Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Fauziyya Kabir Tukur da Umar Mikail

time_stated_uk

  1. Ƙarshen rahotannin kenan

    Ƙarshen rahotannin kenan a wannan shafi. Umar Mikail ke fatan za ku kasance tare da mu gobe da safe domin sanin halin da duniya ke ciki.

    Kafin nan, za ku iya duba ƙasa don karanta labaran da muka wallafa a yau tun daga farar safiya.

    Mu zama lafiya.

  2. Za a fara yi wa malaman makaranta rigakafin cutar korona a Poland

    Poland za ta soma yi wa malaman ƙasar allurar rigakafin korona daga mako mai zuwa bayan shawarar da majalisar likitoci ta ƙasar ta bayar.

    Malaman da suke shiga azuzuwa domin koyar da ɗalibai a nazire da firamare ne za su zama na farko da za a fara yi wa rigakafin.

    Za a ci gaba da yin sauran darussa ta inatent. Wani jami'in gwamnatin ƙasar ya ce ƴan sanda da kuma sojoji ne rukuni na gaba da za a yi wa rigakafin.

    A ƙarshen watan Disamba ne ƙasar ta Poland ta fara rigakafin cutar, inda malaman lafiya da dattijan da suka haura shekara 70 suka zama rukunin farko da aka fara yi wa.

  3. Amurka za ta daina tallafa wa Saudiyya a yaƙin Yemen

    Yemen

    Amurka za ta janye goyon bayan da take bai wa Saudiyya a yaƙin da take jagoranta a Yemen na tsawon shekara 10.

    Alƙaluma sun nuna cewa aƙalla mutum 110,000 aka kashe tun daga shekarar 2014.

    Mai bai wa sabon Shugaban Amurka Joe Biden shawara, shi ne ya sanar da sauyin manufar a yau Alhamis.

    Sanarwar na nufin matakin zai shafi harin da gwamnatin Yemen ke kai wa kan Houthi da kuma tallafa wa Saudiyya da bayanan yaƙi da Daular Larabawa (UAE), a cewar Jake Sullivan yayin wani taro a birnin Washington.

    Amurka ta goyi bayan ƙawancen ƙasashen da Saudiyya ke jagoranta a ƙarƙashin shugabancin tsofaffin shugabannin ƙasar guda biyu kafin Biden.

    Yaƙin ya jefa miliyoyin 'yan Yemen cikin matsananciyar yunwa.

    Yaƙi ya ɓarke tsakanin gwamnatin Yemen mai rauni da kuma 'yan tawayen Houthi a 2014. Ya ƙara rincaɓewa a 2015 bayan Saudiyya da ƙawayenta guda takwas sun fara luguden wuta tare da goyon bayan Amurka da Faransa da Birtaniya a kan Houthi.

  4. An hana Liverpool shiga Jamus don buga wasan Champions League

    Liverpool

    Hukumomi a Jamus sun hana ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool shiga ƙasar domin buga wasan farko na zagayen 'yan 16 a gasar Champions League da ƙungiyar RB Leipzig saboda cutar korona.

    An tsara buga wasan ne ranar 16 ga watan Fabarairu a gidan Leipzig kafin daga baya ma'aikatar cikin gida ta bayar da sanarwar hana tawagar Liverpool shiga ƙasar.

    Leipzig ta yi fatan a yi mata alfarma bayan gwamnatin Jamus ta haramta wa 'yan ƙasashen da ke fama da sabon nau'in cutar korona shiga ƙasarta har zuwa 17 ga watan Fabarairu.

    Bisa tanadin dokar UEFA, ya rage wa Leipzig ta naemi wani wurin da za a buga wasan, yayin da ake tunanin za a buga shi a birnin Landan.

    Wani zaɓin shi ne, ƙungiyoyin za su iya yanke shawarar sauya wurin buga wasan, abin da ke nufin za a iya fara bugawa a Anfield, gidan Liverpool.

    Ita ma Manchester City za ta fuskanci Borussia Moenchengladbach a Jamus ranar 24 ga Fabarairu, sai dai ana sa ran za a ɗage haramcin shiga ƙasar kafin loƙacin.

