Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Mukhtar Adamu Bawa da Abdullahi Bello Diginza

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.

    Da fatan za ku ci gaba da bibiyar mu a wannan shafi na BBC Hausa.

    Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya!

  2. APC ta kori ɗan takarar gwamna da zaɓaɓɓen sanata a Taraba

    hah

    Jam'iyyar APC a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya ta kori ɗan takararta na gwamnan jihar a zaɓen 2023 da aka kammala David Sabo Kente kan zargin yi mata zagon- ƙasa.

    Haka kuma jam'iyyar ta ce ta kori zaɓaɓɓen sanatan Taraba da Kudu David Jimkuta sakamakon zarginsa da ta yi da yi mata zaon-ƙasa a lokacin zaɓukan da suka gabata.

    Shugaban jam'iyyar na jihar Elsudi Ibrahim ne ya bayyana a haka a wajen taron manema labarai da ya gudanar a Jalingo babban birnin jihar.

    Mista Elsudi ya ce daga yau Sabo Kente ya daina ɗaukar kansa a matsayin mamban jam'iyyar.

    Elsudi ya jaddada cewa har yanzu shi ne halastaccen shugaban jam'iyyar na jihar, kamar yadda kotu ta tabbatar, bayan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan ƙuri'ar yankan ƙauna da wasu mambobin kwamitin gudanarwar jam'iyyar suka kaɗa masa.

  3. Matashi sabon jini da ya zama ɗan majalisar tarayyar Najeriya

    Bashir Usman Gorau, matashi sabon jini da ya zama ɗan majalisar tarayya da ke wakiltar mazaɓar Gada/Goronyo daga jihar Sokoto, ya ce ɗaya daga cikin ƙalubalen da ya fuskanta shi ne 'yan uwansa matasa.

    Sabon zaɓaɓɓen ɗan majalisar ya ce babu abin da matashi ba zai iya yi ba, abin da ba sai sa kansa ba.

    ''Abin da duk ka tashi ka nema kuma ka kyautata niyyarka, to tabbasa za ka samu'', in ji shi

    Video content

    Video caption: Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon
  4. Na yi farin ciki da tarbar da aka nuna min - Tinubu

    Tinubu

    Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Nejeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce ya yi farin cikin komawa ƙasar bayan hutun mako biyar da ya yi a birnin Paris na ƙasar Faransa.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa Tuwita, Bola Tinubu ya ce ya yi matuƙar farin ciki da annashuwa kan irin gagarumar tarbar da aka yi masa a lokacin da ya sauka a filin jirgin saman Abuja babban birnin ƙasar.

    Zaɓaɓɓen shugaban ya kuma gode wa ɗimbim masiya da magoya bayansa kan irin ƙaunar da ya ce suna nuna masa.

    Ya ƙara da cewa yana nan a kan alƙawarin da ya ɗauka na samar da sabuwar Najeriya.

    View more on twitter

    Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya kuma ce yana cikin ƙoshin lafiya saɓanin jita-jitar da ake yaɗawa cewa yana cikin halin rashin lafiya.

  5. Tottenham ta kori kocin riƙo-ƙwaryarta bayan shan kaye 6-1 a hannun Newcastle

    Cristian Stellini

    Tottenham ta kori Cristian Stellini ƙasa da wata guda da kama aiki a matsayin kocin riƙon-ƙwaryar ƙungiyar.

    A yanzu, Ryan Mason - wanda a baya ya taɓa riƙe ƙungiyar bayan korar Jose Mourinho a shekarar 2021 - ya karɓin aikin harar da ƙungiyar na riƙo.

    Matakin ya zo ne bayan da ƙungiyar ta sha mugun kaye a hannun Newcastle da ci 6-1 ranar Lahadi, sakamakon da shugaban ƙungiyar Daniel Levy ya ce ƙungiyar ba za ta ''amince'' da shi ba.

    Ƙungiyar ta naɗa Stellini, mai shekara 48, ranar 26 ga watan Maris bayan da yarjejeniyar ƙungiyar da Antonio Conte ta zo ƙarshe.

    Rashin nasarar da ƙungiyar ta yi a hannun Newcastle, gagarumin koma-baya ne ga ƙoƙarin da ƙungiyar ke yi na shiga sahun huɗun farko a saman teburin Premier, matakin da zai sa ta samu gurbin shiga gasar Zakarun Turai ta baɗi.

