Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Nabeela Mukhtar Uba

time_stated_uk

  1. Amurka ta bayar da tallafin $100m don yaƙar ta'addanci a Afirka

    Kamala Harris

    Mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Kamala Harris, ta sanar da tallafin dala miliyan 100 don aikin dakile tashe-tashen hankula a yammacin Afrika, a yayin da ta fara ziyarar aiki ta mako guda a nahiyar.

    A wani jawabi da ta gabatar a Ghana, ta ce za a yi amfani da kudin ne don tallafawa kasashen Ghana da Benin da Guinea da Ivory Coast daTogo, don yakar ayyukan masu tsattsauran ra’ayin addini da tashe-tashen hankli a kasashen.

    Wannan ce ziyara ta baya-bayan nan da wani babban jami’in kasar Amurka ya kai nahiyar, yayin da gwamnatin Washington ke kokarin dakile karuwar tasirin China da Rasha a Afrika.

    Shugaba Biden ya ayyana wani shirin dakile barazanar tsaro na shekaru 10 a yammacin Afrika.

  2. Kotu ta haramta wa Ayu bayyana kansa a matsayin Shugaban PDP

    PDP

    Wata Kotu da ke zamanta a birnin Makurdi ta bai wa Dr Iyorchia Ayu umarnin daina nuna kansa a matsayin Shugaban Jam'iyyar PDP a Najeriya.

    Alƙali Wilfred Kpochi wanda ya bayar da umarnin, ya buƙaci Ayu ya janye daga shugabancin jam'iyyar har zuwa lokacin da za a saurari ƙarar da tuni aka shigar.

    Tun farko, ƙarar da Injiniya Conrad Utaan ya shigar ta nemi kotu ta hana Ayu daga bayyana kansa a matsayin shugaban PDP kasancewar dakatarwar da aka yi masa.

    PDP ta dakatar da Ayu NE bisa zargin sa da wasu ayyuka na cin amanar jam'iyyar.

    Shugabannin jam'iyyar a matakin gundumarsa da ke ƙaramar hukumar Gboko, a jihar Benue ne suka ɗauki matakin.

    Sun ce sun dakatar da shi ne bayan kaɗa ƙuri'ar rashin ƙwarin gwiwa kan ayyukansa.

  3. An zaɓi Musulmi na farko don ya jagoranci Jam'iyyar SNP ta Scotland

    Scotland

    An zaɓi Humza Yousaf a matsayin jagoran Jam'iyyar SNP domin maye gurbin Nicola Sturgeon.

    Yousaf ya samu kashi 52 na ƙuri'un da aka kaɗa yayin da Kate Forbes ta samu kashi 47 na ƙuri'un.

    Da wannan zaɓe, Yousaf mai shekara 37 ya zama Musulmi na farko da zai jagoranci wata babbar Jam'iyya a Ingila.

    A yanzu, Yousaf ne sakataren lafiya na yankin Scotland kuma ana tunanin shi ne wanda ake goyon baya ya gaji Ms Sturgeon sai dai ba ta fito ƙarara ta nuna goyon bayanta ga wani ɗan takara ba.

    SNP ce Jam'iyya mafi girma a Scotland inda take da mafi yawan kujeru a majalisar dokokin yankin.

  4. Isra'ila ta jinkirta ƙudirin sauya fasalin tsarin shari'ar ƙasar

    Isra'ila

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya jinkirta shirin gwamnatinsa na yi wa tsarin shari'ar kasar garanbawul mai cike da cece-kuce har zuwa zaman majalisa na gaba.

    Ya ce kasar na fuskantar rikicin da ke barazana ga hadin kan kasa.

    An dai gudanar da zanga-zanga a sassan kasar tare dayajin aikin domin adanawa da sauyin .

    Tun farkon wannan shekara, mutane suka fara haɗa manya-manyan zanga-zanga ta mako-mako domin nuna adawa da shirin gwamnati na kawo sauyi a wasu tsare-tsarenta.

