Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail da Awwal Ahmad Janyau

time_stated_uk

  1. Nan za mu rufe wannan shafin sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu

  2. An kawo ƙarshen mulkin Netanyahu a Isra'ila

    Benjamin Netanyahu

    Benjamin Netanyahu ya rasa ikonsa na shekaru 12 kan mulkin Isra'ila bayan da majalisar dokokin kasar ta kada kuri'ar amincewa da sabuwar gwamnatin haɗaka.

    Naftali Bennett na jam'iyyar Yamina zai jagoranci sabuwar "gwamnatin ta canji."

    Shi zai jagoranci gamayyar jam'iyyun da suka samu rinjayen ƙuri'a ɗaya wanda ya kai ga kawo ƙarshen mulkin Netanyahu.

    Mr Bennett zai zama Firaminista har zuwa watan Satumban 2023 ƙarƙashin tsarin karɓa-karɓa.

    Daga nan zai miƙa mulki ga Yair Lapid, shugaban jam'iyyar Yesh Atid, na tsawon shekara biyu.

    Mr Netanyahu - wanda ya fi daɗewa kan mulki a Isra'ila ya mamaye siyasar Isra'ila na tsawon shekaru.

    Yanzu zai kasance shugaban jam'iyyarsa ta Likud kuma jagoran adawa.

  3. Novak Djokovic ya lashe Roland Garros

    Djokovic

    Novak Djokovic ya zama zakara karo na 19 a manyan gasannin ƙwallon Tennis bayan ya doke ɗan wasan Girka Stefanos Tsitsipas a wasan ƙarshe da suka fafata na French Open a ranar Lahadi.

    Djokovic, mai shekara 34, wanda ya taɓa lashe Roland Garros a 2016, ya zama mutum na farko da ya lashe dukkanin manyan gasannin Tennis sau biyu tun fara gasar ƙwararru a 1968.

    Yanzu ya kusan kamo abokan hamayyarsa Rafael Nadal da Roger Federer da suka fi shi yawan lashe kofunan manyan gasar Tennis.

    Zai iya kamo Nadal da Federer da suka lashe kofi 20 idan har ya kare kambunsa a Wimbledon a wannan watan.

  4. Netanyahu na fuskantar ƙarshen wa’adinsa

    Netanyahu shi ne shugaban da ya fi daɗewa a Isra'ila
    Image caption: Netanyahu shi ne shugaban da ya fi daɗewa a Isra'ila

    Majalisar dokokin Isra’ila na tafka mahawara kan batun kafa sabuwar gwamnati da zaikawo ƙarshen mulkin shekaru 12 na Firaminista Benjamin Netanyahu.

    Gwamnatin da za a kafa za ta ƙunshi gamayyar jam'iyyun da ba a taɓa gani ba waɗanda ke da rinjayen kujera ɗaya a majalisa.

    Idan har suka yi nasara a ranar Lahadi, hakan zai kawo ƙarshen ruɗanin siyasa da ya kai ga gudanar da zaɓe sau uku.

    Ɗan kishin ƙasa Naftali Bennett na jam’iyyar Yamina ake sa ran zai zama Firaminista.

    Kuma tsarin zai kasance na karɓa-karɓa tsakaninsa da abokin ƙawancensa Yair Lapid na jam’iyyar Yesh Atid.

    Netanyahu wanda ya fi daɗewa a mulki tare da mamaye siyasar Isra’ila zai koma madugun adawa kuma shugaban jam’iyyar Likud.

  5. Mutumin da ya fi yawan mata a duniya ya mutu

    Ziona Chana yana da mata 39
    Image caption: Ziona Chana yana da mata 39

    Wani mutum a arewa maso gabashin Indiya, wanda ya fi yawan iyali a duniya, ya mutu.

    Ziona Chana mai shekaru 76, iyalinsa sun ce ya yi fama da ciwon suga da hawan jini.

    Mista Chana yana da mata 39 da yara 89 da kuma jikoki da yawa.

    Ya zauna tare da dukkanin iyalinsa a wani gida bene hawa hudu da ke wani kauye mai tsaunuka a jihar Mizoram, da ke iyaka da Myanmar.

    Jami'ai sun ce gidan ya zama wani babban wurin jan hankali ga 'yan yawon bude ido saboda yawan iyalin mutumin.

    Mista Chana ya shugabanci wata kungiyar mabiya addinin Kirista da ke ba da damar auren mata fiye da daya.

