Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Buhari Muhammad Fagge da Abdullahi Bello Diginza

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, a madadin sauran abokan aiki Abdullahi Bello Diginza ke cewa sai da safe.

  2. Mutum 50 sun mutu a hatsarin mota a Pakistan

    Mutum fiye da 50 ne suka mutu sakamakon haɗurran mota biyu daban-daban a Pakistan.

    Mutum 41 sun rasu ne lokacin da motar bas ɗin da suke ciki ta afka cikin kwata a gundumar Balochistan.

    Hukumomi sun ce akwai yiwuwar sitiyari ne ya ƙwace wa direban saboda yana gudu sosai.

    A arewa maso yammacin ƙasar kuma, yara 10 ne suka mutu bayan kifewar kwale-kwalensu.

    Suna cikin mutum kusan ashirin da biyar da jirginsu ya kife a Tafkin Tanda Dam yayin da suke yawon buɗe-ido.

    Yaran ɗalibai ne - da ke tsakanin shekaru bakwai zuwa sha huɗu - da ke yin balaguro zuwa gundumar Kohat daga makarantar Islamiyyarsu. Sauran yara da yawa na cikin mawuyacin hali a asibiti.

  3. Mutum tara sun mutu bayan da tirela ta faɗa kan gadar Legas

    hatsari

    Fasinjoji tara sun mutu yayin da wata motar ɗauka kaya ta faɗa kan gadar Ojuelegba a birnin Legas da ke kudu maso yammcin Najeriya.

    Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar ta ce jami'anta na aiki domin ceto rayuwar waɗanda lamarin ya rutsa da su.

    Rahotonni sun ambato babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas ya ce mutum tara ne suka mutu ciki har da ƙananan yara biyu.

    “Bayan mun hallara inda lamarin ya faru, mun iske motar ɗaukar kontena ce ta faɗa kan wata motar fasinja'' in ji babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar.

    Rahotonni sun ce motar na cikin ɗaukar fasinjia ne a lokacin da motar ɗaukar kontenan ta ƙwace wa direban inda ta faɗa kan gadar.

  4. Zaɓen 2023: Yadda na'urar BIVAS za ta tantance masu zaɓe

    Shin ya na'urar BIVAS za ta tantance masu kaɗa ƙuri'a a lokacin zaɓe?

    Saurari cikakken bayani game da yadda sabuwar na'urar da Hukumar Zaɓen Najeriya INEC ta ɓullo da ita domin yin amfani da ita a zaɓen ƙasar da ke tafe a watan gobe.

    Video content

    Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin sauraron shirin
  5. Chelsea ta ɗauki Malo Gusto daga Lyon

    BBC

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta ɗauki ɗan wasan bayan Faransa Malo Gusto daga Lyon kan kuɗi fam miliyan 30.7

    Gusto mai shekara 19 ya sanya hannun kan kwantiragi da Chelsea har zuwa kakar wasa ta 2030.

    A wata sanarwa da Chelsea ta fitar, ta ce matashin ɗan ƙwallon zai ci gaba da taka-leda a Lyon har zuwa ƙarshen kakar wasa ta bana kafin ya fara wasaa ƙungiyar a sabuwar kakar wasa mai zuwa.

    Gusto ya fara buga wa Lyon wasa ne a watan Janairun 2021, inda kawo yanzu ya buga wa ƙungiyar - wadda ke mataki na tara a kan teburin Ligue 1 - wasa 15

    Kawo yanzu Chelsea ta sayi 'yan wasa shida a cikin Janairun da muke ciki, bayan karɓo aron Joao Felix daga Atletico Madrid.

  6. Kusan naira tiriliyan uku ne mutane ke ci gaba da ɓoyewa a Najeriya- CBN

    KUDI

    Babban Bankin Najeriya CBN ya ce bayanan alƙaluman da yake da su sun nuna cewa ya zuwa watan Octoban 2022 yawan kuɗin da ke ɓoye a hannun mutane a ƙasar ya kai naira tiriliyan biyu da biliyan 700.

