Benjamin Netanyahu: An kawo ƙarshen mulkin firaiministan Isra'ila na shekara 12

Benjamin Netanyahu

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Mr Netanyahu ya koma shugaban masu adawa a Isra'ila

Benjamin Netanyahu ya rasa ikonsa na shekaru 12 kan mulkin Isra'ila bayan da majalisar dokokin kasar ta kada kuri'ar amincewa da sabuwar gwamnatin haɗaka.

Naftali Bennett na jam'iyyar Yamina zai jagoranci sabuwar "gwamnatin ta canji."

Shi zai jagoranci gamayyar jam'iyyun da suka samu rinjayen ƙuri'a ɗaya wanda ya kai ga kawo ƙarshen mulkin Netanyahu.

Mr Bennett zai zama Firaminista har zuwa watan Satumban 2023 ƙarƙashin tsarin karɓa-karɓa.

Daga nan zai miƙa mulki ga Yair Lapid, shugaban jam'iyyar Yesh Atid, na tsawon shekara biyu.

Mista Netanyahu - wanda ya fi daɗewa kan mulki a Isra'ila ya mamaye siyasar Isra'ila na tsawon shekaru.

Yanzu zai kasance shugaban jam'iyyarsa ta Likud kuma jagoran adawa.

Lokacin da ake tafka mahawara a majalisa, Mr Netanyahu ya yi alwashin cewa: "Za mu dawo."

Tuni shugaban Amurka Joe Biden ya aika da sakon taya murna ga Mista Bennett, yana mai cewa a shirye yake ya yi aiki tare da shi.

Me ya sa hakan ta faru?

Mista Netanyahu ya yi wa'adin mulki sau biyar, na farko daga 1996 zuwa 1999, sannan daga 2009 zuwa 2021.

Ya kira sabon zaɓe a 2019 amma ya kasa yin nasarar kafa gwamnatin haɗaka. Daga baya aka sake yin wasu zaɓuka guda biyu, waɗanda dukkaninsu ba a kammala ba.

A zaɓe karo na uku ya haifar da gwamnatin haɗin kai inda Mista Netanyahu ya amince da tsarin karɓa karɓa ga jagoran adawa Benny Gants. Amma daga baya ƙawancen ya rushe a watan Disamba, ya kai ga yin zaɓe kawo na huɗu.

Duk da jam'iyyar Likud ta Netanyahu ta samu kujeru 120 a majalisa, amma Netanyahu ya kasa kafa gwamnati, inda aikin ya koma ga Mista Lapid, wanda jam'iyyarsa ta zo na biyu da yawan ƙuri'u.