Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nasidi Adamu Yahaya da Buhari Muhammad Fagge

time_stated_uk

  1. Rufewa

    A nan muka kammala bayanai da muka kwashe wunin yau muna kawo muku game da halin da duniya take ciki.

    Ku tare mu gobe da safe domin samun sabbin labarai da rahotanni.

    Kafin na, za ku iya lekawa kasa don karanta abubuwan da muka wallafa a wannan shafi tun daga safiyar yau.

    Kuna iya ci gaba da tafka muhawa da bayyana ra'ayoyinku kan dukkan labarai da rahotannin da muke kawo muku a shafukanmu na sada zumunta.

    A madadin abokin aikina Buhari Muhammad Fagge, ni ne Nasidi Adamu Yahaya nake cewa mu kwana lafiya.

  2. Abiola Ajimobi: Ganduje ya je ta'aziyya wurin surukansa

    Gwamnan jihar Kano da ke Najeriya ya kai ziyarar ta'aziyya a gidan iyalan surukinsa, Sanata Abiola Ajimobi wanda ya rasu ranar Alhamis sakamakon cutar korona.

    Bayanin da mai taimaka wa gwamnan kan shafukan zumunta Yusuf Shuwaki ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Asabar ya ce gwamnan da tawagarsa sun je gidan iyalan marigayin da ke Lagos, inda ya rasu, domin mika ta'aziyyarsu.

    Idris Ajimobi, wato dan gidan marigarin wanda kuma miji ne ga Fatima Ganduje, shi ne ya tarbi tawagar gwamnan, ciki har da mai dakinsa Hajiya Hafsatu Ganduje.

    Sanata Ajimobi wanda ya yi gwamnan Oyo na tsawon shekara takwas ya rasu yana da shekara 70 a duniya.

    View more on twitter
  3. Brazil na fafutukar samun rigakafin korona

    Gtty

    Brazil ta kulla yarjejeniyar dala miliyan 150 da kamfanin samar da magani na AstraZeneca, don samar da rigakafin annobar Korona.

    Rigakafin da jami'ar Oxford da ke Burtaniya ta samar shi ne ake yi wa kalllon wanda babu irinsa daga cikin wadanda Hukumar Lafiyar ta Duniya ta aminta da gwajinsu.

    Tuni Astrazeneca ya kulla yarjejeniyar samar da rigakafi ga kasashen India da Burtaniya da kuma Amurka.

  4. Mutum uku sun mutu bayan sun sha sinadarin wanke hannu

    Getty

    Mutum uku ne suka rasa rayukansu bayan bayan kwankwadar sinarin wanke hannu a Jihar News Mexico a Amurka, in ji hukumomin lafiyar kasar.

    Wasu karin mutum ukun na cikin mawuyacin hali wasu kuma sun samu matsalar makanta ta dindindin.

    Mai magana da yawun ma'ikatar lafiya na jihar ya ce, gubar da suka sha na da alaka da sinadarin allcohol.

    Kamar inda shi ma sinadarin wanke hannu yake da sinadarin alcohol mai yawa a cikinsa wanda kuma zai iya cutar wa idan ya shiga cikin.

    Wannan na zuwa ne jim kadan bayan hukumar abinci da magunguna ta Amurka ta yi gargadi kan siyan sinadarin wanke hannin wani kamfani da ke Mexico saboda yana dauke da sinadarin Methanol mai yawa a cikinsa.

  5. Labarai da dumi-dumiBurtaniya ta sanar da karin mutum 100 da suka mutu saboda korona

    BBC

    Sabbin alkaluman sun nuna karin mutum 100 da aka gwada suna dauke da korona sun mutu a fadin Burtaniya cikin sa'a 24.

    Wannan ne ya kai adadin wadanda cutar ta kashe a fadin kasar 43,514.

  6. 'Yan tawaye sun raunata sojin Rwanda

    BBC

    Rundunar soji Rwanda ta ce gwamman 'yan tawaye sun tsallaka iyakarta daga Burundi cikin dare tare da kai farmaki kan dakarunta.

    Kakakin rundunar ya ce an kashe hudu daga cikin 'yan tawayen, an kuma kama uku yayi da sauran suka tsere suka bar kayan aikinsu.

    Ya ce an raunata sojin Rwanda uku a harin da aka kai a gundumar Nyaruguru.

    Kasashen da ke makwabtaka da juna sun kwashe shekaru suna zargin junansu da tallafa wa kungiyoyin 'yan tawaye.

  7. Za a sallami 'ya'yan 'yan cirani daga ciboyoyin killace masu korona

    Getty
    Image caption: An ajiye yaran 'yan ciranin ne a cibiyoyikamar wannan da ke Florida

    Wata mai shari'a a babbar kotun tarayya a Amurka ta yi umarnin a saki 'ya'yan 'yan cirani 124 daga cibiyar killace 'yan ciranin da suka kamu da cutar korona a kasar.

