Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail da Abdullahi Bello Diginza

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a najeriya da sauran sasan duniya

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Wani mahaifi ya kashe 'yarsa a Iraki

    iran

    'Yan Iraƙi da dama na kira a kawo sauyi kan dokokin ƙasar, bayan labarin wani mahaifi da ya kashe 'yarsa ya karaɗe kafafen sada zumunta a kasar.

    Matashiyar mai suna Tiba al-Ali ta je ziyarar mahaifanta daga Turkiyya, inda take zaune ita kaɗai.

    Mahaifinta ba ya jin daɗin zaman da take yi ita kaƙai a Turkiyya, ko da yake 'yan sanda sun yi yunƙurin kai mata ɗauki amma kafin su je mahaifin ya kasheta.

    Kisan nata dai ya sake farfaɗo da mahawarar da 'yan kasar suka jima suna yi a intanet, kan abin da suka kira 'kisan ban kunya'

    Sun yi kira ga gwamnati ta ɗauki tsattsauran doka kan cin zarafin da ake yi wa mata a ƙasar.

  3. IPMAN ta koka kan rashin samun wadataccen man fetur

    ED

    Ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu ta Najeriya (IPMAN) ta ce ba za a kawo ƙarshe matsalar ƙarancin man fetur a yankin kudu maso gabashin ƙasar nan kusa ba.

    Ƙungiyar ta ce ana samun karancin man fetur ɗin ne sakamakon matsalar da 'yan kasuwa ke fuskanta wajen samun man.

    A hirarsa da kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN ranar Asabar shugaban ƙungiyar reshen jihar Enugu Chinedu Anyaso ya ce yawan man da ke shiga yankin kudu maso gabashin ƙasar ya yi matuƙar raguwa da kusan kashi 50 cikin 100.

    Lamarin da ya sa Wasu gidajen mai suka ƙara farashin man, inda rahotonni ke cewa ana sayar da litar man tsakanin naira 400 zuwa naira 500 a wasu gidajen man fetur a yankin kudancin ƙasar.

    Mista Anyaso ya ce da yawa daga gidajen man jihar Enugu sun kasance a rufe sakamakon rashin man, inda kuma ake samun dogayen layuka a gidajen da ke sayar da man.

  4. Amurka na lura da balan-balan ɗin China da ke yawo a sararin samaniyarta

    b

    Shugaban Amurka Joe Biden ya ce ƙasarsa za ta ci gaba da ''lura da balan-balan'' ɗin China da ake zargi leƙen asiri wadda ke shawagi a sararin samaniyar Amurka a 'yan kwanakin nan.

    Mista Biden wanda bai yi cikakken ƙarin bayani ba , na fuskantar matsin lamba a cikin gida inda wasu ke cewa a harbo balan-balan ɗin ƙasa

    To sai jami'ai na bayar da shawarar cewa za a iya fuskantar haɗuran da ke tattare da ɓaraguzan balan-balan ɗin idan aka harbo shi ƙasa.

    Lamarin dai na zuwa ne yayin da tsamin dangantaka tsakanin ƙasashen biyu ke ƙara zafafa, inda Sakataren wajen Amurka Antony Blinken ya soke ziyarar da ya yi niyyar kai wa birnin Beijing.

    Mista Blinken ya ce bayyanar balan-balan ɗin mai leken asirin abu ne da bai dace ba. To sai dai China -wadda ta ce iska ce ta sauya wa balan-balan ɗin alƙibla - ta ce a kai zuciya nesa domin warware wannan matsala.

    An yi balan-balan ɗin ganin ƙarshe a sararin samaniyar gari Missouri ana kuma sa ran za ta isa gabashin Carolina zuwa ƙarshen mako.

    A wani labarin na daban kuma ranar Juma'a Amurka ta bayar da rahoton ganin wani balan-balan ɗin na daban a yankin Latin.

    Ƙasar China ta bayyana da-na-sani game da lamarin, tana mai cewa ba ta saɓa wa dokar iyakar ƙasa da sararin samaniyar wata ƙasa ba.

