Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Awwal Ahmad Janyau da Buhari Muhammad Fagge

time_stated_uk

  1. Ban kwana

    Nan muka kawo karshen labarai da rahotannin da muke kawo muku na wannan rana.

    Buhari Muhammad Fagge ke fatan sake saduwa da ku a gobe.

  2. Hukumar NDLEA ta ce ta kama kwayoyin biliyan 10 a Kano da Legas

    NDLEA

    Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce ta kama wasu kwayoyi da suka kai darajar naira biliyan 10 a filayen jirgin saman Murlata Muhammed da ke Legas da kuma na Mallam Aminu Kano da ke jihar ta Kano.

    Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin hukumar Femi Babafemi ya ce an gano kayan ne a cikin wani jirgin daukar kaya da ya taso daga Afrika Ta Afrika da kuma na Habasha.

    A cewar sanarwar yayin wani bincike da jami'an hukumar suke yi an gano wasu abubuwa da ke cikin wata jaka da ake kira da Ghana-must-go.

    "Yayin wata tattaunawa da aka yi da wadanda ake zargi, wani jami'i ya kara gano wasu mutane shida da ake zargi tare da wasu kaya da aka auna aka ga kwayoyi ne da suka kai nauyin kilogiran 24.05.

    "Kazalika an akara kama wasu kayan masu nauyin kilogiram 1.25 wanda hakan yakai kayan da aka kama 25.3kg.

    "Jirgin dai ya iso Najeriya ne ranar 16 ga wtaan Afrilun da muke ciki kuma an gudanar da binciken da ya kamata a kanshi," in ji sanarwar.

    An kuma kara kama irin wadannan kwayoyi a Kano da aka yi shirin fitar da su Manchester, wadanda suka kai nauyin kilogiram 36, hakan ya kai kayan da aka kama duka zuwa 63kg.

    View more on twitter
  3. Manchester City ta lashe Caraboa na hudu a jere

    Getty Images

    Manchester City ta lashe Caraboa Cup na bana, bayan da ta yi nasarar doke Tottenham da ci 1-0 ranar Lahadi a Wembley.

    Sauran minti takwas a tashi daga wasan ne City ta ci kwallo ta hannun Aymeric Laporte.

    An buga wasan karshen da 'yan kallo sama da dubu bakwai a gwajin da ake yi ko magoya baya za su iya shiga stadiya nan gaba.

    Sabon koci, Ryan Mason ne ya ja ragamar Tottenham wadda ta sallami Jose Mourinho ranar Lahadi, bayan da kungiyar ke mataki na bakwai a kan teburin Premier.

    Wannan ne karo na hudu a jere da City ta dauki kofin na takwas jumulla, inda ta yi kan-kan-kan da Liverpool wadda itama keda takwas a tarihi.

  4. An nadi muryar Javad Zarif na sukar Janar Qassem Soleimani

    Getty Images

    Wani sauti da aka nada ya ambato ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif na sukar rundunar tsaron kasar ta musamman kan tsaikon da ta ke kawo wa harkar diflomasiyya.

    Sautin ya ambato shi yana sukar Janar Qassem Soleimani, wanda Amurka ta kashe bara.

    Mr Zarif ya ce Janar Soleimani ya tursasa shi daukar wani mataki da cutar wane ga tsarin Diflomasiyyar Iran.

    To sai dai ma'aikatar harkokin wajen Iran ta ce an shirya sautin ne da nufin bata sunan ministan.

  5. Mutum daya ya mutu an sace da yawa a harin da yan bingida suka kai coci a Kaduna

    Getty Images

    Kwana biyu bayan kashe uku daga cikin daliban Jam'ar Greenfield ta Kaduna, yan bindigar sun kai hari wata coci tare da kashe wani likita suka kuma sace mutane da dama.

    Rahotanni sun ce 'yan bindigar sun zagaye cocin ne da misalin karfe 9 na safe a kauyen Manini Tasha da ke karamar hukumar Chikun a jihar.

