Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umaymah Sani Abdulmumin da Nasidi Adamu Yahaya

time_stated_uk

  1. Mu kwana lafiya

    A nan muke rufe wannan shafi da ke kawo muku labarai da rahotanni kai-tsaye.

    Ku kasance tare da mu gobe domin samun sabbin bayanai da suka shafi rayuwarku.

    Kuna iya ci gaba da tafka muhawara da bayyana ra'ayoyinku a ko da yaushe kuke so a shafukanmu na sada zumunta da muhawara.

    Mu kwana lafiya.

  2. Ana shirin kwashe 'yan Birtaniya daga Afghanistan

    Sojin Birtaniya

    A yayin da dakarun Amurka suka isa Kabul, gwamnatin Birtaniya ta sanar da shirin soma janye 'yan kasarta da sauran mutane da suka dace su tafi Birtaniyar.

    An soma aikewa da dakaru 600 domin taimakawa wajen kwashe 'yan kasar a shirin da ake kira Operation Pitting, yayin da kuma za a tura da jami'ai domin gaggauta tsarin bayar da biza da sauran takardu daga Afghanistan,a cewar sanarwar da gwamnati ta fitar

    Za a yi amfani da jirgi samfurin RAF idan bukatar hakan ta taso.

    Tun watan Afrilu aka kwashe fiye da ma'aikata 2,000 'yan kasar ta Afghanistan da ke yi wa Birtaniya aiki a kasar zuwa Birtaniya tare da iyalansu, in ji gwamnati.

    Birtaniya ta nemi 'yan kasarta su yi gaggawar ficewa daga Afghanistan kafin lamura su kazanta.

  3. Buhari ya dawo daga Birtaniya bayan an duba lafiyarsa

    Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma Abuja, babban birnin kasar daga Birtaniya bayan kwashe kwana 18 a kasar.

    Shugaban kasar ya isa Abuja da yammacin Juma'a bayan ya halarci taro kan ilimi a kasashen duniya wanda Firaiministan Birtaniya Boris Johnson da shugaban Kenya Uhuru Kenyatta suka jagoranta.

    Daga bisani likitoci sun duba lafiyar shugaban na Najeriya.

    Manyan jami'an gwamnati da ministoci na ciki wadanda suka tarbi Shugaba Buhari bayan isarsa filin jirgin saman Nnamdi Azikwe.

  4. Ahmed Joda ya ceto Najeriya daga rugujewa — Obasanjo

    Obasanjo

    Tsohon shugaban Najeriya cif Olusegun Obasanjo ya ce Malam Ahmed Joda, tsohon babban sakataren gwamnatin tarayyar kasar, yana cikin wadanda suka tabbatar da wanzuwar kasar a matsayin dunkulalliya.

    Ya bayyana haka ne a sakon ta’aziyyar da ya fitar domin alhinin rasuwar tsohon gogaggen ma’aikacin gwamnatin na Najeriya wanda ya rasu ranar Juma’a.

    Ya rasu ne a Yola babban birnin jihar Adamawa da shekara 91 a duniya.

    A sanarwar da Kehinde Akinyemi, mai magana da yawun cif Obasanjo ya fitar ranar Juma’a, ya ambato tsohon shugaban kasar yana cewa “wannan labari ne maras dadi na mutuwar abokina da muka yi fiye da shekaru 60 tare. Da a ce kowanne dan Najeriya yana da hali irin na Joda, da ta fi haka kyawu.”

    Ya kara da cewa Ahmed Joda da sauran manyan sakatarorin gwamnatin tarayya ne suka ceto kasar daga wargajewa “bayan hatsaniyar shekarar 1966”.

    Cif Obasanjo ya yi addu’ar Allah Ya jikan Ahmed Joda, Ya bai wa iyalansa hakurin jure rashinsa.

  5. Amurka za ta tura wakili na domin kawo karshen rikicin Ethiopia

    Habasha

    Amurka za ta tura jakada na musamman Ethiopia domin kawo karshen fadan yankin Tigray wanda ya yadu zuwa wasu yankunan kasar.

    Shugaba Joe Biden ya bukaci jakadan na musamman, Jeffrey Feltman, da ya koma Ethiopia a wannan matsanancin lokacin a cewar mai ba da shawara kan tsaro na kasa Jake Sullivan a shafin Twitter.

    Yakin a cikin watanni ya haifar da matsananciyar wahala da rarabuwar kawuna, da ba za a samu maslaha ba idan aka ci gaba da yakin.