  5. Na'urar BVAS na aiki yadda ya kamata – INEC

    INEC

    Shugaban Hukumar Zaɓe Mai zaman kanta a Najeriya INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce ba su samu matsala da na'urar BVAS da ke tantance masu kaɗa ƙuri'a ba, a lokacin aikin gwajin na'urar da ake gudanarwa a faɗin ƙasar, ya kuma sha alwashin cewa ba za a samu matsala da na'urar ba a lokacin babban zaɓen ƙasar da ke tafe

    Farfesa yakubu ya bayyana haka ne ranar Asabar a Abuja babban birnin ƙasar a lokacin da yake yabawa da yadda aikin gwajin ke tafiya a fadin ƙasar, bayan da ya halarci wasu rumfunan zaɓe da ake gudanar da gwajin na'urar.

    “A duka rumfunan zaɓe biyu da muka ziyarta, ba mu samo rahoton matsala da na'urar ba, na'urorin suna aiki yadda ya kamata, kuma wannan shi ne rahoton da muke samu daga ko'ina a inda ake gudanar da gwajin a faɗin ƙasar nan''.

    “Mun kuma yi wani tsari kamar yadda za mu gudanar a ranar zaɓe, akwai na'urorin da za mu ajiye na shirin ko ta-kwana, idan muka samu wata matsala za mu ɗauko su domin ci gaba da aiki'', in ji Yakubu

    Shugaban hukumar ya ce daga wannan gwajin da ya gani, cikin ƙasa da daƙiƙa 30 ne na'urar ke tantance masu kaɗa kuri'a, kuma wannan shi ne rahoton da suke samu daga duk wuraren da aka gudanar da gwajin na'urar.

  6. Zaɓen Najeriya: hira da Atiku Abubakar

    Shirin Gane Mini Hanya na wannan mako ya tattauna da ɗan takarar shugabancin Najeriya ƙarƙashin jam'iyyar PDP Atiku Abubukar kan shirye-shiryen da yake yi domin tunkarar babban zaɓen ƙasar da ke tafe.

    Video content

    Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin sauraraon shirin
  7. NBA ta yi Allah -wadai kan kisan alkali a jihar Imo

    m

    Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) ta yi Allah wadai kan kisan da wasu 'yan bindiga suka yi wa Nnaemeka Ugboma wani alƙali da ke jagorantar wata ƙaramar kotu a ƙaramar hukumar Oguta a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya.

    A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran ƙungiyar Akorede Habeeb Lawal, ya fitar ya ce ƙungiyar Lauyoyin ta tabbatar da kisan mista Ugboma ranar Juma'a da rana da wasu 'yan bingiga da ba a san ko su wane ne ba suka yi a harabar kotun da yake jagoranta.

    Shaidun gani da ido sun ce alƙalin ya kammala wata shari'a kenan a daidai lokacin da maharan masu yawan gaske suka shiga cikin kotun inda suka karɓe wayoyin mutanen da ke cikin kotun, tare da kewaye alkalin daga bi sani kuma suka harbe shi da bingida.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa ''Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya NBA ta bayyana damuwarta kan kisan Nnaemeka Ugboma, wanda shi ne kisa na baya-bayan nan da 'yan bindiga ke yi wa ma'aikatan shari'a da aƙalai a wani abu da ya zama mai matukar tayar da hankali a jihar Imo''

    Ƙungiyar ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta ɗauki matakai domin kare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar musamman ta hanyar girke jami'an tsaro masu yawa a harabar gine-ginen kotunan jihar.

    Haka kuma NBA ta ce tana bincike domin gano waɗanda suka aikata wannan kisa don gurfanar da su gaban kotun don su girbi abin da suka shuka.

  8. Everton ta taka wa Arsenal burki

    f

    Sabon kocin Everton Sean Dyche ya fara wasa da ƙafar dama bayan da ya samun nasarar doke Arsenal da ci 1-0.

