Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Ahmad Tijjani Bawage, Buhari Muhammad Fagge da Mukhtari Adamu Bawa

time_stated_uk

  1. Bankwana

    Sai da safenmu daga nan BBC.

  2. Ƙasa ta rufata kan masu haƙar ma'adanai a Sudan

    Aƙalla masu haƙar ma'adanai 10 ne suka mutu a wani hatsari da ya rutsa da su a arewacin Sudan, wasu mutum 20 na daban suka jikkata.

    Kafaffen yaɗa labarai na cikin gida sun ɗora alhakin faruwar hakan kan ruftawar ƙasa wajen yaƙar da ake yi da manyan injina.

    Irin waɗannan lamura ba baƙi ba ne a harkokin ma'adanai a Sudan.

    Wata shida da suka gabata, mutum 11 sun mutu a irin wannan lamari kuma yankin arewacin Sudan din, yayin da ake samun rahotanni marasa dadi irin waɗannan a yammacin Darfur da kudancin Kordofan.

    An yi amannar cewa mutum miliyan biyu ne ke aiki a yankin da ake haƙar ma'adanai a Sudan.

  3. 'Yan Habasha 11 sun mutu a hatsarin mota a Somalia

    Said Fadhaye/IOM

    Mata shi da maza biyar 'yan asalin Habasha sun mutu a wani hatsarin mota da ya ritsa da su a Somalia, In ji hukumar kula da 'yan cirani ta duniya.

    Rahotanni sun ce masu safarar mutane ne suka shirya shigar da su Yemen ta tashar ruwan Bosasom in ji IOM.

    Amma motar da ke ɗauke da su ta faɗi ne a ranar Talata, lokacin da ta kusa kaiwa ga tashar ta Bosaso. kamar yadda IOM ta bayyana.

    Ana ci gaba da bincike kan yadda lamarin ya faru, sai dai wasu na cewa wataƙila motar tasu ce ke da matsala, saboda ba a ga wani abun hawa da suka yi hadarin ba tare.

    An tabbatar da an binne gawa 11. akwai kuma aƙalla mutum 20 da suka jikkata a motar.

  4. Italiy ta haramta amfani da manhajar GPT

    BBC

    An haramta amfani da ƙirƙirarriyar basira da ke kwaikwayon halayyar ɗan adam ta ChatGPT.

    HHukumar da ke lura da lamuran bayanai na intanet ta ce manhajar na da barazana.

    Masu ƙirƙira na Amurka ne suka samar da ita a matsayin mafari kuma tuni Microsoft suka zuba hannun jari ciki.

    Hukumomin sun ce sun dakatar da amfani da manhajar ne ba tare da bata wani lokaci ba, kuma za ta yi bincike a kai cikin gaggawa.

    Manahajar tana amsa tambayoyin da ɗan adam ke da su a ransa, kuma tana kwaikwayon yadda mutum yake rubutu da wasu abubuwan na daban.

    Microsoft ya kashe bilioyin dala kan wannan manhaja da ya ce ta bincike ce kawai da aka fara aiki da ita a watan jiya.

  5. Dakata! Har yanzu ni ne gwamna - Ganduje ya faɗa wa Abba Gida-Gida

    Ganduje

    Gwamnatin Kano ta yi kira ga zaɓaɓɓen gwamnan jihar Engr Abba Kabir Yusuf ya yi haƙuri, ya daina fitar da sanarwar hukuma da sunan shawara ga jama'a.

    A cewarta, irin wannan shawara za ta iya haddasa ruɗani na babu gaira babu dalili a cikin jihar.

    Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Muhammad Garba ya fitar don maida martani ga ofishin zaɓaɓɓen gwamnan a kan su guji janye daga filayen gwamnati.

    Gwamnatin Kano ta ce abin da zaɓaɓɓen gwamnan ya yi na bayar da umarni a kan wani batu da ya shafi manufar gwamnati, daidai lokaicn da gwamna mai c har yanzu yake kan muli, tamkar riga mallam masallaci ne.

    Ta ƙara da cewa kamar yadda yake ƙunshe a cikin tsarin mulkin Najeriya, Dr. Abdullahi Umar Ganduje zai ci gaba dazama gwamna mai cikakken iko har zuwa ranar 29 ga watan Mayu, kuma yana da damar gudanar da ayyukansa hatta a ranar jajiberen saukarsa daga mulki.