    Jakadan na musamman zai tafi Ethiopia dake makwabta da Djibouti da Hadaddiyar Daular Larabawa UAE na kwana 10 daga Lahadi domin haduwa da hukumomin kan tattauna yadda za a tabbatar da zaman lafiya a yankin, a cewar ma’aikatar harkokin waje ta Amurka.

    Wannan mataki na zuwa ne bayan shafe wata 9 ana gwabza yaki tsakanin ’yan tawayen Tigrayan da sojin Ethiopia da kawayenta wanda a kwanakin nan ya yadu zuwa yankin Afar da Amhara.

    Rikicin ya tilasta mutane sama da miliyan guduwa daga gidajensu, inda dubbai suka shiga halin talauci.

  6. An dakatar da sanar da sakamakon zaben Zambia

    Hukumar zaben Zambia ta dakatar da bayyana sakamakon zaben kasar na dan wani lokaci, kamar yadda wakilyar BBC Nomsa Maseko ta wallafa a shafinta na Tuwita daga babban birnin kasar, Lusaka.

    Wasu daga cikin wakilan jam'iyyu sun soki hukumar zaben bisa yunkurin sanar da sakamakon zaben da ba a tantance ba.

    Wakilan jam'iyyun sun fice daga zauren da ake taro da jami'an hukumar zaben, a cewar wakiliyarmu.

    Kazalika ta wallafa bayanan da ake fitarwa daga wurin bayar da sakamakon.

    View more on twitter
  7. An yanke wa wani ɗan jaridar Algeria hukunci ɗauri

    Algeria

    An yanke wa wani dan jarida a Algeria Rabah Kareche hukuncin daurin wata 8 a gidan yari sakamakon wani rahoto da ya bayar kan zanga-zanga, a cewar gidan jaridar da yake yi wa aiki Liberte.

    An yanke wa M Kareche hukuncin shekara daya, sai dai an mayar da shi na wata takwas.

    A yanzu wata hudu ya rage masa a gidan yarin tunda ya riga yaci wata hudu daga Afrilu da aka kama shi da laifi zuwa yanzu.

    An kama shi bayan ba da rahoto a kan wata kungiyar tsiraru da ta gudanar da zanga-zanga kan tattalin arziki da nuna musu wariya.

    An same shi da lafin yada labaran karya da ka iya taay da rikici cikin al’umma.

    Kama shi da tsare shi sun jawo zanga-zangar ’yan jarida inda lamura suka tsananta bayan Shugaba Abdelmadjid Tebboune ya kamanta shi da mai tayar da fitina.

    Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty ta ce kama dan jaridar barazana ce ga 'yancin aikin jarida a kasar.

  8. Labarai da dumi-dumiTsohon Babban Sakataren Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ahmed Joda ya rasu

    Ahmed Joda

    Tsohon Babban Sakataren Gwamnatin Mulkin Sojin Najeriya kuma gogaggen ma'aikacin gwamnati, Malam Ahmed Joda, ya rasu.

    Daya daga cikin 'ya'yansa, Asma'u Joda, ta shaida wa BBC Hausa cewa mahaifin nasu ya rasu ne a birnin Yola na jihar Adamawa ranar Juma'a.

    Ya rasu yana da shekara 91 a duniya.

    Alhaji Ahmed Joda ya yi karatunsa a Najeriya da kuma Birtaniya inda ya halarci Kwalejin Pitmans da ke birnin London daga 1954 zuwa 1956.

    Ya yi aiki a bangarori daban-daban a Lardin Arewa kuma daga bisani ya rike mukamai da dama a gwamnatin tarayya.

    Yana daya daga cikin mutanen da ke yi wa lakabi da Super Permanent Secretaries, wato manyan sakatarorin gwamnati, a gwamnatin mulkin soja ta Janar Yakubu Gowon.

  9. Rikici tsakanin Shuwa Arab da masunta ya yi sanadin mutuwar mutum 12

    Gwamnatin Kamaru ta ce wani rikici da ya barke tsakanin Shuwa Arab da masunta na kabilar Mosgoum a yankin Arewa Mai Nisa.

    Gwamnan lardin Midjiyawa Bakari, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kara da cewa mutum 48 ne suka jikkata sakamakon rikicin wanda ya faru a Logone Birni, yankin na kusa da Kogin Logone da ke tsakanin Chadi da Kamaru.

    Masuntan sun gina wata matattara da kifaye suke shiga a yankin inda kuma a nan ne makiyayan suke bai wa dabbobinsu ruwa.

    Daya daga cikin shanun makiyayan ce ta mutu a wurin lamarin da ya haddasa rikici tsakanin bangarorin biyu.

