Sudan: Tsohon Firaministan kasar Sadiq al-Mahdi ya rasu

Sadiq al-Mahdi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Marigayi Sadiq al-Mahdi

Tsohon Firaministan Sudan, Sadiq al-Mahdi ya rasu, sakamakon cutar korona.

Tun a farkon watan Nuwamba tsohon Firaministan mai shekaru 84 ke jinya a Hadaddiyar Daular Larabawa.

Jam'iyyar adawa ta Umma, wadda ya jagoranta, ta mika ta'aziyyarta ga mutanen Sudan.

An hambarar da Sadiq al-Mahdi, wanda shi ne zababben Firaministan Sudan na karshe da aka zaba ta hanyar dimokiradiyya a shekarar 1989 yayin juyin mulkin da ya kawo tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir.

Marigayin jika ne ga Muhammad Ahmad, mutumin da ya jagoranci tawaye ga mulkin mallakar da Masar ta yi wa Sudan.