Karim Benzema: An yanke wa dan wasan Faransa da Real Madrid ɗaurin shekara ɗaya a kurkuku

Karim Benzema

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Badaƙalar ce ta sa Benzema ya daina bugawa Faransa wasa

An samu ɗan wasan Real Madrid Karim Benzema da laifin cin amana kan batun da ya shafi wani faifan bidiyon lalata na wani tsohon dan kwallon Faransa da suka taka leda tare.

An yanke wa Benzema hukuncin ɗaurin gyara hali na shekara ɗaya tare da umartar ya biya tarar dala 84,000.

Benzema mai shekara 33 yana cikin mutum biyar da aka gurfanar a watan da ya gabata, domin karbar kudi a hannun Mathieu Valbuena da ikirarin zai wallafa bidiyon ga duniya a 2015.

Badaƙalar ta tayar da ƙura a Faransa inda dukkanin ƴan wasan aka dakatar da su daga buga wa Faransa wasa.

Masu gabatar da ƙara sun ce Benzema ya tursasawa Valbuena ya biya masu ɓata sunan waɗanda kuma ya haɗa baki da su.

Benzema ya sha musanta laifin da ake tuhumarsa yana mai jaddada cewa ya yi ƙoƙarin taimakawa Valbuena domin kawar da bidiyon.

Ɗan wasan na Real Madri ba ya cikin kotun Versailles lokaci da aka zartar masa da hukuncin, haka ma Valbuena wanda ke buga wa Olympiakos ta Girka wasa.

An kuma samu sauran mutanen huɗu da laifi a hukuncin da aka yanke ranar Laraba.

Lauyan Benzema ya ce za su ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin.