Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Jabir Mustapha Sambo da Imam Saleh

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Imam Saleh

    Multimedia Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu ta wannan shafi a nan za mu muku sallama sai kuma gobe in Allah ya kaimu za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku labaran halin da duniya ke ciki kai tsaye.

    Za ku iya dubawa ƙasa don samun dukkan labaran da muka wallafa a yau.

    Sunana Imam Saleh, mu kwana lafiya.

  2. Gwamnonin PDP ba sa son kawo karshen rikicin makiyaya - Fadar Buhari

    Muhammadu Buhari
    Image caption: Buhari

    Fadar Shugaban Najeriya a ranar Laraba, ta zargi gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP, da kin goyon bayan kudirin kawo karshen rikicin makiyaya a kasar ta yadda za a ceci rayukan jama'a da dukiyoyinsu.

    Fadar Shugaban kasar na bayyana hakan ne bayan taron da kungiyar Gwamnonin PDP ta gudanar a karshen mako a Uyo, jihar Akwa Ibom ranar Litinin.

    A martaninta fadar shugaban kasar a cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar a Abuja, ya ce gwamnonin PDP ba su samar da mafita ga matsalolin kasar ba amma sun fi sha'awar abin da ya shafe su .

    A cewar sanarwar: “Wannan shirin na samar da matsuguni ga makiyaya ya kawo 'yanci da sauyi na zamani don kawo mafita ga kalubalen da al'ummomi daban-daban na kasarmu suka fuskanta amma gwamnonin PDP suka ki amincewa da shi, suka hana dukkan' yan Najeriya 'yancinsu na tsarin mulki na rayuwa da aiki a kowace jiha ta Tarayya sun fi son yin kira ga rarrabuwar kawuna a tsakanin 'yan Najeriya''

  3. Putin da Biden sun gana

    Putin da Biden
    Image caption: Putin da Biden

    Bayan taron da aka rika zaman jira a birnin Geneva, shugabannin kasashen Amurka da Rasha sun yi magana mai kyau game da tattaunawarsu inda suka bayanna ta a matsayin mai maana, ko dayake an samu wasu banbance banbance.

    Yayinda suke amsa tambayoyin yan jarida Shugaba Biden ya ce duk da cewa ya bayana wuraren da za su iya ciyar da muradunsu gaba amma ya fadawa Mista Pootin cewa Amurka za ta maida martani a kan duk wani mataki da ya sabawa muradunta.

    Ya ce ''Na fada masa cewa a ko yaushe batun kare hakkin bildama shi ne gaba a teburin shawara''

    A dayan bangaren shugaba Pootin ya kira tattaunawar ta su muhimiya kuma sun fadawa juna gaskiya.

    Ya kuma ce kasashen biyu za su dawo da jakadunsu da suka janye a watan Afilun daya gabata

  4. Zaɓen shugaban ƙasar Iran: 'Shin ƙwaryar sama ce take dukan ta ƙasa?'

    Masu kada kuri'a a Iran sun ce ba su da wani zabi na hakika a zaben shugaban kasar da za a gudanar ranar 18 ga watan Yuni.

    A yayin da saura kwanaki kadan a gudanar da zaben, dan takara daya tilo da ke da ra'ayin kawo sauyi ya janye daga takarar - cikin sauran 'yan takara shida da suka rage, biyar masu tsattsauran ra'ayi ne. (Jan hankali: Dan takarar ya janye daga shiga takara ne bayan an fitar da wannan bidiyon).

    Video content

    Video caption: Zaben shugaban kasar Iran: 'Shin kwaryar sama ce take dukan ta kasa?'
  5. ISWAP ta banka wa wani sansanin sojin Najeriya wuta ta kwashe makamai

    Mayakan ISWAP
    Image caption: Mayakan ISWAP

    Wasu masu tayar da kayar baya da ake zargin 'yan kungiyar ISWAP ne sun mamaye wani sansanin sojoji a kudancin jihar Borno a ranar Talata sannan suka kwashe makamai bayan wani kazamin artabu da sojojin.

