Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Halima Umar Saleh, Muhammad Annur Muhammad da Umaymah Sani Abdulmumin

time_stated_uk

  1. Bankwana

    Da haka muke sallama da ku a wannan shafin da ke kawo labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. Sai kuma gobe Asabar da yardar Allah.

  2. An bada sanarwar sake fasalin tsarin biyan haraji a duniya

    An bada sanarwar sa ke fasalin tsarin biyan haraji na kasa da kasa wanda shi ne mafi girma bayan watanni ana tattaunawa tsakanin kasashe 140.

    An kamala Tattaunawar da aka yi a Paris karkashin jagorancin kungiyar hadin-kan tattalin arziki da ci gaba da matsayar da ta nemi kamfanonin kasashen waje biyan mafi kankanta haraji na kashi goma sha biyar.

    A shekarar 2023 matsayar da aka cimma za ta soma aiki.

    Wakilin BBC ya ce kwararu daga kungiyar ta OECD sun yi ammanar cewa kasashe za su samun karin kudin da yawansu ya kai dala biliyan 150 daga harajin da za a karba a kowace shekara a duniya.

    Sai dai kasashe hudu da suka hada da Kenya da Najeriya da Sri lanka da kuma Pakistan kawo yanzu ba su shiga cikin yarjejeniyar ba.

  3. Mutane sun mutu a wajen tsare 'yan ci-rani a Tripoli

    Tripoli

    Ma’aikatan agaji sun ce akalla mutum biyar aka harbe a wani wuri da ake tsare da 'yan cirani a Tripoli babban birnin kasar Libya.

    Hukumar kula da kaura ta duniya wato IOM ta ce cunkuso ne ya haddasa hargitsi a wurin, daga nan kuma aka soma harbi.

    Akwai rahotanin da ke cewa fursononi da dama sun tsere aga cibiyar.

    Mahukuntan Libya sun kama 'yan cirani sama da dubu biyar a baya-bayanan a samamen da suka kai a wurare daban daban da ke birnin Tripoli.

    Ma’aikatan agaji sun yi magana akan mutanen da aka lakadawa duka da aka ajiye a cikin mawuyacin hali kurkukun da suka cika makil a wurare da dama.

  4. An kashe kauyawa, da cinna wuta a masarauta a wani samamen sojoji a Imo

    Aƙalla mutum uku suka mutu da kona gidaje 15, ciki harda fadar masarautar Aborshi na al'ummar Izombe da ke karamar hukumar Oguta a jihar Imo da ke kudancin Najeriya.

    Shaidu sun daura alhaki kan sojoji da suka kai harin ramuwar gayya a cewar Jaridar Daily Trust ta Najeriya.

    Rahotanni na cewa sojojin sun fusata ne bayan kisan abokan aikinsu biyu da ake zargin matasan Izombe da aikatawa.

    Wani shaida ya sanar da cewa matasa na bore kan kisan wani matashi da aka bayyana sunansa da Chukwunoso Iherue, zanga-zangar ce ta kai ga hallaka sojojin biyu.

    Kakakin sojin runduna ta 34, Capt Joseph Akubo, a lokacin da aka tuntube shi ya shaida cewa ba shi da cikakken masaniya kan abin da ya faru.

    Sai dai ya alkawarta bada bayanai da zaran ya samu karin haske.

  5. Buhari ya kai ziyara Kaduna

    Shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci Kaduna a wannan Juma'ar domin halarta bikin yaye sojoji daga makarantar sojoji ta NDA.

    Buhari ya samu tarba daga gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da wasu manyan jami'an gwamnati da na tsaro.

    B
    B
    B
    B
  6. Na yi farin cikin dawowar hada-hadar kasuwar dare a Banki - Zulum

    ZULUM

    Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum ya ce yana cikin farin ciki ganin dawowar hada-hadar kasuwanci a kasuwar dare ta Banki.

