Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Buhari Muhammad Fagge, Ahmad Tijjani Bawage da Abdullahi Bello Diginza

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Masu bin mu, nan muka kawo ƙarshen labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    Abdullahi Bello Diginza a madadin sauran abokan aiki, ke cewa mu kwana lafiya

  2. Tarayyar Afirka ta yi kira a dakatar da abin da ta kira 'ruguza Sudan'

    Faki

    Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka, Moussa Faki Mahamat, ya fitar da wata sanarwa kan abin da ke ci gaba da faruwa a Sudan.

    Sanarwar ta ambato shugaban Tarayyar Afirka na roƙon "ɓangarorin siyasa da soji su samo mafitar siyasa ta adalci ga rikicin da ya taso bayan juyin mulkin 25 ga watan Oktoban 2021 da kuma miyagun abubuwan da suka biyo baya.

    Mahamat na magana ne kan abin da ke faruwa game da ranar da sojojin Sudan ƙarƙashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan suka ƙwace iko da gwamnati a Sudan.

    Sanarwar Mista Mahamat ta yi kira ga sojoji da kuma dakarun RSF masu kayan sarki cewa: "Cikin gaggawa a dakatar da ruguza ƙasar, da tafka ta'addanci ga al'ummarta, da kuma zubar da jini a wannan lokaci na goman ƙarshe cikin watan Ramadan mai alfarma''.

    An dakatar da Sudan daga ƙungiyar ƙasashen ta Tarayyar Afirka a watan Yunin 2019.

  3. Girke-girken Ramadan: Yadda ake sarrafa Scones

    Video content

    Video caption: Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  4. ‘Yan sanda sun kama fasto kan yi wa mabiyansa fatawar yin azumin ganin Yesu

    e

    Rundunar 'yan sandan Kenya ta kama wani fasto kan zargin hannu a mutuwar mutum huɗu, sakamakon azumin da ya ce su yi don haɗuwa da Yesu.

    'Yan sanda sun ce faston mai suna Makenzie Nthenge na cikin ƙungiyar asiri a yankin Kilifi, wanda mabiyansa ke cike da burin yin azumi domin su mutu.

    Malamin cocin dai yana shaida musu cewa hakan ce hanya mafi sauƙi ta haɗuwa da Yesu.

    A yanzu dai mutum 11 ne ke karɓar magani a asibiti bayan kuɓutar da su daga inda suke ɓoye, suna azumin.

    Rahotonni sun ce wasu sun yi kwana 21, ba tare da cin abinci ba, da nufin idan sun mutu za su haɗu da Yesu.

    Mista Nthenge ya ce ya rufe cocin tasa tun a 2019, to sai dai ya koma amfani da shafin YouTube don yin da'awa.

    A watan jiya ma, an tuhumi mista Nthenge da hannu a mutuwar wasu yara biyu, waɗanda iyayensu ke bin shafin YouTube na Mista Nthenge.

  5. Bayan tsawon wuni ana rikici an kasa sanin wani fayyataccen lamari a Sudan

    Wannan shi ne abin da aka fi fargaba, kuma mafi munin lamari. Wato Gwagwarmayar ƙwatar iko tsakanin manyan janar-janar biyu da suka fi ƙarfin faɗa-a-ji a Sudan.

    Yayin da aka ci gaba da gwabza faɗa tsawon sa'a 12, babu wani abu da ya bayyana a fili game da ɓangaren da ke da galaba, kuma abin da ke faruwa a wajen Khartoum a duƙunƙune yake kuma cike da ruɗani.

    A tsawon ranar, ɓangarorin biyu sun yi iƙirarin cewa dakarunsu ne ke iko da Khartoum, sai dai rahotannin baya-bayan nan, na nuna cewa abubuwa na iya canzawa cikin sauri, don haka da wuya a iya wani hasashe.

    Janar-janar ɗin biyu da daɗewa abokan ƙawancen juna ne, tun lokacin rikicin Darfur mai cike da zubar da jini da kisan kiyashi a farkon shekarun 2000.

    Tun a shekara ta 2019, mayaƙan runduna masu kayan sarki ta RSF take jin ta isa ta gabatar da kanta a matsayin wata halastacciyar rundunar tsaro ta ƙasa maimakon sojojin sa-kai na wata ƙabila da aka yi amfani da ita wajen murƙushe rikicin 'yan ta-da-ƙayar-baya.

    Rundunar tana gudanar da ayyukan sojojin haya mafi girma a duniya kuma dakarunta sun yi dumu-dumu a yaƙe-yaƙen Yemen da Libya.

