Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Muhammad Annur Muhammad da Ahmad Tijjani Bawage

time_stated_uk

  1. Mu kwana lafiya

    Nan muka zo karshen rahotanni a wannan shafi na kai tsaye, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.

    Ahmad Tijjani Bawage ke cewa sai da safen ku.

  2. Birtaniya ta sanar da sabbin matakan haraji da za su janyo masu zuba jari

    EPA-EFE/REX/SHUTTERSTOCK

    Ministan kuɗin Birtaniya ya sanar da sabbin matakan haraji da za su karfafa gwiwar kamfanoni su zuba jari sannan mutane su koma aiki yayin da hasashen da aka yi ya nuna cewa ƙasar za ta kaucewa durkushewar tattalin arziki a shekarar da mu ke ciki.

    Wakilin BBC ya ce tattalin arzikin ƙasar zai cigaba da tafiyar hawainiya kuma gwamnati za ta ci gaba da tsuke bakin aljihu na tsawon shekaru biyar.

    Ministan ƙudin ƙasar Jeremy Hunt ya faɗawa yan majalisar dokoki cewa gwamnati ta ɗauki matakan rage matsin da mutane suke ciki sakamakon tsadar rayuwa.

    Dubban ma’aikata sun shiga yajin aiki a yau a sassan Birtaniya a kan karin albashi da kuma inganta musu yanayin aiki.

  3. Hannayen jari a kasuwannin Turai ya faɗi da fiye da kashi uku

    Credit Suisse

    Hannayen jarin kasuwannin Turai ya faɗi fiye da kashi uku cikin ɗari bayan fargabar da masu zuba jari suka nuna a kan fannin banki ta sake haɗuwa da wata matsala da ta shafi kaso mai tsoka na hannun jarin bankin bada lamuni na ƙasar Switzerland da aka sayar.

    Kasuwar hada- hadar kudi ta Dow Jones a Amurka ta fuskanci koma baya a cinikinta na yau.

    Hannun jarin bankin Swiz ya faɗi warwas bayan wanda ya fi zuba jari a cikin bankin ya ce ba zai sake ba shi tallafi ba.

    Wannan na zuwa ne bayan durkushewar bankin Silicon valley na Amurka a kwanakin baya.

  4. Ministan harkokin wajan Rasha ya caccaki Amurka kan arangama da jiragen ƙasashen suka yi

    Segei Lavrov

    Ministan harkokin wajan Rasha Segei Lavrov, ya caccaki Amurka, inda ya ce yankin da jirgin samanta mara matuki ya faɗa a tekun bahar Maliya a jiya Talata, ba wuri bane da ya kamata a ce jirginta ya je ba.

    Segei Lavrov ya ce Amurka ta san cewa Rasha ta hana zirga zirgar jiragen sama a tekun bahar Maliyar tun bayan mamayar da ta yi wa Ukraine.

    Tun farko, shugaban Majalisar koli kan tsaro na kasar ya ce sojojin kasar za su nemi takarcen jirgin da ya faɗo.

    Sai dai wakilin BBC ya ce kakakin fadar White House a kan tsaron kasa John Kirby ya ce jirgin ya faɗa ne a cikin ruwa mai zurfi sosai , a dan haka zai yi wuya a iya tsamo shi.

    Amurka ta ce Jiragen saman yakin Rasha ne suka kai wa jirgin hari abin da ya tilasta masa faɗawa cikin ruwa sai dai Rasha ta musanta zargin.

  5. An gano ƙarin gawarwaki a Gabon bayan kifewar kwale-kwale

    STEPHEN MSENGI

    Adadin waɗanda suka mutu sakamakon hatsarin jirgin ruwa da ya afku a ƙasar Gabon a makon da ya gabata ya ƙaru zuwa 21, kamar yadda jami'an yankin suka bayyana, bayan da masu bincike na cikin ruwa suka gano wasu gawarwaki.

    Jirgin mai suna Esther Miracle yana ɗauke da fasinjoji 161 da suka taso daga Libreville babban birnin ƙasar zuwa Port-Gentil lokacin da ya nutse a ranar Alhamis kusa da ƙauyen Nyonie dake gaɓar teku.

