Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Buhari Muhammad Fagge da Umaymah Sani Abdulmumin

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Masu bibbiyarmu a wannan shafin da haka muke bankwana da ku, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu. Umaymah Sani Abdulmumin ke cewa a huta lafiya.

  2. Amnesty ta ce ta ga bidiyon da ke nuna sojoji na halaka mutane a Masar

    Kungiyar Amnesty International ta ce wani bidiyon Farfaganda na rundunar sojin Masar ya nuna yadda sojojin suka halaka mutane.

    Amnesty ta yi nazari kan bidiyon da aka dauka daga tsibirin Sinai wanda kungiyar ta ce an ga wani soja ya harbi wani mutum yana tsaka da bacci a cikin wani tanti.

    Wani bidiyon kuma ya nuna yadda aka harbe wani mutum daga sama yayin da yake gudu.

    Kungiyar ta ce hoton bidiyon ya bayyana manyan laifukan da aka tafka da sunan yaki da ta'addanci a Masar.

    Amnesty ta kuma nemi a gudanar da bincike. A farkon makon nan ne, Rundunar sojin ta wallafa bidiyon a kafafen sada zumunta a matsayin karin bayani kan yakin da take da mayaka a Sinai.

  3. An kashe mutum da jikkata da dama sakamakon rikici kan rusa coci a Maiduguri

    BABAGANA UMARA ZULUM

    An kashe mutum guda da jikkata da dama sakamakon rikicin da ya biyo bayanrusa coci a Maiduguri.

    Wasu bayanai da PRNigeria ta fitar na cewa wasu matasa da suka fusata ne suka yi arangama da jami'an da ke aikin rusa cocin.

    Wannan hatsaniya ya tursasawa jami'an tsaro na Civilian TFJ wuta kan dandazon mutane da ke rikici, yanayin da ya kai ga mutuwar wani matashi Ezekiel Bitrus mai shekara 29, sannan mutum biyar sun jikkata.

    Sannan anyi kone-kone da lalata motoci agaji.

    Gwamna Borno Babagana Umara Zulum ya yi tir da rikicin da ya biyo bayan rusa coci tare da umartar ƴan sanda su yi bincike.

    Ya kuma mika sakon jaje da ta'aziya ga iyalan wadanda fada ya ritsa da su.

  4. Uwa da ƴaƴanta ƴan maɗigo da zaman Rasha ya gagare su

    Madigo

    Wasu iyalai ƴan maɗigo da aka haska su a wani tallan abincin gina jiki, sun ce sun bar Rasha sakamakon tsangwama da barazanar kashe su.

    Iyalan sun fuskanci kalaman ƙiyayya bayan haskasu a wani tallan abinci kamfanin VkusVill. Kamfanin daga baya ya nemi afuwa da sauya tambarinsa da hoton ɗaya daga cikin iyalan masu maɗigo.

    Ɗaya daga cikin ƴaƴan mai suna Mila ta rubuta wani saƙo a intanet cewa a yanzu suna Barcelona, saboda hankalisu ya fi kwanciya a can.

    Dukkanin yara mata biyu Yuma da ƴaƴarta Alina na rayuwar madigonci.

    Sun kuma nuna godiyarsu ga magoya bayansu a shafukan sada zumunta, da jadada cewa tserewa daga Rasha ya bar su cikin kaɗuwa.

    A watan da ya gabata kamfanin VkusVill ya nemi afuwa bayan wallafa hoton farko, da ke nuna iyalan gida ɗayan, abin da ya haddasa cacaka a shafukan sada zumunta.

    A shekara ta 2013 wata doka a Rasha - ta yi alla-wadai da ƙasashen yamma - ta haramta tallata maɗigonci da luwaɗi.

  5. Sojojin Isra'ila sun ƙaddamar da hare-hare a Lebanon karon farko cikin shekara 7

    Sojojin saman Isra'ila sun kaddamar da hare-hare a kudancin Lebanon a karon farko a cikin shekaru bakwai.

    Farmakin da aka kai shi a cikin dare, martani ne ga makaman rokar da aka harba daga cikin Lebanon.

    Isra'ilawa sun ce jiragensu na yaki sun hari abinda suka kira wuraren da ake amfani da su saboda ayyukan ta'addanci.

    Jamian tsaron Israilar sun ce sun yi imanin cewa mayakan Palasdinawa ne suka harba rokokin.

  6. Yan bindiga da suka sace yara a Neja sun rage kudin fansa zuwa N50m

    Bindiga

    Ƴan bindiga da suka sace yara biyu da manya 7 a Anguwar Kwankwashe na yankin Suleja a Jihar Neja sun zabtare kudin fansa da suka bukata daga naira miliyan 100 zuwa miliyan 50.

    Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa ƴan bindiga da ake zargi sun kai hari ne a ranar Litinin a yankin Anguwar Kwankwashe tare da yin awon gaba da mutanen.

    Wata majiya ta shaida cewa mutanen da suka bukaci a sakaya sunansu, sun tuntubi iyalansu ta wayar masu garkuwar a ranar Talata, suna cewa ana bukatar miliyan 100 kudin fansa.

    Ya ce, bayan dogon tattaunawa har zuwa safiyar yau Alhamis, masu garkuwar sun zabtare kudin da suke bukata zuwa naira miliyan 50, sannan ya ce jami'an tsaro na bin sahu domin gani ko za su yi nasarar ceto mutane.

  7. Kwalara na barazana ga ɗaruruwan ƴan Najeriya

    Mahukuntan jihohin Kano da Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya sun ce barkewar kwalara ta hallaka mutum 300.

    A kowace shekara Najeriya na fama da barkewar wannan cuta musamman lokutan damuna, sai dai adadin mutane da ke mutuwa a bana ya rubanya na shekarun baya,.

    Hukumar yaki da yaduwar cutuka ta NCDC, ta ce cutar na illa a kusan duk rabin jihohi 36 na ƙasar.

    Dubban mutane sun kamu da cutar sannan akwai daruruwa da suka mutu - akasari kananan yara.

    Cutar ta fi ɓarna a jihohin arewacin Najeriya, inda galibi aka fi kamuwa da cutar.

    Tun a watan Maris cutar ta soma amma a makonni baya-bayanan ta fi kamari.

  8. Mutum 27 ne suka rasa rayukansu a rikicin ƙarshen mako a Kaduna

    Hukumomi a jihar Kaduna sun ce adadin wadanda suka mutu a cikin wani rikici da ake yi tun daga karshen mako a wasu kauyukan jihar masu makwabtaka da Filato ya kai 27.

    Haka ma sun ce an kona gomman gidaje tare da lalata gonakki a cikin rikicin da ya shafi wasu kauyukka hudu na Karamar Hukumar Kauru.

    Sai dai a gefe guda kuma sun ce wasu karin dalibai uku na Bethel Baptist High School sun samu kansu daga wadanda suka yi garkuwa da su.

    Ga dai karin bayanin da Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya yi wa Haruna Shehu Tangaza:

    Video content

    Video caption: Hirar Haruna Shehu Tangaza da Samuel Aruwan
  9. Ƴan Najeriya sun yi asarar naira biliyan sama da 150 sakamakon haramta Twitter

    Twitter

    Ƴan Najeriya da ke harkokin kasuwanci sun yi asarar N150.46bn ($366.88m) sakamakon haramcin da gwamnati ta yi kan amfani da Twitter tun daga 5 ga watan Yuni a faɗin ƙasar.

    Alkaluman da kididdigar cibiyar bincike da sa'ido han harkokin intanet NetBlocks ta wallafa na cewa a kowanne sa'a guda ƴan Najeriya na asarar N102.77m ($250,600) sakamakon haramcin.

    Rahoton ya ce a yanzu an sahfe sa'o'i 1,464 da haramta shafin (kwanaki 61). Wannan na nufin an tafka asarar N150.46bn kenan.

    A ranar 4 ga watan Yuni gwamnatin tarayya ta haramta twitter a faɗin Najeriya sakamakon zargin cewa shafin na zagon-kasa ga zaman lafiyarta

    Ƙungiyoyi da dama sun yi ta suka da alla-wadai da matakin da gwamnati ta dauka.

  10. Zakuna sun kashe yaran makiyaya a Tanzania

    zaki

    Zakuna sun kashe yaran makiyaya uku da suka je wani gandun daji a arewacin Tanzania domin cigiyar saniyarsu, a cewar ƴan sanda.

    Yara da shekarunsu ke tsakanin 9 zuwa 11 - sun je neman dabbar ta su ce jim kadan da dawo wa daga makaranta, a cewar shugaban ƴan sanda Justine Masejo.

    "A lokacin ne zakuna suka kai musu hari tare da kashe yaran uku da jikkata guda," a cewarsa.

    "Ina kira ga sauran makiyaya da ke kusa da yankunan gadun daji su kasance masu takatsantsan da irin waɗannan dabobbi musamman wajen aike yara domin kula da dabobbinsu. Hakan zai taimaka wajen kare yaran da iyalansu."

    Yankin Ngorongoro da sauran yankunan gadun daji da wuraren shakatawa, wurare ne da ake karewa amma mahukunta na amincewa kabilar Maasai su yi rayuwa a can da kiwon dabobbinsu.