    Wannan na ƙunshe ne cikin sanarwar ƙara wa'adin amfanin da tsoffin takardun kuɗin ƙasar da CBN ɗin ya fitar ranar Lahadi.

    CBN ya ce “bayanan da muka samu tun a shekarar 2015, sun nuna cewa kuɗaɗen da ke yawo a hannun ‘yan Najeriya sun kai naira tiriliyan ɗaya da biliyan 400. Amma ya zuwa watan Oktoban 2022, alƙaluma sun nuna cewa akwai sama da naira tiriliyan uku da biliyan 230 da ke yawo a hannu mutane.

    “Wannan na nuna cewa naira biliyan 500 ne kacal a hannun bankuna, yayin da naira tiriliyan biyu da biliyan 700 ke ɓoye a hannun wasu ƙalilan'', in ji sanarwar

    Gwamnan CBN ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su zama masu biyayya da haɗin kai wajen tabbatar an gama mayar da kuɗaɗen ba tare da wani tashin hankali ba.

    A yanzu dai CBN ɗin ya tsawaita wa'adin amfani da tsoffin kuɗin zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu, a yayin da bankuna za su rufe musanya kuɗaden ranar 17 ga watan Fabrairu

  7. Gwamnatin Somaliya ta kashe mayaƙan al-Shabab fiye da 130

    BBC

    Gwamnatin Somaliya ta ce hukumar tsaron ƙasar da sashen tattara bayana sirri na ƙasar sun ƙaddamar da hare-hare kan ƙungiyar Al-Shabab.

    Gwamantin ƙasar ta ce ta kashe mayaƙan ƙungiyar fiye da 136 a yankin Shabelle na kasar.

    Haka kuma bayanan da gwamnatin ke fitarwa sun nuna cewa dakarun gwamnatin sun raunata mayaƙan ƙungiyar 98 a hare-haren da ta ƙaddamar a yankin.

    Gwamnatin Somaliya dai ta kwashe shekaru tana yaki da ƙungiyar al-Shabab a ƙasar.

  8. Zaɓen 2023: 'Yan sandan Najeriya sun samu horo kan kunce abubuwa masu fashewa

    'yan sanda

    Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kammala bayar da horo ga jami'anta masu aiki a ɓangaren lura da abubuwan fashewa, gabanin babban zaɓen ƙasar da ke tafe.

    A wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce Babban Sifeton 'Yan sandan ƙasar Usman Baba Alakli ne ya amince da bayar da horo a kan hanyoyin da ya kamata a bi domin kare kai daga abubuwan fashewa gabanin babban zaɓen ƙasar da ke tafe

    Sanarwar ta ce horon na daga cikin tsare-tsaren babban sifeton 'yan sandan na tabbatar da bayar da horo a kan lokaci ga jami'an 'yan sandan musamman waɗanda suke da wata ƙwarewa ta musamman.

    Bayan kammala horon wanda aka gudanar a birnin Legas, an kuma raba wa jami'an wasu na'urorin gano abubuwan fashewa da na kunce boma-bomai, waɗanda Majalisar Dinkin Duniya da haɗin gwiwwar ƙasar Amurka suka bai wa rundunar 'yan sandan.

    'Yan sanda

    Babban Sifeton 'Yan sandan ƙasar ya kuma tabbatar wa 'yan ƙasar cewa rundunar ta ɗauki matakai domin tabbatar da cewa ta daƙile yaɗuwar abubuwan fashewa musamman a wuraren da al'umma suke harkokinsu.

    Haka kuma ya ce an girke jami'an 'yan sandan da suka samu horon tare da na'urorin cikin shirin ko-ta-kwana domin sanya ido kan shigo da abubuwan fashewa cikin ƙasar ta ɓarauniyar hanya.

    'Yan sanda

    Yayin da yake jawabi kan shirin da rundunar ta yi kan babban zaɓen ƙasar da ke tafe, Babban Sifeton 'yan sandan ya umarci kwamishinoni da mataimakansa a faɗin ƙasar da su ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaron ƙasar domin tabbatar da yin zaɓen ƙasar cikin kwanciyar hankali.