    "Dukkan fasinjojin suna sanye da rigar ceto," in ji mai shigar da kara na gwamnati André Patrick Roponat, wanda ya ba da tabbacin cewa har yanzu kungiyoyin ceto na ci gaba da binciken jirgin don ganin ko wasu gawarwakin na maƙale".

    View more on twitter

    A cewar jagoran binciken, ya ce an tura sojoji 350 da wasu kwale-kwale na sintiri da kuma robobi masu nutsewa domin aikin.

    Amma iyalan waɗanda abin ya rutsa da su, sun ce fatan da suke da shi na gano ‘yan uwansu a raye yana ƙara yi musu nisa.

    Wata uwa da BBC ta zanta da ita ta koka da cewa: "Ba a gano 'ya'yana huɗu ba... fatan da iyalai ke da shi na ƙara raguwa."

    Hukumomin ƙasar sun dakatar da ayyukan mai kwale-kwalen har sai an baba ta gani.

    Rahotanni sun ce jirgin wanda ya fara aiki a watan Nuwambar bara, ya yi lodi fiye da kima, kuma mai yiwuwa ma yana ɗauke da dabbobi.

  6. 'Mun shirya tsaf don gudanar da zaɓen gwamna a jihar Adamawa cikin kwanciyar hankali'

    Ƴan sanda

    Rundunar `yan sanda a jihar Adamawa ta ce ta ɗauki matakan da za su taimaka wajen gudanar da zaɓen gwamna da na `yan majalisun dokoki na jiha cikin kwanciyar hankali.

    Jihar Adamawa dai na cikin jihohin da ba su samu wata hatsaniya ba a zaɓen shugaban ƙasa da aka yi a karshen watan Febrairu.

    Ku danna kasa domin sauraron tattaunawar da Ibrahim Isa ya yi da kakakin 'yan sandan jihar SP Sulaiman Yahaya Nguroje.

    Video content

    Video caption: 'Mun shirya tsaf don gudanar da zaɓen gwamna a jihar Adamawa cikin kwanciyar hankali'
  7. Tsadar rayuwa ta ƙaru a Najeriya - NBS

    Yadda tsadar rayuwa ta ƙaru a Najeriya

    Hukumar Kididdiga ta Najeriya ta ce an samu ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki a watan Janairun 2023.

    Hukumar ta ce ta sanar a ranar Laraba cewa hauhawar farashin kayayyakin ya haura zuwa kashi 21.82 cikin ɗari idan aka kwatanta da kashi 21.34 cikin dari a watan Disamba.

    Rahoton ya yi nuni da cewa hauhawar farashin kaya a shekara ya kai kashi 6.22 bisa ɗari idan aka kwatanta da na watan Janairun 2022, wanda ya kai kashi 15.60.

    Rahoton ya ce kayayyakin da farashinsu ya tashi sun haɗa da burodi wanda ya kai kashi 21.67 da dankali da dawa, da doya da kuma na kayan lambu.

    Bugu da ƙari, rahoton ya bayyana cewa farashin kayayyakni a cikin Janairu 2023 yana kashi 1.87 a kowane wata.

    Haka na zuwa ne yayin da 'yan ƙasar ke ci gaba da fuskantar matsalar ƙarancin sabbin takardun kuɗi sakamakon sake fasalin kuɗi da gwamnati ta yi.

    Matsalar ta jefa ‘yan ƙasar da dama cikin wahalhalu, inda suke fuskantar kalubale wajen biyan bukatun yau da kullum.

    Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta yi gargaɗin cewa wannan manufar na iya jefa tattalin arzikin ƙasar cikin wani mawuyacin hali.

  8. Birtaniya na fuskantar yajin aiki mafi girma a ƙasar

    Birtaniya na fuskantar yajin aiki mafi girma tun bayan da aka fara jerin yajin aiki a bara sakamakon hauhawar farashin kayyayaki.

