Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail da Haruna Kakangi

time_stated_uk

  1. Karshe!

    Nan muka kawo karshen rahotanni da muke kawowa kai-tsaye a wannan shafi game da zaben gwamna a jihohin Kogi da Bayelsa.

    Mun gode!

  2. Zaben Bayelsa bai inganta ba - CDD

    Cibiyar Demokradiyya da Ci gaba ta Najeriya CDD ta ce yin amfani da aka yi da 'yan bangar siyasa wurin tayar da hankali da sata da kuma lalata kayan zabe a jihar Bayelsa sun raunana duk wani sakamako da zai fito na zaben gwamnan jihar.

    A cikin rahoto na farko-farko da ta fitar ta bakin shugabarta Idayat Hassan, CDD ta ce mummunan tashin hankali da aka tsara kuma aka tayar da gangan a rumfunan zabe da dama, sun hana mutane fitowa domin kada kuri'a domin tsira da rayukansu.

    A karshen rahoton nata kungiyar ta CDD ta ce da alama zabe a Najeriya ya koma na a-mutu ko a yi-rai, kuma akwai jan aiki gaba kafin a magance wannan matsala.

    Rahotanni sun ce an samu tashe-tashen hankula a zaben Bayelsa
    Image caption: Rahotanni sun ce an samu tashe-tashen hankula a zaben Bayelsa
  3. Mutane suna dakon sakamakon zaben Kogi da Bayelsa

    Al'ummar Kogi da Bayelsa na dakon sakamakon zaben gwamnoni da za su ja ragamar jihohin na wa'adin shekaru hudu masu zuwa.

    A jihar Kogi, fafatawa ce tsakanin 'yan takara guda 24.

    Sai dai hamayya ta fi zafi ne tsakanin gwamnan jihar Yahaya Bello na jam'iyyar APC, wanda ke neman a zabe shi a wa'adi na biyu, da kuma Musa Wada na jam'iyyar PDP, wanda kani ne ga Bello Wada, wanda mulkin jihar ya kubuce daga hannun jam'iyyarsu shekara 4 da suka gabata.

    A jihar Bayelsa kuma akwai 'yan takara 45 da ke neman kujerar gwamnan jihar, kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana.

    Manyan 'yan takara biyu su ne Mr David Lyon na jam'iyyar APC, sai kuma Sanata Douye Diri na jam'iyyar PDP mai mulkin jihar.

    Daya daga cikin su ne ake sa ran zai gaji gwamnan jihar mai ci Seriake Dickson na jam'iyyar PDP.

    Ana kirga kuri'u a zaben gwamnonin Kogi da Bayelsa
    Image caption: Ana kirga kuri'u a zaben gwamnonin Kogi da Bayelsa
  4. An fara kirga kuri'u a zaben Kogi da Bayelsa

    An fara kirga kuri'u a runfunan zabe na jihohin Kogi da Bayelsa bayan kammala jefa kuri'a a zaben gwaman a jihohin biyu.

    Fafatawa ta fi zafi ne a zaben gwamna na jihar Kogi tsakanin mutane uku, wato gwamna Yahaya Bello na jam`iyyar APC, da Musa Wada na jam`iyyar PDP, sai kuma Natasha Akpoti ta jam`iyyar SDP.

    A jihar Bayelsa kuma hamayya ta fi kamari ne tsakanin Sen. Douye Diri wanda ke takarar gwamna a jam'iyyar PDP mai mulkin jihar, sai kuma mista David Lyon na jam'iyyar APC mai adawa.

    Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ta ce kimanin mutane miliyan 1.6 suka yi rajistar kada kuri'a a jihar Kogi, yayin da mutum 923,182 suka yi rajistar kada kuri'a a jihar Bayelsa.

    An dai samu rahotanni na tashe-tashen hankula, da satar akwatin zabe, da sayen kuri'a da kuma harbe-harbe a lokacin zaben a dukkanin jihohin biyu.

  5. An raba daloli a zaben Kogi - CDD

    Cibiyar Dimokradiyya da ci gaba ta Najeriya CDD, ta ce an yi amfani da kudi fiye da kima a zaben gwamnan jihar Kogi da aka gudanar a yau Asabar.

    A wani taron manema labarai da CDD ta gudanar a garin Lokoja, babban birnin jihar ta Kogi ta yi zargin cewa jam'iyyu sun ringa sayen kuri'u a fili a mazabu da dama a fadin jihar.

    A wurare da dama a cewar cibiyar, wakilan jam'iyyu ne suke tabbatar da mutum ya zabi jam'iyyarsu, sai kuma su damka masa kudi.

    "A mazabar makarantar firamaren LTU a Okene, wakilan jam'iyyu suna tura mutane bayan sun yi zabe, zuwa wajen wani mutum da ke zaune a kan babur, inda suke karbar Naira 2,000 kowannen su.