    Ya fara yin aure yana da shekara 17.

    Ziona Chana yana da ƴaƴa 94 da jikoki
    Image caption: Ziona Chana yana da ƴaƴa 94 da jikoki
  6. Ingila ta samu sa’ar Croatia 1-0

    Raheem Sterling yanzu ya ci kwallo 13 a wasa 17da ya buga wa Ingila
    Image caption: Raheem Sterling yanzu ya ci kwallo 13 a wasa 17da ya buga wa Ingila

    Ingila ta samu sa’ar Crotia ci 1-0 a fafatawar rukuni da suka yi a gasar cin kofin Turai a ranar Lahadi.

    Raheem Sterling ne ya ci wa Ingila ƙwallonta a ragar Croatia a fafatawar da ƙasashen biyu suka yi a Wembley.

    Karon farko kenan da Ingila ta lashe wasan farko a gasar cin kofin Turai a haɗuwa 10.

  7. Al'adar cirani a wajen 'yan Jamhuriyyar Nijar Kashi na 4

    Video content

    Video caption: Latsa hoton sama ku saurari shirinTaɓa Kiɗi Taɓa Karatu

    A wannan makon ta cikin shirinmu na Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu, mun kawo muku kashi na 4 na al'adar cirani a wajen 'yan Jamhuriyyar Nijar.

  8. Majalisar Isra'ila na kaɗa ƙuri'ar korar gwamnatin Netanyahu

    Netanyahu

    A yau Asabar Majalisar Wakilan Isra'ila ke kaɗa kuri'ar amincewa da sabuwar gwamnatin haɗaka wadda mai ra'ayin sassauci Yair Lapid ya yi kokarin kafawa.

    Gwamnatin ta ƙunshi jam'iyyun masu sassauci da tsattsauran ra'ayi da jam'iyyar Larabawa ta Arab Islamic Conservative.

    Idan har aka amince da hakan, wannan zai kawo karshen mulkin Firaminista Benjamin Netanyahu.

    Karkashin yarjejeniyar raba madafun iko da aka cimma, hamshakin attaijiri kuma mai tsattsauran ra'ayi, Naftali Bennett, zai zama firaminista na shekara biyu kafin daga bisani ya mika ga Mr Lapid.

    A jiya Asabar, kusan mutum 2,000 ne suka yi zanga-zanga a kofar gidan Mista Netanyahu.

  9. Ƙasashen G7 za su bayar da tallafin rigakafin korona biliyan ɗaya

    Boris Johnson

    Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya ce ƙasashen G7 za su kauce wa "son kai" wajen tunkarar annobar korona ba kamar yadda suka yi ba tun farkon ɓarkewar cutar.

    Ya bayyana haka a yau Asabar yayin kammala taron ƙasashe bakwai mafiya girman tattalin arziki da ke gudana a birnin Landan.

    Ya ce shugabannin sun yi alƙawarin bayar da tallafin rigakafin korona guda biliyan ɗaya ga ƙasashe matalauta - ko kai tsaye ko kuma ta hannun shirin Covax.

    Ya ƙara da cewa Birtaniya za ta bayar da miliyan 100 daga ciki. "Wani mataki ne babba na yi wa duniya rigakafi," in ji shi.

  10. China ta gargaɗi ƙasashen G7: 'Lokaci ya wuce da za ku dinga juya duniya'

    G7

    China ta gargaɗi ƙungiyar G7 ta ƙasashe mafiya girman tattalin arziki cewa lokaci ya wuce da wani "ƙaramin rukunin" ƙasashe zai dinga bai wa duniya umarni.

    Kalaman na jakadan China a Birtaniya na zuwa ne yayin da shugabannin da ke taro a ƙasar suka nemi a haɗa kai domin tunkarar manufofin China.

    Shugabannin sun zayyana kuɗaɗen da za su kashe domin daƙile take-taken China a faɗin duniya.

    Masana na ganin cewa Shugaban Amurka Joe Biden da gaske yake wajen ganin shugabannin Turai sun ɗauki mataki kan China.

    A yau Lahadi ake sa ran shugabannin za su sanar da ƙarin tallafi ga ƙasashe masu tasowa da ke fama da matsalolin sauyin yanayi, da kuma kuɗaɗen gudanar da ayyukan more rayuwa a matsayin kishiyar wanda Chinar ke gudanarwa.

