Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Awwal Ahmad Janyau da Buhari Muhammad Fagge

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Nan ne muka kawo ƙarshen labarai da rahotanni na wannan rana sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.

    In da za mu kawo muku wasu sabbin labarai da rahotanni daga ko ina a faɗin duniya.

    Buhari Muhammad Fagge ke cewa mu kwana lafiya.

  2. An yankewa mutane da dama hukuncin daurin rai da rai a Turkiyya

    AFP
    Image caption: Fethullah Gülen ake zargi da kitsa juyin mulkin da bai yi nasara ba

    Akasarin mutanen da suka yi gaba-gaba a yunkurin yin juyin mulkin da bai yi nasara ba a Turkiyya a shekarar 2016 na daga cikin sama da mutum dari uku da aka yankewa hukuncin daurin rai da rai bayan shafe tsawon shekara fiye da uku ana sauraron kararsu.

    Daga cikin wadanda aka samu da laifi har da yan kasuwa da suka ba da gudummawa wajen kitsa lamarin da jami'an soji da kuma matuka jirgin saman da suka yi ruwan bama-bamai a yankunan ciki har da majalisar dokokin Turkiyyan.

    Wani wakilin iyalan wadanda lamarin ya shafa ya ce "Mun yi imanin cewa an yanke hukuncin daidai da dokokin da ke akwai. Muna tunanin an yi adalci".

    An wanke mutum 70 daga cikinsu sannan ana neman mutum hudu ciki har da malamin da ake zargi da jagorantar juyin mulkin ruwa a jallo.

    Iyalan wadanda abin ya shafa sun ce an yi adalci amma wsu yanuwan mutanen da aka samu da laifi sun ce hukuncin bai dace ba kuma za su daukaka kara.

    BBC
  3. Za a gina hedikwatar kamfanin harkokin zuba jari kan makamashi ta Afrika a Abuja

    BBC

    Shugabn Najeriya Muhammadu BUhari ya yi maraba da matakin ƙungiyar kasashe masu samar da mai ta Afrika APPO, na gina hedikwatar kamfanin harkokin zuba jari kan makamashi ta Afrika a babban birnin kasar Abuja.

    Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimaki na musamman ga shugaban Najeriyan kan kafofin yaɗa labarai Malam Garba Shehu.

    Yayin wani taro da sakataran ƙungiyar Dakta Omar Farouk a fadar shugaban ƙasar, Buhari ya ce Najeriya za ta ba da duka wata gudummawa da ta dace domin tabbatar da ganin an cika wannan buri.

    Cikin sanarwar shugaba Buhari ya ce matsalolin da bangaren samar da mai ke fuskanta tun a baya, shi yasa suka tattau ƙarƙashin kungiyar domin bayyana kwarewar da suke da ita dan lalubo bakin zare matsalolin nahiyar.

    Sanarwar ta ƙara da cewa duk da kiraye-kirayen da ake yi na a rage amfani da makamashi irin na su man fetur da ɗangonsu, Najeriya na da buƙatar kara samar da man saboda masana'antu da ke bukatar sa, da kuma samar da aiki ga 'yan ƙasar.

  4. ‘Bakuwar cuta ta kashe yara 15 a jihar Naija’

    A Najeriya a ƙalla yara 15 ne da shekarun su basu kai biyar ba suka rasa rayukansu sakamakon bullar wata baƙuwar cuta a jahar Naija da ke arewacin kasar.

    Hukumomin lafiya a jahar sun ce har yanzu ba su kai ga gano musabbabin cutar ba, sai dai cutar ta fi kama da amai da gudawa,

    Kwamishina lafiyan jihar Muhammad Maku Muhamamd ya alakanta cutar matsalar rashin kula da tsaftar gurin zama da sauyin yanayi da ake samu duk shekara, wanda ke janyo barkewar annoba irin amai da gudawa da cutar sankarau da makamantansu.

    Kwamishinan ya ce tuni dai suka dukufa wajen gano musabbanin cutar tare da daukar matakai.

    Ga dai ƙarin bayanin da kwamishinan ya yi wa Khalifa Shehu Dokaji.

    Video content

    Video caption: Wata bakuwar cuta ta kashe yara 15 a jihar Naija
  5. An dakatar da wasu 'yan sanda daga aiki kan cin zarafin masu zanga-zanga

    BBC

    Hukumomin 'yan sanda a Faransa sun dakatar da yan sanda uku bayan da aka gansu cikin wani hoton bidiyo suna dukan wani furodusan waka bakar fata a birnin Paris.

