Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail da Ahmad Tijjani Bawage

time_stated_uk

  1. Mu kwana lafiya

    A nan muka zo karshen rahotanni a wannan shafi na kai-tsaye da muka shafe tsawon yinin yau muna kawo muku.

    Sai kuma gobe Asabar idan Allah ya kaimu.

    A madadin sauran abokan aiki, Ahmad Tijjani Bawage ke cewa asuba ta gari.

  2. 'Yan sandan Kwara sun kama yaron da ya yi garkuwa da mahaifinsa

    Police

    Rundunar 'yan sandan jihar Kwara, ta kama wani yaro mai suna Issa Naigheti saboda zarginsa da yin garkuwa da mahaifinsa, inda ya karɓi naira miliyan 2.5 a matsayin kuɗin fansa.

    Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Ajayi Okasanmi ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai.

    Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ambato shi yana cewa rundunarsu ta musaman ce da ke ƴaki da masu garkuwa da mutane suka kama yaron da ake zargi a lokacin da suke neman wasu masu garkuwa da mutane na daban.

    Ya kara da cewa yaron ya amsa laifinsa, inda ya ce ya haɗa baki ne da wasu mutum biyu don garkuwa da mahaifin na sa mai suna Bature Naigboho da ke yankin Igboho/Ibeti na jihar Oyo inda ya karbi naira miliyan 2.5

    Kakakin 'yan sandan ya ce za a tura batun zuwa jihar Oyo saboda a can ne lamarin ya faru domin ci gaba da bincike.

  3. An gudanar da zanga-zanga a lardin Khyber Pakhtunkhwana Pakistan kan ƙaruwar rashin tsaro

    Dubban mutane sun gudanar da zanga-zanga a arewa maso gabashin gundumar Khyber Pakhtunkhwa, da ke Pakistan, domin nuna rashin jin dadi kan karuwar tashin hankali.

    Masu zanga-zangar dauke da tutar kasar a garin Wana a kudancin Waziristan sun yi ta rera waken goyon bayan zaman lafiya.

    Kungiyar Tehreek-i-Taliban ta Pakistan da ta rikide kungiyar Taliban, ta kai munanan hare-haren bama-bamai kan jami'an tsaro a 'yan watannin nan, musamman bayan kawo karshen yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta a watan Nuwamba.

    A jiya Alhamis, sojoji sun sanar da kashe masu kaifin kishin islama 11, a yankin Waziristan.

  4. Borno na da cikakkiyar tsaro da za a iya gudanar da zaɓe - Zulum

    Zulum

    Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce jihar Borno na da ingantaccen tsaro za a iya gudanar da zabukan 2023.

    Gwamnan ya bayyana hakan ne yau Juma'a yayin ziyara ga shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja.

    Ya tabbatar wa masu 'yan jihar cewa za a basu cikakkiyar tsaro kafin da lokaci da kuma bayan zaɓe.

    A baya-bayan nan ne ake nuna fargaba kan tsaro a jihar bayan da aka kai wa tawagar ƴakin neman zaɓen shugaban kasa na jam'iyyar PDP hari a Maiduguri a ranar 22 ga watan Nuwamba.

    ''Muna iyakar bakin kokarin mu a yanzu, muna shirye-shiryen sake mayar da mutane garuruwansu da kuma ganin yadda za mu sake gyara hanyar Maiduguri da Gamborun-Gala da kuma ta Maiduguri zuwa Banke da zimmar ganin mutane sun koma rayuwa kamar a baya,'' in ji Gwamnan.

  5. Jamus ta amince ta bai wa Ukraine makamai

    Germany

    Jamus ta ce za ta bai wa Ukraine tankokin ƴaki arba'in da motoci masu sulke wadanda za su iya harba manyan rokoki.

    Mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa daga karshe za su aike da daukacin rundunarsu da jiragen yaki domin su taimaka wajen dakile mamayar Rasha a Ukraine, amma suna fatan za a kai kashin farko kafin karshen watan Maris.