  5. An yi wa Fulani makiyaya biyar yankan rago a Jihar Filato – Miyetti Allah

    Video content

    Video caption: Latsa hoton sama ku saurari rahoton Zahradden Lawan

    Ƙungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti-Allah reshen Jihar Filato ta yi zargin an yi wa makiyaya biyar yankan rago yayin wani hari da aka kai a kauyen Maiyanga da ke yankin Ƙaramar Hukumar Bassa ta Jihar.

    Lamarin dai na zuwa ne mako guda bayan maharan da ake zargi sun aikata kisan sun kashe Fulani biyu lokacin da suke kiwo a ƙauyen na Maiyanga, lamarin da ya kara zaman ɗar-ɗar a yankin.

    Wani mamba a ƙungiyar mai suna Zakari Ya'u Idris ya shaiada wa BBC cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na ranar Talata wasu mutane suka auka wa makiyayan.

    Ya ce an kashe mutum biyar sannan guda ɗaya ya ɓace tare da sace musu shanu fiye da 40.

  6. Belgium ta ɗaure jami'in Iran tsawon shekara 20 a gidan yari

    Wata kotu a Belgium ta yanke hukuncin ɗaurin shekara 20 ga wani jamni'in diflomasiyya na Iran sakamakon samunsa da laifin kitsa kai harin bam ga dubban 'ƴan Iran da ke gudun hijira a Faransa 2018.

    Kotun ta bayyana cewa Assadollah Assadi, wanda ke zama a birnin Vienna, ya samu goyon bayan gwamnatin ƙasarsa a harin.

    Wakilin BBC ya ce 'ƴan sanda sun tabbatar cewa jakadan ya bai wa wasu ma'aurata sinkin bama-bamai, inda suka yi niyyar tayar da su yayin wata zanga-zangar 'ƴan hamayyar Iran a 2018.

    Masu gabatar da ƙara a Belgium din sun bayyana cewa, da ba don an daƙile harin ba da abin da zai faru zai yi matuƙar muni.

    Wannan ce sharia ta farko da aka yi wa wani jami'in gwamnatin Iran a Tarayyar Turai kan batun ta'addanci tun bayan juyin-juya halin da aka yi a Tehran a 1979.

  7. Mutum 18 sun kammala digiri a gidajen yarin Najeriya

    'Yan gidan yari

    Hukumar kula da gidajaen yari ta Najeriya ta ce ɗaurarru guda 18 ne suka kammala karatun digiri daga jami'ar karatu daga gida ta National Open University.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar mai suna Francis Enabore ya fitar a yau Alhamis ta ce tsararrun sun kammala jami'ar ne a fannoni daban-daban.

    Sanarwar ta ambato shugaban hukumar Mista John Mrabure yana taya su murnar kammala karatun sannan ya umarce su da su ɗauke shi a matsayin tubalin ginin rayuwarsu ta nan gaba.

    "Kusan 'yan gidan yari 3,000 ne ke karatu a jami'ar Open University yanzu haka, yayin da 50 ke karatun shaidar koyarwa ta NCE a kwalejin Yewa da ke Jihar Ogun," a cewar Francis Enabore.

    Ya ƙara da cewa hukumar na da cibiyoyin karatu guda 12 a gidajen yari da ke faɗin Najeriya.

    Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa wani ɗan gidan yari ne ɗalibi mafi hazaƙa a jami'ar Open University a shekarar 2014 daga gidan yari na Jihar Enugu, inda wani ɗaurarren ya sake cimma wannan matsayi a 2018 da gidan.

  8. Man City ta yi wasa 13 ba a doke ta ba a Premier League

    Manchester City

    Ranar Laraba Manchester City ta yi nasara a gidan Bunley a wasan mako na 22 a gasar Premier League ta ƙsar Ingila.

    Gabriel Jesus ne ya fara ci mata kwallo minti uku da fara tamaula, sannan Raheem Sterling ya kara na biyu saura minti bakwai su tafi hutun rabin lokaci.

    City mai kwantan wasa daya tana nan a matakinta na daya da tazarar maki uku tsakaninta da Manchester City ta biyu.

    Kawo yanzu kungiyar ta Etihad ta yi wasa 13 a gasar Premier ba tare da an doke ta ba ciki har da canjaras biyu.

    Rabon da City ta sha kash a gasar Premier tun bayan da Tottenham ta doke ta 2-0 ranar 21 ga watan Nuwamba, inda Heung-Min Son da kuma Giovani Lo Celso suka ci kwallayen.

