Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

time_stated_uk

  1. Bankwana

    Muhammad Buhari Fagge ke fatan an sha ruwa lafiya da fatan a yi sahur lafiya.

  2. An yanke wa wani musulmi hukuncin kisa a Pakistan

    g

    Wata kotu da ke Peshawar a Pakistan ta yanke wa wani musulmi hukuncin kisa bayan da aka same shi da laifin yin ɓatanci.

    Ana zargin Syed Muhammad Zeeshan, daga Mardan da ke arewa maso yammacin ƙasar da wallafa wani saƙon ɓatanci a Whatsapp da sauran shafukansa na zumunta.

    An kuma yanke masa hukuncin ɗaurin jimillar shekara 23 sannan aka buƙaci ya biya tarar sama da dala dubu huɗu.

    Hukumomi a Pakistan dai ba su taɓa yanke hukuncin kisa ga wanda ya yi ɓatanci ba.

    Sai dai a tsarin ƙasar Mista Syed yana da damar ɗaukaka ƙara.

  3. Za a kama wasu manyan 'yan kasuwar Venezuela kan badaƙalar mai

    bbc

    Gwamnatin Venezuela ta ce an bayar da izinin kama wasu mutum goma sha daya da ake zargi da tafka cin hanci da rashawa a kamfanin mai na kasar.

    Babban mai gabatar da kara Tarek William Saab ya ce akasarin mutanen yan kasuwa ne da ke da hannu a sayar da danyen mai ta haramtacciyar hanya da kuma almundahana.

    Tuni aka kama wasu daga cikinsu. A ranar Litinin ne, ministan man Venezuela mai karfin fada a ji ya yi murabus bayan da aka tsare mutane da dama da ke da alaka da shi.

    Bangaren hamayya ya ce watakila zarge-zargen na da nasaba da wata yar tsama ta siyasa a cikin gwamnati gabanin zaben shekara mai zuwa.

    Ana sa ran Shugaba Nicolas Maduro wanda ya shafe shekara 11 a kan mulki ya sake neman yin tazarce.

  4. Sati 12 kenan a jere ana gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnati a Isra'ila

    BBC

    Al'ummar Isra'ila da ke adawa da kudirin gwamnati na yi wa ɓangaren shari'a garambawul na ci gaba da gudanar da gangami a sassan ƙasar mako goma sha biyu jere.

    Ƴan sanda sun rufe manyan tituna a Tel Aviv inda ake gudanar da tattakin.

    Kusan masu zanga-zanga dubu ɗaya ne suka taru a wajen gidan ministan tsaron ƙasar inda suke zarginsa da rashin ɗaukar mataki saboda tsoro bayan da aka ga kamar zai yi murabus game da batun kwanaki biyu da suka gabata.

    Sojojin ko-ta-kwana sun yi gargaɗin cewa ba za su yi aiki a rundunar sojin ƙasar ba idan har aka sauya fasalin ɓangaren shari'ar suna mai cewa matakin barazana ne ga dimokraɗiyyar Isra'ila.

  5. An cire Reece James daga tawagar Ingila saboda rauni

    g

    Dan wasan bayan Chelsea Reece James ba zai buga wasan samun gurbi na Euro 2024 ba da Ingila za ta yi da Ukraine a ranar Lahadi sakamakon raunin da ya ji.

    Dan wasan mai shekara 23 ya komo gasar Premier ne bayan hukumar FA ta ce tana tantance abubuwan da suke gudana.

    James ya sauya dan wasan Arsenal Bukayo Saka a minti na 85 a wasan da ruka yi nasara da ci 2-1 a kan Italiya a Naples.

    Kocin tawagar Gareth Southgate ya ƙi kiran kowa domin maye gurbin shi.

  6. 'Yan bindiga sun kashe malamin coci sun sace matarsa a Kaduna

    .

    Wasu 'yan bingida sun kashe Musa Mairimi, wanda ke lura da cocin ECWA da ke ƙauyen Buda a ƙaramar hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna.

    'Yan bindigar sun kuma sace matar malamin da suka kashe.

    Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, wani mutum da ya nemi a boye sunansa ya tabbatar mata da faruwar lamarin.

    Ya ce lamarin ya faru ne a safiyar ranar Alhamis.

    Jaridar ta ce ta yi ƙoƙarin kiran kakakin 'yan sandan jihar Muhammed Jalige domin jin ta bakinsa amma abin ya ci tura, wayarsa a kashe.