    Bayanai sun ce maharan sun kai farmakin ne a kan wasu motocin yaki 100, sannan suka yi wa sansanin sojin da aka kafa a garin Kwambi dake karamar hukumar Damboa kawanya.

    A cewar wani mamba na kungiyar hadin gwiwa ta Civilian JTF, kungiyar ta kai farmakin ne kan sansanin sojin ba wai ga jama’a ba.

    Ya kuma bayyana cewa an lalata sansaninsu, sannan maharani sun sace makamai da alburusai.

    Jaridar Daily Trust ta rawaito shi yana cewa “Sun zo da misalin karfe 4 na yamma. kuma saboda guguwa mai hade da yashi da aka rika yi, hakan ya kawowa sojoji cikas a kokarinsu na fatattakarsu.

  6. Mun harbe wata mata Bafalasɗiniya - Isra'ila

    Sojan Isra'ila
    Image caption: Sojan Isra'ila

    Rundunar sojin Israila ta ce ta harbi wata mata yar Falasdinu da ta yi kokarin kai hari da mota da wuka a yammacin kogin Jodan.

    Rahotanni sun ce ta mutu ne sanadin raunukan da ta samu.

    Rundunar sojin Israilar ta ce matar ta yi kokarin afkawa sojojinta da ke arewa maso gabashin Qudus.

    Tun farko Israilar ta kai hare hare ta sama a zirin Gaza wanda shi ne na farko tun bayan yarjejeniyar dakatar da bude wuta da ta kawo karshen rikici a wannan wuri a watan daya gabata.

    Sai dai wata yar jarida a birnin Qudus din ta ce ga dukkan alamu bangarorin biyu ba sa son halin da ake ciki ya rincabe

  7. An kama mutane 7 bisa zargin satar mutane a Kaduna

    'Yan sandan Najeriya
    Image caption: 'Yan sandan Najeriya

    Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta cafke wasu mutane bakwai da ake zargin masu satar mutane ne a garuruwan Zariya da Kaduna.

    Kakakin rundunar, Mohammad Jalige, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Laraba a hedkwatar rundunar da ke Kaduna.

    Ya ce wadanda aka kama sun hada da wani mai suna Mannir Salihu, wanda aka damke kan kisan wani Idris Bashir, wanda ya bar gidansa na Zariya, a ranar 4 ga Yuni, 2021 kuma bai dawo ba.

    Salihu, wanda aka ce aboki ne ga mamacin, ana zargin ya kashe shi ne don gudun kar ya dawo da Naira 385,000.00, wanda ake bin mamacin.

    A cewar Jalige, "A ranar 5 ga Yuni, 2021 da misalin karfe 9 ne rundunar ta samu korafi daga wani basarake na garin Zariya cewa a ranar 4 ga Yuni, 2021 da misalin karfe 10 na dare dansa mai suna Idris Bashir ya bar gida bai dawo ba."

  8. Me ƴan Najeriya ke cewa kan Bola Tinubu?

    Jagoran jam'iyyar APC mai mulki Asiwaju Bola Tinubu ya koma Najeriya daga bulagurin da ya yi.

    Babu wasu bayanai da suka nuna inda Tinubu ya tafi, to amma ana ta ce-ce-ku-ce kan inda tsohon gwamnan na Lagos yake kafin dawowarsa jiya.

    Akwai jita-jitar da ake yadawa cewa jagoran na jam'iyyar APC ya tafi kasashen waje a duba lafiyarsa, duk da har yanzu bai ce uffan ba kan batun.

    Tun ranar 25 ga watan Mayun 2021 rabon da aga Tinubu cikin jama'a, a lokacin da ya jagoranci wasu shugabanni zuwa fadar Shugaban kasa.

    Ziyarar tasu a loakcin ta zo ne kwanaki biyu bayan Shugabannin kabilar Yarbawa sun nuna goyon bayansu kan batun samar da burtalai a fadin kasar.

    Duk da tsohon gwamnan na jihar Lagos har yanzu bai fito ya bayyana sha'awarsa ta takarar Shugabancin kasa ba a shekarar 2023, hotunansa na neman takarar sun karade sassan Najeriya.