    A ranar Litinin ne aka naɗa Dyche bayan tafiyar Frank Lampard, wanda aka kora yayin da ƙungiyar ke ƙasar teburin Premier.

    Ƙungiyar ta samu nasararta ta farko cikin wasa 11 da ta buga a duka gasannin Ingila.

    Ɗan wasan tsakiya James Tarkowski ne ya zura ƙwallo ɗaya ta ka, da ta bai wa ƙungiyar nasara a kan Arsenal wadda ke mataki na ɗaya a teburin.

    Da wannan sakamako, tazarar da ke tsakanin Arsenal da Manchester City ta biyu zai ragu zuwa maki biyu idan Cityn ta yi nasara a kan Tottenham ranar lahadi.

  9. An gano gawarwakin 'yan Birtaniya biyu da aka kashe a Ukraine

    CHRIS PARRY/FAMILY OF ANDREW BAGSHAW

    An gano gawarwakin wasu 'yan Birtaniya biyu da aka kashe a gabashin Ukraine

    Shugaban ma'aikata na fadar shugaban Ukraine ya ce an gano da gawarwakin Chris Parry, mai shekara 29 da Andrew Bagshaw, mai shekara 47.

    Ba a dai sanya lokacin da za a miƙa gawarwakin nasu zuwa ofishin jakadancin Birtaniya ba.

    An dai kashe mutanen biyu a watan da ya gabata a bayan da aka kama su a lokacin da ake ruwa harsasai a gabashin Ukraine.

    Rabon da a ga mutanen biyu tun ranar 6 ga watan Janairu lokacin da suka nufi garin Soledar.

    Iyalan ɗaya daga cikinsu sun ce mutanen biyu na yunƙurin kuɓutar da wata tsohuwa ne a lokacin da aka yi wa motar da suke ciki ruwan harsasai.

    Garin Soledar ya kasance fagen da yaƙi ya fi ƙamari a watan da ya gabata, inda sojojin Rasha suka yi iƙirarin kama garin mai arzikin gishiri da ke gabashin Ukraine bayan shafe tsawon lokaci tana luguden wuta a kan garin. To sai Gwamnatin Ukraine ta musanta wannan iƙirari.

  10. Ra'ayi Riga: Muhawara kan sauya takardun kuɗi a Najeriya

    Video content

    Video caption: Danna hoton sama ku saurari Shirin Ra'ayi Riga

    Shirin Ra'ayi Riga na wannan makon ya taflka muhawara ne kan sauya takardun kuɗi na naira a Najeriya.

  11. ICPC ta kama manajojin banki biyu kan zargin ɓoye sabbin kuɗi

    Sababbin kuɗi

    Hukumar yaƙi da laifukan cin hanci da rashawa a Najeriya, ICPC, ta kama manajan ayyuka na reshen bankin FCMB a Jihar Osun saboda zargin ɓoye sababbin takardun naira.

    ICPC ta ce ta gano an zuba kuɗi a cikin na'urorin ATM na bankin amma a ɗaɗɗaure ta yadda ba za su iya fita ba idan mutane suka je cira, inda ta yi gargaɗi da a gyara.

    "Sai dai da tawagar ta sake kai ziyarar duba a rana ta biyu, sai ta tarar ɗaya daga cikin ATM ɗin na ɗauke da ɗaurarrun kuɗin," a cewar sanarwar da ICPC ta wallafa a shafukan zumunta.

    Bisa wannan dalilin ne kuma jami'an hukumar suka tafi da manajan mai kula da ayyuka, wanda ba ta bayyana sunansa ba, na reshehn bankin na FCMB.

    Haka nan, ICPC ta kama wata manajar bankin a Abuja "saboda ƙin saka kuɗi a ATM da gangan ko kuma sabo da mugunta duk da cewa akwai kuɗin," in ji hukumar.

    Jami'an tsaro da suka haɗa da na 'yan sanda da EFCC na ci gaba da bin sawun bankuna da ɗaiɗaikun mutane don yaƙi da masu ɓoyewa da sayarwa da kuma yaɗa takardun jabu na sababbin kuɗin.

