Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Haruna Kakangi

time_stated_uk

  1. Assalamu alaikum

    Masu bin mu

  2. Mu wayi gari lafiya!

    Masu bibiyar wannan shafi na kai tsaye, a nan za mu dakata sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu.

    Amadadin Abdullahi Bello Diginza da ku ka kasance tare da shi tun daga safiyar yau har zuwa lokacin da na ɗora daga inda ya tsaya, ni Nabeela Mukhtar Uba ke muku fatan alheri.

    Kuna iya sake duba labaran da muka wallafa muku daga Najeriya da sassa daban-daban na duniya.

    Ku huta lafiya. Da fatan kuma za ku tara da mu gobe, Talata idan mai duka ya kai mu.

  3. Ma'aikatan jinya ƴan Najeriya na fuskantar tuhuma a Amurka

    Tambarin Hukumar kula da aikin jinya ta Texas

    Hukumar kula da ayyukan ma'aikatan jinya ta Texas da ke Amurka ta fitar da jerin sunayen mutum 75 da ake gudanar da bincike a kan su saboda gabatar da shaidar karatu ta bogi - 43 daga cikinsu ƴan Najeriya ne.

    A cewar bayanin da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet kan binciken da ake gudanarwa, mutanen da suka samu shaidar kammala karatun na bogi sun yi amfani da shi wajen samun aikin jinya.

    Bayan kammala jarabawar, mutanen sun samu lasisin yin aikin jinya a jihohi da dama.

    Hukumar ta ce ta shigar da ƙara kan ma'aikatan jinyar saboda takardun bogin.

    Wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet ta bayyana cewa hukumar kula da lafiya ta Amurka da sauran hukumomin tabbatar da tsaro sun ɗauki matakin kama mutanen da suke sayar da shaidar digirin aikin jinya na bogi.

    Hukumar ta ce tana aiki tuƙuru da hukumomin da lamarin ya shafa domin gudanar da bincike tare da warware matsalar nan kusa har da neman a ƙwace lasisin da suka samu ta haramtacciyar hanya.

  4. Ban umarci CBN ya ƙi bin umarnin kotu kan takardun ƙudi ba – Buhari

    Buhari

    Fadar shugaban Najeriya ta ce Babban Bankin ƙasar ba shi da wani dalili na ƙin bin umarnin Kotun Ƙoli kan sabbin takardun kuɗi don fakewa da sunan jiran umarni daga Shugaba Muhammadu Buhari.

    Mai taimaka wa Shugaba Buhari kan kafafen yaɗa labarai, Garba Shehu ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa inda ya ce Shugaban ƙasar bai umarci atoni janar na ƙasa, Abubakar Malami da Gwamnan CBN, Godwin Emiefele su ƙi martaba umarnin kotu ba da ya shafi gwamnati da wasu ɓangarorin.

    A ranar 3 ga watan Maris ne Kotun ƙolin ta bayar da umarnin ci gaba da amfani da tsofaffin takardun ƙudi har zuwa 31 ga watan Disamban bana.

    Umarnin kuma ya zo ne bayan da gwamnonin jihohi 16 suka ƙalubalanci matakin sauya fasalin kuɗin.

    Jihohi 16 ƙarƙashin jagorancin Kaduna da Kogi da Zamfara sun buƙaci kotun ƙolin ta soke matakin gwamnatin bisa dalilan cewa hakan ya jefa ƴan Najeriya cikin ƙunci da wahala.

    Kotun ta ƙara da cewa rashin martaba umarnin kotun na ranar 8 ga watan Fabrairu, alama ce ta mulkin kama-karya inda ta bayyana cewa shugaban ya saɓa wa Kundin tsarin mulkin ƙasa a yadda ya bai wa CBN umarnin sake fasalta kuɗin ƙasar.

    Sanarwar dai ta ce Shugaban ƙasar babban mai mutunta dokoki ne kuma babu adalci a yadda ake yi sukar Shugaban da yi masa mummunan zato.

  5. NLC ta yi barazanar tsunduma yajin aiki saboda ƙarancin mai da takardun kuɗi

    NLC

    Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya ta bai wa gwamnatin ƙsar wa'adin mako ɗaya ta warware matsalar ƙarancin mai da takardun kuɗi da ake fama da su ko kuma ta tsunduma yajin aiki.