  6. Buhari zai tafi taro Ghana

    a

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai halarci taron ƙolin shugabannin ƙasashen yankin tekun Guinea da za a gudanar a Accra babban birnin ƙasar Ghana.

    Cikin wani saƙo da fadar shugaban ƙasar ta wallafa a shafinta na Tuwita, ta ce shugaban zai bar Najeriya ranar Talata 25 ga watan Afrilu domin halartar taron, wanda shugaban ƙasar Ghana Nana Akuffo-Ado zai jagoranta.

    View more on twitter

    Ana sa ran shugaban zai gabatar da jawabi a taron wanda zai tattauna dabarun ƙarfafa zaman lafiya da tsaro da yaƙi da masu aikata miyagun laifuka a gaɓar tekun yankunan ƙasashen.

    Yayin halartar taron, shugaban zai samu rakiyar ministan harkokin ƙasashen wajen ƙasar Geoffrey Onyeama, da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno mai ritaya, da daraktan hukumar tattara bayanan sirri ta ƙasar Amb. Ahmed Rufai Abubakar, da sauran jami'an gwamnati.

  7. Wani basaraken gargajiya ya mutu a hannun 'yan bindiga a Najeriya

    ww

    Wani basaraken gargajiya a garin Aghara, da ke ƙaramar hukumar Kabba-Bunu a jihar Kogi da ke arewa ta tsakiyar Najeriya ya mutu a hannun 'yan bindigar da suka yi garkuwa da shi.

    Rahotonni sun ce basaraken mai suna David Obadofin, ya shafe kwanaki 12 a hannun 'yan bindiga bayan da suka yi garkuwa da shi.

    Wani mutum daga cikin iyalan basaraken ya ce ya mutu ne sakamakon azabtar da shi da masu garkuwan suka yi.

    Jaridar daily Trust a Najeriyar ta ruwaito wata majiya na cewa waɗanda suka sace basaraken sun nemi a biya su naira miliyan biyu kafin su sake shi tare da wata budurwa mai suna Temidayo Elewa.

    Bayanai sun ce basaraken ya mutu ne kafin a biya kuɗin fansar.

    'Yan bindigar sun sace basaraken - wanda hamshaƙin manomin kashu ne, tare da Elewa a ranar bikin Easter a gidansa da ke Aghara da misalin ƙarfe 11 na dare, inda suka buƙaci a biya kuɗin fansa har naira miliyan 60 domin sakinsu.

  8. Damisa ta biyu ta mutu a Indiya ƙasa da wata guda

    CHARL SENEKAL

    Wata damisa ta mutu a gidan adana kayan namun daji da Kuno da ke jihar Madhya Pradesh, karo na biyu da hakan ke faru cikin ƙasa da wata guda, kamar yadda wani jami'in gandun dajin ya bayyana.

    Ya ce kawo yanzu ba a san musabbabin mutuwar namijin damisar mai shekarar shida.

    Damisar na daya daga cikin damisa 12 da aka kai Indiya daga Afirka ta Kudu a watan Fabrairu.

    A shekarar da ta gabata ne Indiya ta yi yunƙurin sake farfaɗo da kiwon damisa a ƙasar, sama da shekara 70 bayan aka ayyana ƙamfar dabbar a ƙasar.

    Ranar 27 ga watan Maris wata damisar - da ke cikin rukunin farko na dabbobin da ka kai Indiya daga Namibiya - ta mutu, sakamakon ciwon ƙoda.

    A shekarar da ta gabata ne Namibiya ta kai wa Indiya damisa takwas biyar mata, uku maza a wani yunkuri na farfaɗo da kiwon dabbobin a ƙasar.

    A watan Fabrairu kuma Afirka ta Kudu ta aike wa Indiya damisa 12, inda aka tanadi tawagar likitocin dabbobi domin kula da lafiyarsu a gandun dajin da suke.

    A ranar 29 ga watan Maris ne kuma ɗaya daga cikin damisoshin da aka kai daga Namibiya ta haifi 'ya'ya huɗu, a wani abu da ministan muhallin ƙasar ya kira gagarumin ci-gaba.

