Ana ci gaba da bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya
Wannan shafi ne da ke kawo muku bayanai kan abubuwan da ke faruwa a faɗin Najeriya game da zaɓen 2023 da kuma wasu abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku bayanai kan abubuwan da ke faruwa a faɗin Najeriya game da zaɓen 2023 da kuma wasu abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Daga Ahmad Tijjani Bawage, Haruna Kakangi, Muhammad Annur Muhammad da Abdullahi Bello Diginza
time_stated_uk
Rufewa
Masu bibiyar mu a nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa musamman kan zaɓen Najeriya na 2023.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.
Amma ku ci gaba da kasancewa a shafinmu na BBC Hausa.com domin samun labarin sakamakon zaɓen da zarar an sanar da shi komai dare.
A madadin sauran abokan aiki Annur Muhammad tare da Abdullahi Bello Diginza ke cewa ku ci gaba da kasancewa da shafinmu
An tafi hutun minti 40
Bayan karɓar sakamako daga jihohi huɗu shugaban hukumar zaɓen Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu ya bayar da hutun minti 40 domin a dawo a ci gaba da karɓar sakamakon.
Peter Obi ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na Jihar Anambra
Yawan masu rijista 2, 656,437
Yawan waɗanda aka tantance 628, 590
Abin da manyan 'yan takara huɗu suka samu
APC - 5,111
LP - 584,621
NNPP - 1,967
PDP - 9, 036
Peter Obi ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na jihar Ebonyi
Yawan masu rijista 1,597,646
Yawan wadanda aka tantance 337,887
Abin da manyan jam'iyyu huɗu suka samu
APC - 42,402
LP - 259,738
NNPP - 1, 661
PDP - 13, 503
Peter Obi ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na Jihar Delta
Jumullar waɗanda aka yi wa rijista 3,221, 697
Yawan waɗanda aka tantance 667,149
Yawan abin da manyan jam'iyyu huɗu suka samu
APC - 90,183
LP - 341,866
NNPP - 3,122
PDP - 161,600
Peter Obi ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na Jihar Cross River
Jumullar masu rijista 1, 766,466
Yawan waɗanda aka tantance 44, 880
Yawan ƙuri'un da manyan jamiyyu huɗu suka samu:
LP - 179, 917
APC - 130,520
PDP - 95,425
NNPP - 1,644
An tafi hutun sa'o'i biyu
A halin yanzu dai Shugaban hukumar zaɓen Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar da tafiya hutun sa'a biyu daga karɓa da bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasar na jihohi a cibiyar.
Kawo yanzu dai saura jihohi takwas daga cikin jihohin ƙasar 36 da Abuja a kammala karɓa tare da bayyana sakamakon a cibiyar da ke Abuja.
Jihohin da suka rage su ne Borno da Taraba da Cross River da Rivers da Ebonyi da Imo da Anambra da kuma jihar Delta.
Ana sa ran za a koma karɓar sakamakon da misalin ƙarfe tara na daren yau.
Amma kafin lokacin za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran da suka shafi zaɓen da ma wasu abubuwa kamar yadda aka saba.
Atiku ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na jihar Sokoto
Babban jami'in tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar Sokoto ya gabatar da sakamakon zaɓen a zauren karɓa da bayyana sakamakon a Abuja
Ga yadda kowacce jam'iyya ta samu ƙuri'u a zaɓen kamar haka:
APC - 285,444
LP - 6,568
NNPP - 1,300
PDP - 288,679
Tinubu ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na jihar zamfara
Babban jami'in tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar Zamfara ya gabatar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar a zauren karɓa da tattara sakamakon shugaban ƙasa;
Ya karanto sakamakon da manyan jami'iyyun suka samu kamar haka:
PDP - 193,978
APC - 298,396
LP - 1,660
NNPP - 4,044
Atiku ya lashe za ben shugaban ƙasa na jihar Kebbi
Babban jami'in tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar Kebbi ya gabatar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar a zauren karɓa da tattara sakamakon shugaban ƙasa
Jumullar wadanda aka yi wa rijista 2,032,041
Yawan wadanda aka tantance 599,201
Abin da manyan 'yan takara suka samu
PDP - 285,175
APC - 248,088
LP - 10,682
NNPP - 5,038
lashe zaɓen shugaban ƙasa na jihar Cross River
Jumullar waɗanda aka yi wa rijista 1766466
Yawan waɗanda aka tantance 44880
Abin da manyan 'yan takara suka samu
PDP -
APC - 130,520
LP -
NNPP -
Yawan waɗanda ƙuri'un da aka kaɗa
Yawan ƙuri'u masu kyau
Waɗanda suka lalace
Atiku ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na jihar Jihar Bayelsa
Babbar jami'ar tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar Bayelsa ta gabatar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar a zauren karɓa da tattara sakamakon shugaban ƙasa
Jumullar waɗanda aka yi wa rijista 1,056,862
Yawan waɗanda aka tantance 177,368
Abin da manyan 'yan takara suka samu
PDP - 68,818
APC - 42,572
LP - 49, 975
NNPP - 540
Yawan wadanda aka kaɗa 173,111
Yawan ƙuri'u masu kyau 165,325
Waɗanda suka lalace 7,786
Peter Obi ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na Jihar Plateau
Babban jami'in tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar Plateau ya gabatar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar a zauren karɓa da tattara sakamakon shugaban ƙasa
Jumullar wadanda aka yi wa rijista 2789528
Yawan wadanda aka tantance 1139393
Abin da manyan 'yan takara suka samu
PDP - 243,808
APC - 307,195
LP - 466,272
NNPP - 8,869
Atiku ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na Jihar Bauchi
Babban jami'in tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar Bauchi ya gabatar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar a zauren karɓa da tattara sakamakon shugaban ƙasa
Jumullar waɗanda aka yi wa rijista 2749268
Yawan waɗanda aka tantance 899769
Abin da manyan 'yan takara suka samu
PDP - 426,607
APC - 316,694
LP - 27373
NNPP - 72,103
Tinubu ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na jihar Kogi
Babban jami'in tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar Kogi ya gabatar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar a zauren karɓa da tattara sakamakon shugaban ƙasa
Jumullar waɗanda aka yi wa rijista 1,932,654
Yawan waɗanda aka tantance 484,884
Abin da manyan 'yan takara suka samu
APC - 240, 751
PDP - 145,104
LP - 56,271
NNPP - 4,238
Peter Obi ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na jihar Abia
Babban jami'in tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar Abia ya gabatar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar a zauren karɓa da tattara sakamakon shugaban ƙasa
Yawan waɗanda aka yi wa rijista 2,120, 808
Yawan waɗanda aka tantance 384,468
Abin da 'yan takara suka samu
LP - 327,095
PDP - 22,676
APC - 8,914
NNPP - 1239
Peter Obi ya lashe zaben shugaban ƙasa na jihar Edo
Babban jami'in tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar Edo ya gabatar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar a zauren karɓa da tattara sakamakon shugaban ƙasa
Jumullar wadanda aka yi wa rijista 2,501,081
Wadanda aka tantance 603,894
Abin da manyan 'yan takara suka samu
LP 331,163
APC 144,471
PDP 89,585
NNPP 2,743
Atiku ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na jihar Akwa Ibom
Babban jami'in tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar Akwa Ibom ya gabatar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar a zauren karɓa da tattara sakamakon shugaban ƙasa.
Yawan masu rijista 2, 357,418
Wadanda aka tantance 594450
Abin da manyan 'yan takara suka samu
PDP - 214,012
APC - 160620
LP - 132,683
NNPP - 7,796
Yawan wadanda aka kada 587,417
Kuriu masu kyau 555,089
Wadanda suka lalace 32,328
Tinubu ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na jihar Benue
Babban jami'in tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar Benue ya gabatar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar a zauren karɓa da tattara sakamakon shugaban ƙasa.
Abin da kowane dan takara ya samu
APC - 310,468
PDP - 130,081
LP - 308, 372
NNPP -4,740
Tinubu ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na Jihar Neja
Babban jami'in tattara sakamako na jihar Naija ya gabatar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a jihar.
Ga yadda sakamakon ya kasance
Yawan wadanda aka yi wa rijista 2, 698 344
Wadanda aka tantance jumulla 827 416
Yawan wadanda aka kada 813, 355
Yawan kuri'u masu kyau 778,668
Yawan kuri'un da suka lalace 34,687
Abin da jamiyyu suka samu ;
APC - 375, 183
PDP - 284 898
NNPP - 21,836
LP - 80,452