Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nabeela Mukhtar Uba da Mustapha Musa Kaita

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Mustapha Musa Kaita

    Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu Litinin za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan shafin a yau:

    Za ku iya duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da ma wasu muhimmai.

  2. Birtaniya ta jinjina wa Najeriya kan zaɓen Edo

    Gwamnatin Birtaniya ta jinjina wa Najeriya kan zaben Edo da aka gudanar a ranar Asabar.

    Jakadiyar ƙasar a Najeriya Catriona Laing ce ta wallafa hakan a shafinta na Twitter, inda ta ce an gudanar da sahihin zaɓe, kuma duka 'yan takarar na kira da a rungumi zaman lafiya.

    Ta kuma gode wa ƙungiyoyi masu zaman kansu dangane da irin gudunmawar da suka bayar a lokacin zaɓen.

    A yau ne dai hukumar INEC a ƙasar ta sake tabbatar da Godwin Obaseki na Jam'iyyar PDP a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Edo a karo na biyu, bayan ya doke abokin hamayarsa na Jam'iyyar APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu.

    View more on twitter
  3. Sudan za ta tattauna da Amurka a Daular Larabawa

    Sudan ta ce tawagar wakilanta ta tafi Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa domin tattaunawa da jami’an Amurka a yayin da take ƙoƙarin ganin an cire ta daga cikin jerin sunayen ƙasashen da Amurka ta zayyana suna tallafa wa yan ta’adda.

    Janar Abdel Fattah al-Burhan ne ke jagorantar tawagar wakilan na Sudan.

    A 1993, Amurka ta saka sunan Sudan cikin masu taimaka wa ta’addanci saboda goyon bayanta ga mayaƙan da ke iƙirarin jihadi, ciki har da Osama bin Laden wanda ya shafe shekara 5 a ƙasar.

    A tattaunawar, Amurka ta buƙaci Sudan ta biya sama da miliyan 300 a matsayin diyya ga iyalan waɗanda aka kashe a hare-haren ta’ddanci.

    Sannan Amurka za ta yi amfani da damar domin janyo ra’ayin Sudan ta sasanta da Isra’ila

  4. Tattaunawa da Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore

    Video content

    Video caption: Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraren shirin
  5. Yadda jama'ar Edo ke murnar lashe zaɓen da Obaseki ya yi

    Video content

    Video caption: Latsa alamar hoton da ke sama don kallon bidiyon
  6. Shugaban Majalisar Dattawa ya yi ta'aziyya bisa rasuwar Sarkin Zazzau

    ..

    Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan, ya aika saƙon ta'aziyyarsa ga jama'ar Zazzau bisa rasuwar sarkin a yau Lahadi.

    A wani saƙo da shugaban ya wallafa a shafinsa na Twitter, Lawan ya kuma miƙa ta'aziyyarsa ga jama'ar jihar Kaduna kan rasuwar Alhaji Shehu Idris, ɗaya daga cikin manyan sarakunan Najeriya.

    "A lokacin mulkinsa, marigayin ya yi amfani da basira da kuma darajarsa wajen kawo zaman lafiya da kuma ci gaban Masarautar Zazzau.

    "Za a ci gaba da tunawa da shi saboda matsayinsa da gaskiyarsa da kuma soyayyar da ya yi wa mutanensa da son ci gabansu a lokacin da yake raye," in ji Lawan.

  7. An gudanar da jana'izar Marigayi Sarkin Zazzau Shehu Idris

    ...

    An gudanar da jana'izar Marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris a fadarsa da ke Zaria.

    Dubban jama'a ne suka halarci jana'izar sarkin, ciki har da sarakuna da manyan malamai da manyan ma'aikatan gwamnati.

    An gudanar da jana'izar ne a cikin gida sakamakon dubban jama'a da suka cika wajen fadar maƙil.

    Sarkin dai ya rasu yana da shekara 84, ya kuma shafe shekara 45 kan karagar mulki.

  8. Yadda mutane suka cika Fadar Sarkin Zazzau

    ..
  9. Hotuna: Jama'a sun cika maƙil wajen jana'izar Sarkin Zazzau

    ..
    ..
    ..
  10. Buhari ya yi wa Obaseki na PDP murnar lashe zaɓe

    ....

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yaba wa tsarin zaɓen jihar Edo, wanda Godwin Obaseki na PDP ya yi nasara.

    A wata sanarwa da mai ba magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya fitar, shugaban ya taya wanda ya samu nasara murna sannan ya buƙace shi da ya nuna halin sanin yakamata da tawali’u a nasarar tasa.

    Ya kuma ce alwashin da ya sha kan batun gudanar da zaɓe mai gaskiya da adalci na nan daram.

  11. Buhari ya jajanta wa mutanen Kaduna kan rasuwar Sarkin Zazzau

    ..

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana kaɗuwarsa da alhinin rasuwar mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, kamar yadda wani saƙon ta'aziyya da mai taimaka wa shugaban kan harkokin watsa labarai Garba Shehu ya fitar.

    Saƙon ta’aziyyar, wanda shugaban ya aika wa Gwamna El-Rufa’i da kuma mutanen jihar Kaduna, Buhari ya ce Najeriya ta yi babban rashin ɗaya daga cikin sarakunan gargajiya da suka daɗe.