    CDD ta ce duka jam'iyyun APC da PDP na da hannu a wajen rabon kudi ga masu zabe da sassa daban-daban na jihar ta Kogi.

    Haka kuma cibiyar ta yi zargin cewa an karya dokokin zabe da dama inda wasu 'yan banga suka ringa yawo suna kwatar kayan zabe suna tarwatsa mutane.

    CDD ta ce ya kamata a sanya alamar tambaya kan sakamakon zaben na jihar Kogi.

    Dalar Amurka
  6. 'An kashe mutum uku a jihar Kogi'

    Mata da maza na cikin hawaye a yankin Adankolo na jihar Kogi bayan wasu mutane sanye da kakin jami'an tsaro sun kashe mutum uku a garin.

    Yayin da tawagar BBC Pidgin ta isa wurin ta tarar da daya daga cikin wadanda suka rasa ransu ana yunkurin binne shi.

    Maza da mata na cikin alhini a garin da a da yake cike da hadahada.

  7. An raba daloli a zaben Kogi - CDD

    Cibiyar Dimokradiyya da ci gaba ta Najeriya CDD, ta ce an yi amfani da kudi fiye da kima a zaben gwamnan jihar Kogi da aka gudanar a yau Asabar.

    A wani taron manema labarai da CDD ta gudanar a garin Lokoja, babban birnin jihar ta Kogi ta yi zargin cewa jam'iyyu sun ringa sayen kuri'u a fili a mazabu da dama a fadin jihar.

    A wurare da dama a cewar cibiyar, wakilan jam'iyyu ne suke tabbatar da mutum ya zabi jam'iyyarsu, sai kuma su damka masa kudi.

    "A mazabar makarantar firamaren LTU a Okene, wakilan jam'iyyu suna tura mutane bayan sun yi zabe, zuwa wajen wani mutum da ke zaune a kan babur, inda suke karbar Naira 2,000 kowannen su.

    CDD ta ce duka jam'iyyun APC da PDP na da hannu a wajen rabon kudi ga masu zabe da sassa daban-daban na jihar ta Kogi.

    Haka kuma cibiyar ta yi zargin cewa an karya dokokin zabe da dama inda wasu 'yan banga suka ringa yawo suna kwatar kayan zabe suna tarwatsa mutane.

    CDD ta ce ya kamata a sanya alamar tambaya kan sakamakon zaben na jihar Kogi.

    Natasha Akpoti da wani wakilin jam'iyyar SDP
  8. Sakamakon boge ya fara yawo - CDD

    Cibiyar Dimukuradiyya da cigaba ta CDD ta ce tuni sakamakon zabe na boge suka fara karade shafukan sada zumunta.

    Saboda haka cibiyar tana tabbatar wa mutane cewa har yanzu ba a fara bayyana sakamako ba tare da kiran da a daina yada su.

    View more on twitter
  9. PDP na son a soke sakamakon Okene da Okehi

    Jam'iyyar PDP a Najeriya ta bukaci hukumar zabe da kada ta amince da sakamakon zabe na kananan hukumomin Okene da Okehi, bayan da ta yi zargin cewa an tafka magudi.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar, jam'iyyar ta yi zargin cewa wakilan jam'iyyar APC mai mulkin jihar sun rinka tursasa wa malaman zabe amincewa da takardun sakamako na bogi.

    Jam'iyyar ta ce wannan al'amari ya gudana ne a mazabar Kogi ta tsakiya.

    Sai dai har yanzu jam'iyyar APC mai mulkin jihar, da kuma hukumar zabe ta INEC ba su ce komai ba game da zargin.

    PDP
  10. An fara tattara sakamakon zabe a matakin mazaba a Bayelsa

    Tuni aka kammala zabe a mazabar Town Hall da ke karamar hukumar Brass a jihar Bayelsa kuma an fara tattara sakamakon a matakin mazaba.

    View more on twitter
  11. An fara tantance kuri'u a wasu mazabu a Kogi da Bayelsa

    An kammala kada kuri'a a wasu rumfunan zabe da ke birnin Lokoja na jihar Kogi.

    Tuni malaman zabe suka fara tantance kuri'un da aka kada.

    Amma mutum zai iya kada kuri'a matukar an tantance ka ne kafin karfe 2 na rana.

    A jihar Bayelsa kuma tuni aka fara kirga kuri'u a wasu mazabun bayan kammala zabe.