  7. Kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da ƙarar da PDP ta shigar kan Tinubu da Shettima

    Bola Ahmed Facebook

    Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da PDP ta shigar gabanta, na ta yi ƙi amincewa da Tinubu da Kashim Shettima a matsayin yan takarar shugaban ƙasa da mataimakinsa na jam'iyyar APC a zaɓen da aka yi na 25 ga watan Fabirairu.

    PDP ta nemi kotun ta juya hukuncin da mai shari'a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya ya yi a ranar 13 ga watan Janairu, wanda ya ce PDP ta gaza kawo hujja kan ƙarar da ta shigar.

    Cikin wani hukunci da alƙalai uku suka yi ƙarƙashin jagorancin mai shari'a James Abundaga sun yanke hukunci kan cewa PDP ta gza kawo hujja kan ƙarar da ta shigar.

    Yace PDP ta shiga wani lamari ne na harkar cikin gida na jam'iyyar APC.

  8. India ta kwace lasisin kamfanin haɗa maganin tarin da ya kashe raya 18

    BBC

    Hukumomi a India sun kwace lasisin wani kamfani da ke haɗa maganin tari wanda ke da alaƙa da kisan wasu yara 18 a Uzbekistan.

    Hukumar Lafiya ta Duniya a watan Janairu ta yi gargaɗi akan amfani d maganin na kamfanin Marion Biotech, tana cewa ba shi da inganci.

    Sai dai kamfanin Marion Biotech ya musanta zargin.

    Bayan samun rahoton mace-macen a Uzbekistan, ministan lafiya na India ya dakatar da ayyukan kamfanin.

    A ranar Laraba ne hukumomi a jihar Uttar Pradesh ta India suka ce an dakatar da kamfanin har sai baba ta gani.

  9. Ra'ayi Riga

    Ra'ayi Riga kan yadda aka yi shirye-shiryen fara azumin Ramadan a Najeriya da Ghana da Nijar da Kamaru da sauran ƙasashen Afirka.

    Video content

    Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin sauraron shirin
  10. 'Yan bindiga sun sace manoma biyu a jihar Edo

    d

    Rundunar 'yan sandan jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya sun tabbatar da sace wasu mutum biyu da ake zargin wasu 'yan bindiga sun sace a ƙaramar hukumar Owan ta Yamma.

    Rundunar ta ce, tana bakin ƙoƙarinta dan ganin ta kama masu garkuwa da mutanen tare da kuɓutar da mutanen da aka sacen.

    Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito 'yan sanda na cewa mutanen biyu da aka sace masu suna Omafuaire da kuma Folorunsho, sun je gonarsu ne da ke Ugbokuli, domin tsinko kwakwar manja a lokacin da 'yan bindigar suka yi garkuwa da su.

    Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar SP Childi Nwabuzor, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce suna kan bincike domin gano tare da kuɓutar da mutanen.

  11. Guguwa ta kashe mutum 23 a Amurka

    ss

    Aƙalla mutum 23 sun mutu bayan da wata guguwa haɗe da ruwa ta ratsa jihar Mississipi ta Amurka ranar Juma'a da daddare.

    Ana kuma fargabar cewa wasu ƙarin mutane da dama sun maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan gini.

    Guguwar ta yi sanadin lalata garuruwa da ƙauyuka da dama, inda bishiyoyi da turakun lantarki suka faɗi, lamarin da ya kawo ɗaukewar lantaki a dubban gidaje.

    Rahotonni sun ce guguwar mai ƙarfi ta shafi wasu jihohin kudancin ƙasar.

    Hukumar kula yanayi ta ƙasar ta yi gargadin cewar ana iya samun ƙarin wata guguwar haɗe da ruwa mai ƙarfia jihar.

    Mazauna Rolling Fork, wani ƙaramin gari da ke yammacin jihar, sun ce guguwar ta yi sanadin lalata musu gidajensu.

    Brandy Showah ta shaida wa kafar yaɗa labarai ta CNN cewa ''ban taɓa ganin mummunan bala'i ba kamar wannan, wannan ƙaramin garin namu gabaki-ɗayansa guguwar ta tafi da shi".

  12. Lafiya Zinariya: Matsalar ƙiba ko teɓa da alaƙarta da rashin haihuwa

    Likitoci sun ce ƙibar da ta wuce kima nau'i biyu ce, ta waje da kuma ta cikin mutum.

