Sarkin Zazzau: Obasanjo, Jonathan sun je ta'aziyyar Alhaji Shehu Idris

A yau Laraba ne aka gudanar da sadakar uku ta rasuwar sarkin Zazzau Alhaji Sehu Idris, wanda ya mutu yana da shekara 84 a duniya.

Manyan mutane ne, wadanda suka hada da tsoffin shugabannin Najeriya, da gwamnoni da shugabannin majalisar dokokin tarayya, da sarakuna da manyan jami'an gwamnati, na ci gaba da isa birnin Zazzau domin yin ta'aziyyarsa.

Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo(dama) da Gwamna Nasir El-rufai na jihar Kaduna a fadar sarkin Zazzau ranar Laraba

Asalin hoton, Twitter/@GovKaduna

Bayanan hoto, Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo (dama) da Gwamna Nasir El-rufai na jihar Kaduna a fadar sarkin Zazzau ranar Laraba
Shugaban Mjalaisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila ya jajanta wa masarautar Zazzau kan rasuwar mai martaba Sehu Idris a ziyarar ta'aziyyar da ya kai ranar Talata

Asalin hoton, Twitter/@SpeakerGbaja

Bayanan hoto, Shugaban Mjalaisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila ya jajanta wa masarautar Zazzau kan rasuwar mai martaba Sehu Idris a ziyarar ta'aziyyar da ya kai ranar Talata...
Zazzau

Asalin hoton, Twitter/@Bellomatawalle1

Bayanan hoto, ...a ranar ce tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da Gwamnan Zamfara Bello Matawalle da kuma Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Namadi Sambo a wajen ta'aziyyar marigayi mai martaba sarkin Zazzau Dokta Shehu Idris
Zazzau

Asalin hoton, Twitter/@Bellomatawalle1

Zazzau

Asalin hoton, Facebook/Sokoto State Governor's Office

Bayanan hoto, Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal tare da Mai Martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero a wajen ta'aziiyar marigayi Sarkin Zazzau a ranar ta Talata
Zazzau

Asalin hoton, Facebook/Sokoto State Governor's Office

Bayanan hoto, Ɗan siyasa Kawu Sule (tsakiya) da Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal
Zazzau

Asalin hoton, Saudat Photography

Bayanan hoto, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar Sa'ad da Mai Martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero suma sun jajanta wa Masarautar Zazzau bisa rasuwar Dokta Shehu Idris
Zazzau

Asalin hoton, Twitter/@HRH_SarkinRano

Bayanan hoto, Mai Martaba Sarkin Rano Kabiru Muhammad Inuwa a lokacin da ya kai ziyarar ta'aziyyar marigayi Dakta Shehu Idris
Zazzau

Asalin hoton, Twitter/@Hadejia_Emirate

Bayanan hoto, Mai Martaba Sarkin Gombe Dr. Abubakar Shehu Abubakar tare da Mai Martaba Sarkin Hadejia Alh. Dr. Adamu Abubakar Maje a wajen ta'aziyyar Sarkin Zazzau