadanda aka ceto har da wata jaririya 'yar wata 11, sai mata 8 da kuma wani namiji wadanda suka fito daga jihohin Delta da Edo da Enugu da Jihar Ekiti.

    Mutanen na cewa an musu romon baka ne kan cewa wasu kasuwancin za a kai su yi, ba safararsu za a yi ba kamar yadda aka ceto su.

    Da yake tattaunawa da manema labarai kwamandan hedikwatar da ke Katsina kuma kwanturola Abdurrazaq Mu'azu, yace babu ko mutum daya da yake da takardun shaidar yin tafiya.

    An kuma ceto su ne a lokacin da suke yunkurin tsallakawa iyakar kasar Nijar, su kuma shiga Libya daga nan.

  6. Labarai da dumi-dumiTsohuwar Ministar Mata Aisha Alhassan ta rasu

    Mama Taraba

    Tsohuwar Ministar Mata ta Najeriya Hajiya Aisha Alhassan ta rasu.

    Wata majiya ta shaida wa BBC cewa tsohuwar ministar ta rasu ne a wani asbiti da ke birnin al-Kahira na Masar bayan fama da wata gajeriayar rashin lafiya.

    Marigayiyar wadda aka fi sani da 'Mama Taraba' ta rike mukamin Sanata mai wakiltar Taraba ta Arewa.

    Ta yi takarar gwamnan Jihar Taraba a zaben 2015.

    Kuma ta kara yin takarar wannan matsayi a jam'iyyar UDP a zaben 2019.

    An haifi marigayiya Aisha Al-Hassan a ranar 16 ga watan Satumbar 1959 a Jalingo dake jihar Taraba.

  7. A karon farko Saudiyya ta tabbatar za ta tattauana da Iran

    MBS

    A karon farko ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya ta ce tattaunawar da Saudiiya za ta yi da Iran cikin sirri: za ta kawo sauyi mai kyau tsakaninsu."

    Wannan sanarwa da wakilin kasar Raed Karimli, ya fitar wanda shi ne shugaban tsare-tsare na ma'aikatar, ita ce sanarwa irinta ta farko da daga Riyadh kan bangarorin biyun, wadanda suka samu matsala a 2016.

    Saudiyya ta ce tattaunawar na nufin kawo sauki a rikicin da yake damun yankin, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito, sai dai ya ce zai yi wuri wani ya yi hasashen sakamakon tattaunawar ya zuwa yanzu.

    Amma ya ki yin karin bayani kan me tattaunawar za ta mayar da hankali, sai dai majiyoyi da yawa sun bayyanawa kamfanin dillancin labaran cewa tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan rikicin Yemen da yarjejeniyar nukilya ta 2015.

    Fadar Kremli ta Rasha ta ce manufar Saudiyya kan wannan batu a bayyane take, kamar yadda Yarima Salman ya bayyana a watan jiya cewa, yayin da masarautar ke fuskantar bore daga Tehran, amma tana kara matsa lamba kan kyautata alakarta da Iran.

  8. Ba za a yi Sallah a masallatan Idi ba a fadin Ghana

    Ghana

    Hukumomin kasar Ghana sun bayar da sanarwa cewa ba za a yi Sallar Idi ba a fadin kasar baki daya.

    Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da gwamnatin kasar tare da hadin gwiwar shugaban limaman kasar suka fitar sun ce ana tunawa kowa cewa annobar korona har yanzu ba ta bar cikin al'umma ba, don haka dokokin da aka sanya saboda annobar haryanzu suna nan.

    Sanarwar ta shaida wa duka limaman kasar cewa a gabatar da Sallah Idi a masallatan Juma'ar kasar maimakon zuwa masallatan da aka tanada domin gabatar da Sallar Idin.

    Yayin Sallar sharudan da aka sanya a baya dole a bisu yanzu:

    Dole ne kowane masallaci ya sanya takunkumin fuska.

    Wajibi ne a samar da dokiti da ruwan wanke hannu da kuma sinadarin sanitaiza.

    Kuma ko wane masallaci ya je masallaci da daddumarsa ko tabarmarsa.

    Dole a rika ba da tazara da kuma samar da sinadarin duba yanayin zafin jikin duka masallatan.

  9. Sojojin Isra'ila sun kashe Fasalaɗinawa biyu

    Sojojin Isra'ila sun harbe wasu Faladinawa guda biyu tare da jikkata wani mutum bayan sun bude wa wurin binciken ababewn hawa wuta da jami'an tsaron Isra'ila.