    Zanga-zangar ta yi ta yaɗuwa, inda dubban ɗaruruwan mutane suka mamaye titunan Tel Aviv - birnin kasuwancin ƙasar - da kuma da wasu birane da garuruwa a faɗin ƙasar.

    Masu zanga-zanga sun yi kira da a soke shirin kawo sauyi da Firaminista Benjamin Natenyahu ke son yi, inda suka bukaci da ya sauka daga mulki. Ƴan adawarsa na siyasa su ke jagorantar zanga-zangar, ko da yake tsananin adawa da sauye-sauyen ya kasance cikin ƴan siyasa.

    Wasu sojoji ma da suka kasance kashin bayan sojojin Isra'ila - sun nuna adawarsu da sauyin ta hanyar kin zuwa aiki, inda hakan ya ƙara nuna fargabar da ake da ita na cewa yanayi tsaron ƙasar na cikin barazana.

  5. Ƴan Najeriya za su yi kewar Buhari idan ya sauka daga mulki – Garba Shehu

    Garba Shehu tare da Shugaba Buhari

    Babban mai bai wa Shugaban Najeriya shawara kan kafafen yaɗa labarai, Mallam Garba Shehu ya koka kan irin caccakar da ake yi wa shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari.

    Ya ce ba a nuna ƙauna ga shugabanni a lokacin da suke mulki.

    Ya bayar da misali da zamanin mulkin Goodluck Jonathan wanda ya ce mutane sun yi ta sukarsa amma a yanzu, ya zama mutumin da ƴan Najeriya da dama ke yabo.

    Mallam Garba Shehu ya ce irin haka za ta faru idan Buhari ya miƙa mulki ga shugaban ƙasa na gaba.

    Game da manufar taƙaita amfani da garin kuɗi, Garba Shehu ya ce tsarin na gwamnati mai ci abin so ne a don haka ba za a soke shi ba.

    A cewarsa, "taƙaita amfani da takardun kuɗi ci gaba ne ga ƴan Najeriya saboda ƙasashen da suka ci gaba tuni suke tafiya a kan wannan tsarin".

    Al'ummar Najeriya sun yi ta fuskantar matsaloli saboda ƙaranvin takardun kuɗi tun bayan da gwamnati ta bijiro datsarin sauya fasalin takardun kuɗin.

  6. MDD na zargin sojojin Libya da aikata laifukan yaƙi

    Libya

    Jami'an gudanar da bincike daga Hukumar kare haƙƙin bil adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce dakarun Libya da ƙungiyoyin ƴan tawaye sun aikata laifukan yaƙi da cin zarafin bil adama.

    Sun yi gargaɗi cewa baƙin da aka hana tuntuɓar Tarayyar Turai na cikin haɗari.

    Masu binciken sun kuma ce sun gano shaidu da suka bayyana cin zarafi da fyaɗe da kashe-kashe da aka yi a cibiyoyin tsare ƴan ci-rani.

    Za kuma a miƙa sakamakon binciken da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi ga Kotun hukunta manyan laifuka ICC.

  7. "Baƙar fata ƴan Afirka ba su da makoma a Tunisia"

    Tunisia
    Image caption: Wasu baƙar fata ƴan Afirka na ci gaba da zanga-zanga kan irin rayuwar da suke yi a Tunisia

    Wani ɗan ci-rani ɗan asalin Saliyo ya shaida wa BBC cewa baƙar fata ba su da wata makoma a Tunisia saboda yadda Larabawan ƙasar ke ci gaba da nuna musu wariya.

    "A Tunisia, baƙaƙen fata daga yankin kudu da hamadar sahara ba su da wata makoma a nan, haka nan ƴaƴanmu," in ji Josephus Thomas, wani ma'aikacin ƙere-ƙere.

    "Muna buƙatar a ƙwashe mu," daga Tunisia kamar yadda ya ce, "ko da" hakan na nufin tafiya wata ƙasar Afirka, in ji shi.