    Zulum wanda ya je kasuwar a daren jiya Alhamis domin gane wa idonsa ya shaida jin dadinsa ganin har karfe 10:30pm harkokin kasuwanci na tafiya cikin kwanciyar hankali.

    Ya ce wannan yanayi shi ne mafi farin ciki a rayuwarsa tun da ya hau mulki shekaru biyu da suka gabata.

    Bayan tattaunawa da 'yan kasuwar, gwamnan ya bada umarni raba musu naira miliyan 50 domin sa ke habbaka kasuwancinsu da ke tasiri sosai ga tattalin arzikin yankin.

    Banki na ɗaya daga cikin gari mafi girman hada-hadar kasuwanci a Maiduguri wanda ya haɗa iyaka tsakanin Najeriya da Kamaru da ke karamar hukumar Bama a Borno.

    Kuma yankin ya yi fice a kasuwancin dare, kafin mayakan Boko Haram su tarwatsu a 2014, da tilastwa mazauna yankin tserewa da neman mafaka a kasashe makwabta.

  7. Saliyo ta sauke yanke hukuncin kisa

    Saliyo ta sauke hukuncin kisa bayan shugaba Julius Maada Bio ya sa hannu kan sabuwar dokar da 'yan majalisa suka aminta da ita tun watan Yuli.

    Shugaban ya ce wannan na nuna darajar da ake bai wa kowanne rai a kasar.

    Kungiyar Amnesty ta ce hukunce-hukunce 39 da aka yanke na kisa ba a aiwatar da su ba.

    Kuma babu wanda aka kashe a Saliyo tun 1998.

    Saliyo ta kasance kasa ta 23 a Afirka da ke sauke hukunci kisa a cewar jaridar New York Times.

  8. 'Yan jaridar da suka lashe kyautar Nobel

    Jarida

    Wata 'yar jaridar ƙasar Philiphines Maria Ressa da Dmitry Muratov ɗan kasar Rasha su ne suka lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel ta bana.

    Shugabar kwamitin bada Nobel ɗin, Berit Reis Andersen ta ce an ba mutanen biyu kyautar ce sakamakon gwagwamayar da suke yi na samun 'yancin tofa albarkacin baki a kasashensu.

    Ta kuma ce Ms Ressa da Mista Muratov sun wakilici dukkanin 'yan jarida a duniya da ke fafutikar tabbatar da mulkin dimukuradiyya da 'yancin aikin jarida.

    A jawabin da ta yi bayan sanarwar, Miss Ressa ta ce lokaci ya yi da duniya za ta haɗa kai domin magance matsalar labaran karya.

    Ta kuma ce abinda ke faruwa a tsarin yaɗa labarai shi ne labaran karya da aka shigo da su ta kafofin sada zumunta kuma hakan na shaffar mutane.

    Kyautar ta Nobel ta haɗa da kuɗi sama da dala miliyan ɗaya.

  9. Mutum dubu 10 sun tsere sakamakon rikici a Yemen

    Ma’aikatan agaji sun ce karuwar faɗa tsakanin dakarun gwamnati da mayakan Houthi a arewacin Yemen ya tilastawa mutum kusan dubu goma tserewa daga gidajensu a makonnin baya-bayanan.

    Hukumar kaura ta duniya ta ce tashin hankalin da ke faruwa a yankin Marib ya yi sanadin mutuwar farar hula tare da raunata wasu.

    Rahotanni na cewa a wata gunduma an hana mutum sama da dubu talatin samun kayayyaki ma su muhimmanci .

    A baya-baya nan 'yan tawayen sun kara ƙaimi wajan kwato Marib wanda shi ne yanki na karshe da ke karkashin ikon gwamnati a arewacin kasar

  10. Tiwa Savage na fuskantar barazanar ɓacin suna kan bidiyonta na baɗala

    TIWASAVAGE

    Fitacciyar mawakiyar Najeriya Tiwa Savage ta ce ana yi mata barazanar kwarmata wani hoton bidiyonta da saurayinta na baɗala.