  9. Labarai da dumi-dumiTinubu ya sauka a filin jirgin sama na Abuja

    Zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya koma ƙasar, bayan wata ziyara da ya kai ƙasar Faransa inda ya shafe tsawon mako biyar.

    Tinubu ya sauka ne da yammacin Litinin a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, da ke Abuja babban birnin ƙasar.

    Wani bidiyo da Bayo Onanuga mataimaki na musamman ga zaɓaɓɓen shugaban ya wallafa a shafinsa na Tuwita ya nuna manyan jiga-jigai da makusantan zaɓaɓɓen shugaban ƙasar na yi masa maraba.

    Daga cikin waɗanda suka halarci tarbar Tinubun, har da zaɓaɓɓen mataimakin shugaban, Kashim Shettima da Simon Lalong, babban daraktan rusasshen kwamitin yaƙin neman zaɓen Bola Ahmed Tinubu na dakon saukar sa a filin jirgin sama.

    View more on twitter

    Cincirindon 'ya'yan jam'iyya mai mulki wato APC da magoya bayan Tinubu ne suka tarbe shi lokacin da ya sauka a filin jirgin sama da yammacin Litinin.

    View more on twitter

    An yi ta raɗe-raɗi da yaɗa jita-jita game da tafiyar tasa zuwa Paris, inda wasu suka riƙa cewa ganin likita ya tafi, saboda taɓarɓarewar lafiyarsa.

    Komawarsa gida Najeriya ta kawo ƙarshen duk irin waɗannan raɗe-raɗi da jita-jita.

    Kuma a yanzu saura kwana 35 a rantsar da Bola Ahmed Tinubu matsayin shugaban Najeriya, inda zai karɓi ragamar mulki ranar 29 ga watan Mayu.

  10. MDD ta kwashe ɗaruruwan ma'aikata daga Sudan

    asd

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta kwashe ɗaruruwan ma'aikatanta da iyalansu daga Khartoum da sauran yankunan Sudan, cewar wani mai magana da yawun Babban Sakataren ƙungiyar.

    Antonio Guterres dai ya yi ta nanata kiraye-kirayen a tsagaita wuta don barin fararen hula su fice daga yankunan da rikice-rikicen ya shafa.

    Mai magana da yawun Babban Sakataren ya ƙara da cewa Majalisar Ɗinkin Duniya za ta ci gaba da aiki da ma'aikatanta da ke ciki da wajen Sudan kuma ta tabbatar da cewa shugaban harkokin diflomasiyyarta Volker Perthes har yanzu yana cikin ƙasar ta Sudan.

  11. A shirye muke mu kwaso 'yan Najeriya da suka maƙale a Sudan kyauta - Air Peace

    Air Peace

    Shugaban kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Air Peace a Najeriya Allen Onyema, ya ce kamfanin a shirye yake kwaso 'yan Najeriyar da suka maƙale a ƙasar Sudan a kyauta, yayin da faɗa tsakanin rundunonin tsaron ƙasar ke ci gaba da zafafa a birnin Khartoum.

    Sudan ta faɗa rikici tun ranar 15 ga watan Afrilu yayin da manyan rundunonin tsaron ƙasar da ke adawa da juna ke gwambza yaƙi da juna a ƙoƙarinsu na ƙarbe iko da Khartoum babban birnin ƙasar, da kuma yankin Darfur.

    Mista Onyema ya ce a shirye kamfaninsa yake ya taimaka, saboda a cewarsa Najeriya ba za ta so ta rasa mutum guda daga cikin 'yan ƙasarta da ke Sudan ba.

    Ya ƙara da cewa yana da muradin taimakawa wajen ceto 'yan Najeriyar da suka maƙale a Sudan, domin mayar da su ƙasar cikin kwanciyar hankali.

    Yayin da rikicin ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 400, tuni ƙasashen duniya irinsu Amurka da Jamus da Faransa da Netherlands suka fara kwashe 'yan ƙasashensu.

    Tuni dai ɗaliban Najeriya da ke Sudan suka fara kiraye-kirayen a kwashe su daga ƙasar sakamakon rikicin da ke ci gaba da ruruwa ƙasar

  12. 'Duk hanyoyin fita daga Khartoum hatsari ne da su'

    Wani jami'in diflomasiyya na Afirka ta Kudu ya ce kwashe mutane daga Sudan abu ne da ke cike da ƙalubale, ya kuma yi kira da a tsagaita wuta don ba da damar kuɓuta ga fararen hular da aka ritsa da su.

