Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umaymah Sani Abdulmumin da Umar Mikail

time_stated_uk

  1. Ƙarshen rahotannin kenan

    Masu bibiyarmu nan muka zo ƙarshen rahotanni kai-tsaye a wannan shafi.

    Sai gobe Alhamis idan Allah ya kai mu.

    Umar Mikail ke muku fatan alheri.

  2. Namibiya ta yi gwanjon giwaye 57 ga ƴan ƙasashen waje

    giwaye

    Ma’aikar muhalli ta Namibia ta ce ta yi gwanjon giwaye 57 a inda ƴan kasar waje suka sayi kaso mafi yawa.

    Ma’aikatar ta ce an bukaci rage giwayen ne don rage kutsawarsu cikin mutane, sannan ta ce dala miliyan 400,000 da aka samu za ayi amfani da su wajen aikace aikacen tsarin mahalli.

    Amma masu suka sun ce giwayen ba su kai sun kawo ba in aka yi la’akari da ƙiyasin da gwamnati ta yi, sannan kuma hukumar ba ta da ikon sayar da dabbobin da suka saba yin ƙaura daga nan zuwa can a nahiyar.

  3. Shell zai biya mazauna yankin Ogoni na Jihar Rivers naira biliyan 45

    Kamfanin mai na Shell

    Katafaren kamfanin man fetur na Shell Petroleum Development Company ya amince ya biya naira biliyan 45 ga mazauna Ogoni na Jihar Rivers da ke yankin Neja-Delta a kudancin Najeriya.

    Mazauna Ƙaramar Hukumar Ejama-Ebubu waɗanda lauya Isaac Agbara ya wakilta tare da wasu tara, sun shigar da ƙarar ce shekara 32 da suka wuce suna neman a biya su fansar lalata musu ƙasa da Shell ya yi saboda kwararar mai.

    Tun a 2010 wata Babbar Kotun Tarayya a Najeriya ta umarci a biya su fansar amma aka yi ta ɗaukaka ƙarar har zuwa Kotun Ƙoli.

    Kotun Ƙolin ta tabbatar da hukuncin a 2019, sai dai kamfanin na ƙasar Netherlands ya ci gaba da neman yadda zai guje wa biyan kuɗin kafin daga baya ya sake dawo da ƙarar Babbar Kotu Tarayya a Abuja.

    Shell ya bayyana aniyarsa ta biyan kuɗin ta bakin lauyansa Aham Ejelamo yayin zaman kotun na ranar Laraba.

    Mista Ejelamo ya ce ɓangarorin biyu sun cimma yarjejeniyar matakin biyan kuɗin ne tun kafin zaman.

  4. Nijar: Mutum 400 aka kashe a hare-haren ƴan bindiga a bana - Human Rights Watch

    Fararen hula 400 ne suka rasa rayukansu ta dalilin hare- haren 'yan bindiga a wannan shekarar a yammacin Jamhuriyyar Nijar.

    Hakan na ƙunshe ne a wani rahoto da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Human Rights Watch ta fitar kan halin da farar hula ke ciki a yankunan Tillabery da kuma Tahoua.

    Video content

    Video caption: Latsa hoton sama ku saurari rahoton Tchima Ila Yousufu daga Yamai
  5. Birtaniya za ta kashe fan miliyan 14 a harkar ilimi a Kano

    Ganduje da Foreign Commonwealth Development Office

    Gwamnatin Birtaniya ta ce za ta kashe fan miliya 14 a Kano a wannan shekarar a harkar ilimi da sauran ɓangarori na rayuwa.

    Birtaniyan za ta yi hakan ne ta hannun Ofishin Ci gaba na Ƙungiyar Ƙasashe Renon Ingila, Foreign Commonwealth Development Office (FCDO).

    Shugaban FCDO, Dr Chris Pycroft, shi ne ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyara Kano ranar Laraba.

  6. Najeriya na gab da ƙure adadin bashin da Bankin Duniya za i iya ba ta - Masana

    Masana sun fara tofa albarkacin bakinsu a kan wani rahoton da Bankin Duniya ya fitar da ke nuna cewa Najeriya na cikin kasashe goma da suka zarta sauran kasashe cin bashin ci gaban kasa daga bankin duniyar.

    Kasar Indiya da Bangladesh da Pakistan da kuma Viatnem su ne a gaba, yayin da Najeriya da Habasha da Kenya da Tanzania da Ghana da kuma Uganda suka biyo baya.

    Masana dai na cewa rahoton na nuna cewa kasa irin Najeriya na gab da ƙure adadin bashin da bankin duniya za i iya ba ta, don haka akwai bukatar ta yi taka-tsantsan.