    A lokacin da take tattaunawa da wata tashar rediyo a Amurka mawakiyar ta ce ba za ta biya ko sisi ga mutumin da ya ke mata barazana ba.

    Da fari an soma tura sakon barazanar ne ga manajanta a ranar Laraba wanda kuma nan take ya sanar da ita da kuma adadin kudin da aka nema ko a wallafa bidiyon.

    Ta kuma shaida cewa saurayinta ne a bisa kuskure ya soma ɗaura hoton a shafin sada zumunta kuma nan take ya goge, sai dai tuni mai yi mata barazanar ya yi sa'ar sauke bidiyon.

    Tiwa ta ce a halin yanzu saurayinta na cikin damuwa.

    Mawakiyar ta ce da farko ba ta ji dadin faruwar lamarin ba, amma dai kuma ba za ta amince a yi amfani da wannan damar wajen ɓata mata suna ko durkusar da ita ba.

  11. Harim bam ya hallaka 'yan shi'a 50 a masallacin Kunduz

    Kunduz

    Jami'ai a arewacin Afghanistan sun ce mutum sama da hamsin ake fargabar sun rasa rayukansu a harin kurnar bakin wake da aka kai wa masallacin 'yan shi'a.

    Haka kuma gwamman mutane sun jikkata. Hotunan da aka ɗauka daga cikin masallacin da ke Kunduz babban birnin lardin Kunduz sun nuna barnar da bam din ya yi da kuma jina-jina.

    Kawo yanzu ba a san ko su wane ne ba suka kai harin. Sai dai wakilin BBC ya ce a baya wani reshen kungiyar IS ya rika kai wa mabiya shi'a da basu da rinjaye a kasar hari.

    Kungiyar ta kuma kai wa Taliban hari a baya-bayanan wadda ba ta amince da gwamnatinsu ba.

  12. 'Yan sandan sun ceto matasa da ake azabtarwa a gidan-mari a Kano

    kano

    Ƴan sanda a Najeriya sun ceto mutum 47 daga wani gidan mari a jihar Kano.

    Gidan da ake bayyanawa da gidan gyaran hali wuri ne da iyaye kan tura 'ya'yansu da ke muggan dabi'u da shaye-shaye da aikata manyan laifuka.

    Lokacin da 'yan sanda suka kai samame a ranar Alhamis, sun ceto mutum 47 duk maza da shekarunsu ke tsakanin 14 zuwa 35 sanye da sarkoki. Jikinsu duk dauke ya ke da alamar duka.

    kano

    Kakakin 'yan sanda Abdullahi Haruna ya shaidawa BBC cewa an cafke mutumin da ke da gidan mari kuma za a gabatar da shi a kotu.

    Gwamnatin jihar dai ta haramta irin wadannan gidaje watanni 10 da suka gabata bayan kai sameme a ire-iren wadannan gidaje da ake cin zarafi ko azabtar da mutane da sunan tarbiyya.

    'Yan uwa da iyayen yara na cewa su na aike yaransu irin wadannan wurare ne saboda rashin cibiyoyin gwamnatin na gyara hali.

    Mutanen da ake ceto yanzu haka na samun kulawa a asibiti.

  13. DSS ta saki ɗan fim ɗin kudancin Najeriya da ta kama kan zargin alaƙa da IPOB

    Chiwetalu Agu

    Ƴan fim da dama a Najeriya sun yi Allah-wadai da kama wani fitaccen abokin aikinsu, Chiwetalu Agu, wanda rundunar sojin Najeriya ta kama shi sakamakon saka kaya mai zanne tutar ƴan awaren Biafra.

    Sai dai kafar yaɗa labaran Punch ta ruwaito cewa an sake shi da safiyar yau.