    Dubban malamai da malaman jami’o'i da ma’aikatan gwamnati da likitoci da kuma ma’aikatan sufuri ke yajin aiki akan karin albashi da kuma yanayin aiki.

    Wakilin BBC ya ce ma’aikatan na kuma son gwamnati ta inganta ilimin yara ,suna son sakataren kuɗi ya ba wa fanin ilimin yara kaso na musaman a kasafin kuɗi.

    A yau ne gwamnatin Birtaniya za ta sanar da sabon shirinta na haraji da kashe kudi a wani yunkurin na shawo kan matsalar hauhawar farashin kayayaki wadda ta sa kasar ta koma bayan takwarorinta na G 7 watau kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki a Duniya.

  9. Gwamnatin Najeriya ta ɗage ƙidayar jama'a

    KIDaya

    Gwamnatin Najeriya ta ɗage aikin ƙidayar jama'a da ta shirya fara gudanarwa ranar 29 ga watan Maris zuwa watan Mayu mai zuwa.

    Ministan yaɗa labaran ƙasar Lai Mohammed ne ya bayyana haka ga manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartarwar ƙasar da shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya jagronta a Abuja fadar gwamnatin ƙasar.

    Lai Mohammed ya ce matakin ɗage aikin ƙidayar ya zama wajibi ne bayan da hukumar zaɓen ƙasar ta ɗage zaɓukan gwamnoni zuwa ranar 18 ga watan Maris, a maimakon ranar 11 ga watan kamar yadda aka tsara gudanar da shi a baya.

  10. Ambaliya ta hallaka mutum sama da 200 a Malawi

    Malawi flood

    Hukumomi a Malawi sun ce mutum fiye da dari biyu da ashirin aka tabbatar da mutuwarsu a ambaliyar ruwa da zaftarewar laka da guguwar da ke dauke da ruwan sama da iska da aka yi wa lakabi da Freddy ta haddasa.

    Ana sa ran adadin zai karu ya yinda ma’aikatan ceto sun isa wuraren da guguwar ta yi kamari.

    Wakiliyar BBC ta ce a karon farko bayan kwanaki da aka shafe ana tafka ruwan sama an wayi gari babu alamun haɗari a Blantrye wadda ita ce cibiyar kasuwancin ƙasar.

    A yau ne ake sa ran shugaba Lazarus Chakwera zai zagaya wuraren da guguwar ta yi barna sosai.

    Guguwar ta Freddy ta sa an yi ruwan saman da aka saba yi a watani shidda a cikin kwanaki shida a Malawi da Mozambique

  11. PDP da Atiku sun janye ƙarar duba kayan zaɓe

    Hoton Atiku Abubakar

    Ɗan takarar shugaban ƙasa na babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP, wato Atiku Abubakar, shi da jam'iyyarsa sun janye sabuwar ƙarar da suka shigar ta neman tilasta wa hukumar zaɓe ba su damar duba kayan da aka yi amfani da su a zaɓen ranar 25 ga watan Fabarairu.

    Atikun da jam'iyyarsa da ke ƙalubalantar sakamakon zaɓen da aka ayyana Bola Ahmed Tinubu na jam'iyya mai mulki APC a matsayin wanda ya ci zaɓen, sun shaida wa kotun musamman da ke sauraren ƙararraki kan zaɓen shugaban ƙasar a Abuja cewa ba su da buƙatar ci gaba da ƙarar.

    Jagoran ayarin lauyoyin da ke wakiltar Atikun da PDP Mista Joe-Kyari Gadzama (SAN) shi ne ya shaida wa kotun haka lokacin da aka zauna fara sauraren ƙarar a yau Laraba.

    Jaridar Tribune ta ruwaito cewa wani daga cikin lauyoyin na Atiku da PDP, wanda bai yarda a ambaci sunansa ba, ya ce tun da farko sun shigar da ƙarar ne saboda matsaloli da ƙalubalen da suka gamu da su lokacin da wakilan jam'iyyar da Atiku suka je hukumar zaɓen domin a ba su kayan su duba, kamar yadda kotu ta bayar da umarni.