    Karawar da ta yi canjaras biyu a wasa 13 nan sun hada da wanda ta tashi ba ci a Old Trafford ranar 12 ga watan Disamba da wanda kwana uku tsakani ta yi kunnen doki 1-1 da West Brom a Etihad.

  9. Buhari zai naɗa Buratai a matsayin jakada na musamman

    Buhari da Buratai

    Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya aike da sunayen tsofaffin shugabannin tsaro na ƙasar ga Majalisar Dattawa don amincewa da su a matsayin jakadu na musamman.

    Wata sanarwa da Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban, ya fitar ta ce Buhari ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan wasiƙa, inda yake neman amincewarsu.

    "Bisa tanadin sashe na 171 (1) da (2) (c) da sakin layi na (4) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya wanda aka yi wa kwaskwarima, ina mai neman amincewar Majalisar Dattawa don naɗa sunayen mutanen (5) da na lissafa a matsayin jakadu na musamman," in ji Buhari.

    Waɗanda za a naɗa sun haɗa da: Janar Abayomi G. Olonisakin (mai ritaya) da Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya da Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya) da Air Marshal Sadique Abubakar (mai ritaya) da Air Vice Marshal Mohammed S. Usman.

    Sanarwar ta ƙara da cewa shugaban ƙasar ya nemi majalisar da ta gaggauta tabbatar da sojojin a kan matsayin nasu.

    Mohammed S. Usman, shi kaɗai ne ba ya cikin manyan hafsoshin tsaron da Buhari ya sauke ranar Talata da ta wuce sannan ya maye gurbinsu da wasu domin ci gaba da jagorantar ayyukan tabbatar da tsaro a Najeriya.

    Sabbin hafsoshin tsaron da aka naɗa su ne:

    • Janar Leo Irabor - Babban Hafsan Tsaro
    • Air-Vice Marshal I.O Amao - Babban Hafsan Sojan Sama.
    • Rear Admiral A.Z Gambo - Babban Hafsan Sojan Ruwa
    • Janar I. Attahiru - Babban Hafsan Sojan Ƙasa.
  10. Labarai da dumi-dumiCutar korona ta kashe ƙarin mutum 915 a Birtaniya

    Ƙarin mutum 915 sun mutu a Birtaniya cikin sa'a 24 da suka wuce sakamakon cutar korona.

    Mutanen sun mutu ne kwana 28 da kamuwa da cutar, kamar yadda alƙaluman gwamnati suka nuna.

    Ya zuwa yanzu jumillar adadin waɗanda suka mutu cikin kwana 28 bayan sun kamu sun zama 110,250.

  11. Sai nan da 2022 duniya za ta wartsake daga cutar korona - MDD

    Cutar korona

    Al'ummar duniya ba za ta wartsake ba "har sai nan da 2022", a cewar ɗaya daga cikin manyan likitocin Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).

    Farfesa Helen Rees, wadda ke cikin kwamitin MDD kan annobar cutar korona, ta ce rigakafin farko-farko na cutar ba zai yi tasiiri ba sosai a kan sabbin nau'in cutar.

    Sakamakon haka ne, kamar yadda ta shaifda wa BBC, tasiirin allurar rigakafin ba zai yi ƙarfi ba har sai nan da 2022.

    Farfesar ta ce gwajin ƙarshe na rigakafin Novavax da Janssen ya nuna alamun nasara a kan sabon nau'in korona da aka samu a Afirka ta Kudu.

    Sai dai ta ce masana kiwon lafiya na nuna damuwa kan rigakafin AstraZeneca da na Pfizer saboda sun yi amfani ne da ƙwayoyin cutar na asali daga China, yayin da ake kara samun sabbin nau'in nau'i a ƙasashe.

  12. Mozambique za ta yi wa masu iƙirarin jihadi afuwa

    Rikici

    Shugaban Mozambique Filipe Nyusi ya yi tayin afuwa ga 'yan kasar da ke kungiyar masu ikirarin jihadi a lardin Cabo Delgado mai arzikin mai.

    Shugaba Nyusi ya yi alkawarin cewa ba za a hukunta wadanda suka mika wuya ba kuma za a ba su damar komawa wurin iyalansu.

    Ya yi alkawarin ne ranar Laraba a lokacin da kasar ke bikin tunawa da mazan jiya.

