Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail da Awwal Ahmad Janyau

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Nan za mu dakatar da kawo labarai da rahotanni kai tsaye a wannan shafin sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu.

    Kuna iya zuwa har kasan wannan shafin domin karanta labaran da suka faru a Najeriya da sassan duniya.

  2. Labarai da dumi-dumiSojojin Mali sun kame shugaban ƙasa da Firaminista

    Sojoji a Mali sun kame shugaban kasa da firaminista da kuma ministan tsaro na gwamnatin rikon kwaryar kasar ranar Litinin bayan yi wa majalisar ministocin ƙasar garambawul.

    Wasu majiyoyin diflomasiyya da na gwamnati sun tabbatar wa kamfanin dillacin labaran Reuters cewa ana tsare da shugaba Bah Ndaw, da Firaminista Moctar Ouane da mimnistan tsaro Souleymane Doucoure a wani sansanin soji.

    An ɗora wa Ndaw da Ouane alhakin jagorantar zaɓen sabuwar gwamnatin farar hula cikin watanni 18 amma wasu da dama a cikin gwamnati da ƴan adawa na bayyana fargaba kan yadda sojoji suka mamaye manyan kujerun gwamnati.

    Kamen na zuwa bayan sauya wasu daga cikin sojojin da suka jagoranci juyin mulki a watan Agusta a majalisar ministoci.

  3. Ƴan bindiga sun 'tayar da ƙauyuka hudu' a Benue

    Wasu ƴan bindiga sun kai jerin hare-hare a ƙauyukan karamar Hukumar Katsina-Ala da ke jihar Benue a Arewacin Najeriya.

    Mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Benue Shehu Tambaya wanda ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin ya ce an tada kauyuka kusan guda hudu a ƙaramar hukumar Katsina Ala.

    Ya ce ba su kai ga tantance yawan adadin rayukan da suka salwanta ba.

    Amma wasu rahotanni sun ce an kashe sama da mutum 100 a hare-haren da aka kai yankin gabashin Benue.

    Bayanai sun ce maharan sun shiga ƙauyukan ne suka buɗe wata kan mai uwa da wabi tare sace dukiyoyin jama’a.

    Rahotannin sun ce mutane da dama ne suka tsere daga gidajensu a yankin na karamar Hukumar Katsina-Ala

    Sai dai rundunar ƴan sandan jihar Benue ta ce ba ta samu wani rahoto na wani hari da aka kai a yankin ba.

    Gwamnan Benue
  4. Wani Sarkin Zimbabwe ya buƙaci a tono gawar Mugabe a sake binne shi

    Robert Mugabe

    Wani basaraken gargajiya a Zimbabwe ya ba da umarnin a tono gawar tsohon shugaba Robert Mugabe a sake binne shi a babbar maɓabartar kasar.

    Mugabe ya mutu ne a 2019 kuma an binne shi ne a cibiyarsa garin Kutama kamar yadda ya bar wasiyya saɓanin babbar maƙabartar ƙasa da ke Harare babban birnin Zimbabwe kamar yadda wanda ya gaje shi Emmerson Mnangagwa da sauran ƴan ƙasar suka buƙata.

    Iyalansa sun ce Mugabe ya bayyana damuwa kan cewa abokan hamayyarsa na siyasa da suka tsige shi a 2017 za su iya yin tsafi da sassan jikinsa idan an binne shi a maƙabartar ƙasa.

    A ranar Litinin ne Sarkin Zvimba, da ke gundumar yammacin Harare ya ce ya samu koke daga wasu ƴan uwan Mugabe kan wurin da aka binne shi.

    Ya zartar da hukuncin cewa uwar gidansa Grace Mugabe ta saɓa al’ada bayan ta binne mijinta a gidansa.

    Matar Mugabe ba ta halarci fadar sarkin ba lokacin zartar da hukuncin, amma basaraken ya ci tararta inda ya buƙaci ta biya shanu ko akuya biyar.

    Mai magana da yawun iyalan Mugabe sun ce “Sarkin ba ya da iko da Kutama, kuma ko da yana da iko za su iya ɗaukaka ƙara a kotu.”