    Ya ce, to kasancewar kafin a zo sauraren wannan ƙara da suka shigar ta tilasta wa INEC barin wakilan su duba kayan zaɓen, INEC da kanta ta fito ta yi alƙawarin ba su damar su je su duba wasu daga cikin kayan musamman ma takardar da aka yi zaɓe, ya ce saboda haka ne suka janye wannan sabuwar ƙara.

    Atiku da jam'iyyar tasa da kuma ɗan takarar Labour shi ma da jam'iyyar tasa dukkaninsu suna ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasar na Najeriya, inda kowanne daga cikin ɓangaororin biyu ke iƙirarin shi ne ya yi nasara aka yi masa fashi, tare da lasar takobin ƙwato nasarar tasu a kotu.

  12. INEC ta bai wa Hanga shaidar cin zaɓen sanatan Kano ta tsakiya

    Hoton Rufa'i Sani Hanga da takardar shedar cin zaɓensa

    Sanata Rufa’i Sani Hanga ya tabbatar wa BBC cewar Hukumar zaɓen Najeriya (INEC) ta damƙa masa shaidar cin zaben sanatan mazaɓar Kano ta tsakiya.

    A jiya Talata ne INEC ta bai wa Rufa'i shaidar, bayan hukuncin Kotun Ƙolin Najeriya, da ta tabbatar da wanda kotun ɗaukaka ƙara ta yi inda ta umarci hukumar ta ba shi shaidar cin zaɓe duk da cewa babu sunansa a cikin jerin masu takarar sanata a mazaɓar ta Kano ta tsakiya, a zaben ranar 25 ga watan Fabarairun, 2023.

    Da fari, INEC din ta bayyana Mallam Ibrahim Shekarau ne a matsayin wanda ya yi nasara a zaben karkashin jam’iyyar NNPP, duk da cewar ya koma jam’iyyar PDP.

    Tun farko Mallam Ibrahim Shekarau ne ɗan takara, sai dai ya fice daga jam'iyyar ta NNPP daga baya tun kafin zaɓe, inda NNPP ta maye gurbinsa da Sanata Rufa'i Sani Hanga.

    Amma hukumar zaɓen ta ce lokaci ya ƙure na sauya sunan Ibrahim Shekarau da na Rufa'i Sani Hanga.

  13. Ƴan sanda sun ce sun dakatar da shirin kama tsohon firaministan Pakistan Imran Khan

    Hoton gidan Imran Khan an harba hayaƙi mai sa hawaye
    Image caption: Yadda jami'an tsaro suka riƙa harba hayaƙi mai sa hawaye a gidan Imran Khan na Lahore

    Wani babban jamiin Pakistan ya ce jami'an tsaro sun dakatar da yunƙurin da suke yi na kama jagoran ƴan hammaya, Imran Khan domin a samu damar gudanar da gasar kurket, ba tare da wata matsala ba a garin Lahore.

    Ministan lardin Punjab Amir Mirr ya shaida wa BBC cewa, fito na fito da ake yi tsakanin ɓangarorin biyu ya janyo cunkuson ababen hawa wanda wani abu ne da zai iya hana mutane zuwa filin wasan.

    Ya ce za a dakatar da aikin har sai bayan an kammala gasar a ranar 19 ga watan da ake ciki.

    Tun a jiya Talata ne Jami'an tsaro suka riƙa ƙoƙarin kama Imran Khan bayan umarnin kotu abin da ya kai ga yin artabu tsakaninsu da magoya bayan tsohon firaministan.

  14. Babbar mota ta kashe ɗalibai hudu da raunata 18 bayan ta faɗa ajinsu a Uganda

    Hoton mata na kuka

    Aƙalla ɗalibai hudu ne suka rasa ransu wasu 18 suka samu raunuka bayan da wata babbar mota da ta ƙwace ta yi karo ajin ɗaliban a tsakiyar ƙasar Uganda.