    Ya mika tayin afuwar ga 'yan kasar da suka shiga kungiyoyin 'yan tada kayar baya da ke da alaka da jam'iyyar adawa taRenamo.

    Daruruwan mutane ne masu ikirarin jihadin suka kashe a Cabo Delgado, wadanda suka kaddamar da hare-harensu a 2017.

    Kusan mutum 570,000 ne aka tursasa wa tserewa daga muhallansu.

  13. Ƙungiyar AU za ta fara raba wa kasashen Afrika riga-kafin korona nan da mako uku

    Riga kafin korona

    Ƙasashen Afrika goma sha shidda ne suka nuna sha'awar samun riga-kafin cutar korona karkashin tsarin Kungiyar Kasashen Afrika, kuma fatan shi ne a samar da allurar cikin makonni uku masu zuwa.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato shugaban hukumar da ke kula da yaduwar cutuka ta nahiyar da fadin haka.

    Sai dai John Nkengasong, shugaban hukumar bai bayar da ainihin ranar da za a samu riga-kafin ba.

    Dama dai AU ta samu allurar miliyan 270 daga kamfanonin da ke samarwa don rabawa kasashen nahiyar, sannan a karshen watan jiya ta sanar da samun karin alluran miliyan 400 daga kamfanin Astrazeneca.

    Kasashen Afrika da suka fara bayar da riga-kafi sun hada da Egypt da Guinea da Morocco da Seychelles.

    Afrika ta Kudu, wadda ke da yawan mutane masu dauke da cutar da wadanda suka mutu dalilin cutar a nahiyar, ta samu rukunin farko na riga-kafin ranar Litinin.

  14. Labaran BBC Hausa cikin minti ɗaya

    Video content

    Video caption: Minti Ɗaya Da BBC Hausa Na Rana 04/02/2021
  15. An rusa shirin kai harin 'ta'addanci' a ofishin jakadancin UAE

    Jami'an tsaron Habasha sun tsare wasu da ake zargi da aikata ayyukan ta'addaci 15, bayan rusa shirinsu na kai hari ofishin jakadancin Hadaddiyar Daular Larabawa a Addis Ababa.

    A wata sanarwa da ta fitar, Hukumar Leken Asirin Kasar ta ce tana bibiyar wasu mutum 21 da ake zargi.

    Sannan ta ce ana shirin kai wani harin a ofishin Jakadancin Hadaddiyar Daular Larabawa a Khartoum, Sudan amma jami'an tsaron Sudan sun dakile shi.

    An kwace manyan makamai ciki har da abubuwan fashewa a lokacin samamen a cewar Hukumar.

    Sanarwar ta bayyana cewa an kama shugaban 'kungiyar ta ta'addanci', Ahmed Ismael mai zaune a Sweden.

    Karin labarai:

  16. ICC: Shugaban ƴan tawaye a Uganda na fuskantar ɗaurin rai da rai

    Dominic Ongwe

    An yanke wa tsohon shugaban 'yan tawaye a Uganda, Dominic Ongwen, hukuncin aikata laifukan yaƙi a Kotun Hukunta Manyan Laifuka da ke Hague.

    Mista Ongwen, wani kwamanda mai kwarjini na kungiyar 'yan tawaye ta Lord Resistance Army, LRA shi ne mutum na farko a kungiyar da aka gurfanar a gaban kotun.

    Yana fuskantar tuhume-tuhume bakwai ciki har da kisa da daure mutane ba a bisa ka'ida ba.

    Tuhume-tuhumen dai sun danganci wani hari ne da aka kai kan wasu 'yan gudun hijira a Uganda a shekarar2004.

    Wannan shari'ar ta zamo mai sarkakiya ga kotun saboda ya kasance mai kara da wanda ake kara.

    Ya ce kungiyar LRA ta sace shi ne tare da tursasa masa zam soja a lokacin yana yaro kafin daga baya ya bunkasa ya zama mataimakin shugabna kungiyar Joseph Kony.

  17. Faisal Maina, ɗan Abdulrasheed Maina ya tsere Amurka don guje wa shari'a

    Faisal Maina

    Jaridar Vanguard ta Najeriya ta ruwaito cewa Faisal Maina, ɗan Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban kwamitin yi wa tsarin fansho na Najeriya garambawul. ya tsere Amurka, a cewar Hukumar EFCC.