    A gefe guda kuma, 'yan Najeriya na ci gaba da kokawa kan ƙarancin kuɗin, inda suke shafe awanni a kan dogayen layuka don cirar su a na'urorin ATM.

    View more on twitter
  12. Abin da ya janyo dawowar cutar mashaƙo

    Video content

    Video caption: Danna hoton sama ku saurari Shirin Lafiya Zinariya:

    Hukumar lafiya ta duniya ta ce an samu matukar raguwar cuta mashaƙo, amma cutar ta sake karuwa a baya-bayan nan.

    Cutar ta fi tsanani a kan yara da manyan da basu da allurar rigakafinta, domin yawan yin rigakafin ne ya sa cutar ta ragu sosai a tsakanin shekarun 1980 zuwa 2021, a duniya.

    Sai dai a shekarar 2019, cutar mashako da ake kiraDiphtheriaa likitance ta kama sama da mutane 20, 000.

    Najerya, kasar da ta fi kowacce yawan al’umma a nahiyar Afrika, ta fuskanci barkewar tun a watan Oktobar shekarar 2022.

    Kuma tun bayan bullar cutar zuwa watan Janairun 2023, muane 38 ne aka tabatar sun mutu a sanadiyyar cutar, a kasar.

  13. 'Yan sanda sun kama mutum biyu da zargin sayar da jabun sababbin kuɗi a Enugu

    Jabun takardun kuɗi

    Rundunar 'yan sandan Jihar Enugu a kudancin Najeriya ta ce ta kama mutum biyu da zargin sayarwa tare da yin ciniki da jabun sabuwar takardar naira N1,000 ranar Juma'a.

    Cikin sanarwar da fitar ranar Juma'a, rundunar ta ce ta kama Joseph Chinenye mai shekara 39 da Onyeka Kenneth Ezeja mai 29 ɗauke da tsabar kuɗin jabu naira 180,000.

    An kama su ne yayin da suke ƙoƙarin sayar wa wani ɗan POS da kuɗin bayan sun yi amfani da su sun sayi man fetur, in ji sanarwar.

    Ƙarancin sababbin takardun naira ya jefa 'yan Najeriya cikin tasku tun daga makon da ya gabata, inda ɗaruruwan mutane ke hawa kan dogwayen layuka a wuraren cirar kuɗi na ATM.

    Babban Bankin Najeriya CBN ya saka ranar 10 ga watan Fabarairu a matsayin wa'adin daina amfani da tsofaffin takardun N1,000, da N500, da N200. Amma za a ci gaba da sauya tsofaffi da sababbi bayan wa'adin.

    View more on twitter
  14. Zaɓen 2023: Inec na gudanar da gwajin tantance masu kaɗa ƙuri'a a faɗin Najeriya

    Maikatan hukumar zaɓe ta ƙasa a Najeriya, Inec, sun fara gudanar da aikin tantance masu kaɗa ƙuri'a na gwaji gabanin babban zaɓe na 2023 a yau Asabar
    Image caption: Maikatan hukumar zaɓe ta ƙasa a Najeriya, Inec, sun fara gudanar da aikin tantance masu kaɗa ƙuri'a na gwaji gabanin babban zaɓe na 2023 a yau Asabar. Nan ma'aikatan Inec ne a Jihar Ekiti ke gudanar da aiki gwajin.
    A Ƙaramar Hukumar Ife ta Arewa da ke Jihar Osun, wata mai buƙata ta musamman ce ta gabato don yin gwajin tantance masu kaɗa ƙuri'a a kanta.
    Image caption: A Ƙaramar Hukumar Ife ta Arewa da ke Jihar Osun, wata mai buƙata ta musamman ce ta gabato don yin gwajin tantance masu kaɗa ƙuri'a a kanta.
    Kwamashinan hukumar zaɓe a Jihar Ekiti kenan, Ayobami Salam, lokacin da yake duba yadda aikin tantance masu kaɗa ƙuri'a ke gudana a Ƙaramar Hukumar Ado a yau Asabar
    Image caption: Kwamashinan hukumar zaɓe a Jihar Ekiti kenan, Ayobami Salam, lokacin da yake duba yadda aikin tantance masu kaɗa ƙuri'a ke gudana a Ƙaramar Hukumar Ado a yau Asabar.
    Nan kuma, ma'aikatan Inec ne ke gudanar da aikin a Ƙaramar Hukumar Somolu da ke Jihar Legas a yau ɗin
    Image caption: Nan kuma, ma'aikatan Inec ne ke gudanar da aikin a Ƙaramar Hukumar Somolu da ke Jihar Legas a yau ɗin, kuma ana gwajin ne a faɗin ƙasar.
    Ma'aikatan Inec ne ke jiran mutane don tantance su a Jihar Imo
    Image caption: Ma'aikatan Inec ne ke jiran mutane don tantance su a Jihar Imo.
  15. Hatsarin mota ya kashe mutum 17 a Tanzania