    Bola Tinubu
  9. Mutum 17 sun kamu da Korona a Najeriya ranar Talata

    Corona test

    Cibiyar da ke dakile cutuka masu yaduwa ta NCDC ta ce an samu mutun 17 dauke da cutar Korona a ranar Talata.

    NCDC ta sanar da hakan ne a shafinta na intanet yau Laraba.

    Ta kara da cewa 13 daga cikin mutanen sun fito ne daga jihar Lagos, sai Rivers mai mutun 3 kafin Gombe mai mutun daya tilo.

    NCDC ta ce kawo yanzu an yiwa mutun 2,231,409 gwajin cutar Korona a Najeriya tun bayan bullarta a kasar a watab Fabrairu 2020.

    To amma hukumar ta ce ba samu mutuwa ba sanadin Korona a Najeriya a cikin awa 24.

  10. An gano tarkacen jirgin da ya ɓata a shekarar 1965

    plane

    Yayin da fari ya yi kamari a jahar California da ke Amurka, hukumomi sun gano tarkacen wani jirgi da da ake sa ran ya ɓata kusan shekaru 60 da suka wuce.

    Za a iya cewa fari ya yi sanadin kawo karshen binciken da aka shafe kusan shekara 60 ana yi a Amurka, a lokacin da wani jirgi ƙirar Piper Comanche 250 ya ɓata a shekarar 1965.

    Kamfanin Folsom da gano wani abu da ya ce ya maale cikin taɓo, kuma alamu sun nuna cewa jirgin Piper ne da ya ɓata a ranar bikin sabuwar shekarar 1965.

    Daya daga cikin ma'aikatan na Folsom Tyler Atkinson ne ya ce ya ga wani abu da mai ban mamaki kwance a ƙasan ruwa, kuma da aka matsa binciken sai a ka tabbatar da cewa jirgin sama ne.

    Hadarin jirgin na 1965 ya kashe duka mutum huɗu da ke cikin da suka hada da matuƙinsa.

    Kuma yayin da aka gano gawar matukin, har yanzu babu duriyar sauran mutum uku da ke ciki, duk da ci gaba da binciken da aka yi a shekarar 2014.

  11. INEC ta kirkiri sabbin rumfunan zabe sama da dubu 56

    Prof Mahmood Yakubu

    Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta sanar da ƙirƙirar karin rumfunan zabe dubu 56,872 a fadin kasar.

    Shugaban hukumar ta INEC Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a wani taro da ya yi da kwamishinonin zabe na jihohi a yau Laraba.

    Hakan na nufin a yanzu akwai rumfunan zabe 176,846 a fadin Najeriya.

    INEC na ci gaba da damarar tunkarar manyan zabuka da za a gudanar a 2023.

  12. Al-Shabab ta sanar da kashe sojojin Somaliya 40

    Al-Shabaab

    Kungiyar al-Shabaab ta yi ikirarin kashe sojojin Somaliya 40 tare da jikkata wasu 50, a wani harin kunar bakin wake a sansanin Turkisom da ke Mogadishu.

    Sai dai ana samun rahotanni masu karo da juna kan adadin wadanda suka mutu a harin.

    Yayin da hukumomi suka bayyana cewa mutun 10 suka mutu, kafafen yada labarai masu zaman kansu da ke Somaliya sun ce mutun 20 ne.

    A wata mai kama da haka, gidan rediyon Mogadishu ya ruwaito cewa dakarun gwamnati sun tarwatsa wasu sansanonin al-Shabaab a kudanci da kuma tsakiyar Somaliya.

    Kafar ta kara da cewa sojojin Somaliya sun kashe mayakan al-Shabaab kusan 300 yankunan biyu.

  13. Saudiyya ta yanke wa wani hukuncin kisa kan laifin 'da ya aikiata yana yaro'

    Mustafa Hashem al-Darwish

    Hukumomin Saudiyya sun yanke wa wani mutum hukuncin kisa, kan laifin da kungiyoyin kare hakkin dan adam suka ce ana zargin ya aikata a lokacin da yake shekara 17.