    Dr Shamsuddeen Muhammad masanin tattalin arzikin a Jami'ar Bayero ta Kano, kuma ya tattauna da Ibrahim Isa a kan wannan batu, ya ce rahoton bai ba shi mamaki ba.

    Video content

    Video caption: Hirar Ibrahim Isa da Dr Shamsuddeen Muhammad kan bashin da ake bin Najeriya
  7. Ƴan Majalisar dokokin jihar Bauchi sun yi taro kan ƴancin cin gashin kai ta fuskar kudade

    A yau ne ‘yan Majalisar dokokin jihar Bauchi suka kammala wani taron bita kan ‘yancin cin gashin kai ta fuskar kudade.

    SUn gudanar da taron ne a Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.

    A ‘yan watannin da suka gabata ne majalisar dokokin Najeriya ta gabatar da dokar da zata baiwa majalisun dokokin na jihohi ‘yan coi ta wannan fuska, wadda yanzu haka wasu daga cikin jihohin najeriya suka fara aiwatarwa.

    A yayin tattaunawarsu da abokin aikinmu a Kano Khalifa Shehu Dokaji da Shugaban majalisar dokokin ta Bauchi Hon Abubakar Sulieman ya ce ya zuwa yanzu jihohi 10 kaiwa suka kai ga aiwatar da dokar.

    Ga yadda hirar tasu ta kasance:

    Video content

    Video caption: Hirar Khalifa Dokaji da Hon Abubakar Sulieman
  8. Zaftarewar ƙasa ta danne mutane da dama a Indiya

    India Landslide

    A ƙalla mutum biyu ne suka mutu gwammai kuma suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzai a wanta zaftarewat ƙasa da ta faru a jihar Himachal Pradesh da ke arewacin India.

    Manyan duwatsun da suka faɗo sun binne manyan motoci da motar bus da wasu ababen hawa a cewar rahotannin kafafen yaɗa labaran ƙasar.

    ’Yan sanda da hukumomin gida sun fara ƙoƙarin ceto rayuka a cewar Jairam Thakur babban ministan Himachal Pradesh.

    An samu yawan afkuwar zaftarewar ƙasa a watannin baya-bayan nan a India sakamakon mamakon ruwan sama da ba a saba gani ba.

    Har yanzu ba a gano abin da ya jawo zaftarewar ƙasar ba da ta faru a ranar Laraba ba, wacce ta faru a babbar hanyar da ke yankin Kinnaur.

    Kafafen yada labarai na gida sun ce an ceto mutum biyar amma har yanzu kusan mutum 30 na ƙarƙashin baraguzan.

    An rarraba tawagar ’yan sanda da ke iyakar Indo-Tibetan domin taimakawa wajen ceto rayukan sannan an sanar da Hukumar Kare Afkuwar Bala’i.

  9. Najeriya na barazanar sauya dangantakarta da Indonesia kan cin zarafin jami'inta

    Ga alamu dai dangataka tsakanin Indonesia da Najeriya ta kama hanyar tabarbarewa bayan bullar wani bidiyon da ke nuna jami;an shige da ficen Indonesiya na cin zarafin wani ma'aikacin diplomasiyyar Najeriyar a birnin Jakarta.

    Yanzu haka dai Najeriya ta yi wa jakadanta daga Indonesiya kiranye tare da yin barazanar sauya dangantakarta da kasar in in har ba a hukunta jami'an da suka makure dan Najeriyar mai suna Abdurrahman Ibrahim.

    Ga dai Haruna Shehu Tangaza da karin bayani daga Abuja:

    Back Anno: To mu ma muna rokon afuwar tsohon jakadan Najeriyar Ibrahim Maisule kan bayyana sunansa a zaman wanda aka ci wa zarafin a rahotonmu na jiya. Kamar yadda aka ji sunan wanda aka ci wa zarafin Abdurrahman Ibrahim.

    Video content

    Video caption: Rahoton Haruna Tangaza kan alaƙar Najeriya da Indonesia
  10. Twitter ya amince ya kafa ofishi a Najeriya - Lai Mohammed

    Twitter

    Akwai yiwuar buɗe shafin Twitter a Najeriya "nan gaba kaɗan" yayin da kamfanin sada zumuntar ya amince da sharuɗɗan da gwamnati ta saka masa, a cewar Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed.

    Rahotannin da jaridun Najeriya ke ruwaitowa sun ce ministan ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa da aka yi ta intanet ranar Laraba ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo.

    A cewar TheCable, da yake amsa tambayoyin manema labarai, Mista Mohammed ya ce an samu ci gaba tsakanin gwamnati da kamfanin biyo bayan ganawa da yawa a tsakaninsu.