    Cibiyoyi uku ne yaran ake killace su, wadanda suke a Kansasn da Pennsylvania da kuma Texas.

    "Asibitocin sun cika makil da masu cutar, kuma ba zai yiwu ba a rika yiwa aikin kula da yaran kafar angulu," in ji Dolly Gee.

    Ta yanke hukuncin cewa dole a saki yaran daga nan zuwa nan da tsakiyar Yuni kuma a tabbatar an basu kulawar da ta kamata.

    Wannan zai hadar da iyayen yaran da aka tsare wadanda za a saki da na'urar bibiya idan da bukatar hakan.

    Daruruwan mutane ne aka tsare a cibiyoyin wadanda aka yi wa gwaji aka tabbatar suna dauke da cutar korona, kamar yadda kafafen yada labarai na Amurka suka bayyana.

  8. Na yarda da kaddara - Adams Oshiomhole

    Getty
    Image caption: Adams Oshiomhole

    Tsohon shugaban jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya Adams Oshiomhole, ya ce ya amince da rushe kwamitin kolin jam'iyyar, wanda ya ke jagoranta gabanin dakatar da shi da majalisar koli ta yi.

    Wannan ne karon farko da tsohon shugaban ya yi magana kan rikice-rikicen jam'iyyar wadanda suka janyo rushe kwamitin kolin.

    Tsohon shugaban ya ce ba ya nadama kan dukkan abubuwan da ya aiwatar lokacin da yake jagorantar kwamitin, ya kuma yi alkawalin ci gaba da nuna goyon bayan tare da biyayya ga shugaban kasar Muhammadu Buhari.

    Oshiomhole ya ce sakamakon umarnin shugaba Buhari na cewa duka 'ya'yan jam'iyyar su janye kararrakin da suka shigar gaban kotu, shi ma ya bai wa lauyansa umarnin janye ta shi karar kan ƙalubalantar dakatar da shi daga gaban babbar kotun daukaka kara ta kasar.

  9. Dakarun Mozambique na kara kutsawa yankin Mocimboa da Praia

    EPA

    Rahotanni daga arewacin Mozambique na cewa dakarun kasar na can fafatawa da masu tsattsauran ra'ayin addini domin kwace wani gari da ke karkashin ikonsu.

    Mazauna yankin Mocimboa da Praia sun ce an fara fafatawar ne kafin wayewar gari.

    Shi ne dai garin da masu kishin addinin suka kwace mai tsahar jirgin ruwa a watan Maris, wanda wannan harin kuma kungiyar IS ce ta yi ikirarin kai shi.

    Sama da mako dakarun Mozambique na musamman suke kai hari gidaje a birnin bayan samun rahoton mayakan IS na zaune a yankin.

    Rikici a yankin da ke da gas ya fara ne tun a shekara ne tun a 2017 kuma yana ta karuwa a hankali.

    Mayakan dai sun karbe iko da garuruwa da yawa a kasar.

  10. Yadda 'yan sanda suka kashe uba da ɗansa a Indiya

    Getty

    Al'ummar India na kara harzukan kan mutuwar wani uba da ɗansa a hannun 'yan sandan yankin Tamil Nadu da ke kudancin ƙasar.

    P Jeyaraj mai shekara 58, da ɗansa Fenix ɗan shekara 38, an kama su ne bisa zargin bude shago bayan wucewar lokacin da aka yarda a bude - har yanzu ana fama da dokar kulle a Tamil domin shawo kan cutar korona.

    Duka su biyun a rufe su ne a ofishin 'yan sanda na tsawon dare da aka kama su kuma sun mutu ne cikin 'yan sa'o'i da suka kwashe na kwana biyu daga baya.

    'Yan uwan mutanen sun ce dukka sun mutu ne sakamakon zunzurutun ketar da aka yi musu.

  11. Hajj: Za a mayar wa da maniyyata Pakistan kuɗaɗensu

    Getty

    Hukumomi a Pakistan sun ce za a fara mayarwa da mutane kudaden aikin Hajjinsu daga Alhamis mai zuwa, wannan na zuwa ne bayan Saudiyya ta sanar da takaita mutanen da za su aikin Hajjin wannan shekarar saboda cutar korona.

    Mai magana da yawun ma'aikatar da ke lura da harkokin addinai ta kasar ne ya yabbaya hakan, yana cewa za a mayar da kudaden ne ta bankunan kasuwanci da ke fadin kasar.

    Kusan 'yan kasar dubu dari da tamanin ne suka shirya zuwa aikin Hajji kuma ko wanne ya biya kimanin dala 2,900 daga cikin su.