    An sha samun rikici tsakanin mutane da namun daji a baya a yankunan, a cewar kamfanin dilancin labaran Faransa, AFP.

    Zakuna 36 aka maida gadun dajin Serengeri, da ke arewacin Tanzania, sakamakon harin da suka kai wa mutane da shanun makiyaya.

  11. Mafarauta sun hana Fulani masu ƙaura 107 shiga Jihar Adamawa

    Fulani

    Mafarauta sun hana Fulani masu ƙaura shiga ƙaramar hukumar Toungo a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mafarautan ƙaramar hukumar Ganye ne suka hana Fulanin 107 shiga ƙaramar hukumar Toungo.

    Daily Trust ta ce mafarautan waɗanda suka tsaya ne a wani shingen bincike a garin ganye sun dakatar da motar tirela ɗauke da iyalai da suka haɗa da maza biyar da mata 32 da kuma yara 70 a safiyar ranar Litinin ɗin da ta gabata.

    Da ake tuhumarsu, mazan waɗanda suka ce su ne magidantan iyalan, sun ce sun yi ƙaura ne daga garin Doma na jihar Nasarawa da ke yankin tsakiyar Najeriya, zuwa Toungo, bisa izinin hakimin garin Alhaji Hammangabd

    Gabanin faruwar lamarin dai, hakimin Toungo ya aika wasiƙu ga hukumomin tsaro don tantance Fulani masu ƙaura.

    Daily Trust ta tuntuɓi sakataren ƙaramar hukumar Ganye wanda ya ce an dakatar da masu ƙaurar ne a hanyarsu ta shiga Toungo, kuma an ajiye su na ɗan lokaci a makarantar firamare ta Ganye, kafin daga bisani a mayar da su inda suka fito.

    Ya ce an ɗauki matakin mayar da su ɗin ne bayan da aka tuntuɓi ƙananan hukumomin biyu da kuma hukumar tsaro ta farin kaya.

  12. Labaran duniya cikin minti daya

    Video content

    Video caption: Minti Daya Da BBC Na Rana 05/08/2021
    • Kimanin mutum miliyan 4.4 ne ke rayuwa cikin matsananciyar yunwa a arewa maso gabashin Najeriya saboda hare-haren mayakan Boko Haram wadanda suka hana noma aiki, in ji Majalisar Dinkin Duniya.

    Yankin dai na fama da matsalar tsaro na sama da shekara 20, MDD ta ce hakan zai iya kai wa ga rashin abin ci a yankin.

    • Yan bindiga sun sace iyayen kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.

    Mai magana da yawun majalisar dokokin Jihar ta Zamfara Mustapha Jafaru Ƙaura ne ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin.

    • Kungiyar Amnesty International ta ce Jami’an tsaron Najeriya sun aikata laifukan take hakkin dan adam karkashin dokar kasa da kasa a kokarin mayar da martani ga rikicin da ke faruwa a kudu maso gabashin kasar.

    Cikin wani rahoto da ta wallafa a shafinta, Amnesty ta ce hakan dai wata muzgunawa ce da ake yi wa mutan yankin tun daga watan Janairu ciki har da kama mutane da dama, amafani da karfin da ya wuce iyaka, tare da azabtar da wadanda ake zargi da dai sauran laifuka.

    • Inter Milantana sa ran Chelsea ta biya ta £110m kan dan wasan Belgium mai shekara 28 Romelu Lukaku bayan da ta yi watsi da tayin farko na £85m da karin dan wasan Sifaniya Marcos Alonso, mai shekara 30.

    Yiwuwar tafiyar Jack GrealishManchester Cityza ta iya sa wa Bernardo Silva ya bar kungiyar, inda ake sa ran Barcelona da Atletico Madrid za su yi wawason dan wasan tsakiyar na Portugal mai shekara 26.

  13. An kashe mayaƙan Taliban da dama a Afghanistan

    KG

    Rahotanni daga birnin Lashkar Gah da ke Kudancin Afghanistan na nuna cewa an kashe mayakan Taliban da dama sanadin hare-hare ta sama da fadan da aka gwabza titi zuwa titi a kokarin da dakarun gwamnati ke yi na fatattakarsu.

    Tun farko dai Taliban din ta kwace iko da Lashkar Gah, babban birnin Lardin Helmand.

    Akasarin mutanen birnin sun bi shawarar da wani kwamandan sojoji ya basu na cewa su kauracewa gidajensu.

    Mutanen da har yanzu suke can kuma, sun ce suna fuskantar karancin abinci da ruwa da kuma magunguna.