    "Mun yi imani cewa ƙasashe komai girma ko ƙanƙantarsu, ƙarfi ko gazawarsu, arziki ko talaucinsu, duka ɗaya ne," kamar yadda Reuters ya ruwaito kakakin ofishin jakadancin China a Landan yana faɗa.

    "Haka nan, ƙasashe ne baki ɗayansu ya kamata su tattauna makomar al'amuran duniya ta hanyar tuntuɓa," in ji shi.

  11. Wani hari ya halaka mutum 13 a Syria

    Syria

    Harin makaman Atilari da aka kai wani asibiti da wata unguwa da ke arewacin birnin Afrin na kasar Syria ya hallaka akalla mutum 13, yayin da wasu gwammai suka jikkata.

    Bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna yadda gawaRwakin mutane a baraguzan ginin asibitin Al-Shifaa da ke birnin.

    Wakiliyar BBC ta ce kungiyar da ke sa ido kan rikicin Syria mai mazauni a Birtaniya ta ce cikin wadanda suka mutu har da likitan asibitin da ma'aikata uku da yara kanana guda biyu.

    Gwamnatin Turkiyya ta yi Allah-wadai da harin a birnin ke hannun 'yan tawayen da Turkiyyar ke goyon baya, ta kuma dora alhakin harin kan mayakan Kurdawa na kungiyar YPG.

    A bangare guda kuma, ƙungiyar Syrian Democratic Forces wadda YPG ke gudanarawa ta musanta kai harin.

  12. Nakiya ta kashe jami'an tsaron Ivory Coast uku

    Ivory Coast

    Akalla soja biyu da dan sanda ne suka mutu bayan motar da suke ciki ta taka nakiya a arewacin Ivory Coast kusa da iyakar kasar da Burkina Faso.

    Wasu jami'an tsaro uku sun ji mummunan rauni a harin wanda shi ne irinsa na biyu da ya faru cikin mako guda.

    A ranar Litinin din makon da ya wuce ma wani sojan kasar ya rasa ransa lokacin da wasu mahara suka far wa garin Tougbo.

    Mayakan jihadi na zafafa kai hare-hare a arewacin yankin Sahel, yayin masu aiko da rahotanni ke cewa alamu sun nuna cewa suna kara fadada ayyukansu a wannan yankin.

  13. Kwalara ta kashe mutum 37 a Jihar Bauchi - Hukumomi

    Kwalara

    Hukumar lafiya a matakin farko ta Jihar Bauchi ta ce ya zuwa yanzu mutum 37 ne cutar kwalara ta kashe a jihar.

    Kafofin yaɗa labarai sun ruwaito Rilwanu Mohammed, shugaban hukumar, yana cewa cutar ta yaɗu zuwa ƙaramar hukuma 15 na jihar.

    Ya ce daga 25 ga watan Mayun 2021, an samu mutum 1,799 da suka kamu da cutar.

    Ƙananan hukumomin da cutar ta yaɗu su ne: Bauchi; Darazo; Dass; Giade; Ganjuwa; Jama’are; Misau; Ningi; Shira; Tafawa; Balewa; Warji; Alkaleri; Kirfi, Shira, Zaki.

    "Yankunan da suka fi yawan masu cutar su ne Bauchi (1,334) da Ningi (91) Dass (60)," kamar yadda kafar TheCable ta ruwaito shi yana faɗa.

  14. Naushi da barazanar kisa na neman raba kan Afirka

    Afirka

    An samar da majalisar kishin Afirka da burin hada kan nahiyar, to amma a baya-bayannan Pan-African Parliament (PAP ) ta fada cikin rikicin da har ya sa wasu mambobinta na barazanar kashe juna.

    Rikicin na faruwa ne bayan rabuwar kai da ake ta samu kan yankin da zai fito da sabon shugaban majalisar.

    PAP na da mambobi 235, kuma 'yan majalisar daga kudancin Afrika sun kafe cewa su ne za su karbi shugabanci kasancewar an dade 'yan sauran yankunan na jagoranci.

    ''Zan kashe ka'', a cewar dan majalisa daga Afrika ta Kudu Julius Malema, yayin da yake nuna yatsa ga wani dan majalisar.

    Daga baya Mr Malema ya yi kokarin kare kansa da kan kalaman, inda ya ce shi ma an yi masa barazana ne.