    Shugaban ƙungiyar ta ƙasa, Joe Ajaero ne ya bayyana haka yayin tattaunawa da manema labarai game da taron da kwamitin gudanarwar ƙungiyar ya gudanar.

    Ya ce ƙungiyar za ta shiga yajin aikin gama-gari idan aka gaza shawo kan matsalolin biyu cikin mako ɗaya.

    Ajaero ya kuma yi tur da ƙarancin man fetur a ƙsar inda ya koka cewa matsalar ta kai ma'aikata da ƴan Najeriya bango.

    A baya-bayan nan ne Kotun ƙolin ƙasar ta yi umarnin ci gaba da amfani da tsaffin takardun kudi na Naira 200 da 500 da 1,000 har zuwa ranar 31 ga watan Disamban shekarar da muke ciki ta 2023.

    Sai dai har yanzu mutane na fuskantar ƙalubale wajen samun takardun kuɗi a hannunsu.

  6. Mataimakiyar Shugabar Amurka za ta ziyarci ƙasashen Afirka uku

    Hoton Kamala Harris

    Mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala Harris na shirin kai ziyara wasu ƙasashen Afirka uku.

    Wannan ne karon farko da za ta kai ziyara zuwa nahiyar tun bayan da ta hau kan mulki sama da shekara biyu da suka gabata.

    Ziyarar Ms Harris zuwa Ghana da Tanzania da Zambia daga 25 ga watan Maris zuwa 2 ga watan Aprilu za ta mayar da hankali kan faɗaɗa tattalin arziki ta ɓangaren kimiyya da ƙafafa harkokin kasuwanci da zuba jari," kamar yadda wata sanarwa da ofishinta ya wallafa.

  7. Masu yawon buɗe ido biyu sun mutu a hatsarin mota a Kenya

    Yawon buɗe ido

    Wani ɗan ƙasar Jamus da ɗan ƙasar Swistzerland da ke ziyarar yawon shaƙatawa a Kenya sun mutu sakamakon wani hatsarin mota da ya auku a gidan adana namun daji na Maasai.

    'Yan sanda sun ce lamarin ya faru ne bayan da motar da mutane biyu ke ciki ta yi hatsari bayan da ta kauce hanya.

    Mota na ɗauke da Jamusawa uku da 'yan Swistzerland biyu, a lokacin da hatsarin ya auku a kan hanyarsu ta zuwa gandun dabbobin.

    Tuni aka kai sauran masu yawon buɗe idanun asibitin birnin Nairobi domin yi musu magani.

    'Yan sandan ƙasar sun ce suna gudanar da bincike domin gano musabbin hatsarin.

    Gandun dajin Maasai fitaccen wuri ne ga masu yawon buɗe idanu a Kenya.

  8. Guguwa mai ƙarfi haɗe da ruwan sama sun kashe mutum 40 a Malawi

    ...

    Wani jami'a a Malawi ya ce aƙalla mutum 40 ne suka mutu sakamakon mummunar ɓarnar da wata guguwa mai ƙarfi haɗe da ruwa da ake yi wa laƙabi da 'Freddy'.

    Bidiyoyin da aka ɗauka sun nuna yadda rufin gidaje da dama suka ɗaye a wani mummunan ɓarna da ruwan saman yataɓa yi a biranen ƙasar.

    Kawo yanzu ba a kai ga tantance yawan ɓarnan da guguwar haɗe da ruwa mai ƙarfi suka yi a sassan yankunan ƙasar ba.

    Ko a ranar Lahadi ma wata guguwar mai ƙarfi haɗe da ruwan sama ta shafi wasu yankunan ƙasar Mozambique, karo na biyu a cikin ƙasa da wata guda.

    Hukumomin ƙasar sun ce aƙalla mutum shida ne suka mutu a birnin Quelimane.

    Binciken farko da aka gudanar kan ɓarnar da guguwar ta yi, ya nuna cewa gidaje da dama sun rushe a fiye da rabin lardunan ƙasar.

