Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi, Abdullahi Bello Diginza, Nabeela Mukhtar Uba da Buhari Muhammad Fagge

time_stated_uk

  1. Nan muka kawo karshen labarai da rahotannin namu na yau

    Muhammad Buhari Fagge da da Nabeela Muktar Uba da Yusuf Yakasai ke fatan mu kwana lafiya.

  2. EFCC ta kama mutum huɗu kan zargin sayen kuri'u a Cross River

    EFCC

    Hukumar EFCC mai yaƙi da yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon ƙasa ta ce jami'anta sun cafke wasu mutum huɗu kan zargin sayen kuri'a a jihar Cross River.

    EFCC ta bayyana haka ne a shafinta na Tuwita inda ta ce sun kama mutanen ne da suka hada da wata Esther Edem, shugabar mata a karamar hukumar Calabar ta Kudu.

    Sauran mutanen da aka kama akwai Edet Okon Etim da Asanwana Peter Eyo da Joshua Emmanuel.

    View more on twitter

    Tun da farko EFCC ɗin ta ce ta kama wasu mutanen a jihohin Kaduna da Sokoto da Kebbi da jihar Rivers bisa zargin sayen ƙuri'a da yunkurin jan hankalin masu zaɓe ta hanyar ba da kayan masarufi.

    Haka kuma ta ce an kai wa jami'anta hari a Kaduna, yayin da suke yunƙurin kama wani mutum da ake zargin yana sayen kuri'u a filin zaɓe.

  3. An harbe tsohon kansila kan zargin satar akwati

    Ibrahim Nakuzama

    Rahotanni daga jihar Kano na cewa an harbe wani tsohon kansila a bisa zarginsa da sace akwatin kaɗa ƙuri'a.

    Lamarin ya faru ne a yayin da ake gudanar da zaben gwamna da na 'yan majaliasar dokokin jiha a ranar Asabar ɗin nan.

    Rahotannin sun ce sojoji ne suka harbe Ibrahim Nakuzama, wanda tsohon kansila ne a mazaɓar Getso da ke ƙaramar hukumar Gwarzo.

    Sai dai kawo yanzu rundunar sojan Najeriya ba ta kai ga fitar da sanarwa kan lamarin ba.

    Wani makusancin mamacin ya ce tuni aka yi jana'izarsa a mahaifarsa a Getso.

    Makusancin ya ce suna cikin jimamin rashin Ibrahim din, don haka babu wani bayani da zai ƙara.

    Ibrahim Nakuzama ya rasu ya bar mata biyu da ƴaƴa shida.

    Ita ma a na ta ɓangaren, rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce ta kama mutane da dama saboda zargin tayar da hankali a lokacin zaben na ranar Asabar.

  4. An yi zaɓe lami lafiya a jihar Legas in ji Ƴan sanda

    Ƴan sanda

    Kwamishinan ƴan sanda na jihar Legas, Idowu Owuhunwa ya ce zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisar dokoki na jihohi ya gudana lafiya a jihar sai dai an samu tashin hankali a wasu wurare ƙalilan.

    Ya ce tashin hankalin da aka samu bai shafi ɗaukacin tsarin zaɓen ba kuma bai yi muni yadda mutane suke yayata wa a shafukan sada zumunta ba.

    Kwamishinan ya tabbatar cewa sun kama mutane da dama sannan sun ƙwato akwatunan zaɓe da wasu ɓatagari suka sace sannan wani matashi da bidiyonsa ya karaɗe intanet har ake cewa ya mutu, yana nan da ransa.

    "A akasarin jihar Legas, zaɓen ya gudana lafiya. Na ziyarci wurare kamar Ikorodu da Badagry da Ikoyi da wasu yankunan jihar, an yi zaɓe ba tare da tashin hankali ba kuma masu zaɓen sun kaɗa ƙuri'arsu cikin lumana." in ji Owohunwa.

    A lokacin da manema labarai suka tambaye shi game da yankunan da aka samu rikici, kwamishinan ya ce ba zai iya zayyana duka yankunan ba saboda ana ci gaba da tattara bayanai daga jami'ansu da ke aikin zaɓe.

  5. Ana ci gaba da tattara sakamakon zaɓen gwamnoni

    Ana ci gaba da tattara sakamakon zaɓe a wasu sassan Najeriya, duk da cewa an samu an samu rahotannin rikici a wasu wuraren da basu kai sun kawo ba.

    An gudanar zaɓukan a jihohi 28 cikin 36 da Najeriya ke da su.

    An dage zaɓen a wasu sassan jihar Legas da ke kudanci.

    A JIhar Kaduna da ke arewaci kuwa an kai wa jami'an EFCC hari tare da jikkata mutum uku daga cikinsu.

    BBC
    BBC
    BBC
    BBC
    BBC
  6. Masu sayen ƙuri’a sun kai wa jami’an EFCC hari a Kaduna

    An kai wa jami’an EFCC hari a yayin da suke aikin sanya idanu a zaɓen da ake gudanarwa a na gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi.

    Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce an kai wa jami’an nata hari ne a Unguwar Rimi yayin da suke yunƙurin kama wasu da ake zargi da sayen ƙuri’a.