    A jiya ne, gwamnan mai jiran gado, Abba Kabir Yusuf ya fitar da wata sanarwa wadda ya bayyana a matsayin shawara, yana kira ga masu gine-gine a filaye da wuraren gwamnati, ciki har da masallatai da maƙabartu da makarantu da sauransu, su dakata.

    Lamarin da ya janyo zazzafar muhawara da ka-ce-na-ce musamman a shafukan sada zumunta.

  6. Ba za a sa wa Trump ankwa ba idan ya je kotu in ji lauya

    a

    Lauyan tsohon shugaban Amurka ya ce ba za a sanya wa Donald Trump ankwa ba, idan ya halarci zaman kotu a New York a makon gobe.

    An tambaye shi ne a gidan talbijin na ABC News ko yaya yake zaton tsarin gurfanar da Trump gaban kotu zai kasance, Joe Tacopina ya ce ya "tabbata [masu shigar da ƙara] za su yi ƙoƙarin samun duk wani ɗigo na jan hankalin jama'a da za su iya, a kan wannan abu.

    Amma ya ƙara cewa ba za a sa wa shugaban ankwa ba".

    Tun farko rahotanni sun tabbatar da Za a iya kama Donald Trump nan da ƴan kwanaki. Lauyan Trump ya ce: "Na fahimci cewa za su rufe hanyoyin zuwa yankin da ke zagaye da kotun, idan an zo gurfanar da shi, kuma su rufe ginin kotun.

    "Za mu je can… kuma mu ce ba a aikata laifi ba, za a fara magana ne game da hanyar shigar ƙararrakin, abin da za mu yi kenan nan take kuma ba tare da ƙaƙƙautawa ba, dangane da dacewar wannan ƙara ta fuskar shari'a."

    Kotu a birnin New York ce ta tuhumi tsohon shugaban ƙasar Donald Trump da hannu kan zargin biyan kuɗi domin ɓoye alaƙar da ke tsakaninsa da wata mai fina-finan batsa.

    Ana zargin Trump ne da biyan kuɗi ga matar mai suna Stormy Daniels gabanin zaɓen 2016 domin ta rufe baki kan alaƙar da ta wanzu tsakaninsu.

  7. Wasu batutuwa kan wasannin mako na 27 a La Liga

    Wasannin La Liga

    Za a ci gaba da wasannin La Liga karawar mako na 27, inda za a fara wasa tun daga ranar Juma'a.

    Real Mallorca ce za ta karbi bakuncin Osasuna - Osasuna tana ta taran teburi mai maki 34, ita kuwa Mallorca maki 32 ne da ita ta 11 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

    Ranar Lahadi Real Betis za ta ziyarci Atletico Madrid, kungiyoyin da ke fatan zama cikin 'yan hudun farko, suna son tsawaita wasa ba tare da an doke su ba a lik.

    Bayan fara kakar bana da cin karo da kalubale, Diego Simone ya doke Valencia 3-0 kafin ayi hutu, kenan Atletico ta yi karawa 10 a jere ba tare da rashin nasara ba.

    Kwallo hudu ne ya shiga ragar Atletico a cikin karawar 10, Antoine Griezmann ne ya kaita wannan matakin, bayan da ya koma kan ganiya.

    Mai shekara 32 shine ya lashe kyautar gwarzon dan wasan La Liga a watan Maris, wanda ya ci kwallo biyu ya bayar da daya aka zura a raga a wasa uku baya.

    Ku danna kasa don karanta cikakken labarin

  8. Ba zan yi shiru ba kan mulkin Kano - Kwankwaso

    Video content

    Video caption: Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

    Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi bayani kan yadda yake son a tafiyar da mulkin jihar Kano bayan samun nasarar jam'iyyar NNPP.

  9. An gurfanar da jami'in gidan yari kan zargin sayar da aiki

    Kotu

    Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta gurfanar da wani jami'in tsaron gida yari mai suna mista Eyimoga Moses a gaban Babbar Kotun Tarayya a Makurdi, babban birnin jihar Benue, inda take zarginsa da sayar da aiki.