    Lai ya ce Twitter ya yarda da mafi yawan sharuɗɗan da gwamnati ta saka masa, ciki har da kafa ofishi a Najeriya, abin da zai sa a samu wakilansa a ƙasar.

    Sai dai kamfanin ya ce har sai 2022 zai iya kafa ofishin, a cewarsa.

  11. An cafke ɗan Burtaniya da ake zargi da leken asiri a Jamus

    Masu gabatar da kara na gwamnatin tarayya a Jamus sun ce an kama wani dan Burtaniya da ke aiki a ofishin jakadancin kasarsa a Berlin bisa zarginsa da yi wa Rasha leken asiri.

    A cewar wakilin BBC, Masu gabatar da karar sun zargi mutumin da tura wasu takardu ga wani jami'in leken asiri na Rasha fiye da sau daya inda kuma ake biyansa.

    An tsare mutumin mai suna David S jiya Talata a Potsdam kuma a yau ne za a gurfanar da shi gaban alkali.

    Tuni aka gudanar da bincike a gidansa da kuma wurin da yake aiki.

    Hakan na zuwa ne sakamakon wani binciken hadin gwiwa da hukumomin Jamus da Burtaniya suka yi.

    Rundunar yan sandan Burtaniya ta tabbatar da kamen inda ta ce mutumin yana da shekara 57.

  12. Masu fafutuka uku sun mutu a Myanmar

    Myanmar

    Rahotanni daga myanmar na cewa masu fafutika akalla uku sun mutu bayan da suka diro daga wani dogon bene yayin wani samame na 'yansanda a jiya Talata.

    An ce wasu biyu kuma sun ji munanan raunuka.

    Rahotanni a kafofin sadarwar intanit na nuni da cewa wataƙila dama sun buya ne a cikin ginin da ke Yangon babban birnin kasuwancin kasar, kana suka diro ta taga domin kada a kama su.

    Ana dai ci gaba da zanga-zangar adawa da gwamnatin soji ta Myanmar a Yangon da wasu biranen a sassa daban-daban na kasar.

  13. Kotu a China ta samu wani ɗan kasuwa da leken asiri

    Wata kotu a China ta samu wani dan kasuwa dan kasar Canada, Micheal Spavor, da laifin leken asiri, kana ta yanke masa hukuncin shekaru bakwai a gidan yari.

    Dama Mr Spavor yana kasuwanci ne a Dandong - wani birni dake kusa da iyakar kasar da Koriya ta Arewa. Tun karshen shekara ta 2018 ake tsare da shi.

    Hukuncin zai kara zama zakaran gwajin dafi na dangantaka da ta yi tsami tsakanin gwamnatin China da ta Canada.

    Canada dai kafe kan cewa haka nan suddan aka tsare Mr Spavor. A ranar Talata, wata kotun kuma ta jadda hukuncin kisa da aka yanke wa wani dan kasar Canada saboda laifin fasa kwaurin miyagun kwayoyi.

  14. PDP 'ta yi nasarar shawo kan rikicin shugabancin da ya dabaibaye ta'

    Babbar jam`iyyar hamayyar Najeriya, PDP, ta yi nasarar shawo kan rikicin shugabancin da ya dabaibaye ta.

    Jam'iyyar ta tsayar da watan Oktoba mai zuwa domin gudanar da babban taron ta, inda za a zabi sabbin shugabanni.

    Da dama dai ba su yi tsammanin za a wanye a taron lafiya ba, musamman ma yadda rikicin y araba kan `ya`yan jam`iyyar.

    Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Dr Attahiru Bafarawa dan kwamitin amintattun jam`iyyar ne, kuma ya yi wa Ibrahim Isa bayani a kan yadda suka maganace rikicin, kamar yadda za ku ji idan kuka latsa hoton da ke kasa:

    Video content

    Video caption: PDP 'ta yi nasarar shawo kan rikicin shugabancin da ya dabaibaye ta'
  15. An gano ɓaraguzan jirgin yaƙin karni na biyu a tekun Masar

    Gwanayen ninkaya da ke bincike a tsohuwar tashar ruwa ta Thonis-Heraklion sun gano wani tarkacen jirgin yaki da ke binne a can karkashin ruwa sama da shekara 2,000.

    Tawagar masu ninkaya daga Masar da Faransa ta ce jirgin da ke kwance a kasan ruwa ya nutse ne bayan tashar tsayawarsa a kusa da ginin wajen wani bauta ya rufta a cikin teku a karni na biyu kafin bayyanar Annabi Isa (AS).

    Birnin na da nisan tazarar kilomita kadan daga gabar tekun Alexandria.