    Hukumomi sun yankewa Mustafa Hashem al-Darwish hukuncin, duk da tabbacin da kasar ta ba da tun da farko, kan cewa za a daina yankewa kananan yara hukuncin kisan.

    A shekarar 2015 ne aka kama al-Darwish wanda mabiyin mazahabar Shi'a ne marasa rinjaye, kan zargin kitsa zanga-zangar ta'addanci a inda ake tsare da shi da wasu laifukan na daban.

    Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International Mr al-Darwish, wanda a yanzu yake da shekara 26, ya janye amsa laifin da ya yi sakamakon ya yi hakan ne saboda azabtar da shi da aka yi.

    Yayin da 'yan uwansa suka ce an yanke masa wannan hukuncin ne kawai saboda wani hoto da aka gani a cikin wayarsa da ya ci zarafin jami'an taron Saudiyyar.

  14. Hauhawar farashi ya sake jefa ƴan Najeriya miliyan bakwai cikin talauci - Bankin Duniya

    Ƙwararru a fannin tattalin arziƙi a Najeriya sun fara bayyana ra'ayoyinsu kan wani rahoton Bankin Duniya da ya yi gargaɗi game da ƙaruwar hauhawar farashi a ƙasar.

    A cewarsa cikin watan Afrilun da ya wuce an samu hauhawar farashi mafi yawan da ba a taɓa gani ba a cikin shekara huɗu.

    Haka kuma rahoton ya ce hauhawar farashin kaya ya sake jefa 'yan Najeriya kimanin miliyan bakwai cikin matsanancin talauci a bara kaɗai.

    Mukhtari Adamu Bawa ya ga ƙunshin rahoton ga kuma ƙarin bayaninsa.

    Video content

    Video caption: Rahoton Mukhtari Adamu Bawa kan rahoton Bankin Duniya
  15. Dambarwa ta kunno kai tsakanin masu yin gurasa da masu sayar da ita a Kano

    A yayin da yajin aikin masu sana’ar gurasa ya shiga yini na biyu wata sabuwar dambarwa ta kunno kai tsakanin ƴaƴan kungiyar inda wasu daga cikinsu suka nuna rashin goyan bayansu kan yajin aikin da aka fara a jiya.

    Ƙungiyar ‘yan Gurasa ta ce ta janye kanta daga yajin aikin da wasu daga cikin ƴan kungiyar suka shiga saboda rashin tuntuɓa, da bin ƙa’idojinsu da kungiyar masu yin gurasar suka yi.

    Sai dai masu yin gurarsar sun ce zagon kasa masu siyar da gurasar suke yi musu.

    Daga Kano ga rahoton Khalifa Shehu Dokaji:

    Video content

    Video caption: Rahoton Khalifa Shehu Dokaji kan yajin aikin masu sana’ar gurasa
  16. An tsawaita lokacin bayar da fasfo a Najeriya

    Hukumar shige da fice ta Immigration tace ta shigo da wani tsarin bayar da fasfo ga mabukata tafiye-tafiye tsakanin kasa da kasa.

    Daga yanzu za a rika samar da fasfon daga awa 72 zuwa tsawon mako shida ga mai bukatar sabon fasfo a karon farko.

    Shi kuma mai tsohon fasfo da ke bukatar sabunta shi zai same shi a cikin mako uku.

    Tsawaita lokacin karbar fasfo na kasa da kasa wata dabara ce ta samun cikakkun bayanan da zasu inganta al’amura na tsaron kasa.

    Wakilinmu na Legas Umar Shehu Elleman, ya tambayi Konturola mai kula da shige da fice a babban ofishin bayar da fasfo dake birnin Legas, Abdulkadir Sulaiman Garo, wanda ya bayyana dalilansu na tsawaita lokacin bayar da fasfo ga mabukata.

    Ku latsa hoton ƙasa don sauraron hirar:

    Video content

    Video caption: Hirar Umar Shehu Elleman da Abdulkadir Sulaiman Garo
  17. Da wahala a kwashe lafiya tsakanin Biden da Putin a yau

    Joe Biden

    Joe Bien da takwaransa na Rasha Vladimir Putin za su gana a birnin Geneva na Switzerland a yau, a karon farko tun da Mista Biden ya zama shugaban Amurka.