    Sama da musulmai miliyan biyu ne a fadin duniya ke zuwa aikin Hajjin ko wacce shekara.

  12. Coronavirus: Masar na ƙara sassauta dokar kulle

    AFP

    Masar ta bai wa wuraren matsa jiki da ɗakunan haska fina-finai da wuraren shan shayi damar buɗewa domin ci gaba da kasuwanci daga yau, a wani mataki na ci gaba da sassauta dokar da aka ƙaƙaba saboda cutar korona.

    Wannan matakin na zuwa ne duk da cewa adadin masu cutar na karuwa a kasar.

    An kuma ba da umarnin masalattai da coci-coci su ci gaba da gudanar da ibadunsu - amma da sharadin sanya takunkumi.

    Yadda gwamnatin Masar ke tafiyar da matsalar cutar ya janyo mata suka - har ta bangaren ma'aikatan lafiya da ke korafin basu da cikakkun kayan kariya domin tunkarar wannan annoba.

  13. Jam'iyya mai mulki a Malawi ta yi kira a soke zaben da aka yi ranar Talata

    AFP

    Jam'iyya mai mulki a Malawi ta yi kira da a soke zaben da aka yi a ranar Talata bayan korafin hare-haren da aka kai kan masu sanya idon zaben ta da ta wakilta.

    A wata wasika da ta aike wa hukumar zabe ta kasar, Jam'iyyar shugaba Peter Mutharika ta ce 'yan adawa sun shirya wasu dabarun lalata zabe kuma sun aiwatar wanda hakan ya shafi akalla mutum miliyan daya da rabi daga cikin masu zaben.

    Kuri'un da aka tattara da ba na hukumomi ba daga duka gundumomin sun nuna abokin hamayyar shugaban kasar na jam'iyyar adawa Lazarus Chakwera ne ya lashe zaben da tazara mai yawa.

    Tuni hukumar zaben kasa ta wallafa sama da rabi na sakamakon da aka tattara, tare da bai wa Mista Chakwera damar bai wa shugaba Mutharika umarni.

    Tuni dai abokan hamayyar shugaban suka fara murnan lashe zabe.

  14. Murnar lashe Premier ta janyo rikici a Liverpool

    PA MEDIA

    Magajin garin Liverpool Joe Anderson ya yi alawadai da abin kunyar da magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool suka janyo wa birnin a dare na biyu na murnan lashe Premier da kungiyar ta yi.

    'Yan sanda da 'yan siyasa sun ta shawartar magoya bayan da su zauna a gida bayan an bayyana kungiyar a matsayin wadda ta lashe gasar a karon farko cikin shekara 30.

    Magajin garin Anderson ya ce "ran shi ya baci kuma ya yi matukar fusata" da taron da magoya bayan suka yi wadnda suka rika shan barasa kuma suna cinna wuta a ranar Juma'a.

    Ya ce kamata ya yi a ce 'yan sanda sun dauki matakin gaggawa kan batun, tun da wannan taron na jiya dama an tsara shi.

    "Damuwar anan ita ce me ya hana shirya wani abu don tukarar taro," ya shaida wa BBC.

    Ya kara da cewa " Garinmu na fuskatar matsalar lafiya kuma ba za mu yarda da irin wannan dabi'ar ba."

    Ya kamata 'yan sanda su fito su tarwatsa taron domin tsare lafiyar al'umma.

  15. Trump ya bayar da umarnin daure masu tumɓuke mutum-mutumi

    Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan wata dokar shugaban kasa wacce za ta sa a daure masu zanga-zanga idan suka tumbuke mutum-mutumin shahararrun mutane.

    Dokar ta bukaci a "dauki tsattsauram matakin hukunta" kan duk wanda ya tumbuke ko ya lalata mutum-mutumin da aka kafa a wuraren da jama'a suke zuwa.

    Dokar ta Mr Trump ta kuma bukaci gwamnatin tarayya ta rke kudaden kananan hukumomi da rundunonin 'yan sandan da suka gaza hana 'yan ta-more tumbuke mutum-mutumai.

    An tumbuke mutum-mutuman fitattun mutane da dama a Amurka tun lokacin da aka soma zanga-zangar kyamar wariyar launin fata sakamakon kisan da 'yan sanda suka yi wa wani bakar fata da ba ya dauke da makami mai suna George Floyd.

    Shugaban kasar ya bayar da umarnin ne ranar Juma'a da almuru bayan ya soke shirinsa na zuwa wurin buga wasan kwallon golf dinsa da ke Bedminster, a New Jersey, inda ya wallafa sakon Twitter da ke cewa zai zauna a Washington DC domin ya tabbatar an "bi DOKA da ODA".