  9. Kotun ƙwadogon Afirka ta Kudu ta hana ma'aikatan jinya shiga yajin-aiki

    Kotun ƙwadogo a Afirka ta Kudu ya bayar da umarnin dakatar da yajin-aikin da ma'aikatan jinya da malaman makaranta ke gudanarwa a ƙasar kan neman ƙarin albashi.

    Hukumomin lafiyar ƙasar sun yi maraba da hukuncin, suna masu cewa hakan zai taimaka musu wajen aiwatar da tsarin hana albashi ga duk ma'aikacin da bai je wajen aikinsa ba, matuƙar yajin-aikin ya ci gaba.

    Ana kallon ma'aikatan lafiya a ƙasar a matsayin masu aiki na musamman inda aka haramta musu shiga yajin aiki.

    Dubban ma'aikatan ƙwadogon ƙasar na cikin yajin-aiki tun cikin makon da ya gabata kan rigimar ƙarin albashi.

    An girke dakarun soji zuwa wasu asibitocin ƙasar bayan da aka samu rahotonnin da ke cewa ma'aikatan jinyar waɗanda ba su shiga yajin-aikin ba, na fuskantar tsangwama.

    Ministan lafiyar ƙasar ya alaƙanta mutuwar majinyata huɗu da yajin-aikin, to sai ƙuniyar ma'aikatan ta ce mutuwar majinyatan ba ta da alaƙa da yajin-aikin nasu.

  10. Buhari ya koma Abuja daga Daura

    Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma fadar gwamnatinsa da ke Abuja, bayan shafe kwanaki a mahaifarsa Daura ta jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya.

    A wani saƙo da mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa ta Twitter, ya ce shugaban ya koma Abuja ne bayan kwanaki 18.

    Saƙon ya ƙara da cewa shugaban ya yi amfani da lokacin wajen gudanar da zaɓen shugaban ƙasa tare da ziyara da ya kai Maiduguri da taron Majalisar Dinkin Duniya da ya halarta a birnin Doha na ƙasar Qatar.

    View more on twitter

    Malam Garba Shehu ya ƙara da cewa nan gaba kaɗan ne cikin wannan makon shugaban tare da sauran ma'aikatan fadarsa da suka yi rajistar zaɓe a Daura za su sake komawa domin halartar zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisun dokokin jihohi.

  11. Tawagar lauyoyin Jam'iyyar LP na ganawa da hukumar INEC don duba kayan zaɓe

    Peter

    Tawagar lauyoyin jam'iyyar LP na ganawa da jami'an hukumar zaɓen Najeriya a Abuja babban birnin ƙasar.

    An ganawar ne a shalkwatar hukumar zaben ƙasar domin fara duba kayyakin da aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasar ranar 25 ga watan Fabrairu.

    Ana sa ranar tawagar lauyoyin 60 ƙarƙashin jagorancin Dakta Livy Uzoukwu, za su yi manema labarai bayanai bayan ganawar.

    Jam'iyyar ta LP dai ta shigar da ƙara gaban kotu, inda ta nemi kotun ta ba ta damar duba kayayyakin da aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasar da su, bayan da jam'iyyar ta yi zargin tafka maguɗi a zaɓen.

  12. Yaƙin Ukraine: An bayar da rahoton asarar rayuka a Bakhmut

    Yaƙi

    Ukraine da Rasha sun bayar da rahotonnin asarar rayuka yayin da faɗa a yankin Bakhmut ke ƙara munana.

    Rasha ta kwashe watanni tana ƙokarin karɓe iko da birnin da ke gabashin Ukraine.

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce an kashe dakarun Rasha fiye da 1,000 yayin da wasu da dama suka jikkata a 'yan kwanakin nan.

    Rasha ta ce ta kashe sojojin Ukraine fiye da 221 a cikin kwana guda.

    To sai dai BBC ba ta tabbatar da sahihancin rahotonnin da duka ɓangarorin biyu suka bayar ba.

    Masharhanta na cewa birnin Bakhmut na da matuƙar muhimmanci ga dakarun Rasha waɗanda ke ƙoƙorin ƙwace iko da birnin.

    Kame birnin zai bai wa Rasha damar mallakar kusan ilahirin yankin Donetsk, ɗaya daga cikin yankuna huɗu a gabashi da kudancin ƙasar da a baya ke hannun dakarun Rasha.