    Yadda ake tantance kuri'u a mazabar Amarata da ke Yenagoa
    Image caption: Yadda ake tantance kuri'u a mazabar Amarata da ke Yenagoa
    A wasu mazabu da ke Lokoja na fara tantance kuri'a
    Image caption: Yadda ake tantance kuri'a a zaben gwamnan jihar Kogi
    Yadda ake tantance kuri'a a zaben gwamnan jihar Kogi
    Image caption: Yadda ake tantance kuri'a a zaben gwamnan jihar Kogi
  12. An saki malaman zaben da aka sace a Kogi

    Kwamishinan zabe na jihar Kogi Farfesa Iorliam Apam ya tabbatar da cewa an samu matsalolin satar akwatunan zabe a wasu yankunan jihar.

    Ya kuma ce an sace malaman zabe da aka tura zuwa karamar hukumar Dekina, sai dai an sake su bayan karbe kayan zaben da suke dauke da su.

  13. Hotunan yadda aka lalata akwatunan zabe a Lokoja

    'Yan bangar siyasa sun lalata akwatunan zabe tare da sace wasu akwatunan a rumfar kada kuri'a ta Madabo da ke Lokoja.

    Takardun kada kuri'a warwatse a kasa bayan farfasa akwatunan zabe
    Image caption: Takardun kada kuri'a warwatse a kasa bayan farfasa akwatunan zabe
    Takardun kada kuri'a warwatse a kasa bayan farfasa akwatunan zabe
    Image caption: Takardun kada kuri'a warwatse a kasa bayan farfasa akwatunan zabe
    Takardun kada kuri'a warwatse a kasa bayan farfasa akwatunan zabe
    Image caption: Takardun kada kuri'a warwatse a kasa bayan farfasa akwatunan zabe
  14. 'Yan Najeriya na saurin korafi kan gwamnati - Jonathan

    Bidiyo

    Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya yi kira ga 'yan Najeriya da su zabi shugabanni na gari ta hanyar lumana "domin ba za mu iya zabe cikin tashin hankali ba".

    Ya fadi hakan ne jim kadan ya bayan ya jefa kuri'arsa a Otueke ta jihar Bayelsa, inda ya ce ya kamata 'yan kasa su zabi shugabanni na gari tukunna kafin su zargi gwamnati da gazawa.

    Video content

    Video caption: Mu zabi shugabanni na gari kafin mu zargi gwamanti - Jonathan
  15. 'Harbe-harbe' a mazabar Dino Melaye

    Rahotanni sun ruwaito cewa an samu harbe-harbe a mazabar Ayetoro wato mazabar Sanata Dino Melaye jim kadan bayan ya jefa kuri'arsa.

    Kasa da awa daya bayan fitarsa daga mazabar ne wasu matasa dauke da bindigogi suka far wa wurin kada kuri'ar a cikin mota guda biyu kirar Hilux da kuma Honda, inda suka fara harbi sannan kuma suka hari akwatin zabe.

    Rahotanni sun bayyana cewa an harbi wani matashi mai suna Dami a kafarsa yayin da yake barin wani kantin sayar da abinci kuma yanzu haka yana asibiti.

    A karshe dai sun yi awon gaba da akwatin amma wasu mutane sun bi su, sai dai ba su samu nasarar cimma su ba.

    Dino Melaye
    Dino Melaye
  16. Yadda wasu 'yan Kogi suka kada kuri'unsu

    Wasu 'yan jihar Kogi sun bayyana wa BBC yadda suka kada kuri'unsu a yau.

    Video content

    Video caption: Yadda wasu 'yan Kogi suka kada kuri'unsu
  17. An kone kayayyakin zabe a Bayelsa

    Jami'in hukumar zabe na karamnar hukumar Ogbia a jihar Bayelsa Nkwachukwu Orji ya shaida wa BBC cewa wasu matasan yankin Ologi sun kona kayayyakin zabe a lokacin da ake kokarin rarraba su zuwa yankunan karamar hukumar, abin da ya jawo jingine kada kuri'ar baki daya.

    Ya ce amma zaben yana tafiya lami lafiya a sauran sassan karamar hukumar ta Ogbia.

    Nkwachukwu Orji
  18. 'Yan sandan boge sun sace wakilanmu - Natasha Akpoti

    'Yar takarar jam'iyyar SDP kuma mace tilo da take takarar gwamna a jihar Kogi Natasha Akpoti ta yi zargin cewa an jikkata wakilan jam'iyyarta sannan kuma 'yan sanda sun yi awon gaba da wasu.

    Ta kara da cewa 'yan sanda sun shaida masu cewa ba su suka kama 'ya'yan jam'iyyar ba kuma a saboda haka ne suke zargin cewa dakarun jam'iyya mai hamayya da ita ne suka sace su.

    Video content

    Video caption: 'Yan sandan boge sun sace wakilanmu - Natasha Akpoti
  19. Goodluck Jonathan ya kada kuri'arsa

    Tsohon Shugaban Najeroiya Goodluck Ebele Jonathan ya kada kuri'arsa a mazaba ta 13, rumfar zabe mai lamba 39, Otuoke.

    Goodluck Ebele Jonathan