    Lauyan EFCC, Mohammed Abubakar, ya bayyana wa Justice Okon Abang na Babbar Kotun Taryya a Abuja.

    Ana dai zargin Faisal Maina ne da halatta kudin haram.

    Lauya Mohammed Abubakar ya ce daga bayanan da suka samu Faisal ya tsere Amurkar ne ta jamhuriyar Nijar.

    A farkon zaman kotun na ranar Alhamis ne Justice Abang ya umarci wanda ya tsaya wa Fisal, Honorobul Sani Dan-Galadima mai wakiltar Kaura-Namoda a majalisar wakilai, da ya mika gida ko fili a matsayin kuɗin beli, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

    An bayyana cewa an bayar da belin Faisal ne bisa kudi Naira miliyan 60 da mai tsaya masa wanda dole ya kasance dan majalisar wakilai.

  18. An fara yi wa mutane gwajin allurar riga-kafin korona kala biyu

    Riga-kafin cutar korona

    An kaddamar da wani bincike a Burtaniya don ganin ko za a iya yi wa mutane allurar riga-kafin korona na kamfanonin daban-daban.

    Gwajin ya kunshi yin allurar farko da riga-kafin wani kamfani sannan a yi allura ta biyu da ta wani kamfanin na daban.

    Ana yi wannan ne don ganin ba a rasa yadda za a yi ba dangane da samuwar allurar.

    Masana kimiyya sun ce bayar da allura daga kamfanoni daban-daban na iya bayar da kariya mafi inganci.

    Ministan harkokin riga-kafi ya ce ba za a yi wasu suye-sauye dangane da tsarin riga-kafin BBC ba sa nan da a kalla wata 4.

    Dama dai a kan yi haka, duk da cewa ba a cika yi ba, idan babu kala guda ko kuma ba a san allurar wane kamfani ba ne aka bayar da farko.

    Masana na ganin cewa harhada riga-kafin da ake gwadawa yanzu zai amfani mutane - a lokacin da aka yi fama da cutar Ebola an yi irin wannan hade-haden kuma an ga alfanunsa.

  19. Gobara ta cinye wata kasuwa a Abuja

    Gobara

    Gobara ta tashi da asubahin ranar Alhamis a kasuwar Tippee da ke 3rd Avenue a unguwar Gwarimpa a Abuja,.

    Rahotonni sun nuna cewa gaba daya shagunan kasuwar sun kone yayin da mutum daya ya rasa ransa wasu da yawa kuma sun samu raunuka.

    Wasu mazauna unguwar sun ce gobarar ta faru ne sanadiyyar wutar lantarki a wasu shaguna da misalin karfe sha biyu na dare.

    An ruwaito cewa ta yi kusan awa biyu tana ci kafin jami'an kashe wuta suka iso kuma a lokacin wutar ta riga ta yi nisa.

    Jaridar The Nation ta bayyana cewa wasu bata-gari sun yi amfani da wannan damar wajen sace kayan wasu shagunan.

  20. Saudiyya ta rufe gidajen cin abinci da na kallo saboda korona

    Saudiyya

    Saudiyya ta sanar da dakatar da harkokin nishadi da rufe gidajen kallo da gidan cin abinci tsawon kwanaki 10, a wani mataki na daƙile cutar korona.

    Ma'aiktar harkokin cikin gida ta ce adadin masu fama da cutar na ƙaruwa a kasar kuma tana ganin wannan matakin zai taimaka wajen hana cutar ci gaba da yaɗuwa.

    An kuma dakatar da shagulgula ciki har da bikin aure da taruka tsawon kwana 30.

    Kawo yanzu, mutum 369,000 ne suka kamu da cutar korona a Saudiyya yayin da mutum 6, 400 suka mutu. Ita ce kasar da ta fi ko wacce yawan mutanen da suka mutu saboda cutar a kasashen yankin Gulf.

    A jiya ne kasar ta ɗauki matakin rufe iyakokinta ga baki daga wasu ƙasashe 20 cikin har da Amurka da Masar da Lebanon da Turkiyya.

    Ranar 17 ga watan Disamba ne Saudiyya ta kaddamar shirin riga-kafin korona bayan samo allurar daga Veserbiontech.