Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Buhari Muhammad Fagge da Sani Aliyu

time_stated_uk

  1. Sai anjima!

    Asisat Oshoala has scored 13 goals this season
    Image caption: Asisat Oshoala - 'yar wasan kwallo a kungiyar Barcelona Femení ta mata

    Masu bibiyar wannan shafi, zan tsaya a nan domin abokan aikina su ci gaba da aikin da na fara tun bayan sallar Azahar.

    A koyaushe, Nine naku Sani Aliyu..ke muku fatan alheri.

    Kafin in tafi, ga wannan labarin: 'Yar Najeriyar nan Asisat Oshoala, mai buga wa kungiyar kwallon kafa ta mata ta Barcelona Femení a kasar Sfaniya ta kafa tarihi, bayan da ta jefa kwallaye uku a raga yayin wasa na 50 da kungiyarta ta yi tana samun nasara a jere.

    Asisat ta kasance gwarzuwar shekara sau biyar cikin 'yan wasan kwallo mata a nahiyar Afirka.

    Tun watan Yunin 2021 kungiyar ba ta yi tuntube ba a dukkan wasannin da ta buga na cikin gida.

    A wannan wasan, Barcelona ta lallasa Levante ne da ci 7 - 0.

  2. Majalisar wakilai ta umarci a kai gwamnan CBN gabanta ranar Talata

    Gbajabiamila

    Majalisar wakilan Najeriya ta umurci babban sufetan 'yan sandan kasar ya kai mata gwamnan babban bankin kasar nan da ranar Talata mai zuwa.

    Majalisar ta yanke wannan hukuncin ne bayan ta gayyaci gwamnan babban bankin har sau biyu ba ya zuwa.

    Wani rahoto na cewa 'yan majalisar suna so ne su ji daga bakin gwamnan dalilin da ya sa ba za a kara wa'adin daina amfani da tsofaffin takardun naira ba, wadanda bankin ya ce za su daina aiki daga ranar 31 ga wannan wata na Janairu.

    'Yan majalisar sun kai har wuya ne sakamakon gazawar gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele wajen bayyana a gaban wani kwamiti na musamman da majalisar wakilan ta kafa.

    Kasancewar har sau biyu kwamitin yana sa lokaci, amma gwamnan babban bankin ya bar su suna jiran gawon shanu… shi bai je ba bai kuma tura wakili ba, wato ba wan ba kani…ga shi kamar yadda 'yan majalisar ke cewa sun zaku su ji daga bakinsa ko wane dalili ne zai hana kara wa'adin daina amfani da tsoffin takardun kudin da bankin ya bayar, wato ranar 31 ga wannan wata na Janairu.

    Kazalika kwamitin ya gana da shugabannin bankunan kasuwanci da ke Najeriya, duka dai da nufin jin ta bankin su inda gaskiyar maganar take game da karancin da ake fama da shi na sabbin takardun kudin.

  3. Falasdinawa sun janye daga shirin hadin sasantawa da Isra'ila

    Falasdinawa

    Gwamnatin Falasdinu ta ce ta kawo karshen hadin gwiwar tsaro da Israila domin mayar da martani ga samamen da sojojin Israilar suka kai wa yankin yammacin kogin Jordan da suka mamaye inda Falasadinawa tara da suka hada da mayaka da farar hula sun rasa rayukansu.

    Kakakin gwamnatin Falasdinu ya ce, "Bisa la'akari da yadda ake ci gaba da cin zarafin alumarmu da kuma yadda ake ci gaba da karya yarjeniyoyi, ciki har da na tsaro, mun dakatar da shirin hadin gwiwar tsaro tsakaninmu da Israila."

    Rundunar sojin Israila ta ce ta kai wa mayakan kungiyar Islamic Jihad farmaki ne a sansanin 'yan gudun hijira da ke Jenin wadanda a cewarta suna shirin aiwatar da wani babban hari.

    Sakataren harkokin wajan Amurka Anthony Blinken zai yi tafiya zuwa yankin domin ya nemi bangarorin biyu da su kwantar da hankulansu.

  4. 'Yan bindiga sun kashe shugaban jam'iyyar APC, sun sace mutum biyar a Imo

    Gunmen

    Rahotanni daga Jihar Imo na cewa wasu 'yan bindiga sun kashe shugaban jam'iyyar APC na gundumar Umuchoke a garin Okwe da ke cikin karamar hukumar Onuimo.

    Mutumin mai suna Christian Ihim ya rasa ransa ne yayin da 'yan bindigan suka kai wani hari zuwa gidansa ranar Talata da dare.