    ICPC ta ce tana zargin Moses wanda ke aiki a gidan yari da ke jihar Nasarawa da laifin karɓar 800,000 daga hannun wasu ma'aurata da karyar cewa zai sama musu aiki a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Lafia.

    Sai dai Moses ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa da shi, inda aka bayar da belinsa yayin da ake ci gaba da tsare shi a gidan gyaran hali a Makurdi har sai ya cika sharuɗan belinsa da aka bayar.

    An ɗage zaman kotun har sai 20 ga watan Yunin 2023 domin ci gaba da sauraron shari'ar.

  10. Ƴan sanda a Kano sun kama mutum 14 da zargin aikata fashi da dabanci

    Ƴan sanda

    Rundunar ƴan sanda a jihar Kano ta sanar da kama mutum 14 waɗanda take zargi da aikata fashi da makami da tu'ammali da ƙwayoyi da kuma aikata dabanci a makon farko na watan azumin Ramadan.

    Rundunar ta ce an samu nasarar kama mutanen ne a wani samamen da rundunarta ta dawo da zaman lafiya ta kaddamar.

    Ta ce ta kuma ƙwato muggan maƙamai da haramtattun ƙwayoyi da kuma kayayyaki da aka sata.

    A wata sanarwa da kakakin runduar ƴan sanda jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce kwamishinan ƴan sandan jihar, Mamman Dauda ya ayyana yaki kan duk wani nau'i na aikin dabanci a faɗin jihar.

    Ƴan sandan sun ce suna iyaƙar kokarinsu wajen dakile dukkan ayyukan ɓata-gari a jihar.

    CP Mamman Dauda ya gargaɗi duk masu aikata laifi da su guji yin hakan saboda za su iya fuskantar hukunci mai tsanani idan aka kama su.

    Ya kuma bukaci al'umma da su kai rahoton duk wani abu da ba su yadda da shi ba, su kuma guji ɗaukar doka a hannunsu.

  11. Ƴan sanda sun kama ƴan Shi'a 19 kan zanga-zanga a Abuja

    Yan sanda

    Rundunar ƴan sanda a babban birnin tarayya Abuja sun tabbatar da kama mambobin kungiyar ƴan shi'a 19 kan gudanar da zanga-zanga ba tare da izini ba.

    A cikin wata sanarwa da ta samu a hannun mai magana da yawun ƴan sandan, SP Josephine Adeh, ta ce mambobin kungiyar sama da 400 sun fito zanga-zanga daga Babbar Kotun Tarayya zuwa dandalin Eagle Square.

    Sanarwar ta ce bayan fitowarsu sun kuma toshe hanyoyi bayan hukuncin da kotu ta yanke na yin watsi da bukatar bai wa jagoran kugiyar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky fasfo din sa.

    El-Zakzaky ne ya shigar da ƙarar Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS, inda ya bukaci ta sake masa fasfo ɗin sa da na matarsa da ta ƙwace.

    Sai dai da yake yanke hukunci, mai shari'a Obiora Egwuatu, ya ce El-zakzaky ya kasa gabatar da hujjoji da suka nuna cewa DSS ɗin ta karɓe masa fasfo bayan dawowarsa daga Indiya.

    Josephine ta ce mmbobin kungiyar sun yi ta jifar duwatsu da wasu abubuwa masu haɗari kan ƴan sanda, amma daga bisani aka samu damar tarwasa su tare da kama 19 daga ciki waɗanda ta ce za a kai su kotu.

  12. Ƴan fashin teku sun yi garkuwa da ma'aikatan jirgi 16

    Fashin teku

    Mamallakan jirgin ruwan ƙasar Denmark da masu fashi a teku suka ƙwace a mashigar Guinea a makon da ya gabata sun ce ƴan fashin sun tsere sun bar jirgin, inda suka tafi da ma'aikatansa guda 16.

    Sai dai an samu nasarar kuɓutar da wasu da ke cikin jirgin mai suna Monjasa Reformer.

    Waɗanda suka mallaki kwale-walen sun bayyana a ranar Talata cewa wasu ma'aikatan jirgin biyar sun samu mafaka a cikin wani ɗaki jirgin lokacin da ƴan fashin suka afka cikinsa.