    Wakilin BBC ya ce a daren jiya, daruruwan yan Afghanistan sun sake gudanar da zanga-zanga a birane da dama don nuna goyon baya ga sojoji da gwamnati.

  14. Tsohon gwamnan Kano Dominic Oneya ya rasu

    Google

    Tsohon gwamnan Kano karkashin mulki soji Dominic Oneya ya rasu.

    Marigayin ya mutu ne a ranar Laraba a gida a garinsu Agbarho da ke jihar Delta kamar yadda iyalansa suka bayyana a ranar Alhamis.

    Rahotanni sun ce Oneya ya mutu ne bayan fama da wata 'yar gajeriyar rashin lafiya, inda ya dan yi jinya a Abuja mako guda kan ya rasu

    An haifi Dominic Obukadata Oneya a ranar 26 ga watan Mayun 1948 a Jihar Legas a Karamar Hukumar Apapa

    Ya shugabanci Jihar Kano tsakanin watan Agustan shekarar 1996 zuwa Agustan 1998 karkashin shugabancin Marigayi Janar Sani Abacha.

  15. Labarai da dumi-dumiYan bindiga sun sace iyayen kakakin majalisar dokokin Jihar Zamfara

    Getty Images

    Yan bindiga sun sace iyayen kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.

    Mai magana da yawun majalisar dokokin Jihar ta Zamfara Mustapha Jafaru Ƙaura ne ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin.

    "Da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin ranar Laraba ne 'yan bindiga suka shiga wasu ƙauyuka a garin magarya, amma daga baya suka dawo suka shiga gidan mahaifin kakakin majalisa Nasiru Mu'azu Magarya.

    "Ba su kai ga iya shiga gidan ba kai tsaye sai da suka yi amfani da manyan makamai suka harbi wayar da aka zagaye gidan da ita sannan suka samu shiga," in ji Mustapha Ƙaura.

    Ƙaura ya ce an sace mahaifin Kakagin majalisar wanda yake rike da matsayin magajin garin magarya tare da wasu mutane shida da ke zaman fada.

    An tambayi Ƙaura dangane da rahotannin da ke cewa an tafi da mahaifiyar kakakin, sai ya ce "tabbas tana cikin mutane shida da na ce an dauka an tafi da su."

    Amma dai ya ce babu ko daya daga cikin 'ya'yansa da aka tafi da su kamar yadda rahotanni ke bayyana wa.

    Har yanzu dai 'yan bindigar ba su kira kowa ba, kuma babu wata hanya da za a yi tubtubarsu.

    Ya zuwa yanzu Mustapha Jafaru ya ce yanayin garin Magarya ya sauya, kowa yana cikin jimami.

    Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro a kasar.

  16. An rantsar da sabon shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi

    EPA

    An rantsar da sabon shugaban kasar Iran Ebrahim, bayan lashe babban zaben shugaban kasa da aka yi a watan Yuni.

    Ana sa ran shugaban zai kama aiki nan da ba jimawa ba.

    Sabon shugaban mai wa'azi ne da ke da ra'ayin riƙau kuma zai gaji Hassan Rouhani, wanda kasashen yamma ke masa kallon mai ra'ayin tsaka-tsaki.

    Ya karbi mulki ne lokacin da Iran ke tsaka da fuskantar matsala daga kasashen duniya sakamakon takunkumin da ake ƙaƙaba mata.

    Haka kuma ana ƙara fusknatar matsin lamba daga kasashe masu karfin fada a ji a duniya, kan zargin kai wa jirgin dakon man Isra'ila hari a Oman a makon jiya, wanda Iran ta musanta.

    An kashe ma'aikatan jirgin biyu dan Burtaniya da Romaniya.

  17. Tsawa ta kashe yan bikin aure 17 ana tsaka da cashewa

    Getty Images

    Akalla mahalarta wani bikin aure 17 ne suka mutu a Bangaladesh kamar yadda jami'ai suka bayya.

    Wasu mutum 14 kuma na daban ciki har da angon sun jikkata. A lokacin da abin ya faru amaryar ba ta halarci taron ba.

    An shirya bikin ne a cikin wani jirgin ruwa a gefen tekun Shibganj, kuma na cikin jirgin sun dauki hanyar zuwa gidan su amarya ne lokacin da tsawar ta same su.

    Mutanen da suka ga faruwar abun sun ce kashi-kashi na tsawar ne ya afkawa jirgin.

    Tsawa na kashe daruruwan mutane a fadin kudancin Asiya.