    An tura sojoji domin su kwantar da hankali a yankin.

  10. An gano gawawwaki 6 na bakin-haure yashe a Sahara

    An gano gawarwakin mata biyu da yara hudu yashe a wani yankin saharar da ke kudu maso yammacin Tunisia.

    Rahotanni sun ce an gano cewa ’yan gudun hijira ne daga Jamhuriyar Nijar wadanda rashin ruwa yayi ajalinsu.

    Wanda ya rayu cikinsu ya bata garin nemo ruwan sha.

    ’Yan gudun hijirar sun tsallaka zuwa Tunisia daga Algeria a tafiya cikin tsananin zafin sahara.

    Tunisia masauki ne ga dimbin mutane da ke son ketarawa zuwa Turai.

  11. 'Abin da ya sa 'yan bindigar da suka yi garkuwa da ni suka zub da hawaye'

    Video content

    Video caption: Nasihar da na yi wa 'yan bindiga ta sa sun zub da hawaye - Kwamishinan jihar Neja

    Latsa hoton da ke sama domin sauraren hira da Kwamishina:

    Kwamishinan watsa labarai na jihar Neja da ke arewacin Alhaji Muhammad Sani Idris ya ce nasihar da ya yi wa mutanen da suka yi garkuwa da shi ta sa sun rika zubar da hawaye.

    Ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da BBC Hausa bayan ya kubuta daga hannun 'yan bindigar.

    A cewar "daga karshe da za mu rabu na ce don Allah su ba ni dama na yi musu bayani. Na ce da sun san yadda saduwarsu da Allah za ta kasance, ni na tabbatar ba za su yi [garkuwa da mutane] ba... Ina wannan maganar yawancinsu suka fashe da kuka."

    Ya kara da cewa ko da yake sun nemi ya bayar da kudin fansa da suka kai mnaira miliyan 200 amma ya gaya mus ba shi da wadannan makudan kudi.

    Sai dai ya ce sun daure hannaye da kafarsa tsawon kwana biyu suka kuma hana shi abinci.

  12. An tsare dubban yan ci-rani a iyakokin Amurka

    Jami'an da ke kula da iyakokin Amurka sun ce sun tsare sama da yan ci-rani dubu dari biyu da suka so shiga kasar daga Mexico watan da ya gabata.

    Wannan ne adadi mafi yawa na yan cirani da aka tsare lokaci guda a cikin shekaru 20.

    Shugaba Joe Biden ya ce yana son magance matsalar da ke haifar da kwarar yan ci-ranin tun daga tushe.

    Wakilin BBC yace shugaban ya sha alwashin hana zuwa kasarsa ci-ranin daga Tsakiyar Amurka ta hanyar rage talauci da cin hanci da kuma tashin hankali a kasashensu.

    Sai dai masu suka sun ce ya cika sanyin jiki wanda hakan ya sa ake samun karuwar tudadowar bakin haure.

  13. Yadda yara mata ke wahala wajen zuwa makaranta a kauyukan Kano

    Daya daga cikin matsalolin da yara ke fuskanta a bangaren neman ilimi a karkara musamman a kasashe irin Najeriya shine sukan yi doguwar tafiya kafin kaiwa ga makarantunsu.

    Garin Katarkawa da ke karamar hukumar warawa a jahar Kano na daga cikin yankuna da yara mata ke fuskantar irin wannan matsala, da ke barazana ga burinsu na ci gaba da karatu.

    Abokin aikinmu a Kano Khalifa Shehu Dokaji ya ziyarci garin, a saurari rahoton da ya hada.

    Video content

    Video caption: Rahoton Khalifa Shehu Dokaji
  14. Babban ɗan adawa ya buƙaci a maido da layukan intanet a Zambia

    Zambia

    Ɗan takarar bababr jam'iyyar adawa a Zambia ya yi kira ga gwamnatin ƙasar ta mayar da kafofin sadarwa na intanet da ta toshe yayin da ake manyan zaɓukan ƙasar.

    Hakainde Hichilema ya kuma nemi hukumar sadarwa ta ƙasar da ta kyale 'yan Zambia su rika samun sakamakon zaɓukan wanda ya ce yana cikin hakkokinsu na 'yan kasa.

    Tun ranar Alhamis aka rufe shafukan WhatsApp da Twitter da Facebook.

    Babu wani rahoton tashin hanakali da aka samu yayin zaɓukan da aka gudanar ranar Alhamis.

    Amma shugaba Edgar Lungu - wanda ke neman wa'adi na biyu ya yi korafi, yana cewa an tayar da hankula a yankin arewa maso yammacin ƙasar - yankin da abokin takarar sa ya fito.