    Ƴan fashin sun ƙwace ikon jirgin ne a ɓangaren yammacin birnin Pointe-Noire da ke Jamhuriyar Kongo.

  13. Kashim Shettima ya kai wa tsofaffin shugabannin Najeriya ziyara

    Shettima

    Sabon zaɓaɓɓen mataimakin shugaban ƙasar Najeriya Sanata Kashim Shettima ya kai wa tsofaffin shugabannin Najeriya Ibrahim Badamasi Babangida da kuma Abdulsalami Abubakar ziyara a Minna, babban birnin jihar Neja.

    Shettima ya kwatanta tsoffin shugabannin a matsayin mutanen dattaku da kuma ubannin ƙasa, inda ya ce gwamnati mai zuwa za ta yi aiki da su domin ciyar da ƙasar gaba.

    Kashim Shettima
    View more on twitter

    "Za mu ci gaba da tuntuɓarsu a kowane lokaci domin samun shawarwari kan hanyoyin da za a bi wajen magance matsaloli da ƙasa ke fuskanta," in ji Shettima.

    Daga bisani kuma ya jagoranci tawagarsa wajen kai gaisuwa ga Sarkin Minna Dakta Umar Farouq Bahago, inda aka yi addu'o'i don samun zaman lafiyar ƙasa.

    Kashim Shettima
  14. Jagoran ƴan adawar Kenya ya ce ana barazana ga rayuwarsa

    Kenya

    Tsohon Firaministan Kenya Raila Odinga ya y iƙirarin cewa an harbe motarsa har sau bakwai a zanga-zangar adawa da gwamnati da ya jagoranta a jiya Alhamis.

    Odinga ya ce hakan barazana ce ga rayuwarsa.

    A wani taron manema labarai, mista Odinga ya ce ƴan sanda sun cammaci motarsa da kuma na sauran jagororin ƴan adawa lokacin zanga-zangar da aka yi a Nairobi, babban birnin ƙasar.

    Ya kuma zargi ƴan sanda da tasamma ƴan jarida yayin zanga-zangar, inda ya yi iƙirarin cewa akwai shirin far wa ofisoshin kafar yaɗa labarai da ke sahun gaba a Nairobi.

    Mista Odinga ya soki al'ummomin ƙasashen waje saboda nuna halin ko-in-kula kan cin zarafin bil'adama da hukumomi suka yi yayin zanga-zangar.

    Ya ce ƴan adawa za su gudanar da babbar zanga-zanga a ranar Litinin domin matsa wa gwamnati da ta shawo kan tsadar rayuwa da kuma yin sauye-sauye a harkar zaɓe da sauran bukatu.

    An raunata ƴan jarida shida a zanga-zangar ta ranar Alhamis, inda alkaluman ƴan jarida da aka jikkata ya kai 22 tun soma ta a makon da ya gabata.

    Jakadiyar Amurka a Kenya, Margaret Cushing Whitman, ta ce ƙasar ta nuna damuwa kan rahotannin far wa ƴan jarida da ake samu a ƙasar, inda ta ce kare ƴancin jarida da ba su kulawa ita ce dimokuraɗiyya.

  15. Bashin da ake bin Najeriya ya kai tiriliyan 46.25 - DMO

    Muhammadu Buhari

    Ofishin Kula da Basussuka a Najeriya ya bayyana cewa bashin da ake bin ƙasar ya tashi zuwa N46.25trn ya zuwa watan Dismanban 2022.

    A wata sanarwa da Ofishin ya fitar a ranar Alhamis, ya ce an samu ƙarin tiriliyan bakwai cikin basukan da ake bin ƙasar.

    DMO ya ce dalilin da ya sa aka samu ƙarin bashin shi ne saboda ciyo sabbin basuka da gwamnatin tarayya da ta jihohi suka yi domin gudanar da manyan ayyuka da kuma cike gibin kasafin kuɗi.

    Ofishin ya ce kokarin da gwamnati ke yi na ƙara samun kuɗaɗen shiga daga ɓangaren albarkatun mai da kuma ɓangarorin da ba na mai ba, za su taimaka a gudanar da ayyuka ba tare da cin bashi ba.