    Wasu ƙasashe suna tayin kwashe jama'arsu, kamar KIvory Coast da Guinea.

    Tashin hankali ya soma ne bayan da Shugaba Kais Saied ya zargi baƙi daga yankin Kudu da hamadar sahara da ke zaune a ƙasar da haifar da zama ɓata-gari inda ya bayyana su a matsayin barazana ga ƙasar.

    Tun lokacin kuma baƙaƙen fata ƴan Afirka suka shaida wa BBC irin wariyar launin fatar da ake nuna musu a Tunisia.

    Mista Thomas ya bayyana wani al'amari na firgitarwa da ya gani "Wasu maza ƴan Tunisia riƙe da sanduna da wani ƙarfe mai kaifi da wuƙaƙ da duwatsu" suna bin wasu baƙi yan Gambia da Senegal da Guinea.

    Ya ƙara da cewa halin da ake ciki a Tunisia ya munana har yake cewa ya sha yin ƙoƙarin ficewa daga ƙasar ta kwale-kwale.

    "Idan na samu damar barin ƙasar ta jirgin ruwa, zan rungume ta saboda ya fi rayuwa a Tunisia inda ba ka da tabbacin abin da za su iya yi maka a gaba ba."

  8. Harin bom ya kashe mutum shida a Kabul

    Kabul

    Wani harin ƙunar baƙin wake a tsakiyar Kabul, babban birnin Afghanistan ya kashe akalla mutane shida.

    'Yan sanda sun ce fashewar ta faru ne a kusa da ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, kuma dukkan waɗanda suka mutu fararen hula ne.

    An dai tsaurara matakan tsaro a yankin, mai gine-ginen gwamnati da kuma ofisoshin jakadancin ƙasashen waje.

    Kawo yanzu dai babu wanda ya ɗauki alhakin harin.

    A watan Janairu ma an ƙaddamar da harin bama-bamai mafi muni a ma’aikatar harkokin wajen Afghanistan.

  9. Jack Ma ya bayyana a bainar jama'a bayan dogon lokaci

    Jack Ma

    Hamshaƙin attajinan nan ɗan ƙasar China Jack Ma, ya bayyana a bainar jama’a, bayan dogon lokaci ba a ji ɗuriyarsa ba sakamakon rashin jituwarsa da gwamnatin ƙasar.

    An ga mista Ma a yayin ziyarar da ya kai zuwa wata makarantar da ya ba da tallafin ginawa a birnin Hangzhou.

    Ana kyautata zaton hamshaƙin ɗan kasuwar ya shafe tsawon shekara guda yana ƙasashen ƙetare.

    A shekarar 2020 gwamnati ta shirya dakatar da ɗaya daga cikin kamfanoninsa na intanet, bayan da ya soki dokokin gwamnatin China.

  10. Majalisar dokokin Indiya ta katse zamanta bayan kaurewar hargitsi

    An katse zaman majalisar dokokin ƙasar Indiya sakamakon masu zanga-zangar adawa da dakatar da shugaban jam’iyyar adawa ta Congress party, Rahul Gandhi da majalisar tayi.

    An dai tilasta wa majalisar wakilan ƙasar ɗage zamanta da safiyar ranar Litinin ne, bayan da ‘yan majalisar na jam’iyyar Congress party suka harzuƙa a zauren majalisar inda suka dinga jifan kakakin majalisar da takardun zaman majalisar.

    Galibin ‘yan majalisar na jam’iyyun adawa sun sanya baƙaƙen kaya ne a matsayin nuna ɓacin-ransu.

    A majalisar dattijan ƙasarsa an samu makamancin wannan hargitsi a lokacin da hayaniya ta kaure tsakanin ‘yan majalisar na jam’iyya mai mulki da ‘yan adawa.

  11. 'Yan tayar da ƙayar baya sun kashe mutum 17 da suka sace a DR Kongo

    kkk

    Ƙungiyar 'yan tayar da ƙayar baya ta Codeco ta kashe mutum 17 da ta sace tare da yin garkuwa da su a garin Djuru da ke gabashin jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo.