    Rundunar sojin ta ce ɗan fim ɗin yana tunzura mutane mutane su shiga cikin ƙungiyar da ke fafutukar masu son kafa ƙsar Biafra ta IPOB.

    Sai dai rundunar sojin ta musanta rahotannin da ke cewa an ci zarafinsa lokacin da aka kama shi a birnin Anaca na jihar Anambra a jiya Alhamis.

    Hukumomin Najeriya sun alaƙanta IPOB da kashe-kashen da aka dinga yi a wannan shekarar a yankin kudu maso gabashin ƙasar - inda yawancin waɗanda aka kashe ɗin ƴan sanda ne.

    Sai dai ƙungiyar IPOB ta sha musanta zarge-zargen.

  14. An tashi taron PDP lafiya babu saɓani

    PDP

    Taron jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya da gabaninsa aka dauka za a tashi baran-daran ko kuma a yi ta kare tsakanin ‘yan arewa da kudu, sai ga shi an shiga daki an rufe kofa an yi shi kalau.

    Abin da aka yi tsammani za a samu ƙiƙi-ƙaƙa da rarrabuwar kawuna a taron kwamitin zartarwar PDP a jiya shi ne shugabancin jam’iyyar sai dai hakan bai yiwu ba.

    Hakan ya faru ne kasancewar jam’iyyar ta amince da warewa bangaren arewaci shugabancin PDP ɗin, amma kowanne yanki na da damar fitowa a dama da shi a takarar shugabancin kasa.

    Felix Hassan shugaban PDP na jihar Kaduna kuma shugaban kungiyar shugabanin jam’iyyar PDP na jihohi, ya ce abin da ya faru ba sabon abu ba ne, kuma a cewarsa ganin yadda ‘ya’yan jam’iyyar suka tashi suna haba-haba da juna to sun dauki turbar dinke barakar da ke neman yi musu sakiyar da ba ruwa.

    Shugabancin PDPn dai ya nanata cewa matakin rarraba mukaman bai shafi shugabancin kasa ko na majalisa ba.

    A karshen wannan watan ne jam`iyyar PDP za ta yi babban taron ta na kasa, inda magoya bayan ta za su zabi sabbin shugabanni.

    Tun da farko dai a kalamansa gabanin fara taron kwamitin zartarwar, tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya ce matakin da PDP ta dauka kan yankin da zai fitar da dan takara da sauran batutuwa su ne za su yanke hukunci kan zaben 2023.

    Wasu na kalloon kalaman a matsayin ba-girin-girin-ba ta yi mai.

  15. Jiragen yaƙi na sojin Najeriya sun hallaka ƴan bindiga a dazukan Sokoto da Katsina

    sojin Najeriya

    Sojojin Najeriya sun yi nasarar hallaka ɓarayin daji da dama tare da lalata maɓoyarsu a dazukan jihohin Sokoto da Katsina a yankin arewa maso yamma, kamar yadda jaridar intanet ta PRNigeria ta ruwaito.

    A jihar Sokoto sojojin ƙarƙashin shirin HADARIN DAJI sun kai hare-hare ne ta sama a dazukan Mashema da Yanfako da Gebe da Gatawa a ƙananan hukumomin Isaa da Sabon Birni.

    Wata kafa ta sojojin Najeriyar ta sheda wa jaridar ta PR cewa an samu nasarar hakan ne a ruwan bama-bamai da suka yi ranar biyar ga watan Oktoba 2021, bayan binciken da aka yi ta yi ta sama inda aka gano wuraren da ɓarayin dajin ke zaune.

    Rahotan ya bayyana cewa mutanen yankunan da aka kai hare-haren sun bayar da labarin cewa sun ga ɓarayin da ke tserewa sun fake a wata makarantar furamare a ƙauyen Bafarawa.