    Sai dai ta cikin ta fi haɗari, domin takan shafi al'adar mace.

    Hukumar lafiya ta duniya, WHO ta ce an fi samun mutane masu teɓa, a kan waɗanda ƙibarsu ta wuce kima, a kowane yanki na duniya.

    Amma ban da yankin Kudu da hamadar Sahara Afrika da kuma yankin Asia., a cewar hukumar wannan matsalar a baya ta fi ƙamari ne a ƙasashen da suka ci gaba.

    Sai dai a yanzu matsalar teɓa na ƙaruwa a ƙasashe masu ƙaranci da matsakaicin kuɗin shiga, musamman a birane.

    WHO ta bayyana cewa matuƙar ƙiba ko teba da kan shafi kiwon lafiya, abu ne da ya kai matakin annoba a duniya. Inda kimanin mutane fiye da miliyan huɗu ke mutuwa duk shekara, a dalilin hakan.

    Alkaluman hukumar sun nuna cewa daga shekarar 1975 zuwa shekarar 2016, an samu yawaitar yara masu shekara biyar zuwa shekara 19, da ke fama da teɓa fiye da ninki hudu.

    Wato daga kashi hudu cikin 100 zuwa kashi 18 cikin 100, a cikin sama da shekara arba'in, a fadin duniya.

    A shekarar 2019 kacal, an samu yara 'yan ƙasa da shekara biyar, miliyan 38 da dubu dari uku, waɗanda ko dai ƙibarsu ta wuce kima ko kuma suna da matuƙar teɓa. In ji hukumar.

    Hukumar ta ƙara da cewa ta ɓangaren manya kuma an samu kashi 39 cikin dari na waɗanda ƙibarsu ta yi yawa sosai, yayin da masu teɓa sosai kuma suka kai kashi 13 cikin dari, a shekarar ta 2016.

    Alkaluman da ke nufin a shekarar an samu manya biliyan ɗaya da miliyan ɗari tara da ƙibarsu ta wuce kima, yayin da a cikin wannan jimilla kuma yawan masu matuƙar teɓa ya kai miliyan 650.

    Haka kuma mafiya yawan yaran da ke fama da teɓa an fi samunsu ne a ƙasashe masu tasowa. Inda ake samun ƙaruwarsu har ta kai sun haura na ƙasashen da suka ci gaba da kashi 30 cikin dari.

    To domin jin cikakken bayani kan yadda matsalar teɓa ke shafar mata masu neman haihuwa da masu ciki, sai ku saurari hirar da Habiba Adamu ta yi da Dakta Mairo Mandara.

    Video content

    Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin sauraron shirin
  13. Ƙayyade farashi: Hukumomin Saudiyya sun kai samame kasuwannin ƙasar

    'yan kasuwa

    Ma'aikatar kasuwanci ta ƙasar Saudiyya ta ce ta tura tawagar masu sanya ido domin duba kasuwanni a biranen Makka da Madina don lura da farashin kayayyaki a cikin watan Ramadan.

    Tawagar masu sanya idon waɗanda ke aiki kafaɗa-da-kafaɗa da sauran hukumomi, an ƙaddamar da ita ne da nufin duba ko 'yan kasuwa na biyayya ga dokokin kare haƙƙin mai saye ko akasin haka.

    Haka kuma hukumar ta ce aikin wani ɓangare ne na aikin da ma'aikatar ke gudanarwa domin tabbatar da wadatuwar kayyakin masarufi da za su wadaci 'yan ƙasar, tare da samun hanyar da za a wadata kasuwanni da kayayyaki.

    Tawagar masu sanya idon na tsaurara bincike a shagunan da ke kan titunan biranen Makka da Madina, musamman a wannan lokaci da ake samun yawaitar masu Umrah a ƙasar.

    Haka kuma suna duba gidajen mai da shagunan sayar da kayyayakin gyaran ababen hawa, domin tabbatar da 'yan kasuwa na bin umarnin ƙayyade farashi da ma'aikatar ta sanya.

    Tun kafin fara azumin watan Ramadan ma'aikatar ta ɗauki matakai domin samar da wadatattaun kayayyakin buƙatun azumin a kasuwannin ƙasar, da kuma tabbatar da ingancinsu.

    Tare kuma da duba kayayyakin da kwanan watan lalacewarsu ya cika domin ɗaukar matakan shari'a kan 'yan kasuwar da suka ƙi fitar da su daga shagunansu.