    Ga cikakken labarin a nan:

  15. Hukumar NDLEA ta kama codeine kwalaba 100,000

    Wani mutum

    Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya, NDLEA, ta kama kwalaba 100,000 ta maganin tari na codeine mai nauyin jumillar kilogiram 15,325 a Jihar Rivers da ke kudancin ƙasar.

    An gano ruwan maganin tun ranar Alhamis, 10 ga Yuni wanda aka zuba a katan 500 kuma aka ɓoye shi cikin wata kwantena mai laƙabin MRKU 1565305 da nufin kayan abinci ne daga Indiya.

    Amma sai a ranar Asabar hukumar ta bayyana kamen ta bakin mai magana da yawunta Femi Babafemi cikin wata sanarwa.

    Sanarwar ta ce an gano kayan ne yayin wani binciken haɗin gwiwa tare da jami'an hukumar kwastam.

    "An gano kayan ne sakamakon wasu bayanan sirri da NDLEA ta samu, abin da ya sa aka dakatar da kwantenar kuma aka kai ta gidan kwastam da ke cikin tashar jiragen ruwan Onne," in ji shi.

  16. 'Yan bindiga sun kashe mai gadin Seini Oumarou a Nijar

    Nijar

    Wani hari da aka kai kan gidan tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Nijar, Seini Oumarou, ya yi sanadiyyar kashe jami'in tsaro ɗaya tare da jikkata wani, a cewar hukumomi ranar Asabar.

    Harin wanda ya faru a daren Juma'a, wasu mutum biyu ne a kan babur suka kai shi, kamar yadda mataimaki na musamman ga Mista Oumarou mai suna Osseini Salatou ya bayyana.

    "Sun harbe masu gadi (waɗanda ke gadin gidansa), inda suka kashe ɗaya kuma suka ji wa ɗayan mummunan rauni," in ji shi.

    Ma'aikatar harkokin wajen Nijar ta tabbatar da faruwar harin a jiya Asabar, tana mai cewa maharan sun so su tafi da wata mota da ke farfajiyar gidan kafin daga baya su gudu.

    Seini Oumarou ne ya zo na uku a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar zagayen farko a Disamban 2020, kafin daga baya ya mara wa Shugaba Mohamed Bazoum baya, wanda ya lashe zaɓen a zagaye na biyu.

  17. An yi jana'izar Musulman da aka kashe a harin ƙiyayya a Canada

    Canada

    Ɗaruruwan mutane ne suka halarci jana'izar iyalan nan Musulmai huɗu da wani mahari ya bi ta kansu da motar a kori-kura a ranar Lahadin makon da ya wuce a birnin Landan na Canada.

    Masu makokin sun taru a cibiyar Musulunci da ke birnin, inda aka ajiye akwatin da gawar mamatan ke ciki, kowanne an nannade shi da tutar kasar ta Canada, inda aka dauke su domin yi musu jana'iza.

    Lamarin ya girgiza kasar kuma Firaiminista Justin Trudeau ya kira harin da na ta'addanci.

    Ana tuhumar matashin da ya bi ta kansu mai suna Nathaniel Veltman da laifi huɗu na aikata kisa kuma a gobe Litinin zai gurfana gaban kuliya.

    Kawo yanzu yaro ɗaya da ya kubuta daga harin mai shekara tara na kwance a asibiti ana ba shi kulawar da ta dace.

    'Yan sandan ƙasar sun ce harin na ƙiyayya ne, wanda aka kai musu kawai su Musulmai ne.

  18. Ƙarin mutum takwas sun kamu da korona a Najeriya

    Korona

    Sabbin alƙaluma daga hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya sun nuna cewa mutum takwas ne suka kamu da cutar korona ranar Asabar a ƙasar.

    Hukumar NCDC ta ce sabbin kamuwar sun fito ne daga jiha biyu sannan kuma babu wanda cutar ta yi ajalinsa.

    Jihohin su ne Akwa Ibom da kuma Rivers masu mutum hurhuɗu kowaccensu.

    Ya zuwa yanzu, NCDC ta ce jumillar mutum 167,059 ne suka harbu da cutar a Najeriya, 2,117 daga cikinsu sun rasu sannan an sallami 163,436 bayan sun warke daga cutar.

  19. Maraba

    Sannunmu da shigowa wannan shafi mai kawo rahotanni kai-tsaye.

    Umar Mikail ne zai kasance da ku a wannan hantsi na Lahadi. Da fatan hutun ƙarshen mako na tafiya yadda ya kamata.