    A jihar Katsina jaridar ta PRNigeria ta ce ta gano cewa jiragen yaƙin sama na Najeriya sun yi ruwan bama-bamai a maɓoyar ɓarayin a dajin Rugu da ke da iyaka da Karamar Hukumar Ƙanƙara a tsakanin ranar 30 ga watan Satumba da 3 ga watn Oktoba na wanan shekara.

    A ɗaya daga cikin hare-haren an lalata sansanin wani ɗan ta'adda da ake kira Gajere inda aka kashe yaransa 34, wasu kusan 20 kuma suka samu raunuka in ji rahoton jaridar.

  16. Sama da mutum 60 sun ɓata bayan da jirgin ruwa ya kife a Mozambique

    Taswira

    Sama da mutum sittin yawancinsu yara sun ɓace ɓat, bayan da jirgin ruwan da suke tafiya a cikinsa ya kife da su a wani yanki na gaɓar tekun Mozambique kamar yadda rahotanni suka ce.

    Jirgin wanda ke ɗauke da mutane da kaya ya bar tashar jirgin ruwa ta Nacala ne da misalin karfe uku da rabi na rana agogon ƙasar, ranar Alhamis, inda zai je lardin Nampula da ke arewacin ƙasar, kamar yadda gidan rediyon gwamnatin ƙasar ya bayyana.

    Ana ganin rashin kyawun yanayi ne ya haddasa haɗarin, saboda daman an yi fama da rashin kyawun yanayi a ranar ta Alhamis a lardin.

    Wasu rahotanni sun ce mutum 17 daga cikin waɗanda ke cikin jirgin sun tsira bayan da suka yi iyo suka fita daga ruwan.

    Wani jami'in ƴan sanda da ya tabbatar da aukuwar haɗarin ya ce tuni an tura ma'aikatan lafiya da ƴan sanda da kuma wasu shugabannin yankin wurin da abin ya faru.

    Masu aikin ceto na can na neman gawarwaki domin tantance yawan waɗanda haɗarin ya rutsa da su kamar yadda jami'in ya kara da cewa.

    Ya ce sun samu labarin haɗarin ne daga shugabannin al'ummar yankin, kuma matsalar sadarwa da ake da ita a wurin ta sa ba a samu cikakken bayanin lamarin ba da wuri.

  17. Wasu shugabannin Kirista sun kai wa El-Zakzaky ziyarar jaje

    Zakzaky

    Wasu shugabannin addinin Kirista sun kai wa shugaban kungiyar ƴan Shi'a a Najeriya ta Harakar Islamiyya, IMN, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ziyarar goyon baya, sakamakon sakinsa da babbar kotun jihar Kaduna ta yi bayan tsare shi da matarsa Zeenat da aka yi kusan shekara shida.

    Ƴan tawagar ta fasto-fasto da suka ziyarci jagoran na IMN wata biyu bayan da kotun ta sake shi, sun ce ƙari a kan goyon bayan sun kuma je ne domin su nuna godiya kan taimakon abincin da yake bai wa matan Kiristoci da suka rasa mazajensu a sanadiyyar matsalar rashin tsaro, kamar yadda sanarwar da mataimakin sashen yada labarai na kungiyar ta IMN Abdullahi Usman ya fitar ta nuna.

    A sanarwar wadda jaridar Punch ta Najeriya ta wallafa, El-Zakzaky wanda ya bayyana irin mawuyacin halin da ya shiga da matarsa, ya ce kusan shekara shida bayan harin watan Disamba na 2015 da sojoji suka kai masa da magoya bayansa har yanzu akwai ɓurɓushin harsashi a jikinsa da na matarsa Zeenat.

    Ya yi alƙawarin ci gaba da gudanar da aikin jin ƙai, yana mai cewa bayar da taimakon abinci abu ne da ya wajaba domin yaƙi da yunwa a Najeriya.

    Da yake bayyana malaman Kiristan da suka ziyarce shi a matsayin 'yan uwa wajen kyautata wa al'umma, malamin ya ce in ba domin yanayin lafiyarsa ba da rashin tsaro a kasar da zai so ya hadu da ƙarin mutane.