    Mai magana da yawun harkokin wajen Afirka ta Kudu Clayson Monyela ya ce duk hanyoyin fita daga Khartoum babban birnin ƙasar Sudan suna da "hatsari kuma kasada ce bin su".

    Ya ce har yanzu filin jirgin sama a rufe yake kuma babau alamun da ke nuna cewa faɗa yana ƙaƙƙautawa.

    Wannan ce tasa muke ci gaba da kiran a tsagaita don a bar wata hanyar ficewa mai aminci ga mutanen da ke son su fita kuma a ba da dama ga ma'aikatan agaji, in ji jami'in diflomasiyyan.

    Clayson Monyela ya ce hukumomin Afirka ta Kudu na "aiki ba dare ba rana don ganin mun fitar da mutanenmu".

  13. An kashe mutum ɗaya a rikicin Gwarimpa

    FCT
    Image caption: An ga bidiyon wasu matasa suna jifa da ƙona tayoyi a kan titi, amma 'yan sanda sun ce an shawo kan rikici

    'Yan sandan babban birnin Abuja sun tabbatar da mutuwar mutum ɗaya a wani rikici da ya ɓarke a unguwar Gwarimpa.

    Mai magana da yawun 'yan sandan Abuja SP Josephine Ade ta faɗa wa BBC cewa rikicin ya ɓarke tsakanin wasu ƙabilu guda biyu mazauna wani yanki da ake kira Gwarimpa village.

    Bayanai sun ce tun ranar Asabar ne tarzomar ta fara bayan ƙabilar Gbagyi sun yi yunƙurin korar wasu da suke zargin suna dillancin ƙwayoyi a yankin.

    'Yan sanda sun ce mutumin da aka kashe matashi ɗan shekara 20, kuma ya rasu ne sanadin raunukan da aka ji masa a jiya Lahadi.

    Sun ce rikicin ya sake tashi da safiyar Litinin, bayan Hausawa sun samu labarin rasuwar ɗan'uwan nasu da aka kai asibiti sanadin raunukan da ya ji, ko da yake sun yi ƙoƙari, a cewar Josephine sun shawo kan al'amuran.

    Ta ce ba gaskiya ba ne jita-jitar da ake yaɗawa cewa Fulani makiyaya ne suka kai hari unguwar Gwarimpa a cikin birnin Abuja.

    Wasu kafofin yaɗa labarai sun ba da rahoton cewa faɗan ƙabilancin ya yi sanadin mutuwar mutum uku, zargin da mai magana da yawun 'yan sanda ta ce shi ma babu ƙanshin gaskiya a ciki.

  14. Faransa ta rufe ofishin jakadancinta a Sudan

    Ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta ce ta rufe ofishin jakadancinta a ƙasar Sudan.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma'aikatar ta ce ofishin jakadancin ba zai zama wata matattarar jama'ar da ke son barin birnin Khartoum ba.

    Ofishin jakadancin ya ce zai ci gaba da aiki daga birnin Paris na ƙasar Faransa ƙarƙashin kulawar jakadanta a Sudan ɗin.

    Sanarwar ta ƙara da cewa ''Faransa na ƙoƙarin ganin an tsagaita wuta, tare da maido da tattaunawar miƙa mulki a Sudan''.

    ''Faransa na goyon bayan yunƙurin da ƙungiyoyin Tarayyar Afirka, ta ƙasashen gabashin Afirka, da ƙungiyar ƙasashen Larabawa, da ta Tarayyar Turai, da Majalisar Dinkin Duniya, ke gudanarwa wajen kawo zaman lafiya a ƙasar'', in ji sanarwar.

    ''Faransa na kira ga duka ɓangarorin da ke rikici da juna, da su bari a kai kayayyakin jin-ƙai, da kwashe fararen hula tare da maido ta tattaunawar siyasa a ƙasar'', in ji sanarwar.

    Tuni dai ƙasashen duniya suka fara yunƙurin kwashe jami'an diflomasiyyarsu da kuma 'yan ƙasashensu daga ƙasar ta Sudan tun bayan ɓarkewar rikicin ƙasar a ƙarshen makon da ya gabata.