    Al'ummar Najeriya dai na ci gaba da nuna damuwa kan irin bashin da ƙasar ke ciwowa.

    A shekarar 2005 ne ƙasar ta cimma wata yarjejeniyar yafiyar bashi da ƙungiyar Paris Club, abin da ya sanya aka yafe wa ƙasar dala biliyan 18 daga cikin bashin da ake bin ta.

  16. Amurka za ta tallafa wa Tanzaniya da $500m

    Kamala Harris

    Mataimakiyar shugaban ƙasar Amurka Kamala Harris ta yaba wa Tanzaniya kan sauye-sauyen da ta kawo wanda ke da zimmar ƙarfafa dimokuraɗiyyar ƙasar.

    Ms Harris na a Tanzaniya a ci gaba da ziyara da take yi a Afirka bayan farawa Ghana, inda za ta kammala ziyarar a karshen mako da ƙasar Zambia.

    An yi wa Ms Harris kyakkaywar tarba ta hanyar rera wakoki da yin rawan al'adu daban-daban.

    Shugabar ƙasar ta Tanzaniya, Samia Suluhu Hassan, ta kwatanta ziyarar da wani babban ci gaba ga ƙasar.

    Ms Harris ta ce Amurka za ta bai wa Tanzaniya tallafin $560m don buƙasa kasuwancinta da kuma karfafa dimokuraɗiyya.

    Abu ne da ba a saba gani ba na ziyarar wani babban jami'in gwamnatin Amurka zuwa ƙasar, inda wasu da dama ke ganin ziyarar a matsayin nuna goyon baya ne ga sauye-sauye da Samia ke yi.

    Tun bayan karɓe iko da mulkin ƙasar bayan mutuwar shugaba John Magufuli shekara biyu da suka gabata, Samia ta ɗage haramci kan yakin neman zaɓen ƴan adawa da kuma karfafa ƴancin ƴan jarida. Ƴan siyasa da suka tafi neman mafaka duka sun dawo gida.

    Ms Harris ta yaba da matakan da ƙasar ke ɗauka na kawosauye-sauye, inda ta ce hakan ya taimaka wajen kara kyautata dangantakar ƙasashen biyu.

  17. Kowane lokaci daga yanzu za a iya kama Donald Trump

    Donald Trump

    Donald Trump ya zama shugaban Amurka na farko a tarihi da za a tuhuma da aikata wani laifi.

    Za a tuhumi tsohon shugaban kasar ne a New York a bisa zargin bayar da wasu makudan kudade na toshiyar-baki, kafin zaben shugaban kasar na 2016, ga wata tauraruwar fim ɗin baɗala, domin hana ta magana kan zargin da ake masa na yin mu'amulla da ita.

    Za a tuhumi Mr Trump ne a yayin da yake shirin sake yin takarar shugaban kasa.

    Ofishin babban lauyan Manhattan, ya ce an tuntubi lauyoyinsa akan yadda zai mika wuya.

    Wannan mutumin na daga cikin mutanen da suka taru a kofar gidan Mr Trump da ke Florida, ya ce

    Ya ce Donald Trump ya san cewa ina kaunarsa, zan iya sadaukar da rayuwata gareshi saboda na san shi ma zai iya yi mana haka.

  18. An kama mutum biyar kan zargin tayar da gobara a cibiyar tsare ƴan cirani

    Gobara

    Mahukunta a Mexico sun ce sun kama mutane biyar da ake zargi sun taka rawa a mutuwar 'yanci rani 39 a yayin wata gobara da ta tashi a wata cibiyar tsare 'yanci rani a ranar Litinin.

    Sun ce ana ci gaba da neman mutum na shida da ake zargi.

    Ofishin babban mai shari'ar kasar, ya ce mutanen da aka kaman sun hadar da jami'an hukumar shige da fice uku da wasu masu gadi biyu da kuma mutumin da ake zargi ta haddasa gobarar.

  19. Buɗewa

    Masu bibiyar mu a wannan shafi barkan mu da safiyar Juma'a - Hajj Babbar Rana.

    Ahmad Tijjani Bawage ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.

    Za mu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwaɓtanta da kuma sauran sassan duniya.