Tsohon gwamnan Sokoto Garba Nadama ya rasu

Nadama

Asalin hoton, NADAMA FAMILY

Bayanan hoto, Ya yi mulki a Jamhuriya ta biyu tsakanin watan Nuwamban 1981 zuwa watan Disamba 1983.

Tsohon gwamnan jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya, Alhaji Garba Nadama, ya rasu.

Alhaji Garba Nadama ya rasu ne ranar Litinin yana da shekara 82 a duniya bayan ya yi fama da gajeriyar rashin lafiya.

Garba Nadama shi ne gwamnan farar-hula na biyu da ya shugabanci jihar Sokoto.

Ya yi mulki a Jamhuriya ta biyu tsakanin watan Nuwamban 1981 zuwa watan Disamba 1983.

Ya zama gwamnan jihar ta Sokoto ne bayan mutuwar Alhaji Shehu Kangiwa.

Garba Nadama ya yi Digirin Digirgir a fannin Tarihi a Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria a shekarar 1977.

Ya bar mulki sakamakon juyin mulkin shekarar 1983 wanda ya dora Manjo Janar Muhammadu Buhari a matsayin shugaban mulkin sojin Najeriya.