  15. Tinubu zai koma gida Najeriya bayan hutun mako biyar

    Tinubu
    Image caption: Zaɓaɓɓen shugaban ya bar Najeriya tun ranar 22 ga watan Maris don zuwa Paris da London da kuma Saudiyya

    A Litinin din nan ne ake sa ran saukar zaɓaɓɓen shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu a Abuja, babban birnin ƙasar.

    Zai koma Najeriya ne bayan ya shafe tsawon mako biyar a Paris, inda ya huta, bayan kammala yaƙin neman zaɓen da ya ba shi nasara.

    Tun farko an tsara cewa zaɓaɓɓen shugaban na Najeriya zai kwan biyu a Paris cikin ƙasar Faransa, daga nan kuma ya wuce zuwa birnin London, kafin ya dangana da ƙasar Saudiyya.

    Sai dai rashin ganin sa a ƙasar Saudiyya lokacin aikin umra, musamman daidai lokacin da shugaban ƙasar mai barin gado, Muhammadu Buhari yake can, ya haifar da jita-jita da raɗe-raɗi.

    Wani mataimakinsa na musamman Bayo Onanuga ne ya tabbatar da rahoton komawar Tinubun Najeriya, ko da yake bai cewa ga taƙamaimai lokacin da zai sauka a ƙasar ba.

  16. Ga wasu alƙaluma game da ƙasar Sudan

    Sudan, wadda ta taɓa zama ƙasa mafi girma kuma mafi rarrabuwar yankunan al'ummomi a nahiyar Afirka, ta kasu zuwa ƙasashe guda biyu a watan Yulin 2011, bayan jama'ar kudancin ƙasar sun kaɗa ƙuri'ar samun 'yanci.

    Gwamnatin Suda ta sanya wa matakin 'yancin cin gashin kan Sudan ta Kudu albarka, inda mafi akasari mabiya addinin Kirista da masu addinin gargajiya suka shafe tsawon shekaru gommai suna gwagwarmayar adawa da mulkin Larabawa Musulmai 'yan arewa.

    Sai dai kuma, har a lokacin ba a kammala warware wasu batutuwa ba - musamman game da yadda za a raba arziƙin man fetur da shata kan iyaka - batutuwan da suka ci gaba da haifar da tunzuri tsakanin ƙasashen biyu maƙwabtan juna.

    Rikici ya daɗe yana addabar Sudan.

    Yaƙin basasa har karo biyu tsakanin arewa da kudu ya yi sanadin mutuwar mutum miliyan ɗaya da rabi - kuma yaƙin da ake ci gaba da fama da shi a yankin Darfur ya yi sanadin tserewar mutum miliyan biyu daga gidajensu, wasu fiye da 200,000 kuma suka halaka.

  17. An kashe gomman fararen hula a Burkina Faso

    Burkina
    Image caption: Kamar sauran ƙasashen Sahel da dama, Burkina Faso ma tana fama da rikicin masu iƙirarin jihadi

    Hukumomi a arewacin Burkina Faso sun ce an kashe fararen hula kusan 60 a ƙauyen Karma da ke kan iyaka da ƙasar Mali.

    Wani mai shigar da ƙara a yankin ya ce an sanar da shi faruwar lamarin ne ranar Juma'a inda ya ƙara da cewa wasu mutane ne da ke sanye da kakin sojoji suka aiwatar da kisan.

    Ko a makon jiya ma, an far wa sojojin Burkina Faso da wasu sojojin sa-kai a yankin da ke kusa da Wahiguya inda mutane kusan 40 suka mutu tare da raunata fiye da 30.

    An kashe dubban mutane tun a lokacin da masu tada kayar baya suka fara kai hari a yankin.

  18. Ga bayanin ƙasashen da suka kwashe mutanensu daga Sudan zuwa yanzu

    Daidai lokacin da yaƙin da ake gwabzawa ya shiga mako na biyu, ƙasashen waje sun fara ƙoƙarin kwashe jami'an diflomasiyyarsu da kuma'yan ƙasashensu a ƙarshen makon da ya wuce.