  18. Inter Milan na son sayar da Lukaku

    REUTERS

    Inter Milantana sa ranChelseata biya ta £110m kan dan wasan Belgium mai shekara 28 Romelu Lukaku bayan da ta yi watsi da tayin farko na £85m da karin dan wasan Sifaniya Marcos Alonso, mai shekara 30.(Mail)

    Yiwuwar tafiyar Jack GrealishManchester Cityza ta iya sa wa Bernardo Silva ya bar kungiyar, inda ake sa ran Barcelona da Atletico Madrid za su yi wawason dan wasan tsakiyar na Portugal mai shekara 26.(Mundo Deportivo - in Spanish)

    Ana sa ran Aston Villata nemi daukar dan wasanNorwichda Ingila Todd Cantwell, mai shekara 23, idan Grealish ya kammala tafiya Etihad Stadium a kan £100m.(Sky Sports)

    Atalanta za ta tattauna daChelseaa karshen makon nan domin duba yiwuwar kulla yarjejeniya kan dan wasan Ingila Tammy Abraham, mai shekara 23.(Gianluca di Marzo)

    Paul Pogba zai soma kakar wasan bana a Manchester United amma zai yanke shawara game da makomarsa kafin a rufe kasuwar musayar 'yan kwallo, a yayin da har yanzu PSG take son daukar dan wasan na Faransa mai shekara 28.(Telegraph - subscription required).

  19. Akalla mutum 115 jami’an tsaro suka kashe a kudu maso gabahsin Najeriya - Amnesty

    Amnesty

    Jami’an tsaron Najeriya sun aikata laifukan take hakkin dan adam karkashin dokar kasa da kasa a kokarin mayar da martani ga rikicin da ke faruwa a kudu maso gabashin kasar.

    Cikin wani rahoto da ta wallafa a shafinta, Amnesty International ta ce hakan dai wata muzgunawa ce da ake yi wa mutan yankin tun daga watan Janairu ciki har da kama mutane da dama, amafani da karfin da ya wuce iyaka, tare da azabtar da wadanda ake zargi da dai sauran laifuka.

    Quote Message: Wasu hujjoji da Amensty ta tattara sun nuna wasu hotuna masu tayar da hankali da kuma yadda dakarun Najeriya ke amfani da karfin da ya wuce iyaka a Jihar Imo da Anambra da kuma Abiam” in ji babban daraktan hukumar a Najeriya Osai Ojigho,

    Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani da kakkausan yanayi kan kisa da kuma tashin hankalin da ake alakanta shi da wani bangare na kungiyar IPOB masu rajin kafa Biafra.

    Kamar yadda jami’an gwamnati suka ce wannan kungiya ta kashe gwamman jami’anta da kuma kai hari kan gine-gine 10 na mutane ciki har da gidajen yari da ofishin ‘yan sanda daga watan Janairu zuwa watan Yuni.

    Cikin yanayin daukar mataki jami’an tsaro da suka hada da sojoji da ‘yan sanda da kuma jami’an fararen kaya DSS sun kashe gwamman masu rike da makamai da kuma fararen hula a hare haren da suka kai in ji Amnesty.

    Quote Message: Wasu da abin ya faru akan idonsu sun shaida wa Amnesty cewa, jami’an tsaro sun yi amfani da karfin da ya wuce iyaka, sun ci zarafin mutane a bayyane, sun rika kama wasu a asirce, sun tatsi kudi daga hannun wasu da dama. An ce sun sun kona gidaje kazalika sun rika yin sata da kuma kisan azarbabi, Amnesty ta wallafa.

    Kungiyar kare hakkin dan adam din ta yi kiyasin kisan da aka yi a wadannan jihohi daga watan Janairu da kuma Yuni 2021 ya kai dari.

    ‘Yan sanda sun ce mayakan sun kashe mutum 21 a Imo kadai, gamayyar ‘yan sanda da sojoji kuma sun kama mutum sama da 500 sannan ana ta yi masu zargin azabtar da mutane da yawa.

  20. Wutar dajin da ta tashi a Turkiyya ta isa tashar samar da wutar lantarki

    Getty Images

    Wata wutar daji da ta kwashe kwanaki takwas tana ci ta isa wata tashar samar da wutar lantarki a gaɓar Aegean ta Turkiyya.

    Wasu rahotanni sun ce wutar ta mamaye tashar da ke lardin Mugla.

    Tuni aka kwashe duka mutane da abubuwan da ka iya fashewa daga tashar, wadda ke aiki da kwal don samar da makamashi.

    Amma masu rajin kare muhalli sun bayyana damuwarsu inda suke tunanin cewa idan wutar ta shiga ma'ajiyar kwal da ke tashar, hakan na iya haifar da gurbatar muhalli.

    BBC