  13. Tsohon Kocin Super Falcons Ismaila Mabo ya rasu

    NFF

    Tsohon kocin tawagar ƙwallon ƙafar mata ta Najeriya 'Super Falcons' Ismaila Mabo ya rasu yana da shekara 79 a duniya.

    Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ruwaito cewa tsohon kocin ya rasu ne bayan wata jinya mai tsanani a gidansa da ke birnin Jos da ke jihar Plateau ta tsakiyar ƙasar.

    Marigayin ya jagoranci tawagar Super Falcons zuwa gasar Kofin Duniya ta mata a shekarar 1999 da gasar wasannin Olympics a shekarar 2000 da 2004.

    A shekarar 1999 ya jagoranci tawagar wajen samun nasarar da ba ta taɓa samu ba a tarihin wasan Kofin Duniya inda ta kai wasan zagayen kusa da ƙarshe.

    A shekarar 1998 ya taimaka wa tawagar matan lashe kofin ƙasashen Afirka ta mata 'AWCON', bayan da suka zura ƙwallaye 28 a gasar.

    Haka kuma a shekarar 2000 ya jagoranci tawagar wajen kare kofin ƙasashen Afirka 'AWCON' da aka yi a Afirka Kudu.

  14. Fiye da 'yan ci-rani 20 ne suka mutu bayan da kwale-kwalensu ya kife a Madagascar

    Madagaska

    Aƙalla 'yan ci-rani 22 ne suka mutu lokacin da wani kwale-kwale ɗauke da mutum 47 ya nutse a kogin madagascar alokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa tsibirin Mayotte na Faransa.

    Hukumar kula da jiragen ruwa ta Madagascar ta ce an kuɓutar da mutum 23 yayin da ake ci gaba da neman wasu mutum biyu da ba a gani ba kawo yanzu.

    Hukumar ta ce 'yan ci-ranin na kan hanyarsu ta zuwa tsibirin Moyotte, lokacin da hatsarin ya auku a ranar Asaabar.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito rundunar 'yan sanda na cewa mafiya yawan waɗanda aka kuɓutar sun tsere don gudun kada a kama su.

  15. Zan rufe duk bankin da ya ƙi karɓar tsofaffin takardun kuɗi - Soludo

    Soludo

    Gwamnan jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya Charles Soludo ya umarci mazauna jihar da su ci gaba da amfani da tsofaffin takardun naira 200 da 500 da 1,000 tare da sababbin takardun kuɗin a ko'ina cikin jihar.

    Cikin wata sanarwa ta musamman da Charles Soludo - wanda tsohon gwamnan babban bankin Najeriya ne - ya fitar, ya ce babban bankin ƙasar ya umarci bankunan kasuwanci a ƙasar da su ci gaba da biyan masu ajiyar kuɗi a bankunan da tsofaffin takardun kuɗi.

    Sannan kuma su ci gaba da karɓar tsofaffin takardun kuɗin a duk lokacin da aka gabatar da su.

    Gwamnan jihar ta Anambra ya ce ya tabbatar da sahihancin umarnin yayin wata hira da yayi da gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ta wayar tarho a ranar lahadi da daddare.

    Soludo ya ce gwamnan CBN ya bayar da wannan umarnin ne yayin wani taro da babban bankin ya yi da bankunan ƙasar da aka yi a ranar Lahadi 12 ga watan Maris.

    Gwamnan na Anambra ya kuma buƙaci al'ummar jihar da su kai ƙarar dukkan bankin da ya ƙi bin umarnin babban bankin na biya da karɓar tsofaffin takardun kuɗin.

    Yana gargaɗin cewa gwamnatinsa za ta rufe duk bankin da ya bijire wa wannan umarnin.

    A ranar 3 ga watan Maris ne kotun ƙolin Najeriya ya yanke hukuncin ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin ƙasar har zuwa 31 ga watan Disamban 2023.

    Wasu jihohin kasar ne dai suka shigar da ƙara a gaban kotun, suna neman a ɗage wa'adin da CBN ya sanya na daina amfani tsofaffin kuɗin.