    An ruwaito cewa likitan da aka kashe mai suna Dakta Zakariah Dogo Yaro,na aiki ne da ma'aikatar lafiya ta Kaduna, kuma sun kada mutane da yawa sun tafi da su.

    Wani da ya ga faruwar lamarin ya shaida wa jaridar The Nation cewa "mutanen sun kama harbi ne kan me uwa da wabi kan ya samu ya sha da kafarsa".

    Kamar yadda ya shaida wa jaridar mutane da dama sun jikkata yayin harin.

    Da yawan daga cikin mazauna kauyen sun gudu sun bar muhallansu, saboda yawan hare-haren da ake kai musu.

  6. Gobara ta kashe mutum 82 a Iraki

    GETTY IMAGES

    Akalla mutun 82 sun mutu a Iraqi yayin da sama da dari suka samu raunuka bayan mummunar gobara da ta tashi a wani asibiti da ke Bagdaza babban birnin kasar.

    Mafi yawan wadanda suka mutu majinyatan cutar Korona ne.

    Rahotanni sun ce gobarar ta tashi ne bayan da wani tankin iskar shaka ya fashe.

    Tuni Firanminista Mustapha al-Kadhimi ya dakatar da ministan lafiyan kasar, yayin da al'umma ke ci gaba da nuna bacin rai kan abin da ya faru.

  7. Afghanistan ta ce 'yan Taliban 20 sun mutu a wani wurin da suke hada bam

    BBC

    Gwamnan lardin Herat a Afghanistan ya ce akalla mutum 20 ne 'yan kungiyar Taliban ne suka mutu a wata fashe wa da aka samu a wurin da ya kira kamfanin hada bam.

    Hakan ya faru ne a yankin da Taliban din ke iko da shi da ke tsakiyar Pashtun Zarghun a Herat.

    An ruwaito cewa mayakan na kokarin hada bam din kunar bakin wake.

    Har yanzu dai kungiyar ba ta ce komai ba game da batun.

    Wannan dai na zuwa ne lokacin da kwamandan Amurka a kasar ke nuna damuwa kan karuwar hare-hare da tashe-tahsen hankula a kasar.

  8. A hubbaren gidan Sarkin Kano za a binne Mai Babban Ɗaki

    Majalisar masarautun jihar Kano ta ce ana dakun isowar gawar Mai Babban Ɗakin Kano Hajiya Maryam Ado Bayero a ranar Lahadi bayan Sallar Magariba.

    Mai Babban Ɗakin Kano ta rasu ne a ranar Asabar a ƙasar Masar.

    Sanarwar da majalisar masarautun Kano ta fitar da ke dauke da sa hannun Madakin Kano ta ce a ranar Litinin misalin ƙarfe 11:00 na safe za a yi jana’izarta a ƙofar kudu fadar Sarkin Kano

    “Za a binne ta ne a hubbaren gidan Sarkin Kano,” in ji sanarwar.

    Hajiya Maryam Bayero matar marigayi Sarkin Kano Ado Bayero mahaifiya ce ga Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da kuma Sarkin Bichi Nasir Ado Bayero.

    Sanarwar majalisar masarautun Kano
  9. Yariman Saudiyya ya zanta da Mahamat Idriss Deby

    Yariman Saudiyya mai jiran gado Mohammed bin Salman bin Abdulaziz da mataimakin Firaminista da kuma ministan tsarp sun tattauna da shugaban sojin Chadi Mahamat Idriss Deby. Ta wayar tarho a ranar Lahadi.

    Kamfanin dillacin labaran Saudiyya SPA ya ce Yarima bin Salman ya yi wa Janar Mahamat Deby ta’aziyyar rasuwar mahaifinsa Idriss Deby wanda ya rasu a ranar Litinin sakamakon samun raunika a fagen daga.

    Yariman ya yi wa Chadi fatan ɗorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali.

    A nasa ɓangaren kuma Janar Mahamat ya gode wa Yariman kan karamcin da ya nuna masa.

    Janar Mahamat Deby shugaban riƙo na Chadi
  10. Filin Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu

    Video content

    Video caption: Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu 25/04/2021
  11. Ga ƙasashen da ba su san Maleriya ba tsawon shekaru 20

    Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce duk minti ɗaya zazzabin maleriya na kisan yaro ɗaya.