    Baya ga halaka shi, 'yan bindigan sun kuma sace wasu jami'an jam'iyyar ta APC biyar.

    Daga nan rahotanni sun ce 'yan bindigan sun isa kauyen Okwelle inda suka sace wata jami'ar APCn mai suna Onyinyechi Egenti.

    Kakakin rundunar 'yan sanda a Jihar ta Imo, Henry Okoye ya tabbatar da aukuwar hare-haren amma ya bukaci a ba shi karin lokaci domin tattaro cikakken bayani kan batun.

    Shi ma kakakin jam'iyyar ta APC a Imo, Cajethan Duke ya sanar da manema labarai kisan Mista Ihim, da kuma sace jami'ansu na APC.

  5. Sojojin Najeriya sun sami galaba kan mayakan Boko Haram da ISWAP

    Sojojin Najeriya

    Ma'aikatar tsaron Najeriya ta ce ta sami gagarumar nasara a ayyukan tsaro da dakarun kasar ke gudanarwa tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, a shiyyoyi 6 na kasar cikin makwanni biyu da suka gabata.

    Hakan dai ya hada da murkushe masu tayar da kayar baya da sauran masu aikata miyagun laifuka, da kama makamai da kudade da baura da dai sauransu.

    A bayanan da hedikwatar tsaro ta Najeriya ta saba yi wa manema labarai duk bayan makwani biyu, daraktanta mai kula da harkokin watsa labarai, Manjo Janar Musa Danmadami, ya ce cikin makwanni biyun da suka gabata, rundunar sintiri ta HADIN KAI ta ci gaba da yin tsayuwar daka, wajen gudanar da ayyukanta na tsaro a kauyuka da dazuka da tsaunuka, har ma da garuruwa da birane da dama na shiyyar arewa maso gabashin Najeriyar.

    Alal misali, rundunar sintirin ta yi gumurzun gumaza da mayakan Boko Haram da na ISWAP da sauran masu aikata miyagun laifuka, a kauyukan Kwaatan Turare da Azir Bri a yankunan kanan hukumomin Kukawa da Damboa na jihar Barno.

    Baya ga kubutar da fararen hula 6 daga hannun 'yan bindiga da rundunar sintirin ta yi, Manjo Janar Musa Danmadami ya ce, masu tayar da kayar baya 267 da iyalansu sun mika wuya ga dakarun Najeriyar.

    A shiyyar arewa maso yammacin Najeriya ma, daraktan watsa labarai na hedikwatar tsaron kasar, ya ce rundunar sintiri ta HADARIN DAJI ta ci gaba da kai hari kan sansanoni da sauran wuraren da 'yan bindiga ke boye, a wasu kauyuka na yankunan kananan hukumomin Maru da Gusau na jihar Zamfara, da yankin karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina.

  6. Majalisa za ta umarci 'yan sanda su kamo Emefiele

    Governor of the Central Bank of Nigeria, (CBN) Godwin Emefiele and President Buhari during the unveiling of the New Naira Notes

    Kakakin majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila ya ce ba zai yi kasa a gwuiwa ba wajen neman Sufeto-Janar na 'yan sandan Najeriya Usman Baba ya fitar da sammacin kama Godwin Emefiele, wanda shi ne gwamnan babban bankin kasar.

    Wannan gargadin ya biyo bayan kin bayyana gaban majalisar a dalilin gayyatar da ta mika wa gwamnan. Mista Gbajabiamila ya sanar da haka ne a ranar Alhamis bayan da Alhassan Doguwa, shugaban masu rinjaye na majalisar ya gabatar da rahoton kwamitin majalisar bincike kan ayyukan banki na kasar.

    Alhassan Doguwa ya sanar da majalisar cewa Mista Emefiele bai bayyana a gaban kwamitin ba kamar yadda aka bukace shi yayi a ranar Laraba.

    A nasa bayanin da ya gabatar, Mista Gbajabiamila ya ce a shirye yake ya yi amfani da sashe na 89(1)(d) na kundin tsarin mulkin Najeriya wanda ya ba majalisa ikon umartar jami'an tsaro su kamo wanda ya ki bayyana a gaban majalisar.

    Sai dai Mista Emefiele ya bayyana cewa matsalar da aka kira shi akai ta karancin sababbin takardun kudi ce, kuma alhakin haka ya rataya ne a wuyan bankunan kasuwanci na kasar.

    Ya kuma kafe cewa ba zai tsawaita kwanakin da bankin ya tanadar wa 'yan Najeriya su sauya tsofaffin takardun kudinsu da sababbin ba.