  9. Sauya fasalin naira: Majalisar wakilai ta yi watsi da ƙarin wa'adin da CBN ya yi

    majalisa

    Kwamitin majalisar wakilan Najeriya kan sauya fasali da musanya tsoffin kuɗi ya yi fatali da ƙarin wa'adin kwana 10 da Babban Bankin ƙasar ya yi na amfani da tsoffin takardun kuɗi.

    A wata sanarwa da gwamnan Babban Bankin Godwin Emefiele ya fitar ranar Lahadi ya ce shugaban ƙasar Muhammdu Buhari ne ya sahale wa CBN ɗin yin ƙarin wa'adin zuwa ranar 10 ga watan fabrairu.

    To sai dai a martanin kwamitin ƙarƙashin jagorancin shugaban masu rinjaye na majalisar Alhassan Ado Doguwa, ya yi watsi da ƙarain wa'adin, yana mai cewa dole CBN ya yi biyayya da sashe na 20, ƙaramin kashi na 3, da 4 da kuma 5 na dokar CBN.

    Idan za a iya tunawa dai a ranar Talata ne majalisar ta kafa kwamitin da zai duba batun wa'adin da CBN ɗin ya saka, bayan 'yan ƙasar da dama sun yi ta kokawa kan irin wahalhalun da suke sha a ƙoƙarinsu na musanya kuɗadensu.

    Doguwa ya ce "Wa'adin kwana 10 da CBN din ya ƙara ba mafita ba ne, mu abin da kawai muke buƙata a matsayinmu na 'yan majalisa shi ne CBN ya yi biyayya ga sashe na 20 ƙaramin kashi na 3 da na 4 da kuma na 5 na dokar CBN''.

    " A matsayin Najeriya na ƙasa mai tasowa, kuma mai bin tafarkin dimokradiyya dole mu yi biyayya da abinda doka ta tanadar.

    Ya ƙara da cewa majalisar wakilan za ta bayar da umarnin kamo gwamnan Babban Bankin domin tilasta masa bayyana a gaban kwamitin.

    Doguwa ya ci gaba da cewa kwamitinsa zai ci gaba da aiki har sai ya tabbatar da biyan buƙatun 'yan ƙasar kamar yadda doka ta tanadar.

    Yayin da yake bayyana ƙarin wa'adin kwana 10 da cewa ba wani abu ba ne illa yaudarar 'yan ƙasar tare da ƙara jefa tattalin arzikin ƙasar cikin halin ni-'yasu, Doguwa ya ce dole ne gwamnan Babban Bankin ya bayyana a gaban Majalisar wakilan ko kuma ya fuskancoi barazanar kama shi, ta hanyar yin amfani da ƙarfin da doka ta bai wa majalisar.

    Doguwa ya kuma ce matakin na Babban Banki na iya yin barazana ga babban zaɓen da ke tafe.

  10. Zamu farfaɗo da Borno ta ci gaba da zama jihar da ke samar da kayayyaki – Obi

    Obi

    Dan takarar shugabancin Najeriya a Jam'iyyar Labour Peter Obi, ya yi alƙawarun farfaɗo da Jihar Borno ta zama cikin jihohi masu samar da abubuwa ta zama cikin waɗanda Najeriya ke alfahari da su, idan aka zaɓe shi ya zama shugaban ƙasa.

    Obi ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da wasu ɗalibai da matasa a wani taron da ya yi da jama'ai kafin ya fara gangamin neman zaɓe a Maiduguri.

    Ya ce yana fatan sauya Najeriya zuwa yanayi mai kyau, inda zai tabbatar da adalci da daidaito da kuma samar da ayyukan more rayuwa, kuma su ne za su zama manyan abubuwan da na sa a gaba.

    "Borno ta fi girman Belgium da Netherlands da Poland da kuma Isra'ila.

    Muna tabbatar muka rashawa ba za ta samu wurin zama ba kazali rashin tsaro da yawan yajin aikin ASUU idan Obi ya zama shugaban ƙasa."