    Lamarin da ya faru ranar Asabar ya fusata jama'a kan dabi'un jami'an tsaron.

    A ranar Litinin ne aka zargi 'yan sanda da yin amfani da karfi kan masu zanga-zangar nemarwa yan cirani hakki.

    Gwamnatin Faransa dai na kokarin samar da dokokin da za su haramta nuna fuskokin 'yan sanda, amma masu suka na cewa da ba a nuna fuskokin yan sandan ba, babu wanda zai san abin da ya faru a makon da ya gabata.

  6. Nanono ya musanta badaƙalar naira biliyan uku a ma’aikatar gona ta Najeriya

    Ma`aikatar aikin gona a Najeriya ta musanta rahoton da ke cewa ta saɓa wa ka`ida wajen kashe fiye da naira biliyon uku a shekarar da ta wuce.

    Wani bincike da jaridar Premium Times ta yi ya nuna cewa an saka kudade a asussan jami`an ma`aikatar maimakon a biya `yan kwangila kai tsaye.

    Kazalika an cire wasu kudade ana bai wa fiye da mutum guda da sunan aiki daya.

    Mallam Ahmad Amin shi ne mai magana da yawun Ministan gonar, kuma ya shaida wa Ibrahim Isa cewa kudaden da ake magana na wasu ayyuka ne da aka yi tun shekaru masu yawa da suka wuce:

    Video content

    Video caption: Nanono ya musanta badaƙalar naira biliyan uku a ma’aikatar gona ta Najeriya
  7. Kanun labaran korona a nahiyar Afrika

    • Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Afirka ta ce adadin mutanen da suka kamu da annobar korona sun zarce miliyan biyu.

    Kudancin Afirka ne yankin da annobar ta fi shafa sannan Arewacin Afirka.

    • Gamayyar kamfanoni masu zaman kansu a Najeriya ta samar da kimanin naira biliyan 39 domin tallafawa yakin da ake da cutar korona.

    Gamayyar ta kara da cewa an yi amfani da kudaden wajen sayen kayan asibiti da shirye-shiryen samar da abinci

    • Ba za a rufe makarantu a Uganda ba duk da karuwar masu fama da annobar korona.

    Hukumomin lafiya a kasar sun ce sake rufe makarantun ba a bin da zai haifar sai kara yaduwar cutar a tsakanin al’umma da kuma kara tabarbara harkokin karatun dalibai.

  8. Ba za mu yarda yaƙin satar mutane har gida ya ci mu ba - Zulum

    Governor Borno

    Gwamnan Borno da ke arewa maso gabshin Najeriya, Farfesa Babagaba Umara Zulum ya ce dole ne a tashi tsaye domin daukar matakan da suka dace kan masu satar mutane har gidajensu.

    Gwamna Zulum ya yi wannan bayani ne a yayin taron ƙungiyar gwamnonin arewa maso gabashin ƙasar karo na uku da yake jagoranta,

    Governor Borno

    Zulum ce ganin yadda wannan matsala ke ta'azzara wadda kuma tuni ta yi ƙamari a johohi irinsu Kano da Kaduna, akwai buƙatar kungiyar tasu ta ɗauki matakin daƙile wannan mummunan aiki karya ƙarasa yankinsu.

    Ya ce a matsayinsu na gwamnonin da al'umma suka bai wa yardarsu, dole ne su samar da aminci ga matafiya daga jiha zuwa wata, ya nemi kuma kwamitin kwamishinonin shari'ar yankin da su samar da tsarin shari'a da zai tun kari wannan annoba.

    Ya kuma yi bayani game da abin da ke ƙara addabar mutane a ƙasar baki ɗaya,wato matsalar fyaɗe.

    Farfesa Zulum ya ce dole ne a lalubo hanyar da za a kare mata tare da basu ƙarfin gwiwar yin rayuwa kamar kowa.

    Cikin matsalolin da aka tattauna a kwai maganar Boko Haram da kuma maganar kan Almajirci da fatan ganin an kawo ƙarshen shi ta hanyar da ta dace.

  9. Buhari zai jefa Najeriya cikin rikici - Nyesom Wike

    RIVERS STATE GOMENT HOUSE PRESS

    Gwamnan jihar Rivers da ke kudancin Najeriya Nyesom Wike, ya ce ba za a zauna lafiya ba a kasar matukar shugaba Buhari ya gaza biyan wasu daga cikin bukatun ‘yan Najeriya.

    Gwamnan ya yi wannan bayani ne a ranar Alhamis ta cikin shirin Sunrise na kafar yada labarai ta Channels, kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito.