    Amurka da Faransa sun yi irin wannan alkawura a cikin kwanaki biyun da suka gabata, inda masu sharhi ke ganin hakan na iya kawo wani gagarumin sauyi ga karfin fada a ji da sojojin kasa ke da shi.

  6. An haramta zanga-zanga kan ɓatar kuɗin korona a Senegal

    Senegal

    Hukumomin Senegal sun haramta zanga-zangar da aka shirya gudanarwa yau Juma'a don yin watsi da binciken wani rahoto da aka yi kan yadda gwamnatin ƙasar ta kashe kuɗaɗen tallafi na cutar korona da ya kai dala biliyan 1.5.

    Rahoton wanda aka wallafa a shafin Court of Auditors makonni biyu da suka gabata, ya ce akwai kurakure kan yadda aka kashe kuɗin.

    Sai dai gwamnatin ƙasar ta mayar da martani da cewa an samu gazawa ce ta kashi 1 na kuɗaɗen, inda ta ce za ta yi amfani da shawarwarin rahoton wajen binciken jami'ai a ma'aikatunta.

  7. 'Yan sandan Bauchi sun ce sun kashe 'yan bindiga tare da kwato makamai

    Police

    Wata haɗakar jami'an tsaro karkashin jagorancin rundunar 'yan sandan jihar Bauchi, sun ce sun kashe 'yan bindiga da dama tare da kwato bindigar AK-47 guda biyu a Karamar Hukumar Alkaleri na jihar.

    A wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Ahmed Wakili ya fitar, ta ce sun samu nasarar kashe 'ya bindigar ne a lokacin bukukuwan karshen shekara a Dajin Madam da kuma Dajin Yankari.

    Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa yayin samamen, an samu nasarar kashe 'yan bindiga da dama da korar su zuwa cikin dazuka da kuma raunata sauransu.

    SP Ahmed Wakili ya ce sun kuma kama wasu mutane biyu da ake zargi da garkuwa da mutane.

  8. Kotu a Legas ta ɗaure wani matashi bisa zargin yin lalata da matar aure

    Kotu ta musamman mai shari’a kan laifuka na musamman da cin zarafin mata da yara ta garkame wani matashi a gidan gyara halinka, bisa zargin yin lalata da wata malaman jinya kuma matar aure.

    Shi dai wanda ake zargin ya kasance mai gadi a cibiyar jinya.

    Latsa hoton da ke kasa domin saurarin rahoton wakilinmu na Legas Umar Shehu Elleman.

    Video content

    Video caption: Kotu a Legas ta daure wani matashi bisa zargin yin lalata da matar aure
  9. Mutum 16 sun rasu a hatsarin bas a Uganda

    Uganda

    Mutum 16 sun rasu a Kampala bayan da motar bas da suke ciki ta afka wa wata babbar motar dakon kaya kusa da garin Gulu a safiyar yau Juma'a.

    'Yan sanda sun ce mutum 12 ne suka rasu nan take yayin da sauran hudun suka karasa a asibiti. Wasu fasinjoji da dama kuma sun samu raunuka.

    An bayyana cewa motar dakon kayan na tsaye ne ana loda mata kaya kusa da wani wurin bincike da ke arewacin ƙasar.

    A baya-bayan nan ana nuna damuwa kan lalacewar hanyoyi a ƙasar musamman ma lokutan bukukuwan karshen shekara, inda mutane kusan 35 suka mutu a wannan hanyar.

    A farkon makon nan ne, wani rahoton jami'an lura da hanya ya bayyana afkuwar haɗuran kan hanya 104 tsakanin 30 ga watan Disamba zuwa 1 ga Janairu.

  10. Iƙirarin Yarima Harry na kashe mayaƙanmu 25 laifukan yaƙi ne - Taliban

    Jami'in Taliban

    Kungiyar Taliban ta mayar da martani kan iƙirarin Yarima Harry na Masarautar Birtaniya cewa ya kashe mayaƙan Taliban 25 a lokacin da yake aiki a matsayin sojan sama a Afghanistan.