    View more on twitter
  16. Maradona na son dauko Ronaldinho, Arsenal na son Partey

    KocinArsenalMikel Arteta ya kasa ba dan wasansa Matteo Guendouzi tabbacin cewa zai bar kulub din a karshen kaka bayan dan wasan tsakiyar na Faransa ya nuna yana son barin kungiyar.(Guardian)

    Manchester Unitedta shiga sahun manyan kunhiyoyin da ke neman Guendouzi, kamar yaddaBarcelonadaParis St-GermaindaInter Milanda kumaAtletico Madriddukkaninsu suka nuna sha'awar dan wasan na tsakiya.(L'Equipe, via Mail)

    Celticna tunanin dauko Joe Hart, mai shekara 33, bayanBurnley,ta rabu da shi idan kuma har kungiyar ta Scotland ta kasa samun dauko aron golan Ingila Fraser Forster, mai shekara 32, dagaSouthampton.(Telegraph)

    Arsenalna sanya ido kan dan wasan tsakiya Danilo Pereira, indaPortota nuna za ta karbi fam miliyan 20 kan dan wasan mai shekara 28, yayin da kuma Arsenal ta ke son dauko dan wasanAtletico Madridda Ghana Thomas Partey, mai shekara 27.(ESPN)

    Maradona
  17. Babu 'wanda ya kamu da cutar korona' a Kano ranar Juma'a

    View more on twitter

    Gwamnatin jihar Kano da ke Najeriya ta yi ikirarin cewa babu mutumin da ya kamu da cutar korona a jihar ranar Juma'a.

    A sakon da ma'aikatar lafiyar jihar ta wallafa a shafinta na Twitter da tsakar daren ranar, ta ce cikin ba a samu ko da mutum daya da ya harbu da cutar ba cikin mutum 154 da aka yi wa gwaji ranar

    Ta kara da cewa an sallami karin mutum 25 bayan sun warke daga cutar, don haka yanzu masu dauke da cutar jumulla su ne 322 inda kuma cutar ta yi ajalin mutum 51.

    A makon jiya ne Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar ta Kano ya musanta rahoton gwamnatin tarayyar kasar da ya gano cewa cutar korona ce ta yi ajalinkashi 50 zuwa 60 cikin 100 na mutanen da suka mutu a baya bayan nan.

    Tun da fari, Ministan Lafiya na Najeriya Osagie Ehanire ya bayyana wa manema labarai a Abuja cewa binciken da tawagar gwamnatin tarayya ta gudanar game da ƙaruwar mace-mace a jihar Kano ya nuna cewa mutum 979 ne suka mutu a kwanan nan sanadin mace-macen da ba a saba gani ba a jihar.

    Ganduje
  18. Coronavirus: Amurka tana cikin 'gagarumar matsala'

    Shugaban hukumar yaki da cutua masu yaduwa ta Amurka Dr Anthony Fauci ya ce kasar tana cikin "gagarumar matsala" a yayin da aka samu karuwa mai yawa ta mutanen da cutar korona ta kama a jihohi 16 na kasar.

    A taron da aka gudanar karon farko cikin wata biyu a fadar White House na kwamitin yaki da cutar korona, Dr Fauci ya ce: "Hanya daya kawai da za mu bi wajen kawo karshen wannan cuta ita ce mu hada hannu ba tare da kowa ya yi gaban kansa ba."

    A yayin da masana kiwon lafiya ke cewa akwai bukatar zage damtse wurin shawo kan cutar, mataimakin shugaban Amurka Mike Pence ya yaba wa kasar kan ci gaban da ya ce an samu a yaki da ita.

    Karin mutum 40,000 ne suka harbu da cutar korona a fadin Amurka ranar Juma'a.

    Alkaluman da Jami'ar Johns Hopkins University ta fitar sun nuna cewa mutum 40,173, ne suka kamu da cutar a ranar, wanda shi ne adadi mafi girma da aka samu a rana daya a kasar.

    An tabbatar mutum fiye da miliyan biyu da dubu 400 sun kamu da cutar korona a fadin Amurka inda ta yi ajalin mutum fiye da mutum 125,000 - sama da kowacce kasa a duniya.

    An sanmu karuwa sosai na wadanda suka kamu da cutar korona a Texas
  19. Barkanmu da wannan lokaci

    Nasidi Adamu Yahya

    BBC Hausa, Abuja

    Barkanmu da safiyar Asabar. Nasidi AdamuYahaya ne yake tare da ku a wannan lokaci.

    Muna fatan za ku kasance tare da mu tsawon wannan wuni domin sanin halin da duniya take ciki.

    Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.

    Za ku iya tafka muhawara da bayyana ra'ayoyinku a shafukanmu na sada zumuna a BBC Hausa.