    Lamarin ya faru ne a wajen yankin Jenin inda jami'an tsaron Isra'ila ke zama a kusa da yammacin Kogin Jordan.

    Tashin hankali na karuwa a yammacin Kogin Jordan da gabashin birnin Kudus a cikin azumin watan Ramadan bayan 'yan sandan Isra'ila sun tarwatsa masu zanga-zanga a kofar shiga tsohon garin Kudus.

    A ranar Laraba sojojin suka kashe wani matashi Bafalasdine a rikicin da aka yi kan kisan wani dalibi Bayahude.

  10. Jihar Neja ta haramta yin hawa yayin bikin Sallah

    Wasu mahaya dawaki

    Gwamnatin Jihar Neja a arewacin Najeriya ta bayar da umarnin dakatar da kilisa da kuma hawa yayin bukukuwan Ƙaaramar Sallah.

    Sakataren Gwamnatin Jihar, Ahmed Ibrahim Matane, ya ce an ɗauki matakin ne biyo bayan ƙorafin da aka samu cewa wasu miyagu ka iya amfani da taron wajen tayar da hankalin mazauna jihar.

    Matane ya shawarci iyaye da kuma mamallaka dawaki da su ja kunnen yaransu don su bi dokar, yana mai barazanar cewa za a hukunta duk wanda aka kama da saɓa mata.

    Matakin na zuwa ne a lokacin da Neja ke cikin jihohin da 'yan fashin daji ke kai hare-hare kusan kullum, inda suke kashe ɗumbin mutane tare da yin garkuwa da wasu.

    Kazalika, ƙungiyar Boko Haram ta ɓulla wasu yankuna na jihar a 'yan kwanakin nan, a cewar Gwamna Sani Bello.

    Tuni jihohin Kano da Katsina suka hana gudanar da al'adar tashe - wadda ake yi a kwana 20 na ƙarshen watan Ramadana - bisa dalilan tsaro.

  11. Kotun Koli ta jaddada hukuncin soke jam'iyya 74 a Najeriya

    Farfesa Mahmud Yakubu

    Kotun Ƙoli a Najeriya ta tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara da ya soke jam'iyyun siyasa kimanin 74 daga cikin 92 da ake da su a kasar.

    A shekarar da ta gabata ne hukumar zabe INEC ta soke jam'iyyun saboda rashin tabukawa a babban zaben kasar na 2019 .

    Mai shari'a China Nweze da ya yanke hukuncin ya ce soke jam'iyyar NUP - daya daga cikin jam'iyyu 74 wadda kuma ta shigar da karar - an yi ne bisa tsarin doka da kuma tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasa da dokar zaben kasar.

    A yanzu dai wannan hukuncin ya tabbatar da makomar jam'iyyun da aka soke rajistarsu.

    A ranar 29 ga watan Yulin 2020 ne kotun daukaka kara da ke Abuja, babban birnin kasar ta jaddada ikon da INEC ke da shi na soke rajistar jam'iyyun.

    Mai shari'a Mohammed Idris a hukuncin da ya yanke, ya ce INEC ba ta yi kuskure ba wajen daukar matakin soke jam'iyyar NUP.

    Kotun ta tabbatar da hukuncin mai shari'a Taiwo Taiwo na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, wadda a cikin watan Mayu ta soke rajistar jam'iyyar NUP da wasu jam'iyyu 73 saboda saba sashe na 225(a) na kundin tsarin mulkin kasar.

  12. Ghana ta karɓi ƙarin rigakafin korona 350,000

    Rigakafin korona

    Ghana ta karɓi rigakafin cutar korona na AstraZeneca a karo na biyu a yau Juma'a, wanda zai ba ta damar fara yi wa mutane zagaye na biyu na allurar.

    Ƙasar ce ta farko da ta ta karɓi rigakafin daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ƙarƙashin shirin COVAX a watan Fabarairu kuma ta ƙaddamar da shi a watan Maris.

    Ba kamar sauran ƙasashe ba inda ake samun masu ƙin rigakafin da kuma ƙarancin kuɗi, Ghana ta yi wa mutum 900,000 rigakafin, a cewar ma'aikatar lafiya.

