Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Khalifa Dokaji

time_stated_uk

  1. Bankwana

    Da haka ni Umaymah Sani Abdulmumin nake bankwana da ku a wannan shafi da ke kawo labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

  2. Majalisar dokokin Sifaniya ta amince da dokar zub da ciki

    Majalisar dokokin Spaniya ta amince da wata sabuwar doka da za ta bai wa 'yan mata masu shekaru sha shida ko sama da haka damar zubar da ciki ba tare da izinin iyayensu ba.

    Matakin na daya daga cikin sabbin hakokin jima'i da haihuwa da kudirin zai baiwa mata, idan majalisar dattawan Spain ta amince da shi.

    Hakanan zai ba da izinin ba da tallafin gwamnati ga ma'aikatan mata waɗanda ke fama da jin zafi - mai da Spain ta zama wuri na farko a Turai don yin hakan.

    Cocin Roman Katolika da masu fafutukar hana zubar da ciki sun yi Allah-wadai da wannan sabuwar dokar da suka ce ta sabawa kundin tsarin mulkin kasar da kuma kimar kasar.

  3. Indiya ta fitar da sakamakon gwajinta kan maganin tarin da ya hallaka yara a Gambia

    Indiya ta ce gwajin da aka yi kan maganin tari da aka yi a kasar da ake zargin da nasaba da mutuwar yara kusan saba'in a Gambiya bai nuna cewa maganin na da wata illa ba.

    A baya Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce gwajin farko na samfuran maganin hudu sun gano matakan sinadarai masu guba da ba za a amince da su ba.

    Yaran sun mutu ne sakamakon ciwon koda bayan sun sha magungunan da ake kai wa Gambia.

    Kamfanin Maiden Pharmaceuticals da ke samar da maganin ya ce yana bin ka'idojin kula da inganci na duniya.

    Indiya na samar da kashi uku na magungunan duniya.

  4. An wanke magidanta bakwai da ake tuhuma da yiwa yarinya fyaɗe a Sokoto

    o

    Wata babbar kotun jihar Sakkwato a Najeriya ta wanke wasu magidanta bakwai, wadanda aka gurfanar a gabanta bisa zargin yi wa wata yarinya marainiya 'yar shekara 12 fyade irin na taron dangi a shekara ta 2020.

    Wannan dai wata shari'a ce da ta dauki hankalin lauyoyi da kungiyoyin kare hakkin mata da kananan yara, da masu rajin kare hakkin bil'Adama da kafofin watsa labarai suke sa ido kanta, da sauran jama'a a ciki da wajen Najeriya.

    Alkalin babbar kotun jihar Sakkwaton ta biyu, Mai shari'a Malami Umar Dogon Daji, ya sallami mutanen bakwai ne, bayan kammala sauraren jawaban masu kara da na wadanda ake kara, da kuma auna hujjojin da aka gabatar masa bisa mizanin shari'a.

    Barista Muhammad Mansur Aliyu, lauyan da ya tsaya wa marainiyar da babarta, ya ce ba su gamsu da wannan shari'a ba.

    Hakazalika Hajiya Jamila Umar, wato babar yarinyar marainiya, ta ce ba a yi masu adalci a wannan hukunci ba

    A yanzu dai hankalin masu bibiyar wannan shari'a ya koma ne kan ganin mataki na gaba da masu karar za su dauka.

  5. Majalisar Turai za ta yi wa wasu tsare-tsarenta kwaskwarima

    Shugabar Majalisar Tarayyar Turai ta yi alƙawarin yin gyare-gyare a fannoni daban-daban, biyo bayan badakalar cin hanci da rashawa a wannan makon.

    An zargi mutane hudu da laifin karbar cin hanci, inda masu bincike suka gano tsabar kudi sama da Euro miliyan daya da rabi a wurare daban-daban a Brussels.

    Roberta Metsola ta yi alkawarin cewa za su sake duba ka'idojin da'a na majalisar, da kuma nazarin yadda take mu'amala da sauran kasashe.

    Ta ce za mu iya sake tsaurara dokokin da muke da su, da inganta su, wasu ma mu yi musu garambawul, amma abu mafi muhimmanci shine an bankalo wannan badakala.