    Wike ya yi wannan bayani ne a matsayin martini ga bukatun gwamnonin Kudu maso Kudancin kasar, lokacin da suka hadu da wakilcin shugabancin kasar da Ibrahim Gambari shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar ya jagoranta.

    Gwamnoni sun nemi a bar jihohi su rika iko da albarkacinsu sama da gwamnatin tarayya, domin tabbatar da ci gaban mutanensu.

    “Ba wai bani da kwarin gwiwa ba ne, ban yarda da cewa ba dan baka yi abin da aka cimma matsaya da kai ba a jiya, baya nufin ba z aka yi abin da aka cimma da kai ba a yau,” in ji Wike.

    Ko da shugaba Buhari bai yi abinda ya fada zai yi ba a jiya, zai iya sauya wa daga baya ya yi.

    “Mutane sun yi korafin tattaunawa ba za ta haifar da komai ba. Ni ban yarda da su ba. Na yi imanin idan shugaban kasa bai yi hakan ba, wato bayar da dama, zai jefa Najeriya cikin tashin hankali.

    “Bai zama dole ya iya yin komai da ya yi alkawari ba, amma mutane na son suga wata shaida a kasa karkashin shugabancin Buhari, ko ba komai ya yi abu daya biyu uku hudu na bukatun mutane”.

  10. Har yanzu Afrika ta Kudu na tsaka mai wuya kan korona

    Reuters

    Hukumomi a arewacin lardin Cape da ke Afrika ta kudu sun nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da samun ƙaruwar masu korona.

    Cutar na nuna alamun ci gaba da yaɗuwa a sauran sassan Afrka ta Kudu - ita ce dai ƙasar da wannan cuta ta fi yi wa illa a nahiyar.

    Bayan dogon hutu, an ta samun ƙaruwar cutar a yankuna da yawa, musamman a yankin kudancin ƙasar.

    Likitocin a Cape Town da kuma Port Elizabeth na ruwaito cewa ana ƙara samun marasa lafiayar da ake kwantarwa.

    Yanzu dai ƙasar na fuskantar lokacin zafi, lokacin da miliyoyin mutane ke tafiya.

    Duk da matsalar koma bayan tattalin arziƙin da ake fama da ita, gwamnatin ƙasar na duba yiwuwar ƙara sanya dokar hana fita.

  11. An bankaɗo badaƙalar naira biliyan uku a ma’aikatar gona ta Najeriya

    Wani bincike da aka gudanar ya bankaɗo wata badakala ta fiye da naira biliyan uku da ake zargin an yi a ma`aikatar gona ta tarayya.

    Jaridar Premium Times ce ta gudanar da bincike, wadda ta gano cewa an cire kudaden ne ta hanyar saka su a asussan wasu jami`an ma`aikatar.

    Jaridar ta lissafa sunayen ma`aikatan da adadin kudaden da aka saka a cikin asussan nasu, har ma da bayanin irin hidimar da aka yi ikirarin yi da kudaden.

    Ku saurari rahoton Ibrahim Isa.

    Video content

    Video caption: An bankaɗo badaƙalar naira biliyan uku a ma’aikatar gona ta Najeriya
  12. Masoyan Maradona na arangama da ƴan sanda

    Masoyan Maradona na arangama da ƴan sanda

    Dubban masoya Maradona sun yi arangama da ƴan sandan Argentina a yayin da suke ƙoƙarin zuwa wurin da aka ajije gawar fitaccen ɗan ƙwallon na duniya.

    Masoyan Maradona na arangama da ƴan sanda

    Dubban mutane ne ake sa ran za su kai ziyara fadar shugaban ƙasa domin yin gaisuwar girmamawa ta ban-kwana da gawar ɗan ƙwallon.

    A ranar Alhamis aka dawo da gawar Maradona zuwa fadar shugaban ƙasa Buenos Aires domin ba masoyansa damar yin ban-kwana da shi.

    Hukumomi na fargabar yaɗuwar annobar korona.

    Ranar Laraba ne Maradona ya rasu ɗaya daga cikin fitattun ƴan ƙwallon da ake ganin ba a taɓa yi ba.

    Masoyan Maradona na arangama da ƴan sanda
  13. An sake zaɓen Kaboré a Burkina Faso

    Kabore

    Shugaban Burkina Faso, Roch Marc Christian Kaboré, ya lashe zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar ranar Lahadi da kashi 57.9, kamar yadda hukumar zaɓen ƙasar ta bayyana.

    Manyan masu hamayya da shi Eddie Komboigo da Zephirin Diabre, sun samu kashi 15.5 da kuma 12.5

  14. Minti Daya da BBC Rana 26/11/2020

    Video content

    Video caption: Minti Daya da BBC Rana 26/11/2020
  15. An kama waɗanda suka yi wa mutum 5,000 kutse a intanet a Legas

    Masu kutse

    An kama wasu mutum uku a Legas kudancin Najeriya da ake zargi da yi wa mutum akalla 5,000 kutse a intanet a kasashe sama da 150.

    An kama su ne bayan ƙaddamar da wani samame na haɗin guiwa da jami’an Interpol da rundunar ƴan sandan Najeriya da ke yaƙi da kutse a intanet.

    Binciken na tsawon shekara guda, wanda aka yi wa laƙabi da suna Falcon, ya gano aƙalla mutum dubu 50 waɗanda lamarin ya shafa.

    Ana zargin da yin amfani da hanyoyi ta intanet da aika sakwanni da yawa ga ta hanyar yi wa wakilan hukumomi sojan gona.

    Masana sun ce ayyukan kutse a intanet ya ƙaru a Najeriya lokacin annobar korona.

  16. Bidiyon jana'izar tsohon shugaban Nijar Tandja Mammadou

    Video content

    Video caption: Bidiyon jana'izar tsohon shugaban Nijar Tandja Mammadou
  17. Yadda ake jimamin mutuwar Maradona a Argentina

    Gawar Maradona

    Dubun dubatar ƴan kasar Argentina ne suka yi jerin gwano domin girmamawa ta karshe ga gawar Diego Maradona a fadar shugaban kasa da ke Buenos Aires inda aka ajiye gawar fitaccen ɗan ƙwallon ƙasar.

    Wasu na kuka, wasu kuma suna sumbata daga nesa suna addu’a a yayin da suke wuce akwatin gawar Maradona.

    Argentina
    Argentina
    Argentina

    Masoyan sun kafa dogon layi da cunkoson mutane kan tituna a waje, inda masoyan ɗan ƙwallon ke ƙetara shingayen da jami’an tsaro suka kafa.

    Diego Maradona na ɗaya daga cikin ƴan ƙwallon da ake ganin ba a taɓa yi ba, ya mutu ne sakamakon bugun zuciya a ranar Laraba, yana da shekaru sittin.

    Argentina
    Argentina
  18. Tsadar albasa ta tabbatar da wahalar da ake ciki a Najeriya - Sarkin Musulmi

    Mai alfarma Sarkin Musulmi Abubakar Sa'ad III ya yi bayani kan matsalolin tsaro da tattalin arziki da Najeriya ke fama da su.

    Da yake jawabi a wajen taron majalisar shugabannin addinai ta Najeriya, Sarkin Musulmin ya bayyana girman matsalar tsaro inda ya ce "yanzu ƴan fashi har cikin gida suke zuwa su garkuwa da mutane," kamar yadda Shafin Twitter na Majalisar ƙoli ta harakokin addinin musulunci ya bayyana.

    Sarkin Musulmin kuma ya ce yadda albasa ta yi tsada ya tabbatar da girman wahalar tattalin arzikin da ake ciki a yanzu a Najeriya.

    View more on twitter
  19. An yi wa sojojin ruwan Najeriya 203 ƙarin muƙami

    Sojin ruwan Najeriya

    Kimanin sojojin ruwa 203 aka yi wa ƙarin matsayi a Najeriya.

    Sanarwar da rundunar sojin ruwa ta aike wa BBC ta ce an ƙara wa jami’an muƙamin ne a ranar Laraba.

    Masu muƙamin Laftanal kwamanda 122 aka ƙara muƙami zuwa Kwamanda, yayin da kuma masu muƙamin Kwamanda 38 aka ƙara masu matsayi zuwa Kaftin.

    Masu muƙamin Kaftin 25 kuma aka yi wa ƙarin matsayi zuwa Kwamado.

  20. Jiragen Daular Larabawa sun fara jigila zuwa Isra’ila

    An fara jigilar jirage a karon farko daga Dubai zuwa Tel Aviv a ranar Alhamis bayan daidaita alaƙa tsakanin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Isra'ila a watan Satumba.

    Firayiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu yana halartar bikin soma jigilar kamfanin flydubai, wanda zai yi jigila sau biyu a rana

    A watan gobe ne jiragen Isra’ila kuma guda biyu za su fara jigila tsakanin Tel Aviv da Dubai.