    Mutanen dai fasinjoji ne da ke cikin motoci huɗu da aka kama su a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa garin Mungwalu a lardin Ituri.

    Wani gidan Radio mallakin Majalisar Dinkin Duniya a ƙasar ya ce masu tayar da ƙayar bayan sun sace mutanen ne a matsayin martani kan kisan mambobinsu uku a wata arangama da wata ƙungiyar 'yan tayar da ƙayar bayan.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa daga cikin mutanen da aka kaman har da wata mace mai ciki.

    Kawo yanzu dai hukumomin ƙasar ba su ce komai ba game da batun.

    Ƙungiyar masu tayar da ƙayar bayan ta Codeco - wadda ke iƙirarin kare manoma 'yan ƙabilar Lendu a Lardin Ituri -na ɗaya daga cikin ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai da ke ayyukansu a yankin mai arzikin ma'adinai.

  12. INEC ta saka ranar ƙarasa zaɓukan da ba a kammala ba

    j

    Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a Najeriya INEC ta sanya ranar Asabar 15 ga watan Afrilu a matsayin ranakun da za ta kammala zaɓukan da ba a ƙarasa ba a ƙasar.

    A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce ta yanke shawarar ne bayan wata ganawa da ta yi da jami'an hukumar.

    Hukumar ta ce sai a ranar Asabar 15 ga watan Afrilun ne za a ƙarasa zaɓukan gwamnoni da na 'yan majalisun dokokin da ba a karasa ba, sakamakon wasu matsaloli.

    Hukumar zaɓen ƙasar dai ta ayyana zaɓukan gwamnonin jihohin Adamawa da Kebbi a matsayin wanda bai kammala ba.

    View more on twitter
  13. Wasu mutane sun yi wa gonar tsohon shugaban Kenya ƙawanya

    Wasu ɗaruruwan matasa sun kai hari gonar tsohon shugaban ƙasar Kenya Uhuru Kenyatta wadda ke a wajen birnin Nairobi.

    Mutanen sun yi ta sare bishiyoyin dake cikin gonar, tare da sace dabbobi masu yawa kafin su cinna wa gonar wuta.

    Kawo yanzu ba a san dalilin mutanen na aikata hakan ba.

    Lamarin dai na zuwa ne a yayin da 'yan adawa a ƙasar ke gudanar da zanga-zangar nuna adawa da mulkin shugaban ƙasar William Ruto.

  14. 'Yan sanda sun kama mutum 781 bisa laifukan zaɓe a Najeriya

    Baba Alkali

    Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kama mutum 781, kan laifukan da suka shafi zaɓe a lokacin zaɓukan ƙasar na shekarar 2023

    Babban sifeton 'yan sandan ƙasar Usman Baba Alkali ne ya bayyana haka ranar Litinin a lokacin da yake ganawa da kwamishinonin 'yan sanda na jihohin ƙasar 36, tare da wasu manyan jami'an 'yan sandan.

    Yayin da yake cikakken bayani game da kamun, Baba Alkali ya ce an aikata laifukan zaɓe 145 a lokacin zaɓen shugaban ƙasa, inda rundunar ta kama mutum 203.

    Sai kuma a lokacin zaɓen gwamna da na 'yan majalisun dokokin jihohi inda rundunar ta ce an aikata laifuka 304, lamarin da ya sa rundunar ta kama mutum 578.

    Babban sifeton 'yan sandan ya ce rundunar ta shirya ganawa babban sifeton da kwamishinonin 'yan sanda na jihohin ƙasar da kuma sauran manyan jami'an 'yan sandan, don tattauna barazanar da tsaron ƙasar ke fuskanta.

    Wanda a cewarsa 'yan siyasa ke ƙoƙarin tayar da hatsaniya a ƙasar bayan zaɓukan ƙasar da suka gabata.