    Sai dai masu sukar sun ce an dade ana kiraye-kirayen a yi gyara, ba tare da daukar wani muhimmin mataki ba duk da damammakin da ake da su na dakile irin haka.

  6. An sami barkewar amai da gudawa a Goma

    .

    An sami ɓarkewar amai da gudawa a yankin Goma, babban birnin arewacin Kivu a jamhuriyar Damokaradiyar Congo.

    Gwamna Arewwacin Kivu Laftanal janar Constant Ndima ya ce mafi akasari rahotanon bullar cutar ne was wasu daga cikin sanssanin wucin gadi da aka ajiye wadan yakin da ake fama da sh a yanki n yafi shafa.

    Gwaman ya ce kawo yanzu akwa mutum sama da 600 da su ka kamau da cutar.

    Sai dai wasu daga cikin kungiyoyon da ba na gwamnati ba sun ce adadin wadan suka kamu da cutar ya zarta haka.

  7. Bamu gamsu da hukuncin da aka yankewa Sheikh Abduljabar ba, in ji almajiransa

    Sheikh Abduljabar

    Almajiran Sheikh Abduljabbar sun ce akwai abubuwan da basu gamsu da su a cikin hukuncin kotun da yanke.

    Wannan na zuwa ne bayan hukuncin da mai shari’a na babbar kotun musulunci ya same da laifin aibata fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.

    Kamar yadda wa'azinsa da shari'ar ke cike da cece-kuce haka ma hukuncin kisan da aka yanke masa ta hanyar rataya, shi ma a yanzu yana tattare da wannan kace-na-ce din.

    Yayin da kusan mutane da dama suke ganin hukuncin ya dace da tuhume-tuhumen aikata sabo akan fiyayyen halitta da aka samu Sheikh Abduljjabar da laifi, wasu kuma musamman wasu dalibansa suna cewa ba'a yi la'akari da hujjojin da malamin nasu ya gabatar a gaban kotun ba a wajen yanke hukuncin.

    Sai dai kuma daliban nasa sun shaidawa BBC cewa su masu biyayya ne. Amma a cewarsa shari'a tana cike da ayoyin tambaya.

    Wannan hukunci na yau dai, shi ne kusan babban labarin da ya karaɗe ba kawai jihar Kano ba, har ma da sassan musamman arewacin Najeriya.

    Akasari dai hukunci irin wannan ya kan zamo babban kalubale musamman ga mahukunta wajen zartar da shi.

    Babbar kotun musulunci dai ta ce yana da kwana talatin ya daukaka kara.

    Yanzu dama ta rage ga Sheikh Abduljabbar, duk da ya ke har lokacin da ake yanke masa hukunci yana cewa bai aikata laifi ba.

    Sai dai batun mika wuya ga hukuncin yanzu za a zuba ido a gani ko zai yi amfani da wannan damar ko akasin haka.

  8. MDD ta ce sojojin Rasha sun kashe daruruwan fararan hula a Ukraine

    Babban jami'in kare hakkin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya ya ce sojojin Rasha sun kashe daruruwan fararen hula a Ukraine, lamarin da ka iya zama laifukan yaki.

    Volker Turk ya zargi Rasha da aiwatar da hukuncin kisa kan mutanen da ba su da wata barazana, yayin da suka yi saranda.

    Ya ce mun tattara bayanan kisan farar hula 441, maza 341 da mata 72, da yara maza 20 da yara mata 18, kuma muna sa ran adadin zai iya zarta haka, yayin da muke ci gaba da bincike.

    Rahoton ya ce bai iya gano ko da sojan Rasha guda da hukumomin Ukraine suka yi wa irin wannan kisa ba.

  9. Nollywood ta sami tallafin Dala biliyan uku don shirya fim

    Bad Comments

    Bangaren fina-finan Najeirya, da aka fi sani da Nollywood zai bunkasa shirya fina-finai bayan samun tallfin naira biliyan uku a matsayin tallafi habaka bangare.

    Tallafin, wanda wani kamfanin fina-finan Najeirya, Labari Afurka ya kaddamar, ana sa ran amfani da tallafin wajen yin wasu finafinai a Nollywood, kuam zai taimakawa masu shirya finafinai, shirya sababin finafinai.