  7. Babban bankin Najeriya ya kaddamar da katin cinikayya na bai-daya na AfriGo

    gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele
    Image caption: Gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele

    Babban bankin Najeriya ya kaddamar da wani katin cinikayya na cikin gida mai suna AfriGo, wanda 'yan kasar za su rika amfani da shi domin yin dukkan hada-hadar kudi a fadin kasar.

    Sunan tsarin da turancin Ingilishi "Nigerian National Domestic Card Scheme".

    Yayin kaddamar da katin, gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ya ce za a rika biyan dukkan cajin kudi kan cinikin da aka yi da katin da Naira ne, sai dai idan ya shafi hada-hada da kasashen waje.

    Mista Emefiele ya ce "Katin AfriGo alamar martaba ce ga Najeriya, kuma zai ba mu damar sauwaka wsa 'yan Najeriya tsadar da suke fuskanta wajen cinikayya a ciki da wajen kasar."

    Ya kara da cewa 'yan kasar na iya ci gaba da amfani da katunansu da bankunan kasar suka ba su, sai dai ba za a ci gaba da biyan kudin caji da dalar Amurka ba kamar da.

  8. Firaministan Habasha na son bunkasa dangantaka da Sudan

    Firaministan Habasha Abiy Ahmed tare da Shugaba Al-Burhan

    Firaministan Habasha Abiy Ahmed, na wata ziyarar aiki a Sudan domin tattaunawa da Shugaban mulkin soja na kasar Laftana Janar del Fattah al-Burhan.

    A ranar Alhamis Mista Abiy ya sauka a Khartoum, babban birnin kasar.

    Tashar talabijin mallakin gwamnatin Habasha ETV, ta ruwaito cewa firaministan na neman hanyoyin bunkasa dangantaka tsakanin makwabtan kasashen biyu ne.

    Sojojin Sudan da kungiyoyin fararen hula na kasar sun shafe shekaru suna kai ruwa rana kan hanyar da ta dace a mayar da mulki ga fararen hula bayan juyin mulkin watan Oktoban 2021.

    Dangantaka tsakanin Habasha da Sudan ta fara inganta bayan shekarun da suka yi suna karawa da juna bisa mallakin wani yanki mai albarkar noma na Al-Fashaga da ke kan iyakar kasashen biyu.

    Akwai kuma takaddamar da ta taso kan babbar madatsar ruwa mai samar da lantarki ta Grand Ethiopian Renaissance Dam da Habasha ta gina kan kogin Nilu - matakin da Sudan da Masar suke kallo a matsayin wanda zai rage yawan ruwan kogin da ke isa cikin kasashensu.

  9. 'Yan Najeriya 159 sun sauya kasa

    Ministan cikin gida Rauf Aregbesola

    Gwamnatin Najeriya ta ce akalla 'yan Najeriya 159 sun ajiye kasancewarsu 'yan Najeriya kuma sun karbi zama 'yan wasu kasashen na daban.

    Babban sakatare a ma'aikatar cikin gida ta kasar, Dr Shuaib Belgore ne ya sanar da haka yayin wata ganawa da manema labarai da aka shirya a fadar shugaban Najeriya da ke Abuja.

    Dr Belgore ya ce 'yan Najeriya 150 ne suka sauya sheka tsakanin 2006 zuwa 2021.

    A 2022 kuwa, 'yan kasar 159 ne suka dauki irin wannan matakin. Sai dai ministan cikin gida Rauf Aregbesola, wanda shi ma ya halarci wannan ganawar, ya ce tudadar 'yan kasar zuwa kasashen ketare ne ya haifar da karancin fasfuna da ake fama da shi a halin yanzu.

    Ya kara da cewa a 2022 kawai, hukumar shige da fice ta Najeriya (NIS), ta samar da fasfo 1,899,683, wanda ba a taba samun haka a cikin shekara bakwai da ta gabata.

    Ministan ya ce hukumar shige da ficen ta kuma samar da fasfuna fiye da miliyan 9 daga 2015 zuwa 2022.

  10. An sake kai wa Ukraine hari da jirage marasa matuƙi

    bbc

    Ukraine ta sake fuskantar hari daga jiragen sama marasa matuƙa da kuma makamai masu linzami daga Rasha, kwana ɗaya bayan Jamus da Amurka sun sanar cewa sun amince su samar wa kasar da tankunan yaƙi na zamani.

    Magajin garin Kyiv, Vitalyi -Klitschko ya ce an kashe mutun guda kuma an raunata wasu mutum biyu a harin da aka kai kan wani gini da ke kudancin birnin.