    Wani jami'in Taliban ya ce waɗannan kashe-kashen sun kai matakin laifukan yaƙi.

    Da yake ba da tarihin rayuwarsa cikin littafin da yake rubuwa, Yarima Harry ya yi bayanin abubuwan da suka faru da shi lokacin yana Afghanistan a matsayin matuƙin jirgin yaƙi na helkwafta a shekarun 2012 zuwa 2013.

    Hirar da aka yi da Yarima Harry ta taɓo batutuwa da dama da suka shafi Masarautar Birtaniya, batun da ya janyo ce-ce-ku-ce.

  11. Faɗa ya rincaɓe a Ukraine duk da sanarwar tsagaita wuta

    Ukraine

    Faɗa ya ƙara rincaɓewa a gabashin Ukraine duk da sanarwar tsagaita wutar da Shugaba Vladimir Putin ya bayar, wadda Ukraine ta yi watsi da ita.

    Rasha ta ce Ukraine ta ci gaba da ruwan makaman atilare a inda dakarunta suke, dole ta sanya ta mayar da martani.

    Wani ɗan jarida da ke aiki da kamfanin dillancin labarai na AFP a kusa da birnin Bakhmut ya ce sojojin kasashen biyu na mummunar musayar wuta.

    Wakilin BBC ya ce wannan ita ce tsagaita wuta da aka taba cimmawa tun bayan mamayar Rasha a Ukraine a watan Fabarairun bara.

    Amma Shugaba Zalensky ya ce Putin ya ɗauki matakin ne ganin "mummunar ɓarnar da sojin Ukraine suka yi musu a dan tsakanin".

  12. Kisan kai a birnin Landan ya ragu a 2022

    'Yan Sanan Birtaniya

    Adadin kisan kai da ake yi a birnin Landan ya ragu a 2022 yayin da kisan matasa ma ya ragu da rabin adadi, a cewar 'yan sandan Ingila.

    An samu kisan kai 109 a birnin cikin shekarar da ta gabata, abin da ke nufin raguwa daga 132 da aka samu a 2021 wanda kuma shi ne mafi ƙanƙantar adadi tun daga 214.

    Daga cikin waɗanda aka kashe, 14 'yan ƙasa da shekara 20 ne, maimakon 30 da aka kashe a bara.

    Babban Kwamashinan 'Yan Sanda Sir Mark Rowley ya ce "kisan ya yi yawa", yayin da rundunar ke ƙoƙarin daƙile kisan da ake yi wa matasan.

    Cikin kashe-kashen 109 a 2022, karo tara harbe-harbe ne, 69 kuma hari ne da wuƙa.

  13. Ukraine ta yi watsi da tsagaita wutar da Rasha ta ayyana

    Tankokin yaƙi

    Ukraine ta yi fatali da sanarwar da Shugaban Rasha Vladmir Putin ya bayar ta tsagaita wuta na tsawon sa'a 36 saboda zuwan bikin Kirsimeti na Cocin Orthodox a Rasha.

    Shugaba Zelensky ya ce matakin wani yunƙuri ne na dakile hanzarin sojojin Ukraine tare da bai wa sojojin Rasha dama ta ƙara nausawa garuruwan Ukraine.

    Matakin tsagaita wutar zai soma aiki ne a yau Juma'a.

    Shugaba Biden ya ce akwai lauje cikin naɗi a sanarwar ganin cewa shugaban na Rasha ya shirya kai hari kan asibitoci da wuraren rainon jarirai da majami'u ranar 25 ga watan Disamba da kuma ranar sabuwar shekara.