    Ga taƙaitaccen bayani kan abin ya faru zuwa yanzu:

    • Amurka da Kanada da Burtaniya sun ba da sanarwa a ranar Lahadi cewa sun kwashe jami'an diflomasiyyarsu zuwa wajen ƙasar ta Sudan
    • Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya tabbatar da cewa jami'an ƙasarsa sun yi aikin kwashe Faransawa a ranar Lahad da Litinin, inda suka fitar da 'yan Faransa 388 da jami'an diflomasiyyar ƙasar daga Sudan
    • Haka zalika, an kwashe wasu mutanen ƙasar Holland su ƙalilan daga birnin Khartoum a jiragen saman Faransa
    • Rundunar sojojin Jamus ta ce jiragen sama guda uku a karon farko sun bar Sudan inda suka nufi Jordan da mutum 101 a ciki
    • Italiya da Sifaniya sun kwashe mutanensu - Jami'an ofishin jakadancin Sifaniya sun ƙunshi 'yan ƙasar Argentina da Colombia da Ireland da Portugal da Poland da Mexico da Venezuela da Sudan.
    • Turkey- wata muhimmiyar mai ba da gudunmawa cikin harkokin Sudan - ta tattara mutum 640 a cikin motocin bas-bas 13 don kwashe su ta hanyar titin mota - ƙarin wasu 500 kuma sun taru a wata cibiyar kwashe 'yan ƙasashen waje. Ofishin jakadancin Turkey na ƙunshe da 'yan ƙasashen Azerbaijan da Japan da China da Mexico da kuma Yemen
    • Mutanen ƙasashen Turai fiye da 1,000 aka kashe daga Sudan, kamar yadda babban jami'in kula da manufar hulda da ƙasashen ƙungiyar chief Josep Borrell ya ce a ranar Litinin, musammam ma ya gode wa Faransa kan aikin da ta yi.
    • Mutane fiye da 150 ne akasari daga ƙasashen yankin Gulf da Masar da Pakistan da Kanada aka kwashe ta ruwa zuwa tashar tekun Jeddah a ƙasar Saudiyya.
  19. Najeriya za ta kwashe ɗalibai 5000 daga Sudan a motocin bas-bas

    Ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya shaida wa BBC cewa ofishin jakadancin ƙasar a Sudan yana ƙoƙarin shirya motocin bas-bas da za su kwashe ɗaliban ƙasar kimanin 5000.

    Ana dai fatan kwashe ɗaliban ne zuwa kan iyakar Sudan da ƙasar Masar.

    Daga ƙasar Masar ne kuma za a shirya yadda hukumomi za su fara kwaso ɗaliban a cikin jiragen sama zuwa gida Najeriya.

    Sai dai zuwa yanzu, hukumomi a Najeriya ba su ce ga lokacin da za a fara wannan aiki na kwashe ɗaliban ba daga Sudan ɗin ba.

    Sojojin Sudan da rundunar RSF ta masu kayan sarki na ci gaba fafata yaƙi a gwagwarmayar ɓangarorin biyu ta ƙwatar iko.

  20. Ƙasashen duniya na ƙara narka kuɗi kan ayyukan sojoji

    Wata cibiyar bincike kan rikice-rikice da ke ƙasar Sweden ta ce a tarihin duniya ba a taɓa kashe kuɗi kan harkokin sojoji kamar a bara ba.

    Wannan dai ya faru ne saboda yaƙin Russia da Ukraine da kuma zaman ɗar-ɗar da ke ƙaruwa a gabashin Asiya musamman ma Taiwan.

    Wakilin BBC ya ce an riƙa samun ƙarin kuɗaɗen da ake kashewa kan harkoki da sayen kayan aikin sojoji har tsawon shekara takwas a jere, kuma yaƙin Russia da Ukraine ne musabbabin hakan, musamman ma a nahiyar Turai.

    Cibiyar ta ƙasashen duniya mai bincike kan zaman lafiya da ke birnin Stockholm ta ce kuɗin da aka kashe ya kai sama da dala tirliyan biyu a shekarar da ta gabata.

    Binciken ya ƙara da cewa Amurka dai ita ce ta fi kowacce ƙasa kashe kuɗi kan ayyukan soji a duniya.

    Defence spending
    Image caption: Binciken ya ce Amurka ce ta fi kashe kuɗi kan harkoki da ayyukan sojoji a duniya