    Mutum aƙalla 17 ne suka mutu sannan wasu 12 suka jikkata sakamakon hatsarin mota da ya afku a Tanga da ke arewacin ƙasar Tanzania, a cewar hukumomi.

    Hatsarin ya faru ne a ranar Juma'a wanda ya haɗa da wata motar bas ɗauke da fasinja 26 da kuma wata babbar mota.

    A cewar kwamashinan yankin Tanka, Mista Omary Mgumba, bas ɗin na ɗauke da gawa ce tare da masu makoki daga birnin Dar es Salaam zuwa yankin Kilimanjaro, inda ita kuma babbar motar ke ɗauke da kaya.

    Mutum 10 daga cikin da suka ji rauni na cikin mawuyacin hali kuma ana kula da su a asibiti, in ji Mista Mgumba.

    Hukumomi sun ɗora alhakin lamarin kan tuƙin ganganci kan direban babbar motar.

  16. Gwamna Zulum ya gargaɗi bankuna su saki sababbin kuɗi ko ya ƙwace filayensu

    Gwamna Zulum

    Gwamnan Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, Babagana Umara Zulum, ya gargaɗi bankunan kasuwanci a jihar cewa gwamnatinsa za ta ƙwace lasisin filin duk bankin da ya gaza saka sabbin takardun naira a na'urorin cire kuɗi na ATM.

    Gwamnan ya yi gargaɗin ne ranar Juma'a a birnin Maiduguri lokacin da ya kai ziyara don gane wa idonsa irin dogwayen layuka da wahalar da jama'a ke fuskanta na ƙarancin sabbin takardun kuɗin.

    "Duk bankin da ba shi da niyyar cika ATM ɗinsa da sababbin takardun kuɗi don sauƙaƙa wa al'umma wahalhalu, za mu ƙwace filin gininsa nan take," in ji gwamnan cikin wata sanarwa da kakakinsa Isa Gusau ya fitar.

    Sanarwar ta ce ran Gwamna Zulum ya ɓaci ne lokacin da ya tarar da wani dogon layin cirar kuɗi, inda ATM ɗaya ne kacal yake aiki cikin 10 da ke wurin.

    "Kamar yadda kuke gani, talakawa ne kawai a kan layi...An ce wasu tun ƙarfe 3:00 na dare suke a nan, wasu ma ba su ci komai ba. Sababbin kuɗin da tsofaffin duka babu, wanda hakan ke shafar harkokin kasuwanci tare da ƙuntata wa mutane," a cewar Zulum.

    Gwamnan ya ƙara da cewa lokacin da ya je Ƙaramar Hukumar Gubio ya tarar cewa babu naira N100,000 a faɗin ƙaramar hukumar baki ɗaya na tsofaffi ko sababbin kuɗin.