    Tawagar tasu da ke aikin sanya idanu na sirri ta yi zargin wani mutum da ake kira Kabiru Musa da aka gani cikin wani bidiyo riƙe da wayarsa yana aikawa mutane kudi idan suka kaɗa ƙuri’arsu, abin da ya sanya suka kai samamensu yankin ke nan domin su kama shi.

    Da zuwansu suna ƙoƙarin kama shi, sai musa ya sanya ihu wanda tamkar alama ce ga abokan aikisa cewa yana cikin matsala.

    “Sun yi amfani da makamai kan jami’anmu abin da ya kai ga raunata wasunsu. Ya ɗauke su dogon lokaci suna fafatawa da matasan, saboda dagewar da suka yi sai sun kama wanda suke zargi.

    “Bayan sun sanya wanda suke zargi a mota, sai aka fara jifan motar da manyan duwatsu da sauran abubuwa abin da ya sanya aka jikkata ma’aikatanmu uku kenan,” in ji sanarwar.

    Waɗanda aka raunatan yanzu haka suna karɓar kulawa a wata cibiya da ke Kaduna, kuma wanda ake zargin yana hannu har zuwa a kammala bincike.

    An kai wa ma’aikatan EFCC makamancin irin wannan hari a yayin zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana, aka kuma lalata abun hawansu.

  7. Goodluck Jonathan ya yi tir da tashin hankali a ƙaramar hukumarsa

    Zabe

    Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya yi tur da yadda ɓatagari suka ƙona kayayyakin zaɓe a mazaɓarsa da ke ƙaramar hukumar Ogbia a jihar Bayelsa.

    Tsohon shugaban ƙasar ya yi kira ga ƴan sanda su kama mutanen da suka haifar da hatsaniyar inda ya ce Najeriya ba za ta ƙyale ɓatagari su lalata tsarin zaɓe ba.

    Jonathan wanda tsohon gwamnan Bayelsa ne ya faɗa wa manema labarai bayan da ya kaɗa ƙuri'arsa cewa ƴan sandan na iya ganawa da gwamnan jihar idan har suna neman agajin sojoji domin kama mutanen da suka haifar da tashin hankalin.

    Zabe
    Zabe
  8. INEC ta ɗage zaɓen gwamna a wasu mazaɓun jihar Legas

    Masu zaɓe

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC ta ɗage zaɓen gwamna da na ƴan majalisar jiha a mazaɓu 10 da ke jihar Legas.

    Wuraren da wannan ɗagewar ta shafa sun haɗa da rukunin gidaje na Victoria Garden City (VGC) da ke ƙaramar hukumar Eti-Osa.

    Yayin da yake magana da manema labarai, kwamishinan hukumar zaɓe a jihar ta Legas, Mista Olusegun Agbaje ya ce ma'aikatan wucen gadin da ke aiki a yankin sun ƙi gudanar da aikinsu saboda ƙalubalen da suka fuskanta a zaɓen shugaban ƙasa.

    "Muna da mazaɓu takwas a nan da masu zaɓe 6,024 da aka yi wa rajista kuma daga cikinsu 5,624 sun karɓi katin zaɓensu," in ji shi.

    Ya ƙara da cewa lamarin ya shafi wasu mazaɓu biyu a rukunin gidajen.

    "Bayan tuntuɓa, mun sami umarni daga hukumar zaɓe ta ƙasar cewa mu ɗage zaɓen zuwa gobe Lahadi da ƙarfe 8:30." kamar yadda kwamishinan hukumar zaɓn ya shaida.

  9. Ƴan sanda sun kama shugaban Kano Line bisa zargin ta da hankali

    Kano
    Image caption: 'yan sanda

    Rahotannin daga jihar Kano na cewa rundunar ƴan sanda jihar ta kama shugaban kamfanin sufuri na jihar Kano Line bisa zargin tayar da hatsaniya a lokacin zaɓe.

    Rundunar ta wallafa a shafinta na Facebook cewa ta kama mutane uku a unguwar Gwammaja Ƴan Ƙosai, kuma mutanen suna zaune ne a bayan motar ƴan sanda.

    Daya daga cikin wadanda aka kama din dai shi ne shugaban Kano Line Bashir Nasir Aliko.

    Shugaban ɗa ne ga Nasiru Aliko Ƙoki, daya daga dattawan jam'iyyar APC a Kano, kuma na hannun damar gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje.

    Kawo yanzu dai babu wani ƙarin bayani daga rundunar ƴan sanda kio jam'iyyar APC kan kamen

    View more on facebook
  10. El Rufa’I ya koka kan rashin fitowar masu kada kuri’a

    El Rufa'i

    Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa’i ya koka kan ƙarancin fitowar masu zabe da aka fuskanta a jihar.

    Tun da sanyin safiya ne dai ma’aikatan zaɓe suka isa rumfunan zaɓen a kan lokaci tare da tabbatar da kayan aikinsu sun zama cikin shiri.