  11. An rufe rediyon sashen Larabci na BBC da ke aiki sama da shekara 85

    BBC

    A wani bangare na mayar da hankali kan ayyukan da suke gudana a intanet da kuma tsuke bakin aljihu, BBC ta rufe gidan radiyonta na bangaren Larabci wanda yake shekara 85 yana gudamar da ayyukansa.

    A watan Satumbar 2022 ne BBC ta ayyana sashen Larabci cikin sashenta 10 da za ta rufe, tare da na China da na Indiya da kuma na Fasha.

    BBC ta rufe ayyuka 100 tun daga babban sashenta na duniya baki daya da ke Birtaniya, ta kuma ɗauki matakin ne domin rage kashe-kashen kuɗaɗenta saboda Gwamnatin Burtaniya ta ce za ta rage ba ta kudaden gudanarwa.

    Wannan lamari zai shafi aƙalla ayyuka 382, yayin da ma'aikatar ke ƙara karkata wajen koma aiki a intanent kuma take yunkurin toshe giɓin da take da shi na dalar Amurka miliyan 35.

  12. Trump ya ƙaddamar da yaƙin neman zaɓensa

    BBC

    Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump ya soma gangamin neman sake darewa mulkin ƙasar a zaɓen 2024.

    A lokacin wani jawabi a taron shekara-shekara na Republican a New Hampshire, Mista Trump ya zargi gwamnatin Biden da jefa Amurka cikin tasku, yana mai cewa hakan yafi kowa bakanta masa rai da kuma zaburar da shi.

    Ya caccaki Mista Biden kan yada yake tunkarar matsalolin baƙin-haure ta iyakar Mexico, yana mai cewa idan ya sake zama shugaba, zai sake dawo da dokokinsa na tsaro a kan iyakoki cikin sa'o'i.

    Ya ce zaben 2024 dama ce ta ceto ƙasarmu, kuma muna buƙatar shugaba da zai aiwatar da hakan a ranar sa ta farko.

    Mista Trump zuwa yanzu shi kadai ne ya fito ya bayyana aniyarsa ta sake neman kujerar shugaban kasa a badi, koda yake akwai tsoshon gwamnan Florida, Ron DeSantis, da tsohon mataimakin shugaban kasa, Mike Pense da kuma tsohuwar gwamna a South Carolina, Nikki Haley da ake ganin duk za su shiga wannan takara.

  13. Adadin waɗanda girgizar ƙasa ta shafa a Azarbaijan na ƙaruwa

    bbc

    Gwamnan Yammacin Azarbaijan, Mohammad Sadegh Motamedian ya sanar da ƙarin adadin mutanen da girgizar ƙasar da aka yi a Khoi ta shafa.

    Kamar yadda jaridun Iran suka ambato cewa ya bayyana adadin waɗanta suka jikkata ya zuwa 816.

    A jiya aka fuskanci wata girgizar ƙasa da ta faru kan ma'aunin illarta 5.9 da ƙarfe 21:44 a Khoy a yammacin Azerbaijan.

    Hukumomi kuma sun ce adadin waɗanda suka mutu sanadin girgizar ƙasar ya kai mutum uku.

  14. Newcastle ta amince ta ɗauki Gordon daga Everton

    BBC

    Newcastle na dab da ɗaukar dan wasan gaban Everton Anthony Gordon bayan ƙungiyoyin biyu sun amince da cikiniki tsakaninsu kan fan miliyan 45.

    Gordon ya koma filin atisayen Everton a ranar Juma'a bayan share kusan mako baya nan.

    Da wuya a iya dukan ƙirji a ce an kammala cinikin ɗan wasan mai shekara 21 nan da ranar Talata wadda ita ce ta ƙarshe gabanin rufe lokacin musayar 'yan wasa.

    Ainihin kuɗin da aka sayi ɗan wasan an siye shi ne fan miliyan 40 amma daga baya ya koma 45 da sauran tsarafe-tsarafe.

    Chelsea ta so ɗaukar Gordon a wannan kakar, yayin da Everton ta nemi fan miliyan 60.

  15. Ba wani rashin jituwa tsakanina da Buhari - Tinubu

    Tinubu Facebook

    Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce babu wani saɓani tsakaninsa da Shugaba Buhari, yana cewa har yanzu mai biyayya ne shi ga shugaban.