    350,000 da ta karɓa a yau Juma'a wani ɓangare ne na rigakafi miliyan 1.7 da za ta samu ta shirin COVAX, wanda tuni aka kai su ƙasar Dimokuraɗiyyar Congo ranar 2 ga watan Maris.

  13. 'Yar shekara 11 ta harbi mutum uku da bindiga a Amurka

    Amurka

    Wata ɗaliba 'yar shekara 11 ko 12 ta harbi ɗalibai biyu da ma'aikaci ɗaya a makarantarsu da ke Jihar Idaho ta Amurka.

    Ɗalibar wadda ba a bayyana sunanta ba, 'yar aji shida ce a Rigby Middle School, kuma ta fito da bindigar ce sannan ta buɗe wuta.

    Ana sa ran mutanen da ta harba za su warke.

    Wata malama ce ta yi hoɓɓasa ta ƙwace bindigar kuma ta tsare ta har sai da 'yan sanda suka ƙaraso, a cewar hukumomi.

    Ya zuwa yanzu ba a gano dalilin da ya sa ta yi harbin ba.

  14. An kashe 'yan bindiga da dama a Jihar Imo

    Wata mota

    Wata tawagar jami'an tsaro na haɗin gwiwa sun kashe 'yan bindiga da ake zargin 'yan ƙungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) ne da dama a Jihar Imo da ke kudancin Najeriya ranar Alhamis.

    Rahotanni na cewa an kashe aƙalla 'yan bindiga takwas yayin da suka yi yunƙurin kai hari a ofishin 'yan sanda na Orlu.

    Jami'an tsaron sun kuma ƙwace motoci kusan bakwai na 'yan bindigar da suka yi amfani da su yayin harin, waɗanda ake zargin na sata ne.

    Wata mota

    Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan zumunta ya nuna yadda suka ɗaura ɗamarar yaƙin.

    Mazauna yankin sun ce an shafe awanni ana fafatawa tsakanin ɓangarorin biyu, abin da ya sa suka kasa barci da idonsu rufe.

    Fafatawar na zuwa ne ƙasa da kwana ɗaya bayan sabon Kwamishinan 'Yan Sanda Abutu Yaro ya fara aiki a jihar.

    A watan da ya gabata ne wata tawagar jami'an tsaron ta kashe wani kwamandan ƙungiyar ta IPOB mai suna Ikonso da wasu mayaƙansa guda shida.

    'Yan ƙungiyar ta IPOB wadda ke neman kafa ƙasar Biafra a kudu maso gabashin Najeriya sun sha kai hare-hare kan 'yan sanda tare da kuɓutar da waɗanda ake tsare da su a jihohin yankin.

  15. Fiye da mutum miliyan 21 ne suka kamu da korona a Indiya

    Indiya

    Ma'aikatar lafiya a Indiya ta ce jumillar mutanen da suka kamu da cutar korona sun haura miliyan 21 a ƙasar.

    Ƙasar ta shiga yanayi mai tsanani bayan sake barkewar annobar a karo na biyu.

    Jumillar mutum fiye da 230,000 cutar tayi ajalinsu.

    Wakilin BBC ya ce jami'an lafiya sun ce a yanzu annobar na yaɗuwa daga birane zuwa kauyukan da ke da wuyar sha'ani da rashin asibitoci.

    Likitoci a asibitin Delhi, babban birnin ƙasar, sun ce ana samun ƙaruwar mutanen da ke kamuwa da cutuka da annobar ke tafe da su.

  16. 'Yara 22,000 ne ke kamuwa da cutar HIV duk shekara a Najeriya'

    Wata unguwarzoma

    Hukumar taƙaita yaduwar cuta mai karya garkuwar jiki a Najeriya (NACA) ta ce ta bijiro da wani shiri na gwada mata masu juna biyu kimanin miliyan shida duk shekara.

    Shugaban hukumar, Dr. Gambo Aliyu, ya faɗa BBC Hausa cewa wannan wani yunƙuri ne na shawo kan yaɗuwar cutar daga uwa zuwa jaririnta, a cewar hukumar.

    Ya ce yunƙurin na daga cikin ƙoƙarin Najeriya na rage yara kimanin 22,000 da ke kamuwa da cuta mai karya garkuwar jiki duk shekara a ƙasar.

    Hukumar ta ce rashin zuwa awon ciki a asibiti ga miliyoyin mata a Najeriya ya sanya ta ɗaukar matakin bin irin waɗannan mata gidajensu don tabbatar da ana yi musu gwaji.