  5. Dangote na shirin kafa kamfanin taki a Tanzania

    Dangote tare da shugabar Tanzania

    Hamshaƙin attajirin ɗan kasuwa a Najeriya Aliko Dangote ya kai ziyara ƙasar Tanzania domin diba yiyuwar yadda zai faɗaɗa kasuwancinsa a ƙasar, kamar yadda kafofin yaɗa labaran Tanzania suka ruwaito.

    Jaridar Daily News ta ce Dangote ya gana da shugabar Tazania Samia Suluhu Hassan a Dar es Salaam a ranar Litinin kuma ya shaida wa shugabar cewar yana fatan kafa kamfanin taki a ƙasar.

    “Za mu ci gaba da zuba jari a Tanzania domin samar da ayyukan yi da kuɗaɗen shiga da kuma inganta rayukan ƴan Tanzania, in ji Dangote kamar yadda jaridar ta ruwaito.

    Dangote, a cewar Jaridar tuni dama yana da kamfanin siminti a Tanzania amma ya sha fuskantar yajin aiki daga ma’aikata.

  6. Ma’aurata sun yi bikin aurensu sararin samaniya don kaucewa matakan korona

    Bidiyon da aka wallafa a tuwita ya nuna yadda aka yi bikin auren a cikin jirgi
    Image caption: Bidiyon da aka wallafa a tuwita ya nuna yadda aka yi bikin auren a cikin jirgi

    An bayar da rahoton wasu ma’aurata a Indiya da suka yi shatar jirgin sama domin gudanar da bikin aurensu a sararin samaniya domin kaucewa matakan korona.

    An yi bikin auren tare da sama da mutum 160 da ke cikin jirgin.

    Bidiyon auren da aka wallafa a tuwita ya nuna ma’auratan da kuma ƴan biki a cikin jirgin da suka yi shata.

    Bayanai sun ce ma’auratan sun yi hayar jirgin ne na tsawon awa biyu domin bikin aurensu a sararin samaniya.

    View more on twitter

    Jihar Tamil Nadu, da aka bayyana cewa jirgin ya fito, ta tsaurara matakai na kariya daga bazuwar korona, inda aka taƙaita yawan mutanen da za su halarci biki zuwa mutum 50.

    Rahotanni sun ce hukumomin kula da sufurin jiragen sama a Indiya sun ƙaddamar da bincike game da al’amarin

  7. Suu Kyi ta gurfana gaban Kotu kan zargin maguɗin zaɓe a Myanmar

    Aung San Suu Kyi

    Tsohuwar shugabar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi ta gurfana a gaban kotu a karon farko tun bayan da sojoji suka kifar da gwamnatinta a watan Fabrairun da ya gabata.

    Sai dai kotun da ke Naypyidaw, babban birnin Myanmar ta ɗage sauraren ƙarar nan take.

    Tsohuwar shugabar Mayanmar na fuskantar jerin tuhume tuhume da suka haɗa da karya dokar sirrin kasa da yin maguɗin zaɓen da jam’iyyarta ta lashe a watan Nuwamba.

    Mutane da dama sun soki shari’ar da ake yi tsohuwar shugabar a matsayin bita da kullin siyasa domin hanata tsayawa takara a zabukan da zaa yi nan gaba.

    Kafin a soma shari’ar an bata damar ganawa da lauyoyinta a karon farko.

  8. Zulum ya yi umarni a hukunta wasu ma'aikatan lafiya na bogi

    Gwamna Zulum

    Gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya Babagana Umara Zulum ya yi umarni a hukunta wasu ma'aikatan lafiya 21 da aka samu da gabatar da shaidar kammala karatu ta jabu da kuma ma'aikatan bogi 91.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Isa Gusau, ya aike wa manema labarai ranar Litinin ta ambato gwamnan yana bayar da umarni a dauki matakin hukunci bayan wani kwamitin da aka nada domin tantance ma'aikatan ya gano mutum 21, ciki har da ma'aikatan jinya, suna gudanar da aiki ta hanyar amfani da sakamakon makaranta na jabu.

    Kwamitin ya kuma gano ma'aikatan bogi 91 a ma'aikatu daban-daban a fadin jihar.

    Shugaban kwamitin, Dr. Joseph Jatau ya bayyana cewa sun gano ma'aikatan bogi da masu amfani da takardun kammala karatu na jabu ne a rahoton da ya mika wa Gwamna Zulum ranar Litinin a Maiduguri.