    A wata sanarwa da kamfanin Labari Africa ya fitar ta bakin Mr Tunde Leye, na cewar tallafin zai taimakwa wajen samar da horo da bita na kwarewa a harkar fim ga masu mashirya finfinai masu tasowa.

    Za kuma taimaka wajen tallafar rarraba finafinan da tallata shi a kasuwa.

    A cewar Leye, wannan shi ne karon farko da za a su sami jerin tallafin, da ake sa ran kamma karbar sa na da wasu shekaru masu zuwa, kamar dai yadda aka zayyana a ka'idojin sakin tallafin da za'a bayar.

  10. Post update

    .

    A wajen taron shugabanin kasashen Afirka da Amurka, batun karfafawa mata gwiwa na daga cikin batutuwan da aka tattauna a taron, wanda ake sa ran kammalawa a yau Alhamis.

    A wata kasida da aka wallafa ta nuna hadin gwiwa tsakanin yankuna biyu, a wani shiri da aka yi wa take da ƙarfafawa mata a banagren makamashi.

    Fadar White house ta ce za dai a zuba jarin dala miliyan daya "don taimaka wa mata ayyuka masu gwaɓi, ta hanyar da mayar da hankali kan Kenya da Afirka ta Kudu.

    "Shirin zai samar da kudade ga kungiyoyin cikin gida, don cike giɓin da aka bari na mata, da tabbatar da samar da makamashi mai tsafta, da kara yawan shigar mata rajin samar da makamashi mai tsafta.

  11. Gidan yarin Liberia mai cikowa ya fara ƙin karɓar mutane

    Wadan aka yankewa hukucin kisa ne a Ajiye a gidan Yarin - an dauki hoton a watan January 2022

    Babban gida yarin Monrovia da ke Liberia ya fara daina karɓar ɗaurarun da ake turo masa saboda cikar da ya yi da kuma fargabar ɓarkewar cututtuka.

    Minsitan harkokin Shari'a na Liberia Frank Musa Dean ne Ya shaida wa BBC cewar waɗanda aka ƙi karɓar su ana zargin su ne da aikata ƙananan laifuka.

    "Idan ba a yi wa wani rauni ko illa ga wani ba, mutanen da aka tsare kan ƙananan laifuka, yanzu za su koma gida sai masu unguwanninsu su dinga sa ido a kansu.

    Hakan dai ya biyo bayan rahotanin da wasu daga cikin kafafen yaɗa labaran kasar suka yi na yadda masu gadin gidan yarin ke ƙin amincewa da karɓar sababbin ɗaurarun, saboda yajin aikin da suke yi kan jikirin biyansu albashi.

    Sai dai shugabannin gidan yarin sun musanta hakan.

    An gina gidan yarin ne da zummar ɗaukar mutum 300, a lokacin da adadin mutanen Monorovia bai wuce dubu 300 ba.

    Sai dai a yanzu yana dauke da mutum 1,600, yayin da adadin mutanen Monorovia ya kai miliyan daya da rabi.

    Wandan ke zaune a gidan yarin sun hada da waɗanda aka yanke wa hukucin kisa da masu fashi da makami.

  12. Mutum daya ya rasu bayan jirgin kasa ya taka wata mota a Abuja

    Motar da suka jirgin kasan ya taka

    Rudunar 'yan sandan Abuja ta tabbatar da afkuwar wani hatsari da ya faru a Chikasoro a yankin Kubuwa, da jirgin kasa ya yi taho mu gama da wata mota.

    A wata sanarwa da rundunar 'yan sandan Abuja ta futar, mai magana da yawunta DSP Josephine Adeh ta ce likitocin da ke inda hadarin ya faru sun tabbatar da mutuwar mutum daya.

    Ta ce ita ma reshen hukumar jirigin kasa da layin dogon ke karkashin ikonta, sun ƙaddamar da bincike kan faruwar lamarin.

    Sannan ta ce za a mayar da alamun kan hanya da gyara wadanda ake da su don kaucewa faruwar makamancin irin wannan hadarin.

    Jirgi
  13. Paul Kagame ya ce Amurka ba ta isa ta tankwara shi ba

    Shugaban Rwanda ya ce ba za su yarda wata kasa ta ci gaba da tankwara su ba kan harkokin da suka shafi cikin gidansu ba.