  14. 'Yan sandan Zamfara sun kashe 'ɗan fashin daji' tare da kama shida

    Makaman 'yan fashin daji

    Dakarun 'yan sandan Najeriya reshen Jihar Zamfara da ke arewacin ƙasar sun kashe ɗan fashin daji tare da kama wasu shida da ake zargi da fashin da kuma satar shanu, a cewarta.

    Da yake gabatar da waɗanda ake zargin a ranar Laraba, kakakin 'yan sanda SP Mohammed Shehu ya ce dakarun sun ƙwace bindiga ƙirar AK-47 biyu, da fakitin harsasai biyu, da tarin layu, da sauransu.

    A cewarsa: "A ranar 1 ga watan Janairun 2023, rundunar ta samu wani rahoton gaggawa kan 'yan fashin daji a yankin Gusau-Magami-Dansadau. 'Yan sanda sun isa wurin kuma suka far wa 'yan bindigar.

    "Cikin sa'a, an kashe ɗaya daga cikinsu kuma aka daƙile harinsu, suka gudu daji da raunukan bindiga."

    Haka nan, 'yan sandan sun yi nasarar kama wani da ke da alaƙa da jagoran 'yan fashi Halilu Kacalla mai suna Musbahu Aminu.

    SP Shehu ya ce matashin mai shekara 30 ya amsa laifin aikata fashi da makami da satar shanu masu yawa a yankin.

  15. Hatsarin mota ya kashe mutum 14 a Ivory Coast

    Hatsari

    Mutum aƙalla 14 suka mutu sakamakon hatsarin mota a birnin Yamoussoukro na Ivory Coast ranar Alhamis.

    Kazalika, wasu da yawa sun jikkata bayan motocin biyu sun yi karo da juna.

    Waɗanda suka rasu sun ƙunshi maza tara da mata biyar, yayin da aka kai fiye da 70 asibiti.

    Ɗaya daga cikin motocin na ɗauke da 'yan jana'iza, ciki har da 'yan ƙasar waje, da suka tafi jana'izar wata mace da ta rasu a Turai, a cewar rahoton kamfanin labarai na ƙasar.

    Ba a san takamaimaman dalilin da ya haddasa hatsarin ba.

  16. 'Yan sanda sun kama 'ƴan jagaliya' 61 a Kano

    'Yan daba a Kano

    Rundunar 'Yan Sandan Najeriya reshen Jihar Kano ta ce ta kama mutum 61 da take zargi da daba ko kuma jagaliyar siyasa yayin tarukan yaƙin neman zaɓe.

    Kwamashinan 'Yan Sanda Mamman Dauda ya bayyana haka cikin wata sanarwa da kakakinta a jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ranar Alhamis, yana mai cewa an kama su ne a ranar Laraba.

    An kama matasan ne a Filin Wasa na Sani Abacha yayin wani taron siyasa.

    Ya ƙara da cewa daga cikin kayayyakin da aka ƙwace daga hannunsu akwai wuƙa 33, da takobi takwas, da almakashi huɗu, da kuma ƙunshin tabar wiwi 117.

    "Shugabannin jam'iyyu da 'yan takara sun yi alƙawarin za su bai wa 'yan sanda haɗin kai da sauran jami'an tsaro don gudanar da zaɓuka cikin kwanciyar hankali," a cewar sanarwar.

    Makamai na 'yan daban Kano
  17. Ma'aikatar ilimi a Ghana ta umarci jami'o'i su ƙara kuɗin makaranta

    Ministan ilimi na Ghana ya umarci Jami'ar Ghana da sauran jami'o'i su fara aiki da ƙarin kashi 15 cikin 100 na kuɗin makaranta kamar yadda Majalisar Dokoki ta ayyana.

    Lamarin na zuwa ne bayan wasu ƙungiyoyin ɗalibai sun yi zanga-zangar nuna ɓacin rai game da ƙarin kuɗin da ya zarta kashi 30 cikin 100.

    Majalisar ta Ghana ta ƙara kashi 15 ɗin ne daga shekarar karatu da ta gabata, sai dai kuma wasu jami'o'in ciki har da Jami'ar Ghana sun ƙara kuɗin ba tare da amincewar Majalisar ba.