    Ma'aikatar ta kuma buƙaci masu sayen kayyakin da su kai rahoton duk wani ƙorafi da suke da shi kan wani ɗan kasuwa da suka zarga da aikata ha'inci a kasuwancinsa, ta hanyar bayar da lambobin wayar da za a tuntuɓi ma'aikatar

  14. Gane Mini Hanya

    Najeriya na daga cikin ƙasashen da rahotoni suka bayyana a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen da ke fuskantar barazana ta fuskar ‘yancin faɗar albarkacin baki a fadin duniya.

    Sau da yawa aka zargi mahukunta a ɓangarori da dama game da kamawa da tsarewa, ko ma rufe wasu kafofin yaɗa labarai, saboda wasu dalilai masu alaƙa da saɓa ƙa’idar aiki, kodayake wasu na zargin cewa bi-ta-da-ƙulli ne kawai, don hana ‘yancin faɗar albarkacin baki.

    Yayin wata ziyara da ya kawo ofishin BBC da ke Landan, shugaban hukumar kula da kafofin yaɗa labaran ƙasar NBC Balarabe Shehu Illela ya ce babu ƙamshin gaskiya a wannan zargi.

    Ga kuma tattaunawarsu da Imam Saleh

    Video content

    Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin sauraron shirin
  15. CBN ya umarci bankuna su yi aiki a ranakun Asabar da Lahadi don magance karancin naira

    kudi

    Babban bankin Najeriya CBN ya umarci bankunan ƙasar da su yi aiki a yau Asabar da kuma gobe Lahadi domin tabbatar da cewa takardun kuɗaɗen naira sun wadata a hannun jama’a.

    A wata sanarwa da CBN ya wallafa a shafin na Tuwita, ya ce ya fito da maƙudan takardun naira ne a bankunan ƙasar da kuma na’urorin cirar kudi ta ATM domin magance matsalar ƙarancin kuɗin a ake fama da shi a fadin ƙasar.

    Sanarwar ta ƙara da cewa CBN ya bayar da umarnin ɗaukar takardun kuɗaden daga rassansa zuwa bankunan kasuwanci da ke fadin ƙasar

    Ta ƙara da cewa bankunan kasuwancin ƙasar sun samu maƙudan takardun kuɗaɗe domin rarraba wa abokan huldarsu, da nufin wadatar kuɗade a hannun jama’a.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa babban bankin ƙasar ya umarci bankunan kaswunci da su sanya takardun kuɗaden cikin na’urorin cirar kudinsu na ATM, domin sauƙaƙa wa kwastomominsu.

    View more on twitter
  16. EFCC ta sake gurfanar da ɗan tsohon shugaban PDP kan zargin aikata zamba

    x

    Hukumar da ke Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Najeriya Zagon ƙasa EFCC ta sake gurfanar da Mamman Ali, ɗa ga tsohon shugaban jam'iyyar PDP na ƙasar Ahmadu Ali, bisa zargin zambar naira biliyan 2.2 na tallafin man fetur.

    Kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN, ya ruwaito cewa an sake gurfanar da Mamman Ali tare da wani mutum mai suna Christian Taylor da kamfanin mai na Nasaman Oil Services Ltd. a gaban wata kotu a birnin Legas.

    An gurfanar da su ne bisa zarge-zagen laifuka 49 ciki har da haɗa baki, da yaudara da zamba cikin aminci, da yin ƙarya domin karɓar kuɗi da amfani da takardun bogi.

    To sai dai mutanen sun musanta duka zarge-zargen da ake yi musu.

    Lauyan hukumar EFCC Samuel Atteh, ya nemi kotun da ta sanya ranar sauraron ƙarar ta yadda zai gabatar da shaidunsa da za su tabbatar da zargin da hukumar ke yi wa mutanen.

    To sai dai lauyan waɗanda ake zargin Kolade Obafemi ya nemi kotun da ta bayar da belin waɗanda yake karewa.

    To amma lauyan EFCC ya ce abu mafi muhimmaci kan wannan shari'a shi ne waɗanda ake zargi su riƙa halartar kotun don fuskantar tuhumar da ake yi musu.

    Daga ƙarshe alƙalin kotun ya bayar da umarnin cewa waɗanda ake zargin su ci gaba da kasancewa a hannaun hukumar EFCC har zuwa lokacin da za a gabatar da takardun neman belinsu a hukumance.

    Alƙalin ya kuma ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar 30 ga watan Mayu mai zuwa.