    Shugaban na Rwanda na bayyana hakan ne a matsayin martani ga bukatar da gwamnatin Amurka ta gabatar masa ta sakin wani mai kalubalantar gwamnatin kasar Paul Rusesabagina.

    A yayin tattanauwa kan matsalolin da suka shafi Afirka a taron shugaban kasashen nahiyar da aka gudanar a Washington, an tambayi Kagame ko bukatar da wakilin Amurka Antony Bilinken ya gabatar ta sako shari'ar da ake yi wa Mr Rusesabagina, na "taimako ko bata masa rai".

    Mr Kagame ya ce wani da ke Amurka na so a yi bar shari'ar, saboda mutumin tauraro ne."

    A shekarar da ya gabata ne aka sami wasu Rusesabagina da wasu mutanen da laifin ayyukan ta'addanci.

    Mr Kagame ya ce “idan muka sake shi, su kuma sauran mutum 20 din da suka nuna shi a matsayin shugaban su."

    Mr Rusesabagina, mai shekaru 68, ya kasance jarumi na finafinan Hollywood, kan filin din kisan kiyashin da aka yi a Rwanda.

    An yanke masa hukucin daurin shekaru 25 a gidan yari bayan da aka yaudare shi hawa jirigin daga dubai zuwa birnin Riwanda Kigali, a tunanin zai wuce zuwa Burundi.

  14. Gwamnatin Najeriya ta yi gargadin kai hari kan wayoyi ƙirar android 300,000

    Android

    Hukumar Sadarwa ta Najeriya NCC ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar an sace bayanan 'yan kasar ta shafin Facebook ta hanyar wani hari da aka kai ta manhaja mai cutarwa ta "Schoolyard Bully".

    Sashen hukumar sadarwar ta Najerya da ke kula da intanet ya ce ƙwayar cutar ta shafi wayoyi ƙirar android har kusan 300,000, wanda ya ja hankalin masu amfani da manhajar da su tabbatar sun sauke Facebook din daga shafinsa ko ta shagon sauke manhajoji na Apple Store.

    Shugaban sashen yada labarai na NCC, Dr Reuben Mouka, ne ya sanar da haka a ranar Laraba a Abuja.

    Muoka ya ce masu bincike kan tsaro wajen amfani da wayar salula daga kamnfanin Zimperium sun ce sun gano manhajoji masu yawa da ke yaɗa ƙwayar cutar “Schoolyard Bully”.

    Ya ce ƙwayar kan batar da kama zuwa manhajar karatu mai kunshe da littafi ko maudu'ai don yi wa masu amfani da ita shigo-shigo-ba-zurfi.

    Mouka ya ce akwai wannan manhajar a Google Play, sun sauke daya daga ciki kuma suna ci gaba da aiki a wasu shagunan sauke manhajoji.

  15. Majalisar Dattijan Najerya ta umarci CBN ya sauya dokar taƙaita cire kuɗi

    Sabbin takardun Najeriya

    Majalisar Dattaijan Najeirya ta umarci Babban Bankin ƙasar (CBN) ya sake duba matsayarsa na takaita cirar kudi daga bankuna saboda yadda jama'ar kasar ke kokawa kan sabon tsarin.

    Majalisar Dattijan ta bayyana haka ne bayan doguwar mahawara tsakanin 'yan majalisar a jiya Laraba.

    Majalisar ta umarci kwamitin da ke kula da harkokin bankuna da kudade da ya je ziyarar duba ayyukan CBN yayin da yake aiwatar da sabon tsarin kuma ya bai wa majalisar rahotonsa na lokaci zuwa lokaci.

    Wasu daga cikin 'yan majalisar sun kalubalanci sabon tsarin na CBN na rashin tuntuba kan manufar, kafin aiwatar da shi.

    Kazalika, wasu daga cikinsu ke cewa tsarin zai sa masu sana'ar cirar kudi na POS rasa ayyukansu.

  16. Jakadan Najeriya a Spaniya Demola Seriki ya rasu

    Seriki

    Jakadan Najeriya a kasar Spaniya, Demola Seriki ya rasu.

    Ya rasu yana da shekara 63 a duniya.

    Wata sanarwa da iyalansa suka fitar ta ce jakadan kuma tsohon minista ya rasu ne a yau Alhamis.

    A watan Janairun 2021 ne Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi a matsayin jakadan Najeriya a Spaniya.