    Dr Jatau ya ce an gano fiye da N23m da ake kashewa bisa kuskure kowanne wata.

    Ya kara da cewa sun gano yadda ake ci gaba da biyan wasu ma'aikata da suka mutu, ko wadanda suka yi ritaya da kuma wadanda ba sa zuwa aiki.

  9. Sarki Salman ya yi wa Buhari ta'aziyyar rasuwar Laftanar Janar Ibrahim Attahiru

    Sarki Salman da Buhari

    Sarki Salman na kasar Saudiyya ya bayyana alhininsa bisa rasuwar Babban Hafsan sojin kasa na Najeriya Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da wasu sojoji 10 sakamakon hatsarin jirgin sama.

    Sarkin ya mika ta'aziyyarsa ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Litinin lokacin da ya kira shi a wayar tarho, a cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Tuwita.

    View more on twitter

    Sarki Salman ya kuma taya kasar juyayi bisa alhinin da ta tsinci kanta a ciki sanadin mutuwar manyan sojojin na Najeriya.

    Kazalika shugabannin biyu sun yi musayar gaisuwa ta Sallar Idi bayan an kwashe kwanaki talatin ana azumtar watan Ramadan.

  10. An kashe 'yan bindiga bayan sun ƙona ofishin INEC a Jihar Anambra

    Ofishin 'yan sanda

    Wasu 'yan bindiga sun ƙona ofishin hukumar zaɓe a Najeriya (INEC) rashen Jihar Anambra da ke kudancin ƙasar ranar Lahadi.

    Rahotanni sun ce maharan sun yi yunƙurin kai hari a ofishin 'ya sanda na 'B' da ke kusa da ofishin na INEC da ke garin Awka amma sai suka fuskanci turjiya daga jami'an tsaron da ke bakin aiki a lokacin.

    Lamari ya ya jawo an kashe biyu daga cikin maharan, kamar yadda rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar.

    Kwamishinan 'yan sandan jihar wanda ya ziyarci wurin, CP Chris Owolabi, ya ce suna samun nasarar daƙile ayyukan 'yan bindigar da kusan kashi 98 cikin 100.

    Harin shi ne na baya-bayan nan da 'yan bindigar da ake zargin 'yan ƙungiyar IPOB ne masu rajin kafa ƙasar Biafra ke kaiwa a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

  11. Babu adalci wajen raba rigakafin cutar korona - WHO

    Tedros Adhanom Ghebreyesus

    Shugaban hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya ce ya zuwa yanzu ya kamata a ce an yi wa dukkan ma'aikatan lafiya da tsofaffi rigakafin cutar korona da a ce akwai adalci wajen samar da ita.

    Da yake neman a bai wa ƙasashe matalauta ƙarin allurar, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce gwamnatocin da ke yi wa mutanensu rigakafin suna yi ne a madadin wasu mutanen a ƙananan ƙasashe.

    Ya siffanta rashin adalci wajen raba allurar a matsayin laifi kuma hakan na ƙara ta'azzara cutar.

    Mista Tedros ya nemi a ci gaba da tallafa wa shirin WHO na Covax, wanda ke tallafa wa ƙasashe ƙanana da rigakafin.

  12. Labarai cikin minti ɗaya

    Video content

    Video caption: Minti Ɗaya da BBC na Rana 24/05/2021
    • Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin a sassauta tutar ƙasar a dukkan gine-ginen gwamnati tare da yin zaman makoki na kwana uku yayin da ake ci gaba da makokin rasuwar shugaban sojan ƙasa Janar Ibrahim Attahiru da wasu sojoji 10. Kazalika, shugaban ya bai wa dakarun rundunar sojojin ƙasar hutun aiki a yau Litinin
    • Amurka ta ƙaƙaba wa Habasha wato Ethiopia takunkumi daban-daban game da rikicin yankin Tigray. Sakataren Harkokin Waje, Antony Blinken, ya kuma sanar da cewa za a taƙaita bai wa jami'an gwamnatin Habasha da Eritrea biza waɗanda ake zargi da hannu a aika-aikar
    • Rahotanni daga Najeriya na cewa a safiyar yau masu zanga-zanga sun toshe babbar hanyar Kaduna zuwa don nuna ɓacin ransu game da sace-sacen mutane da ake yi a yankin. Masu zanga-zangar sun kwarara kan hanyar ne a yankin Gauraka da ke Tafa a cikin Jihar Neja, inda suka dinga ƙona tayoyi
    • Har wa yau a Najeriyar, kusan mutum 10 ne suka rasu a yankin Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu da ke Jihar Filato a jiya Lahadi sakamakon wani hari da aka kai. Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar wa da BBC faruwar lamarin amma ba ta yi Karin bayani ba
  13. Aman wutar dutse ya jawo kisan mutum 15

    Dutse

    Mazauna yankin Goma a Gabashin DR Congo na komawa gida bayan wani aman wutar dutse da ya faru a birnin.