    Hukumar zaɓen ƙasar ta ce za a sanar da cikakken sakamakon zaɓukan zuwa ranar Lahadi.

  15. Labaran duniya cikin minti ɗaya da BBC na Rana

    Video content

    Video caption: A saurari minti ɗaya da BBC
  16. Abubuwan da ba ku sani ba kan sabon nau'in cutar korona na Delta

    B

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta nahiyar Afirka ta ce an samu ɓullar cutar korona nau'in Delta a wasukarin ƙasashe hudu na nahiyar, abin da ya kai yawan ƙasashen da aka samu ɓullar irin wannan nau'i na cutar zuwa 30.

    Hakan na faruwa ne duk kuwa da cewa ƙasashen na Afirka na ci gaba da fama da cutar nau'ikan Alpha da Beta.

    Ana ci gaba da samun hauhawar masu kamuwa da cutar a ƙasashe daban-daban na nahiyar duk da kokarin da wasu ƙasashen ke yi wajen yin gwaji da kuma rigakafin cutar.

    A kan haka ne muka tuntubi farfesa Abdulsalam Nasidi, tsohon jami'i a cibiyar ta yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta Afirka, domin jin shin ya wannan nau'i na Delta yake.

    Video content

    Video caption: Tattaunawa da Farfesa Abdulsalam Nasidi
  17. An saki mai kamfanin Samsung da aka garkame sama da shekara ɗaya

    Jy Lee

    An saki shugaban kamfanin kayan lataroni na Samsung da ke Koriya ta Kudu bayan ya shafe sama da shekara daya a kurkuku.

    An kama Lee Jae Yong da laifin cin hanci da almuzzaranci, da hakan ya yi sanadin tumbuke tsohon shugaban kasa Park Geun Hye.

    Ma'aikatar shari'ah ta ce an saki Mr Jae Yong lura da halin matsin tattalin arzikin da kasar ta shiga saboda annobar Korona.

    To amma masu suka sun ce akwai lauje cikin nadi, irin yadda gwamnati ke sassauci ga hamshakan masu kudi a duk sadda suka yi laifi.

  18. Ƴan Najeriya na guna-guni kan harajin hawa hanya ga motoci

    Muhukunta Najeriya sun yi Karin haske a kan shirin gwamnatin kasar na karbar harajin hanya daga hannun masu abun hawa da ke bin wadansu titunan gwamnatin tarayya.

    Majalisar zartarwar kasar ce ta amince da tsarin karbar harajin hanyar.

    To, sai dai tsarin ba zai fara aiki ba sai masu zuba-jari sun sake gina ko ku ma gyara hanyoyin da suka lalace.

    Alhaji Babangida Husseini shi ne babban sakatare a ma`aikatar ayyuka da gidaje ta gwamnatin tarayyar, a saurari ƙarin bayanin da ya yi wa Ibrahim Isa.

    Video content

    Video caption: Tattaunawa da Babangida Husseini
  19. Harin ƴan bindiga a Ingila ya yi sanadi rayuka biyar

    Yan sanda a kudu maso yammacin Ingila sun ce an kashe mutun biyar a wani harin bindiga da aka kai birnin Plymouth.

    Wakilin BBC yace baya ga wadanda maharin ya kashe akwai kuma wadanda suka jikkata da yanzu haka ke karbar magani a asibiti.

    Kawo yanzu ba a gama tantance adadin wadanda abin ya rutsa da su ba.

    Jami'an tsaron sun roki wadanda suka dauki hotunan bayan harin da ka da su saka su a kafafen sada zumunta don girmama wadanda abin ya shafa.

  20. Saudiyya ta bai wa makarantu damar ɗaukar ƴaƴan marasa shaidar zama a ƙasar

    S

    Ma'aikatar ilimi a Saudiyya ta bukaci makarantu a duk yankunan kasar su bai wa ƴaƴan bakin da ke zama a kasar ba tare da izini ba gurabe a makarantu.

    Matakin wata dama ce ta baiwa yaran damar karatu a sabon zangon karatu na shekarar musulunci 1443.

    A wata sanarwa da aka turawa daraktan ilimi, mukadashin ministan ilimi, Dr Saad Al-Fohaid ya ce yana fatan makarantu za su gaggauta bin umarninsa domin ganin wadanan yara ba su cigaba da zama babu ilimi ba.A baya dai wasu tsare-tsaren Saudiyya musamman kan iyayen yara marasa shaidar zama ɗan kasar na tasiri wajen hana su samun ilimi da karuwar ɓata gari.