    Kafin wannan mukamin, ya taba rike mukamin karamin minista a ma'aikatar tsaro da kuma na aikin gona.

  17. Buhari ya bude katafariyar Gadar Second Niger Bridge

    Gadar Second Niger Bridge

    Shugaban Najeriya Muhamamdu Buhari ya bude katafariyar Gadar Neja ta Biyu don saukaka wa masu tafiya garuruwansu zuwa bukukuwan karshen shekara cikin kwanciyar hankali.

    Shugaba Muhammadu Buhari wanda Ministan Ayyukan Babatunde Fashola ya wakilta, a ziyarar gani da ido, ya ce an gina gadar ce daga kudaden da ake zargin an sace su daga kasar kuma aka boye a kasashen waje, wadanda aka karbo mafi yawan su daga Amurka.

    Sannan ya ce manufar gina gadar shi ne kare rayuka da magance talauci da ake fuskanta sakamakon yawan sa'o'in da ake dauka a cinkoson da ake samu a tsohuwar Gadar Neja.

    Ya ce yin gadar zai zama maras amfani idan masu amfani da ita suka zabi tukin ganganci da ka iya zama barazana ga rayuwarsu.

    Ministan ya ce da an tsara a bude ta a ranar !4 ga watan Disamba amma saboda wasu dalilai suka sa aka daga zuwa 15 ga watan Janairun 2023.

  18. NEITI: Najeriya ta yi asarar naira tiriliyan 16 na danyen mai

    Rijiyar mai

    Hukumar da ke binciken yadda aka kashe kudaden da aka samu daga ma'adanan man fetur a Najeriya, NEITI, ta ce kasar ta yi asarar gangar mai miliyan 619.7 da kudinsu ya kai naira tiriliyan 16.25 daga 2009 zuwa 2020.

    A wata sanarwa da mai magana da yawunta, Obiageli Onuorah, ta fitar a yammacin ranar Laraba ta ce Najeriya na asarar danyen mai saboda yadda ake sace shi da asarar a wani abu da ta kira yi wa kasar zangon kasa.

    Jaridar the Punch a Najeriya ta rawaito cewar hukumar ta NEIT ta ce ta gano hakan ne a wasu bayanai da ta tattara daga wasu matsakaitan kamfanoni takwas da ke suka yi aiki akansa tsawon shekaru.

    Ta ce ta yaba wa matakin gwamantin ta Najeriya na samar da wani kwamiti na musamman da kan lura da yadda ake sace danyen man.

  19. Biden ya ce Amurka za ta zage dantse don ci gaban Afirka

    Shugaba Biden

    Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da bayar da tallafin biliyoyin daloli don ciyar da Afirka gaba a yayin taron shugabanin kasashen Afirka da ke gudana a Washington.

    "Amurka za ta zage dantse kan ci gaban Afirka," a cewar shugaba Biden da yake sanar da shugaban kasashen Afirka 40 da suka halarci taron.

    Haka kuma ya bayyana aniyar Amurka ta ci gaba da karfafa dangantakarta da Afirka, inda ya sanar da bai wa kasashen tallafin dala biliyan 55 a matsayin sabon tallafi ga Nahiyar na tsawon shekaru uku. Ciki har da dala miliyan 100 na samar da makamashi.

    Ya sanar da mahalarta taron cewar idan Afirka ta yi nasara, haka ma Amurka.

    Mr Biden ya yi jawabi kan muhimmancin shugabanci na gari, samar da jama'a mai koshin lafiya da makamashi mai sauki.

    Ana kallon taron shugabanin kasahen Afirka da ke gudana a Amurka a matsayin wani yunkuri ne kasar na ganin ta dawo da karfin ikon ta kan Nahiyar a daidai lokacin da China, Rasha da Turkiya ke fadada damarsu a nahiyar.

    Wannan ne karo na farko a shekaru takwas da Amurka ta karbi bakunci irin wannan taro.

  20. Barkanmu da safiyar Alhamis

    Khalifa Shehu Dokaji ne ke muku barka da wannan lokaci. Ku kasance da ni tsawon wannan rana domin karanta labaran da suka shafi rayuwarku. Kuna iya tafka muhawara da bayyana ra'ayoyinku a shafukanmu na sada zumunta a bbchausa.