    WHO ta bayyana haka ne a yayin da ake bikin ranar yaƙi da cutar maleriya a duniya.

    Hukumar ta ce a 2019 cutar maleriya ta kashe kusan mutum 400,000 a ƙasashe 87, kuma ta fi kashe yara ƴan ƙasa da cewa biyar.

    Albarkacin ranar WHO ta bayyana jerin ƙasashe 11 da ba su san cutar maleriya ba tsawon shekaru 20.

    Ƙasashen sun ƙunshi Algeria da Argentina da Armenia da El Salvador da Kyrgystan da Morocco da Paraguay da Sri Lanka da Turkmenistan da Daular Larabawa da kuma Uzbekistan.

    View more on twitter
  12. Mutum 19 sun kamu da korona a Yobe

    Sabbin alƙalumman da hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa NCDC a Najeriya ta fitar sun nuna cewa an samu ƙarin mutum 51 da suka kamu da korona a ranar Asabar.

    .Alƙalumman sun nuna cewa mutum 19 cutar ta kama a jiyar Yobe a ranar Asabar.

    Cutar ta kama ƙarin mutum 17 a jihar Legas inda cutar ta fi ƙamari , yayin da jihar Ribas aka samu ƙarin mutum 18.

    Alƙalumman sun nuna tun ranar 12 ga watan Afrilu cutar ba ta yi kisa ba har zuwa ranar 24 ga watan.

    View more on twitter
  13. Faston da ya gina masallaci a Adamawa

    A makon da ya gaba ta ne a wani abu da ba a saba gani ba a kasa irin Najeriya, aka bude wani masallaci a hukumance wanda wani malamin addinin kirista ya gina wa 'yan gudun hijira mabiya addinin Musulunci domin gudanar da ibada.

    Faston na cocin katolika wanda shi ne shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya ta CAN a jihar Adamawa, Most Reverend Stephen Dami Mamza, ya ce ya gina masallacin ne wanda ya cinye sama da Naira miliyan biyar da rabi domin ba Musulmi daga cikin 'yan gudun hijiran damar gudanar da addininsu ba tare da wata tsangwama ba.

    A filin mu na Gane Mini Hanya na wannan makon, abokin aikin mu Salihu Adamu Usman ya kasance daya daga cikin wadanda suka halarci sallar farko a masallacin, sannan ya hada mana rahoto na musamman.

    Video content

    Video caption: Filin Gane Mini Hanya
  14. An kama mutumin da ya shafa wa mutum 22 cutar korona

    An kama wani mutum a Spain da ake zargi da cin zarafi bayan ya yaɗa wa mutum 22 cutar korona.

    Mutumin mai shekara 40 an yi zargin cewa ya ci gaba da zuwa wurin aikinsa da kuma motsa jiki duk da yana tari kuma zafin jikinsa ya kai sama da 40C.

    An bayyana cewa yana yawonsa a wurin da yake aiki a Majorca, yana cire takunkumi idan zai yi tari tare da faɗa wa abokan aikinsa cewa zai shafa masu korona.

    Abokan aikin biyar da wasu mutum uku a wurin da yake zuwa motsa jiki sun kamu da cutar.

    Wasu mutum 14 cikin ƴan uwansa sun kamu da cutar ciki har da ɗan shekara ɗaya.

    Ƴan sandan Spain cikin wata sanarwa sun ce mutumin ya daɗe da nuna alamun cutar, amma ya ƙi killace kansa a gidansa da ke Manacor.

    An yi masa gwaji, amma ya ci gaba da wurin aiki da motsa jiki yayin da yake jiran sakamako ya fito.

    Ƴan sandan sun ce ya bijerewa abokan aikinsa da ke faɗa masa ya tafi gida. Yana cire takunkumin fuska sai ya yi tari ya fada masu cewa “zan shafa maku cutar korona.”