    Da misalin karfe tawkas na safiya ne dai aka fara zaben, shi ma gwamnan jihar ya isa inda zai yi zaɓe da misalin karfe tara na safiyar, sai dai kai tsaye ya bayyana rashin jin daɗinsa kan abin da ya shaida wa idanunsa na ƙarancin masu zaben.

    ‘‘Dole a jinjinawa INEC, abubuwa sun yi sauki sosai kuma ni ban samu matsala ba da zaɓena ba.

    ‘‘Abin da na fuskanta shi ne mutane da dama ba su fito ba, wanda wannan abu ne mara daɗi, amma ina kira ga jama’a da su fito su kaɗa ƙuri’unsu.

    ‘‘Yawan kuri’armu yana nuni da karfin da muke da shi, kuma babu abin da zamu ce sai son barka,“ in ji El Rufa’i.

  11. Gobara ta tashi a kasuwar Gamboru da ke Maiduguri

    kasuwar Gamboru
    Image caption: Yadda gobara ta kama kasuwar Gamboru

    Wata gobara ta tashi a kasuwar gamboru da ke tsakiyar birnin Maiduguri a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

    Rahotonni sun ce gobarar ta ta shi ne da tsakar ranar Asabar lokacin da ake tsaka da kaɗa ƙuri'a a zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisun dokokin jihohi da ake gudanarwa a faɗin ƙasar.

    xzc
    Image caption: Gobara

    Kawo yanzu babu rahotonni rasa rai sakamakon wannan gobara da ta tashi a kasuwar ta kayan abinci a jihar.

    Kuma har yanzu ba a kai ga sanin takamaimen abin da ya ya haifar da gobarar ba.

    a
    Image caption: Gobarar kasuwar Gamboru

    Idan ba a manta ba dai makonni uku da suka gabata wata gobara da ta tashi a kasuwar Monday market a birnin na maiduguri ta yi sanadiyyar asarar miliyoyin dukiyoyi.

    A jihar Kano ma an fuskanci gobara a kasuwanni da dama a ƴan kwanakin nan.

  12. PDP ta kayar da APC a mazaɓar gidan gwamnatin Kaduna

    Sakamakon zaɓe

    Sakamakon zaɓen da aka gudanar na gwamna a jihar Kaduna da jami'in zaɓe ya fitar, ya nuna cewa jam'iyyar PDP ta samu nasara a kan jam'iyyar APC a mazaɓar gidan gwamnatin jihar, wacce aka fi sani da mazaɓar gidan Sir Kashim.

    A mazaɓar gidan gwamnatin Kaduna ta Sir Kashim Ibrahim, akwai cibiyoyin zaɓe biyu.

    A ɗaya daga cikin cibiyoyin, Jam'iyyar PDP ta lashe zaɓe yayin da a ta biyun ake ci gaba da tattara sakamakon zaɓe.

    Sakamakon ya nuna cewa Isa Ashiru na jam'iyyar PDP ya samu ƙuri'u 77, yayin da Uba Sani na jam'iyyar APC ya samu ƙuri'u 40.

  13. Sayen ƙuri'a: EFCC ta ƙwace tufafi a wasu jihohin Najeriya

    Hukumar da ke yaƙi da yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon ƙasa EFCC ta ce ta ƙwace tufafi da kaya masu yawa a jihohin Sokoto da Ribas da Kebbi da kuma Kaduna.

    A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita jami'anta da ke sanya idanu kan zaɓukan gwamnoni da na 'yan majalisun dokokin jihohi ne suka samu nasarar ƙwace kayayyakin.

    View more on twitter
  14. An fara ƙirga ƙuri'a a zaɓen gwamnoni a Najeriya

    Kirge

    A jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya an fara rufe rumfunan zabe don kidayar sakamako na zaben gwamna da `yan majalisar dokoki.

    Mutum goma sha biyar ke takarar kujerar gwamnan, ciki har da gwamna mai ci, Ahmadu Umaru Fintiri. Daga Yola.

    Tun da sanyin safiya ne aka fara shirin zaɓen, kuma haka su ma masu kaɗa ƙuri’ar sun fito da wuri.

    Blessing wata mai zaɓe ce a jihar ta Adawama “Na fito da wuri da misalin ƙarfe hudu na safe, kuma na samu damar kaɗa kuri’ata a kan lokaci,”.

    Wasu kuma da dama ba su fito zaɓen ba domin suna tunanin abin da suka fuskanta a zaɓen shugaban ƙasa a ranar 25 ga watan Fabirairun da ya gabata.

    Wasu kuma sun ce katinsu ne ya ɓata domin haka ba za su iya zuwa kaɗa kuri’ar ba.

    Wakilan BBC a jihohin Kano da Kaduna sun ce tuni aka fara ƙirga ƙuri'u a wasu mazaɓu dake jihohin, bayan kammala zabe.

    Wakilin BBC a jihar Katsina ma, ya bayyana cewa an fara ƙirgen ƙuri'un a wasu mazaɓun jihar.

    Haka ma a jihohin Rivers da Abia wakilan BBC sun ce an fara ƙirga ƙuri'u a jihohin.

    Can ma a jihar Legas wakilan BBC sun ce an fara ƙirgen ƙuri'u.

    Zabe
    Zabe