    Gwamna Zulum
  17. Amuka da Kanada sun shiga sanyi mafi tsanani a tarihi

    Masu hasashen yanayi a NewYork sun ce yanayin tsananin sanyi a Amurka ya kai matakin da ba a taba gani ba a tarihi, inda sanyi ya kai maki -77 a ma'aunin Salsius.

    An fahimci hakan ne bayan wani gwaji da suka aiwatar a tsaunin Washington da ke New Hampshire.

    Shekara 40 da suka gabata, an samu yanayin sanyi da ya kai -89 da digo biyu a Antarctica.

    Wasu yankunan arewa maso gabashi a Amurka da Kanada na cikin barazanar shan irin sanyin Arctic a karshen mako.

    Mahukunta sun yi gargaɗi kan irin wannan yanayi da suka ce na illa sosai ga fata da kuma jikin ɗan Adam.

  18. 'Yan fashin daji sun kashe mutum 41 a Katsina

    'Yan fashin daji

    Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen Jihar Katsina ta ce 'yan bindiga sun kashe mutum aƙalla 41 sakamakon kwanton ɓaunar da suka yi wa 'yan banga a jihar.

    Sanarwar da kakakin rundunar, SP Gambo Isah, ya fitar ta ce lamarin ya faru ne ranar Alhamis da dare lokacin da mayaƙan sa-kai suka tunkari 'yan bindigar da zimmar ƙwato dabbobinsu da ɓarayin shanu suka sace.

    Sai dai mazauna yankin na cewa adadin ya zarta hakan, inda wasu ke cewa an kashe mutum kusan 60.

    "A ranar Laraba da misalin ƙarfe 10:00 na dare, 'yan ta'adda sun kai hari gidan wani mutum mai suna Alhaji Muntari da ke Unguwar Audu Gare a Kandarawa na ƙaramar Hukumar Bakori, inda suka sace shanu 50 da awaki 30," in ji sanarwar.

    "Daga baya a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 10:00 na dare, 'yan sa-kai da aka haramta suka taru daga ƙauyuka 11 na Bakori kuma suka nufi 'yan ta'addan don ƙwato dabbobin da aka sace. Sun bi sawunsu har zuwa dajin Yargoje.

    "Abin takaici, sai 'yan ta'addan suka shirya musu kwanton-ɓauna, suka kashe 41 daga cikinsu sannan suka raunata biyu."

    SP Gambo ya ƙara da cewa kwamandan rundunar na Malumfashi ne ya jagoranci tawagar 'yan sandan da suka kwaso gawar mamatan, yana mai cewa yanzu haka samamen haɗin gwiwa na jami'an na gudana "don gano waɗanda suka aikata kisan".

  19. Amurka ta ce balambalan ɗin da China ta tura mata na leƙen asiri ne

    Balambalan

    China ta ce sakataren harkokin wajenta, Wang Yi, ya tattauna ta waya da takwaransa na Amurka, Antony Blinken kan abin da ya kira Kumbon China da ke shawagi a sararin samaniyar Amurka.

    Mutanen biyu sun tattauna yadda za su tunkari irin wadannan akasi cikin sanyayyar murya da kwarewa.

    Mista Blinken ya soke ziyarar da ya yi niyyar kaiwa Beijing kan balambalan ɗin, abin da Amurka ta ce balambalan ɗin China na leken asiri ya ratsa sararin samaniyarta.

    Wakilin BBC ya ce China ta ce akasi aka samu kuma balambalan ɗin ya ratsa samaniyar Amurka ne bisa kuskure.

    Sai dai kakakin ma'aikatar tsaron Amurka ya ce an hango irin wannan kumbo na China na ratsa wasu yankunan Latin Amurka.

  20. Assalamu Alaikum

    Maraba da sake haɗuwa a wannan shafi na rahotanni kai-tsaye tare da ni Umar Mikail.

    Ku biyo tun daga wannan hantsi na Asabar har zuwa darenta don samun labarai na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Za mu fi mayar da hankali Najeriya da Nijar da Ghana da Kamaru da kuma maƙwabtansu a nahiyar Afirka.

    Ina fatan kun wayi hantsin lafiya.