    Ɗan takarar ya bayyana haka ne ga magoya bayansa lokacin da ke yakin neman zaɓe a Gusau babban birnin Jihar Zamfara, lokacin da ya yi musu alƙawarin zai kawo ƙarshen matsalolin da suka addabi Jihar, tare da bunƙasa harkokin noma.

    Kalaman da ɗan takarar ya yi game da sauyin kuɗi da kuma layin man fetur da ake fama da shi a faɗin ƙasar.

    Tuni aka riƙa ce-ce-ku--ce game da maganganun nasa ana ganin kamar wani saɓani ne ya faru tsakaninsa da shugaba Buhari.

  16. An yi arangama tsakani jami'an tsaro da masu zanga-zanga a Peru

    BBC

    'Yan sanda a Peru sun yi amfani da hayaƙi mai sa kwalla tare da datse hanyoyi a ƙoƙarin daƙile masu zanga-zangar adawa da gwamnati da suka fantsama kan manyan tittunan babban birnin kasar, Lima.

    An dai yi arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami'an tsaro a wajen Kotun ƙoli da ke birnin.

    Masu boren sun yi amfani da ƙarfi wajen tumɓuke shingen da aka kafa tare da kai wa jami'an tsaron hari.

    Kwanaki bakwai kenan da aka soma wannan rashin zaman lafiya, bayan tsige shugaba Pedro Castillo, mai sassaucin ra'ayi kan zargin Rashawa, inda yanzu haka ake tsare da shi.

    Magoya-bayansa na son a sake zabe a ƙasar.

  17. Ana ci gaba da ƙorafi kan ƙarancin sabbin takardun naira

    CBN

    A Najeriya kusan duk inda ka zagaya batu ɗaya ne ya mamaye komai, batun sauyin takardun kuɗi da gwamnati ta ɓullo da shi.

    Haka lamarin yake tsakanin matasa da dattijai har ma da ƙanana yara.

    Saboda mafi yawan mutane sun daina karɓar tsofaffin kudin a kasuwancin da suke yau da gobe, tsoron kada ta rutsa da su su yi hasara nan da 31 ga watan Janairun da muke ciki.

    A ɓangaren cirar kuɗi kuwa, duk wajen ATM ɗin da mutum zai je zai tarar da layi kamar kyauta ake raba kuɗaɗen.

    Wasu ATM ɗin ma babu kuɗin, sa rai da za a sanya su ne ke sa mutane su kafa dogon layi domin jira cirar kudi.

    A farkom makon jiya mutum zai iya cirar abin da ya kai har naira 40,000 da kati ɗaya, amma a yanzu an ƙayyade abin da za a iya cirewa da bai fi 20,000 ba.

  18. Ana tantama game da harin da Ukraine ta kai kan wani asibiti a Luhansk

    BBC

    Ana samun bayanai masu cin karo da juna kan harin makami mai linzami da Ukraine ta kai kan asibiti a wani yankin gabashi na Luhansk da aka mamaye.

    Rasha ta ce harin da aka yi amfani da makamin HIMARS ya yi ajalin mutane 14 da jikkata 24.

    Ta ce asibitin da ke Novoaydar, anan ake kwantar da fararan-hula da sojoji domin basu kulawa, kuma harda jami'an lafiya cikin wadanda aka kashe. Sai dai gwamnan Yankin na cewa gwamman sojojin Rasha da aka kashe.

    Shugaba Zelensky ya ce makaman da Rasha ta harba ya fada kan ginin mutane a Kostyanty-nivka, da ke gabashin Bakhmut, wanda ya kashe mutum uku da jikkata 14.

    Ya kuma nemi taimakon kasasahen yamma na aike masa da naurorin kakabe ko tarwatsa rokokin da Rasha ke harba musu.

  19. Barka da hantsi

    Buhari Muhammad Fagge ke fatan an tashi lafiya.

    Ni ne zan kasance da ku a wannan yini da zan kawo muku labarai da rahotanni daga ko ina sassan duniya.

    Sai ku kasance da mu.