    Mutum 15 ne suka mutu akasarinsu a yayin da suke kokarin tserewa.

    An harbi mutum hudu yayin da suke kokarin guduwa daga wani gidan yari a yankin na Goma.

    Dubban jama'a sun tsere cikin firgici bayan da tsaunin Nyiragongo ya rufta. Lamarin ya janyo barna ga gidaje.

    Wata kungiya da aikinta shi ne yin hasashen yiwuwar fuskantar aman wutar dutse ta ce aikinta ya fuskanci koma-baya saboda rashin kudi.

  14. Kusan mutum 10 sun mutu yayin wani hari a Jihar Filato

    Bindiga

    Mutane da dama ne aka kashe a yankin Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu da ke Jihar Filato a arewacin Najeriya a ƙarshen mako sakamakon wani hari da aka kai.

    Rahotanni na cewa maharan sun kai shi ne a daren Lahadi a yankin Dong.

    Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Ubah Gabriel, ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin amma bai yi ƙarin bayani ba, yana mai cewa "ina kan hanyar zuwa wurin da abin ya faru".

    Sai dai jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mutum bakwai aka kashe tare da sace shanu kusan 52 yayin harin.

    Kazalika, an kashe wasu mutum biyu a yankin Kuru ranar Lahadi, a cewar jaridar.

  15. Najeriya za ta hukunta matafiya 90 bisa karya dokar korona

    Matafiya

    Hukumomi a Najeriya sun bayyana wasu matafiya 90 da suka koma ƙasar daga Brazil da Indiya da Turkiyya a matsayin "masu haɗari" bayan sun ƙi bin dokokin kariya daga cutar korona.

    Ana nemansu ne ruwa a jallo sakamakon sun ƙi kai kansu a yi musu gwajin cutar bayan sun isa ƙasar, kamar yadda kwamitin yaƙi da korona ya bayyana.

    Mutanen sun ƙunshi 'yan Najeriya 63 da 'yan ƙasar waje 27 da suka sauka a ranakun 8 da kuma 15 ga watan Mayu.

    Sun sauka ne a filayen jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas da kuma Nnamdi Azikiwe na Abuja.

    Cikin wata sanarwa, kwamitin ya ce za a hukunta su ta hanyar dakatar da fasfo ɗinsu na tsawon shekara ɗaya da hana su biza ko kuma soke izinin zama a Najeriya ga 'yan ƙasar waje.

    Ya ƙara da cewa suna kawo mummunar barazana ga lafiyar al'umma sakamakon kauce wa killace kansu na kwana bakwai da suka yi, wanda tilas ne ga duk wanda ya shiga Najeriya daga wasu ƙasashen waje.

  16. Labarai da dumi-dumiMasu zanga-zanga sun toshe hanyar Kaduna-Abuja

    Rahotanni daga Najeriya na cewa masu zanga-zanga sun toshe babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja a safiyar yau Litinin don nuna ɓacin ransu game da sace-sacen mutane da ake yi a yankin.

    Masu zanga-zangar sun kwarara kan hanyar ne a yankin Gauraka da ke Tafa a cikin Jihar Neja, inda suka dinga ƙona tayoyi.

    Rahotanni na cewa sun fusata ne bayan wasu 'yan bindiga sun sace mutum kusan 15 a yankin.

    Masu zanga-zangar sun ƙona ofishin 'yan sanda yayin zanga-zangar, a cewar wani ɗan jarida da ya shaida lamarin.

    Hotuna da bidiyo da aka wallafa a shafukan zumunta sun nuna yadda mutane suka yi cirko-cirko a kan titi yayin da hayaƙi ya turnuƙe sama daga wutar da suka kunna.