    Sai dai masu sharhi na ganin da wahala a kwashe lafiya a tattaunawar.

    Dangantaka tsakanin kasashen biyu ta dade da yin tsami saboda Amurka na zargin Rasha da kitsa hare-hare ta intanet da kuma katsalandan a zaɓukanta na 2020.

    Tana kuma zargin Rasha da take hakkin bil Adama ciki har da tsare jagoran 'yan adawa Alexei Navalny.

    Sai dai babu alamun Mista Putin zai taba sauya manufofinsa na maida kasashen yammacin duniya saniyar ware ta fuskar gudanar da ayyukansa.

  18. Ƴan bindiga sun kashe ƴan sanda huɗu a jihar Zamfara

    Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya ta tabbatar da mutuwar jami’anta hudu.

    Lamarin ya faru ne yayin wata arangama da ‘yan bindiga lokacin da suke aikin sintiri a yankin Rini cikin karamar hukumar Bakura.

    Haka kuma ‘yan bindigar sun far wa kauyukan Tataka da Takalmawa a karamar hukumar Zurmi inda ake fargabar fiye da mutum 20 sun mutu tare da kwashe ɗumbin dukiya a karshen mako.

    Hare-haren 'yan bindiga sun dawo sosai a jihar Zamfara.

    Ga rahoton Zahraddin Lawan, ku latsa hoton ƙasa don sauraro:

    Video content

    Video caption: Rahoton Zahraddeen Lawan kan kashe 'yan sanda a Zamfara
  19. Najeriya za ta karbi rigakafin Korona miliyan hudu daga AstraZeneca

    AstraZeneca

    Jami'an lafiya a Najeriya sun ce suna sa ran karbar kusan riga-kafin cutar korona miliyan hudu ta kamfanin AstraZeneca a karshen watan Yuli.

    Za a karbi allurar ne karkashin shirin COVAX da ke tallafawa kasashe matalauta da ke Afirka don samun yi wa al'ummarsu kashi na biyu na riga-kafin cutar ta korona.

    Ana sa ran Najeriyar za ta kammala aikin yin kashi na farko na riga-kafi miliyan hudu da aka ba ta zuwa karshen watan.

    Kawo yanzu kashi daya cikin 100 na al'ummar Najeriya ne aka yi wa kashin farko na riga-kafin.

    A bangare guda gwamnati ta ce tana shirin yi wa a ƙalla kashi 70 cikin 100 na 'yan Najeriya 'yan sama da shekaru 18 allurar riga-kafin korona nan da shekaru biyu masu zuwa.

  20. An yi Allah-wadai da macin da Yahudawa suka yi a Birnin Ƙudus

    Mutumin da ya kafa gwamnatin Gambiza a Isra'ila mai ra'ayin sassauci Yair Lapid, ya yi Allah-wadai da macin da dubban Yahudawa suka yi a kudancin Birnin Kudus, lamarin da ya tunzura Hamas ta harbo balan-balan mai ababen fashewa zuwa Isara'ila.

    Duk da cewa gwamnati ta amince da yin macin tare da sauya hanyar wucewar ta kasuwar Larabawa maimakon cikin birni inda Musulmai ke zama.

    Mr Lapid ya ce matakin abin kunya ne ga Isra'ila.

    Tun da fari Firaministan Falasdinu Muhammad Shtayyeh ya ce macin zai tunzura wadanda har yanzu mikin abin da ya faru na watan jiya ke damunsu, amma masu macin sun ce hakan tauna tsakuwa ne domin aya ta ji tsoro kan harin rokokin Hamas.

    Tun da fari Falasdinawa 30 ne suka jikkata a taho mu gama da suka yi da jami'an tsaro, an kuma cafke wasu 17.

    A watan Mayu aka shirya macin wanda na tunawa ne da lokacin da Isra'ila ta karbe iko da gabashin Kudus, a shekarar 1967.