  18. Majalisar Amurka: Ina samun nasara a yaƙin neman zaɓe, in ji Kevin McCarthy

    Kevin McCarthy

    Ɗan majalisar wakilan Amurka na jam'iyyar Republican, Kevin McCarthy, ya dage cewa yana samun nasara a yaƙin da yake na zama sabon kakakin majalisar.

    Sai dai ya ƙi ayyana wa'adi inda a wannan makon kaɗai ya yi asarar ƙuri'a 11.

    Lokaci na ƙarshe da aka fuskanci irin wannan tsaikon wajen naɗa shugaban majalisa shi ne tun kafin yaƙin basasar Amurka.

    Mista McCarthy dai yana fuskantar ƙalubale daga wasu ƴan jam'iyyarsa masu ra'ayin riƙau da suka hana masa damar samun ɗarewa kan kujerar.

    Wakilin BBC ya ce majalisar ta ɗage zamanta zuwa 12 na ranar yau Juma'a (agogon ƙasar) kuma babu tantama za a ci gaba da kamfe a sirrance.

    Sai dai abu ne mai wuya a iya faɗa kai-tsaye abin da zai kawo ƙarshen taƙaddamar.

  19. An haramta wa gwamnatoci cire tsabar kuɗi daga asusu a Najeriya

    Naira

    Hukumar da ke yaƙi da laifukan da suka shafi hada-hadar kuɗi a Najeriya, NFIU, ta ce dokar hana cire tsabar kuɗi daga asussan gwamnati a kowane mataki za ta fara aiki daga ranar ɗaya ga watan Maris mai zuwa.

    A cewar hukumar Nigeria Financial Intelligence Unit (NFIU), duk wani jami`in gwamnati da ya taka dokar zai fuskanci ɗaurin shekara uku a gidan yari ko kuma tarar da za ta kai ninkin kuɗin da ya cira sau uku.

    Shugaban NFIU Malam Modibbo Hamman Tukur ya faɗa wa BBC Hausa cewa tun daga lokacin da gwamnatin Buhari ta fara mulki an cire jimillar garin kuɗi naira biliyan 225 daga asusun gwamnatin tarayya.

    "Gwamnatocin jiha ne suka fi cirar kuɗin, inda aka ɗauki garin kuɗi biliyan 700. Gwamnatocin ƙananan hukumomi kuma biliyan 156 kawai suka cira," in ji shi.

    Danna hoton ƙasa ku saurari cikakkiyar hirar da Ibrahim Isa ya yi da Malam Modibbo:

    Video content

    Video caption: Danna hoton sama ku saurari hirar:
  20. Chadi ta ce ta daƙile yunƙurin sojoji na tayar da fitina

    Mahamat Idriss Deby
    Image caption: Mahamat Idriss Deby ne ke shugabantar ƙasar tun bayan kashe mahaifinsa Idriss Deby a watan Afrilun 2022

    Gwamantin Chadi ta ce jami'an tsaronta sun daƙile yunkurin wani gungun sojoji na kawo tarnaƙi ga zaman lafiyar ƙasar.

    Wata sanarwa ta ce sojoji 11 ne ke da hannu a lamarin.

    Gwamnati ta ce jami'an tsaron farin kaya sun kama mutanen da ke da hannu a kitsa lamarin da aka yi tun 8 ga watan Disamba.

    Mahukuntan sun ce Baradine Berdei Targuio, Shugaban kungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Chadi, shi ne ya jagoranci yunƙurin.

    Chadi ta kasance cikin ruɗani tun Afrilun bara lokacin da daɗaɗɗen shugabanta Idris Derby ya mutu yayin da ya je filin daga domin yaƙar ƴan tawaye.

    Ɗansa Mahamat Idriss Derby ne ya ƙwace mulki tun daga lokacin.