  17. Nan da Talata ma'aikatan shari'a a Najeriya za su bayyana matsayinsu kan yajin aiki

    Video content

    Video caption: Latsa hoton sama ku saurari hira da mataimakin sakataren ƙungiyar ma'aikatan shari'a

    Ƙungiyar ma'aikatan kotuna da ke yajin aiki a Nijeriya ta gudanar da wani taro da ministan ƙwadago, Chris Ngige da yammacin jiya Alhamis ba tare da cimma sasantawa ba.

    Ɓangarorin biyu sun gudanar da tattaunawar ce da nufin kawo ƙarshen yajin aikin da ƙungiyar JUSUN ta tsunduma a farkon watan Afrilu, lamarin da ya durƙusar da ɓangaren shari'ah na ƙasar.

    Wani taro da aka gudanar tsakanin ƙungiyar gwamnoni da ƙungiyar shugabannin majalisun dokoki na jihohi da Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa Ibrahim Gambari kwanakin baya, ya bai wa ɓangaren shari'a da majalisun dokoki 'yancin cin gashin kansu.

    Sai dai ƙungiyar JUSUN ta ce ba ta gamsu da kalaman fatar baki ba, don haka ta ci gaba da yajin aiki.

    Bayan kammala taron nasu a jiya, mataimakin sakataren ƙungiyar na ƙasa, Kwamared Sa'ido Magaji Ƙarƙarku, ya faɗa wa BBC cewa zuwa nan da ranar Talata za su fitar da matsayarsu kan tayin da minista ya yi musu.

  18. An ci tarar Channels TV kusan miliyan biyar a Najeriya

    Channels TV

    Hukumar kula da kafafen yaɗa labarai a Najeriya, National Broadcasting Commission (NBC), ta ci tarar gidan talabijin na Channels kusan naira miliyan biyar bisa "karya ƙa'idar aiki".

    Shi ma gidan rediyon Inspiration FM zai biya irin wannan tarar.

    An tuhumi Channels da yaɗa labarai masu raba kan ƙasa bayan ya karɓi baƙuncin wani jagoran ƙungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) mai fafutikar ɓallewa daga Najeriya a shirinsa mai suna Politics Today ranar 25 ga watan Afrilu.

    Gidan talabijin ɗin mai zaman kansa da ke da hedikwata a Jihar Legas, na cikin kafa guda uku da NBC ta yi wa tara a Oktoban 2020 saboda "rashin nuna ƙwarewa" yayin bayar da rahotanni game da zanga-zangar EndSARS da aka yi.

    IPOB wadda aka kafa a 2012, na yunƙurin kafa ƙasar Biafra a yankin kudu maso gabashin Najeriya kuma tuni gwamnatin tarayya ta haramta ayyukanta a ƙasar.

  19. An sake samun sabon nau'in cutar korona a Ingila

    Cutar korona

    Ƙwararu a fannin lafiyar al'umma a Ingila sun ce an sake samun sabon nau'in annobar korona da ake kyautata zaton ta ɓullo daga Indiya.

    Sai dai ɗaya daga cikinsu ya shaida wa BBC cewa babu shaida da ke nuna cewa sabon nau'in na bijire wa rigakafi.

    Yanayin yaduwar nau'in cutar da ake gani a yankin Kent da Afirka ta Kudu da Brazil na sake haifar da fargaba a Birtaniya.

  20. Gobara ta laƙume shaguna a Jihar Legas

    Gobara a Legas

    'Yan kwanakwana sun kashe wata gobara da ta tashi a kasuwar Cairo da ke Oshodi ta Jihar Legas a kudancin Najeriya.

    Ya zuwa yanzu ba a san lokacin da wutar ta tashi ba da kuma musabbabinta.

    Hukumar kashe gobara ta Legas ta ce ta yi nasarar kashe wutar sannan kuma babu wanda ya rasa ransa.

    Sai dai ta ce an yi asarar ɗumbin kayayyaki.

    Ita ma hukumar kashe gobara ta tarayya ta nemi mutane da su bar wajen domin ta samu kyakkyawan yanayin kashe wutar.

    'Yan kasuwar sun shaida wa wani wakilin BBC Pidgin da ya ziyarci wurin cewa ana tsammanin gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 8:00 na yammacin Alhamis har zuwa tsakar dare.