    Daga cikin ƴan tawagar Kiristocin akwai Fasto Yohanna Buru daga Kaduna da Rabaran Titus Ishaku daga Cocin Baptist ta Jos da Rabaran John Ahmadu daga Abuja da Rabaran Peter Audu shi ma daga Abuja sai Rabaran George T. John na Kaduna tare da Fasto Julius Audu.

    Rabaran John Ahmadu ya ce kafin haɗuwa da El-Zakzaky, yadda yake ɗaukar Musulmi da Musulunci da ban ne.

  18. Farashin kayan abinci ya tashi a duniya

    shinkafa

    Shugaban daya daga cikin manyan kamfanonin samar da kayan abinci na duniya na Kraft Heinz, ya ce ya kamata mutane su saba da tsadar kayan masarufi.

    Miguel Patricio ya shaida wa BBC cewa matsin tallatin arziki da hauhawar farashin kayayyaki da kasashe ke fuskanta sakamakon barkewar annobar cutar korona na daga cikin dalilan da lamarin ya yi kamari.

    Ya kara da cewa kamfaninsa ya fuskanci tashin farashin kayayyakin da yake amfani da su wajen sarrafa kayan abinci, don haka dole abokan hulda su ma su fuskanci karin farashi.

    Amma ya ce fasahar zamani da sabon irin da ake da su ka iya taimaka wa manoma su kara samun amfanin gona mai kyau.

    Hukumar farashin kayan abinci ta majalisar Dinkin Duniya ta ce an fuskanci tashin farashin da ba a taba gani ba cikin shekaru 10.

  19. Ba mu da shirin dawo da rundunar SARS - Sufeto Janar na Ƴan sanda

    Sufeto Janar na Ƴan sandan Najeriya Usman Alkali Baba

    Rundunar ƴan sandan Najeriya ta musanta wasu rahotanni da ake yadawa a kafafe daban-daban cewa, shugaban rundunar Usman Alkali Baba ya bayar da umarnin sake kafa rundunar musamman ta yaƙi da ƴan fashi da makami da ake kira SARS, wadda aka rushe.

    A wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce ko alama ba ta da wata niyya ta dawo da rundunar, wadda ta riga ta rushe ta, ta kowa ce siga.

    Sanarwar ta ce tuni Sufeto Janar na ƴan sanda ya sake fasalin aikin rundunar kasar, ta yadda aka maye gurbin da aka samu na rashin waccan rundunar ta musamman ta SARS.

    A sanarwar ta ce, yanzu ba abin da shugabancin ƴan sandan na ƙasa ya mayar da hankali fa ce yadda zai ɓullo da sauye-sauye da za su sa ya bar tarihin rundunar da za ta kasance mai aiki tukuru, da amfani da fasahar zamani wajen gudanar da ayyukanta da mutunta jama'a da bin doka.

  20. Wani makusancin Biden ya gargadi Rasha kan amfani da makamashi

    Daya daga cikin makusantan Shugaba Joe Biden ya gargadi Rasha ka da ta yi amfani da damar ƙarancin makamashi ta hanyar da ba ta dace ba.

    Mai bai wa shugaban Amurka shawara kan sha'anin tsaro Jake Sullivan, ya shaida wa BBC cewa a baya-bayan nan Rasha na amfani da makamashi a matsayin makamin yaƙi.

    Wakilin BBC ya ce Rasha ita ce babbar mai sayarwa kasashen Turai makamashi, ana kuma ta kiraye-kirayen ya kamata ta ƙara adadin wanda ta ke saida wa kasashen Turan.

    Sai dai Ministan Harkokin Wajen Rasha Jean-Yves Le Drian, ya bayyana aniyar ƙasarsa na ƙara yawan makamashin da take saida wa kasashen Turai.