    Hukumomin ƴan sanda sun gaya wa manema labarai cewa motar ta ƙwace wa direbanta ne a wata muguwar kwana a lokacin ana ruwa kamar da bakin-ƙwarya, inda ta faɗa wa ajin da ɗaliban suke koyon kwamfyuta.

    Haɗarin ya faru ne a jiya Talata, kamar yadda mai magana da yawun 'yan sanda Faridah Nampiima ta ce inda ta ƙara bayani da cewa direban mai shekara 26 na hannu a yanzu.

    A wani lamarin kuma na daban, wasu ɗalibai uku sun rasu da yawa kuma suka samu raunuka bayan da bangon ajin da suke ciki ya faɗa musu.

    Mai magana da yawun ƴan sanda ya ce ɗalibi ɗaya ya mutu a take yayin da biyu suka cika a asibiti.

    Kakakin ya ce iska ce ta yaye rufin ajin a lokacin ana mamakon ruwan sama, amma ginin bai faɗi ba, lokacin da lamarin ya faru ranar Lahadi.

    To amma kuma bangon ya faɗa wa wasu daga cikinsu lokacin da malaminsu ya sa su ture bangon.

    Ƴan sanda sun kama shugaban makarantar suna tuhumarsa da mummunan sakaci da aiki.

  15. Yadda INEC ta fara raba kayan zaɓen gwamna da ƴan majalisa a jihohin Najeriya

    Kayan zaɓe
    Image caption: Yadda ake raba kayan aikin zaɓe a Naija

    Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta fara rarraba kayan zaɓen gwamnoni da ƴan majalisun dokoki jihohi da za a yi ranar Asabar mai zuwa 18 ga watan Maris.

    Kayan zaɓe
    Image caption: Yadda ake raba kayan aikin zaɓe a Naija

    Tun a ranar Lahadi hukumar ta bayar da tabbacin cewa zuwa jiya Talata, za ta kammala aikin saita na'urorin tantance masu zaɓe na BVAS, waɗanda aka yi amfani da su a zaɓen shugaban ƙasa da ƴan majalisun dokoki na tarayya ranar 25 ga watan Fabarairu.

    kayan zaɓe
    Image caption: Kayan zaɓe a Sokoto

    Na'urorin dai su ne za a yi amfani da su domin gudanar da zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisun dokokin jihohi da za a gudanar a ƙarshen mako.

    Kayan zaɓe
    Image caption: Kayan aikin zaɓe a Sokoto

    Rahotanni sun ce zuwa yanzu an fara rarraba kayan a jihohin Naija da Bauchi Sokoto da Kano da Lagos.

    Kayan
    Image caption: Kayan zaɓe a Sokoto

    Ana raba kayan ne bisa taimakon jami'an 'yan sanda.

    Kayan zaɓe
    Image caption: Kayan zaɓe a Sokoto
  16. Ministan Wajen Amurka, Anthony Blinken ya isa Ethiopia

    Anthony Blinken
    Image caption: Sakatren Harkokin Waje na Amurka Anthony Blinken

    Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya sauka a babban birnin Ethiopia, Addis Ababa a ziyarar ƙasashe biyu da zai yi a nahiyar Afirka.

    Ƙaramin ministan harkokin waje na ƙasar ta Habasha ne, Mesganu Agra, ya tarbe shi.

    Ana sa ran a yayin ziyarar a Addis, Mista Blinken zai gana da manyan jami'an gwamnatin ƙasar da kuma na ƙungiyar Tarayyar Afirka, AU.

    Babban abin da za a tattauna a ziyarar shi ne aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a watan Nuwamba na bara tsakanin gwamnatin Habasha da ƴan tawayen Tigray, yarjejeniyar da ta kawo ƙarshen mummunan yaƙin basas na shekara biyu.

    Ƙungiyoyin masu raji sun buƙaci Blinken ya sanya batun ƴancin dan'Adam da bincike da kuma laifukan yaƙi da aka aikata a lokacin rikicin.

    Bayan ya bar Habashar, sakataren wajen zai tafi Nijar inda zai tattauna batun ƙaruwar barazanar masu iƙirarin jihadi a faɗin yankin Sahel.