    A ɗaya daga cikin zarge-zargen da hukumar EFCC ke yi wa mutanen, shi ne zargin haɗa baki don karɓar naira miliyan 750 daga gwamnatin tarayya, don karyar bai wa kamfanin mai na Nasaman Oil Services Ltd, ƙarƙashin asusun tallafa wa kamfanonin mai don shigo da litar mai 10,031,986, da kamfanin na Nasaman Oil Services Ltd, ya yi iƙirarin cewa ya saya daga kamfanin man Birtaniya na SEATAC Petroleum Ltd.

  17. Ayyana zaɓen gwamnan Adamawa a matsayin wanda bai kammala ba shi ne daidai - Binani

    \

    'Yar takarar kujerar gwaman jihar Adamawa ƙarƙashin jam'iyyar APC Sanata Aishatu Ahmed Binani, ta bayyana goyon bayanta kan matakin hukumar zaɓen ƙasar INEC ta ɗauka na bayyana zaɓen gwaman jihar a matsayin wanda bai kammala ba.

    Yayin da ta bayyana a cikin shirin 'Politics Today' na gidan talbijin ɗin Channels Tv, Sanata Aishatu Binani ta yi maraba da matakin, inda ta yi zargin cewa an aikata kura-kurai da rikice-rikice a wasu ƙananan hukumomin jihar.

    Babban jami'in tattara sakamakon zaɓen jihar Farfesa Muhammadu Mele na jami'ar Maiduguri ne ya ayyana sakamakon zaɓen gwaman jihar da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris a matsayin wanda bai kammala ba.

    Gwaman jihar mai ci Ahmadu Umaru Fintiri, wanda ke neman wa'adin mulkin jihar karo na biyu ƙarƙashin jam'iyyar PDP ya samu ƙuri'u 421,524, yayin da ita kuma Sanata Binani ta jam'iyyar APC ke da yawan ƙuri'u 390,275.

    Jami'in zaɓen ya bayyana cewa ba a gudanar da zaɓen a rumfunan zaɓe 69 a faɗin jihar ba, kuma adadin katunan zaɓen da aka karɓa a duka rumfunan sun kai 37,016, wanda kuma adadinsu ya zarta tazarar ƙuri'u 31,249 da ke tsakanin 'yan takarar biyu.

    Sanata Aishatu ta ce ''matsayina game da matakin shi ne jami'in tattara sakamakon zaɓen jihar ya yi daidai da ya bayyana sakamakon zaɓen jihar a matsayin wanda bai kammala ba''.

  18. Ukraine ta ce tana samun nasara a Bakmut

    b

    Babban hafsan sojin Ukraine ya ce suna samun nasara a ƙazamar fafatarwar da suke yi da dakarun Rasha a birnin Bakmut.

    Dubban sojojin Ukraine da Rasha dai sun mutu a yaƙin ƙwace birnin - da masu sharhi suka jadda muhimmancinsa ga ɓangarorin biyu - duk kuwa da ƙoƙarin da dakarun Rasha suka yi na mamaye birnin ya ci tura.

    A ranar Laraba shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya kai wa dakarun da ke fagen daga a yankin ziyara, yayin da wasu kwamandoji ke cewa sojin Rasha sun rasa ƙwarin gwiwwa a ƙoƙarin da suke na karɓe iko da birnin na Bakmut.

  19. A shirye nake don kare Amurkawa a duk inda suke - Biden

    Biden

    Shugaban Amurka Joe Biden ya ce a shiye yake ya kare Amurkawa ko ta wacce hanya, bayan da ya bayar da umarnin kai hare-hare ta sama babu ƙaƙƙautawa a arewacin Syria.

    Wannan dai martani ne ga kisan da wata ƙungiya mai alaƙa da dakarun juyin-juya hali na Iran ake zargin ta yi wa wani Ba’amurke ɗan kwangila tare da jikkata sojoji biyar.

    Mista Biden ya ce Amurka ba ta da niyyar neman faɗa da Iran, to amma za ta yi duk mai yiyuwa domi kare ‘yan ƙasarta a duk inda suke a faɗin duniya.

    Wasu dakarun da ke goyon bayan Iran ɗin sun fitar da wata sanarwa, wadda a cikin suke cewa suna da ƙarfin da za su mayar da martani matuƙar Amurkan ta ƙaddamar da hare-haren da take iƙirarin kaiwa