    Jami’ai a yankin Odesa da ke Kudanci sun ce an kai wa tashohin wutar lantarki da dama hari a wannan wuri da wasu sassan ƙasar.

  11. Ana tuhumar yaro ɗan shekara 13 da fyaɗe da cin zarafin mata

    HG

    Wani yaro ɗan shekara 13 zai fuskanci tuhuma kan cin zarafin mata da yara mata a Telford.

    Ƴan sanda sun ce sau biyar suna samun rahoto tsakanin 15 ga watan Disamba 2022 zuwa 19 ga watan Janairun, cewa ana yawan kai wa mata manya da kuma ƙanana tsakanin shekara 16 zuwa 34 hari a yankunan Hadley Leegomery.

    Ana tuhumar yaron da aikata laifukan cin zarafi ta hanyar lalata har sau tara, ƙoƙarin fyade sau biyu da kuma cin zarafi har da duka sau biyu.

    Ya bayyana a gaban kotun matasa ta Kidderminster a ranar Laraba, kuma yanzu yana tsare a ƙarƙashin kular hukumomi.

  12. Faransa ta yi wa jakadanta a Burkina Faso kiranye

    KH

    Faransa ta yi wa jakadanta daga BUrkina Faso, kwana guda bayan sanar da ayyukan sojinta a ƙasar sun zo ƙarshe.

    Ministan harkokin wajen Faransa Luc Hallade na dawowa ne daga tattaunawar hulɗar dangantaka tsakanin Faransa da tsohuwar ƙasar da ta yi wa mulkin mallaka.

    An shafe makonni ana gudanar da zanga-zanga kan ci gaba da zaman Faransa a Burkina Faso, wadda sojoji da ke mulki a ƙasar ke neman taimakon soji daga Rasha domin samun galaba a kan masu iƙirarin jihadi.

  13. Zulum ya ba da umarnin kafa ƙananan bankunan al'umma don musayar kuɗi

    z

    Gwamnan Jihar Borno da ke arewacin Najeriya ya bayar da umarnin kafa bankunan al'umma da za su yi aikin sauyawa al'ummar jihar tsofaffin kuɗaɗensu a duka jihohi 27 da Jihar take da su.

    Umarnin na Gwamna Zulum na zuwa ne bayan umarnin da CBN ya yi na a dakatar da karɓar tsofaffin takardun kuɗi a karar nan da 31 ga watan Janairun da muke ciki, umarnin ya shafi duka ƙanann hukumomin jihar 25 cikin 27 da take dasu, wadanda rikicin Boko Haram na tsawon shekara 12 ya shafa.

    Gwamnan ya sanar da ɗaukar wannan mataki ne a Maiduguri a ranar Laraba, yayin wata tattaunawa ta masu ruwa da tsaki wadda Shehun Borno Abubakar Umar Garbai Elkanemi ya halarta, wanda Wazirin Borno ya wakilta.

    Tuni aka yanke shawarar za a fara aiwatar da umarnin a ƙanan Monguno da Gwoza.

  14. Kamfanin da ya ƙera jirgin Boeing da ya yi haɗari zai bayyana gaban kotu

    BBC

    Kamfanin jirgin sama na Boeing zai bayyana gaban kotu game da tuhumar da ake masa ta zamba cikin aminci kan haɗarin da jiragensa biyu suka yi da mutum 346 suka mutu.

    Duka haɗuran biyu sun faru ne saboda gazawar da aka fuskanta ta shawo kan matsalar da jirgin kirar 737 ya fuskanta ta janyo haɗarin.

    Kamfanin ya san cewa bai bayyana komai ba kan matsalar jirgin, kuma ya kaucewa biyan tara da kuma diyya.

    'Yan uwan waɗanda suka rasa rayukansu na yunƙurin dawo da zarge-zagen da ake yi wa kamfanin.

    Wannan na nufin shi ne karon farko da kamfanin zai gurfana gaban kotu a hukumance kan abin da ke da alaƙa da haɗarin biyu, kuma dole a bayyana shi a matsayin mai laifi ko kuma akasin haka.

  15. Zelensky ya yi maraba da matakin Amurka da Jamus

    BBC

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi maraba da matakin gwamnatocin Washington da Berlin na shirin aike musu da tankunan yaƙi.

    Yace abu mai muhimmanci a yanzu shi ne a saki jiki a kawo mana kaya da wuri kuma a ƙara yawansu.

    Sannan kada a ɓata lokaci wurin bai wa sojojinmu horo.