    Annobar korona
  15. Ƴan tawayen Chadi sun yi tayin sasantawa

    'Yan tawaye a arewacin Chadi da sojojin ƙasar suka zarga da kashe shugaba Idris Deby sun ce a shirye su tsagaita wuta da kuma tattauna batun sasantawa a siyasance, a cewar kakakin ƴan tawayen a ranar Lahadi.

    Ƴan tawayen FACT a Chadi da ke arewacin Chadi kan iyaka da Libya a ranar 11 ga Afrilu suka tunkari N'Djamena, suna kiran kawo ƙarshen mulkin Idriss Deby na shekaru 30.

    Sun kusan shiga N'Djamena, kusan tazarar kilomita 200 zuwa 300 kafin sojoji suka kore su.

    An kashe Idriss Deby a ranar Litinin yayin da ya kai wa sojojin Chadi ziyara a fagen daga.

    Mutuwarsa ta girgiza ƙasashen Tsakiyar Afrika da yankin Tafkin Chadi da Sahel saboda rawar da yake takawa ga yaƙi da ƴan bindiga.

    Kakakin FACT Kingabe Ogouzeimi de Tapol ya shaida wa Kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa a shirye suke su tsagaita buɗa wuta da kuma tattaunar da ta mutunta ƴancin Chadi ba juyin mulki ba.

    Bayan mutuwar Deby, Sojojin Chadi suka kwaci mulki inda suka ɗora ɗansa Mahamat Idriss

    Deby tare da alƙawalin zai yi riƙon ƙwarya na watanni 18 kafin gudanar da zaɓe. Matakin da ƴan adawa da ƴan tawaye suka kira juyin mulki.

    Sojojin Chadi sun kori ƴan tawaye bayan sun yi ƙoƙarin shiga N'Djamena
    Image caption: Sojojin Chadi sun kori ƴan tawaye bayan sun yi ƙoƙarin shiga N'Djamena
  16. Ƴan ƙwallon ƙafa a Ingila za su ƙaurace wa kafofin sada zumunta

    Ƙungiyoyin da ke buga gasar wasannin ƙwallon ƙafa a Ingila za su ƙaurace wa amfani da shafukan sada zumunta na Twitter daFacebook da Instagram a ranar Juma’a don neman shafukan su ɗauki matakan magance amfani da su da ake ana cin zarafi.

    Za su ƙauracewa shafukan na tsawon kwana hudu.

    Kungiyoyin kwallon kafa na mata da na maza za su shiga wannan yajin aikin, dama hukumomin dake shirya gasanni daban daban na ƙasar.

    Sun ce suna son nuna wa kamfanonin sadarwar fushinsu

    An sha aikawa manyan ‘yan wasa saƙwannin barazana da wariyar launin fata, duk da cewa kamfanonin sun yi yi alƙawarin ɗaukar mataki.

    Ƴan ƙwallon za su ƙauracewa Facebook da Twitter da Instagram na tsawon kwana huɗu
    Image caption: Ƴan ƙwallon za su ƙauracewa Facebook da Twitter da Instagram na tsawon kwana huɗu
  17. WHO ta yi kiran a ƙara yin ƙoƙarin kawar da zazzabin Maleriya

    Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi kira da a sake kokarin ganin an kawar da zazzabin cizon sauro wato Maleriya.

    Hukumar na wannan roƙo ne yayin ranar yaki da cutar ta duniya da ake gudanarwa a yau Lahadi.

    Cutar na kashe sama da mutane 400,000 duk shekara yawancinsu kananan yara.

    WHO ta ce aƙalla ƙasashe ashirin da biyar da suka hada da Botswana da Thailand da Afirka ta Kudu na da damar kawar da zazzabin cizon sauro a cikin shekaru biyar masu zuwa.

    Gwajin farko da aka yi wa wani rigakafin cutar da aka samar a Birtaniya ya sake bayar da ƙwarin guiwar yaki da ita, sakamakon yadda tasirin rigakafin ya kai kashi 77 cikin 100.

  18. Maraba

    Muna maku maraba da kasancewa a cikin wannan shafin wanda za mu kawo labarai da rahotanni kai tsaye daga BBC Hausa kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Sai ku kasance da mu.