    Ya kuma ce ba za a taɓa mantawa da gudunmuwar da Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ya bayar wajen tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya tsakanin ƴan Najeriya ba a shekaru masu zuwa.

    Shugaban ya kuma yi roƙon Allah ya gafarta wa marigayin, Ya kuma ba iyalansa da waɗanda suke ƙarƙashinsa juriyar babban rashin da suka yi.

  12. Hotuna: Yadda jama'a suka fara taruwa a Masarautar Zazzau kafin jana'izar sarki

    ..
    ..
  13. Gawar Marigayi Sarkin Zazzau Shehu Idris ta isa Zaria

    ..

    Da yammacin yau ne Gawar Marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ta isa Zaria, inda ake sa ran za a gudanar da jana'izar sarkin da misalin ƙarfe biyar na yammaci.

    Sarkin ya rasu ne a yau Lahadi, a asibitin sojoji na 44 da ke birnin Kaduna.

    Sarkin ya rasu yana da shekaru 84, ya kuma shafe shekaru 45 kan karagar mulki.

  14. Hotuna: Yadda ƙafa ta ɗauke a gidan Ize Iyamu

    Edo
    Edo
    Edo
    Edo
    Edo
  15. Obaseki ya yi jawabi bayan lashe zaɓe

    Godwin Obaseki wanda hukumar INEC ta sanar a matsayin wanda ya ci zaɓen gwamna na Edo ya gabatar da jawabi inda ya godewa al'umar jihar bisa zaɓensa domin ya sake jagorantar jihar a zango na biyu.

    "Al'umar Edo sun bayyana zaɓinsu" a cewar Obaseki.

    Obaseki ya kuma gode wa Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari bisa kare dimukraɗiyya tare da bai wa INEC da hukumomin tsaro damar gudanar da aikinsu ba tare da yi musu katsalandan ba.

    Obasekin ya bayyana haka ne cikin wani jawabin kai-tsaye da ya yi wanda aka nuna ta shafin PDP da ke Tuwita

    View more on twitter
  16. Obaseki ya lashe zaɓen Edo

    Edo

    Baturen zaɓen gwamna na jihar Edo, Farfesa Rim-Rukeh ya sanar da gwamna Godwin Obaseki na Jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen da aka gudanar bayan da ya samu ƙuri'u 307,955.

  17. An kammala tattara sakamakon zaɓen Edo

    Edo

    Baturen zaɓe na hukumar INEC Farfesa Rim-Rukeh ya bayyana taƙaitaccen bayani kan zaɓen gwamna na jihar Edo.

    A cewarsa, yawan mutanen da aka tantance a zaɓen sun kai 557,443 sai halastattun ƙuri'u da suka kai 537,407.

    A cewarsa, ƙuri'un da suka lalace sun kai 12,835 inda a jumulla ake da 550,242 a matsayin yawan ƙuri'un da aka kaɗa.

    Ya kuma bayyana yawan ƙuri'un da APC da PDP da SDP da kuma LP suka samu a zaɓen.

    APC: 223,619

    LP: 267

    PDP: 307,955

    SDP:323

  18. Ana dakon sanarwar INEC kan wanda ya lashe zaɓen gwamna na Edo

    A halin da ake ciki, an bayyana dukkanin sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi 18 da ke jihar ta Edo.

    Ana dakon sanarwar baturen zaben hukumar INEC kan wanda ya lashe zaben gwmana na jihar Edo wanda aka gudanar jiya Asabar.

    Ga yadda sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin yake:

    Karamar Hukumar EGOR

    APC: 10202

    PDP: 27621

    Karamar Hukumar OWAN EAST

    APC: 19295

    PDP:14762

    Karamar Hukumar OVIA NORTH EAST

    APC: 9,907

    PDP: 16,987

    Karamar Hukumar ETSAKO WEST

    APC: 26,140

    PDP: 17,959

    Karamar Hukumar ESAN WEST

    APC: 7,189

    PDP: 17,434

    Ƙaramar Hukumar ESAN SOUTH EAST

    APC: 9237

    PDP: 10563

    Ƙaramar Hukumar OREDO

    APC: 1836

    PDP: 43498

    Ƙaramar Hukumar IKPOBA OKHA

    APC: 18218

    PDP: 41030

    Ƙaramar Hukumar IGUEBEN

    APC: 5199

    PDP: 7870

    Ƙaramar Hukumar OWAN WEST

    APC: 11193

    PDP: 11485

    Ƙaramar Hukumar ESAN CENTRAL

    APC: 6719

    PDP: 10794

    Ƙaramar Hukumar ESAN NORTH EAST

    APC: 6556

    PDP: 13579

    Ƙaramar Hukumar UHUNMWODE

    APC: 5972

    PDP: 10022

    Ƙaramar Hukumar AKOKO EDO

    APC: 22963

    PDP: 20101

    Ƙaramar Hukumar ETSAKO EAST

    APC: 17011

    PDP: 10668

    Ƙaramar Hukumar ETSAKO CENTRAL

    APC: 8359

    PDP: 7478

    Ƙaramar Hukumar ORHIONMWON

    APC: 10458

    PDP: 13445

    Ƙaramar Hukumar OVIA SOUTH WEST

    APC: 10636

    PDP: 12659

  19. Sakamakon zaɓen Ƙaramar Hukumar Ovia South West

    Edo

    APC: 10636

    PDP: 12659