    Alƙawarin Jamus na aikewa da tankunan yaƙin 14 ƙirar Leopard na nufin ya zo tare da bai wa sauran ƙasashen damar tura wa Ukraine irinsu.

  16. Noman ƙwayar Opium ya ƙaru a Myanmar - Bincike

    g

    Binciken Majalisar Ɗinkin Duniya ya gano cewa noman ƙwayar Opium ya ƙaru a Myanmar, tun bayan da sojoji suka ƙwace mulki.

    Majalisar Ɗinkin Duniyar ta yi amanna cewa matsin tattalin arziki da rikicin siyasa ne ya haifar da hakan, da kuma cewa tana tsada a kasuwar hada-hadar miyagun kwayoyi.

    Kafin juyin mulkin na 2021 an samu karuwar noman kayan abinci a Myanmar da kuma raguwar noman ya'yan kwayar ta Opium.

  17. An kashe Falasɗinawa takwas a harin da Isra'ila ta kai Jenin

    BBC

    Hukumomin Falasɗinawa sun ce an kashe mutum takwas ciki har da wata dattijuwa, yayin harin da sojin Isra'ila suka kai gaɓar yamma da kogin Jodan.

    Ministan lafiya na Falasɗinawa ya ce yanayi ya ƙazanta a Jenin, yayin da mutane da dama suka jikkata, kuma motocin ɗaukar marasa lafiya ba sa iya kai wa inda suke.

    Wuraren da ake kai yara wasa sun cika da hayaƙi mai sanya ƙwalla, in ji shi.

    Sojojin Irsa'ila ba su yi wani ƙarin bayani kan lamarin ba, sai dai kafafen yaɗa labaran cikin gida suna cewa, suna kai harin ne domin daƙile hare-harem da ake kai wa Isra'ilawa.

  18. Jihar Katsina ta ayyana hutun kwana biyu saboda ziyarar shugaban ƙasa

    AH

    Gwamnatin Jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ta ayyana yau da gobe a matsayin ranakun da babu aiki, domin bai wa ma'aikata damar tarbar shugaban ƙasar Muhammadu Buhari yayin ziyarar da zai yi ta kwana biyu a jihar.

    Cikin wata sanarwa da babban sakataren ma'aikatar yaɗa labarai da al'adu Sani Bala Kabomo ya fitar.

    Ya ce hutun da aka bayar zai taimakawa ma'aikatan jiha da na ƙananan hukumomi da na sauran hukumomi damar yi wa Shugaba Buhari barka da zuwa.

    Ya ƙara da cewa hutun ba zai shafi ayyukan tarayya da na bankuna ko kuma manyan ayyuka.

  19. Hajji a 2023: Saudiyya za ta karɓi baƙunci mahajjata miliyan biyu a bana

    BBC

    Saudiyya na shirin karɓar baƙuncin mahajjata miliyan biyu daga faɗin duniya a wannan shekarar ta 1444, kamar yadda Ministan Hajji da Umrah Dr Tawfiq Al-Rabiah ya bayyana.

    Dr. Al-Rabiah ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara zuwa Algeria a hukumance, inda ya bayyana cewa za a bai wa Algeria kujera 41,3000 ta mahajjatan bana.

    Saudiyya ta ce za ta yi farin cikin karɓar mahajjatan bana kan adadin da aka saba a baya gabanin zuwan annobar korona.Ministan ya bayyana yadda ma'aikatarsa da sauran hukumomin da suke da hannu a aikin hajji da umra suka shirya domin kula da tsarin lafiya da sauran aikace-aikace ga mahajjata.A watan Dismbar da ya gabata ne, Saudiya ta dawo wa da Najeriya adadin kujerun da ta saba ba ta sama da 95, 000, na mutanen da za su je aikin.

  20. Facebook zai iya buɗe shafin Donald Trump a ko wanne lokaci

    BBC

    Kamfanin Meta ya sanar da cewa zai janye dakatarwar da ya yi wa tsohon shugaban Amurka Donald Trump daga shafukansa na Facebook da Instagram.

    Shekaru biyu kenan da ya dakatar da Trump, bayan da ya wallafa sakon jinjina ga mutanen da suka yi kutse a majalisa a Washington.

    Trump na da mabiya miliyan 34 a Facebook, kuma a 'yan makonnin da suka wuce mabiyan sun riƙa kira da a buɗe ma gwanin na su shafinsa.

    Shugaban Meta Nick Clegg ya ce a bitar da suka yi sun gano cewa shafin na Trump ba shi da wani hadari a yanzu ga al'umma.