    Ya kuma yi Allah wadai da 'yan siyasar da suke ƙoƙarin tayar da hargitsi ta hanyar tunzura jama'a domin cimma wasu muradunsu.

  15. Mataimakiyar shugaban Amurka na ziyara a Ghana

    Kamala Haris

    Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris za ta gana da shugaban ƙasar Ghana domin tattauna batutuwan da suka shafi hulɗar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu, kafin yin jawabi ranar Talata.

    Ziyarar tata wani ɓangare ne na sake gina alaƙa tsakanin ƙasashen biyu.

    A ranar Lahadi ne kamala Haris ta sauka ta isa Ghana domin fara ziyarar rangadi da take yi a nahiyar Afirka har zuwa 2 ga watan Afrilu.

    Sauran ƙasashen Afirkan da ake sa ran za ta ziyarta sun haɗar da Tanzaniya da kuma Zambiya.

    Tattalin arzikin Ghana na fama da matsaloli tun shekarar da ta gabata, inda hauhawar farashin kayan masarafi ya haura kashi 50.

    'Yan ƙasar da dama na cike da fatan ziyarar za ta taimaka wajen samar wa ƙasar bashin da take buƙata daga asusun bayar da lamuni na duniya IMF, tare da haɓaka hulɗar kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.

  16. An dakatar da jigilar jiragen ƙasa a Kenya

    Kenya

    Hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta Kenya ta dakatar da zirga-zirgar jiragen ƙasa a Nairobi babban birnin ƙasar gabanin zanga-zangar adawa da gwamnati da shugaban adawar ƙasar Raila Odinga ya kira.

    Hukumar ta ce matakin ya zama wajibi don gujewa gamuwa da cikas.

    "Muna bayar da haƙuri ga duka kwastomominmu kan halin da wannan mataki zai jefa su,'' in hukumar a wata sanarwa da ta fitar.

    Ƙungiyar gamayyar 'yan adawar ƙasar na gudanar da zanga-zanga a Nairobi da wasu sassan ƙasar domin matsa lamba don yin sauye-sauye a fannin zaɓen ƙasar tare da neman rage farashin kayayyakin buƙatun yau-da-kullum a ƙasar.

    A ranar Lahadi Sifeton 'yan sandan ƙasar ya haramta zanga-zangar, to sai dai 'yan adawar sun ce zanga-zangar tasu na kan tsarin doka don haka za a gudanar da ita kamar yadda aka tsara.

  17. Burkina Faso ta dakatar da tashar France 24

    Burkina
    Image caption: Dangantaka tsakanin Faransa da Burkina Faso ta yi tsami tun bayan juyin mulkin soji a bara

    Hukumomi a Burkina Faso sun bayar da umarnin rufe tashar yaɗa labarai ta France 24, bayan ta yaɗa wata wata hira da shugaban ƙungiyar Al-Qaeda na arewacin Afirka. 'Aqim'

    A wata sanarwa da ministan sadarwar ƙasar Jean-Emmanuel Ouedraogo ya fitar ya ce ''Ba murya kawai tashar France 24 ke bai wa 'yan ta'adda ba, a yanzu so take ta halasta ayyukan ta'addanci da yaɗa kalaman ƙiyayya''.

    Ya ce a kan haka ne gwamnatin ƙasar ta ɗauki matakin dakatar da duka shirye-shiryen tashar a fadin ƙasar.

    A farkon wannan watan ne tashar ta yaɗa wata hira da ta yi da shugaban ƙungiyar Al-Qaeda na yankin arewacin Afirka Yezid Mebarek, bayan da Faransa ta kashe tsohon shugaban a wani hari ta sama.

    Dangantaka tsakanin Burkina Faso da Faransa ta ƙara yin tsami tun juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Oktoban bara.

    Burkina Faso dai ta kori dakarun Faransa da ta ce sun kasa fatattakar masu iƙirarin jihadi a ƙasar, inda ta gayyato sojojin hayar Rasha domin gudanar da aikin.