    View more on twitter
  17. Amurka ta ƙaƙaba wa Habasha takunkumi kan rikicin Tigray

    Habasha

    Amurka ta ƙaƙaba wa Habasha wato Ethiopia takunkumi daban-daban game da rikicin yankin Tigray.

    Sakataren Harkokin Waje, Antony Blinken, ya kuma sanar da cewa za a taƙaita bai wa jami'an gwamnatin Habasha da Eritrea biza waɗanda ake zargi da hannu a aika-aikar.

    Mista Blinken ya jaddada cewa akwai buƙatar ƙasashe su taimaka wajen kawo ƙarshen rikicin, yana mai cewa waɗanda ake zargin ba su da niyyar kawo ƙarshen lamarin.

    An kashe dubban mutane sannan an raba wasu da muhallansu tun bayan ɓarkewar rikicin wata shida da suka gabata.

    An zargi dukkan ɓangarorin biyu da take haƙƙin ɗan Adam.

    Tun ranar Lahadi gwamnatin Habasha ta musanta zarge-zargen cewa hare-harenta sun jikkata fararen hula da makamai masu guba.

  18. Za a fara amfani da karnuka wajen gano masu cutar korona

    Kare

    Wani bincike da aka gudanar a Birtaniya ya gano cewa karnukan da suka ƙware wajen sinsina abu na iya gano mutanen da suka kamu da cutar korona.

    Masana kimiyya sun tattaro safuna da kayan dubban mutanen da aka tabbatar suna da cutar, inda kuma karnukan suka iya gano kashi 94 cikin 100 da ke da cutar, har da mutanen da ba su nuna alamomin kamuwa da cutar ba.

    Wakilin BBC ya ce wannan zai ba da damar yin amfani da karnukan a wurare kamar filayen jiragen sama.

    Karnuka biyu na iya tantance fasinjoji 300 cikin kusan rabin sa'a.

  19. Za a yi makokin kwana uku a Najeriya saboda mutuwar sojoji

    Sojojin Najeriya

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin a sassauta tutar ƙasar a dukkan gine-ginen gwamnati yayin da ake ci gaba da makokin rasuwar shugaban sojan ƙasa Janar Ibrahim Attahiru da wasu sojoji 10.

    Kazalika, shugaban ya bai wa dakarun rundunar sojojin ƙasar hutun aiki a yau Litinin. Sannan umarnin zai fara aiki ne daga Litinin zuwa Laraba.

    A ranar Asabar ne aka yi jana'izar Babban Hafsan Sojan Ƙasa Laftanal Janar Ibrahim Attahiru tare da wasu sojoiji 10 bayan sun rasu a hatsarin jirgin sama a kusa da filin jirgin sama na JIhar Kaduna da ke arewacin ƙasar.

    An binne su a Maƙabarta ta Ƙasa da ke Abuja.

    Guda shida daga cikinsu Musulmai ne da aka yi wa sallah a Babban Masallacin Abuja, yayin da aka yi wa Kiristoci jana'iza a Babbar Cocin Abuja.

    Buhari ya bayyana kaɗuwa da rasuwar Janar Attahiru sannan ya umarci a gudanar da bincike game da abin da ya haddasa hatsarin jirgin.

  20. BBC ta bankaɗo halin da yara 'yan cirani ke ciki a Amurka

    Amurka

    BBC ta bankado wasu zarge-zargen rashin ba da kulawa da kuma yadda yaran yan ci-rani da ke tsare a sansanonin da Amurka ta kafa ke kamuwa da cutuka.

    Akwai rahotannin da ke cewa adadi mai yawa na yaran sun kamu da cutar korona a daya daga cikin wuraren mai dauke da mutum 4,500 da ke Fort Bliss a Texas.

    Wata majiya ta shaida wa BBC cewa yara da yawa na zaune da kwarkwata da karzuwa.

    A cewar wakiliyar BBC: "A wani sansanin na daban da ke Dallas kuma, an fada mana cewa yaran matasa na kwana da yunwa sannan kuma ana yi wa wasu kulle."

    Wasu daga cikin yaran sun ce sun tsere ne saboda rikici a nahiyar Tsakiyar Amurka.

    Gwamnatin Amurka ta ce an gina wasu wuraren 14 domin rage cunkoson da ke sansanonin da ke kan iyaka.