Kotu ta samu Ekweremadu da laifin yunƙurin safarar sassan ɗan adam

Ike Ekweremadu

Asalin hoton, FACEBOOK/Ekweremadu

Bayanan hoto, Ike Ekweremadu da matarsa Beatrice

Wata kotu a Birtaniya ta samu ɗan majalisar dattijan Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa da laifin yunkurin safarar sassan ɗan adam.

Shari'ar ta shafi dauko wani dan Najeriya mai shekaru 21 zuwa Birtaniya domin a cire ƙodarsa a bai wa diyar Ekweremadun.

Kotun ta kuma sami wani likita mai shekaru 50, Dr Obinna Obeta da haɗa baki da dan siyasar wajen samo mutumin saboda a cire masa koda.

Masu shigar da kara sun ce za a cire kodar mutumin ne domin a saka wa Sonia, ɗiyar Ekweremadu mai shekaru 25.

Kotun ta wanke Sonia da hannu a tuhumar da ake yi mata.

Ƙarin labaran da za ku so ku karanta:

Matashin da aka so amfani da ƙodar tasa, wani mai ƙaramar sana’a ne a birnin Legas.

An kai shi Birtaniya ne a bara domin gudanar da aiki a asibitin Royal Free Hospital da ke biornin London.

Ya ce an yi alƙawarin samar masa aiki a Birtaniya saboda taimakon da zai yi, sai dai ya ce ya gane cewa ana masa shigo-shigo ba zurfi ne bayan tattaunawa da likitoci a ƙasar ta Birtaniya.

Duk da cewa ba laifi ba ne bayar da gudumawar ƙoda, to amma hakan kan zama laifi idan har za a biya wanda zai bayar da ƙodar.

A lokacin da aka gane cewar ba za a iya amfani da ƙodar mutumin ba, kotun ta gano cewa iyalan na Ekweremadu sun mayar da hakalinsu wurin samun wani mutumin na daban a ƙasar Turkiyya.

Sai iyalan na Ekweramadu waɗanda ke da gida a birnin London sun musanta tuhumar da aka yi masu.