    Dadaddiyar tsohuwar tashar Masar mai dimbin tarihi, Thonis-Heraklion da ke tekun baharum ya nutse a wannan lokaci sakamakon iftilaín girgizar kasa da guguwa da aka samu.

  16. Labarai da dumi-dumiZa a mika wa kotun ICC tsohon shugaban Sudan Omar al-Bashir

    Omar al-Bashir

    Gwamnatin Sudan ta ce za ta mika tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir ga kotun hukunta laifukan yaki ta duniya wato International Criminal Court.

    Ministan harkokin wajen kasar Mariam al-Mahdi, wanda ya tabbatar da hakan ranar Laraba, ya kara da cewa za a gurfanar da hambararren shugaban kasar ne tare da jami'an gwamnatinsa bisa rikicin da ya faru a yankin Darfur.

    Kafofin watsa labaran kasar sun ambato Mahdi yana cewa "majalisar ministoci ta yanke shararar mika jami'an gwamnatin da kotun ICC take nema ruwa a jallo."

    Bashir, wanda ya kwashe fiye da shekara 30 yana mulkin kasar amma aka hambarar da shi a 2019, yana fuskantar zarge-zargen laifukan yaki da na cin zarafin bil adama sakamakon rikicin Darfur.

  17. Amnesty ta ce sojojin Ethiopia na aikata fyaɗe a Tigray

    Tigray

    Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta ce sojojin Ethiopia da abokan aikinsu na aikata fyaɗe a rikicin da ke kara ta'azzara a ciki da kewayen yankin Tigray na ƴan a-ware da ke arewacin ƙasar.

    Kungiyar ta ce ta zanta da mata da kananan yara sittin 'yan Tigray wadanda suka ce sojojin Ethiopia ko na Eritrea ko kuma mayaƙan sa kai da ke taya su yaƙi sun yi masu fyaɗe.

    Wakiliyar BBC ta ce: ''Wasu daga cikin matan da aka zanta da su, sun ce an tsare su tsawon makwanni aka yi ta lalata da su, a wasu lokutan maza da dama suka aikata.''

    Amnesty ta ce irin waɗannan lamura laifukan yaƙi ne, kana ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta aike da tawaga yankin ta bincika.

  18. Labaran duniya cikin minti ɗaya da BBC na Rana 11/08/2021

    Video content

    Video caption: A saurari minti ɗaya da BBC na Rana
  19. An yanke wa sojojin da suka bai wa hammata iska hukunci ɗaurin rai da rai a DR Congo

    DR Congo

    Kotun soji da ke yankin arewa na Kivu a Jamhuriyar Demokradiyar Congo ta yankewa wasu sojoji biyu hukuncin daurin rai da rai sakamakon dambe a filin jirgin sama na Goma.

    A karshen makon da ya gabata an ta yada bidiyon Manjo Rimenze Kangingo Bisimwa da keyftin Mukando Muzito Paulin a yanar gizo suna zagi da naushin junansu.

    Rahotanni kafar yada labarai na kasar, na cewa kotun ta kama su da laifin cin zarafi da musgunawa da kuma karya dokokin aikin soji a yankin.

    An bai wa ma’aikatan damar daukaka kara nan da kwanaki biyar.

    Yankin arewacin Kivu da Ituri na karkashin ikon sojoji da ke yakar masu tada zaune tsaye musamman kungiyoyin mayaka tun a watan Mayu.

  20. MDD ta kafa kwamitin kar-ta-kwana domin shawo kan matsalar yunwa a arewacin Najeriya

    YUNWA

    Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutters ya ce sun kafa kwamitin kar-ta-kwana kan yunwa da haɗin gwiwar wasu kungiyoyin agaji da nufin kawo kan rashin abinci a arewacin Najeriya.

    Mai magana da yawunsa, Stéphane Dujarric, ta tabbatar da hakan a wani taron manema labarai da suka gudanar a hedikwatar majalisar da ke birnin New York.

    Ta kuma shaida cewa jami'ansu a Najeriya sun sanar da su irin matsanancin halin da ake a Najeriya musamman arewacin ƙasar don haka kafa wannan kwamitin ya zama tilas.

    Majalisar Ta kuma ce shirin nasu zai taimaka a fanin abinci da lafiya da kariya da samar da ruwan mai tsafta da inganta tsafta.

    Shirin nasu zai bukaci dala miliyan 250 domin kai wa ga mutanen da suka fi shiga matsananci damuwa sakamakon rashin abinci.

    A ranar Juma'ar da ta gabata Antonio Gutters ya ce ana bukatar sama da dala biliyan guda domin shawo kan matsalolin yunwa a arewacin Najeriya

    Ya kuma shaida cewa kashi 1 bisa 3 na wannan kudaden ne kawai ya samu.