    Tana kuma da kyakkyawar alaƙar aiki da ƙungiyar sojojin hayar Wagner ta Rasha, wadda aka ba da rahoton cewa tana da ɗumbin muradai cikin harkokin kasuwanci da haƙar ma'adanai a Sudan.

    Abokan gabarsu, sojojin Sudan, ɓangaren da ya yi kaka-gida a harkokin siyasar Sudan tsawon gomman shekaru.

    A baya-bayan nan, alaƙa tsakanin sojoji da mayaƙan rundunar masu kayan sarkin ta RSF ta sukurkuce, saboda yunƙurin garambawul a harkar tsaro, kuma da daɗewa rundunar tana so a haɗe mayaƙanta cikin dakarun sojin Sudan.

  6. Duhun dare bai sa faɗa ya tsagaita ba a Sudan

    Yanzu dai maryace ya yi a Khartoum babban birnin Sudan, kuma yayin da mutane ke buɗa-baki bayan wunin azumin Ramadan, shaidu na cewa har yanzu ana iya jin amon bindigogi.

    Wani mai aika rahotanni a Omdurman, ɗaya tsallaken na Kogin Nilu daga Khartoum, ya faɗa wa BBC cewa har yanzu ana jin tashin bindigogi, amma dai jiragen sojoji sun tsagaita shawagi a sama.

    Ɗan jaridan, Isma'il Kushkush wanda ke fitar da bayanai a kai a kai a shafin sada zumunta na Tuwita daga babban birnin na Sudan, ya ce an ci gaba da gagarumin luguden atilare a tsakiyar Khartoum.

    An shiga zaman taraddadi kan abin da zai iya faruwa a cikin dare.

  7. Sojojinmu ne ke iko da muhimman wurare - shugaban Sudan

    General Burhan

    Janar Abdel Fattah al-Burhan, jagoran Sudan kuma babban hafsan hafsoshin sojin ƙasar ya musanta iƙirarin rundunar jami'ai masu kayan sarki ta RSF, cewa dakarunta ne ke iko da fadar shugaban ƙasa da hedkwatar sojoji da kuma filin jirgin sama.

    A wani saƙon waya da aka naɗa lokacin hira da gidan talbijin na Al Jazeera, Janar al-Burhan ya dage kan cewa dakarunsa ne har yanzu ke da iko.

    Ana ci gaba da samun rahotanni masu cin karo da juna game da abin da ke faruwa a tsawon wannan rana kan taƙamaimai wane ne ke iko da muhimman wurare a birnin Khartoum.

  8. Blinken ya yi kira da a dakatar da faɗa a Sudan

    Blinken

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken, ya yi kira ga ɓangarori a Sudan da su gaggauta dakatar da faɗan da suke yi.

    A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, ya ce ya damu matuƙa kan rahotannin faɗa da ake ci gaba da yi a Sudan.

    "Muna kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su dakatar da tashin hankalin nan take, su kauce wa yaɗuwar rikicin, sannan a ci gaba da tattaunawa don warware matsalar," in ji shi. a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa taron ministocin harkokin wajen ƙasashen G7 a Japan.

    View more on twitter
  9. Labarai da dumi-dumiChadi ta rufe kan iyakarta da Sudan

    Ƙasar Chadi ta rufe kan iyakarka ta gabashi da ƙasar Sudan.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce ƙasar ta rufe kan iyakar ne har zuwa wani lokaci da ba a bayyana ba.

    A wata sanarwa da gwamnatin Chadin ta fitar, ta ce tana kira ga ƙasashen Afirka da na duniya da ƙasashen makwabta da su taimaka wajen maido da zaman lafiya a Sudan.

  10. Gane Mini Hanya

    Video content

    Video caption: Latsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  11. MDD ta yi Allah-wadai da faɗan da ya ɓarke a Sudan

    MDD

    Wakilin na musamman na Majalisar Ɗinkin Duniya a kuma shugaban tawagar shirin miƙa mulki aSudan, Volker Perthes, ya yi Allah-wadai da ɓarkewar faɗa a ƙasar.

    Dakarun kai ɗaukin gaggawa na RSF da kuma dakarun sojin Sudan na can suna artabu a Khartoum, da kuma wasu yankunan da ke wajen babban birnin ƙasar.

    Peretz ya yi kira ga ɓangarorin biyu da su gaggauta dakatar da faɗan domin tabbatar da tsaron al'ummar Sudan da kuma kare ƙasar daga tashin hankali.

    View more on twitter
  12. Shugaban rundunar jami'ai masu kayan sarki ya zargi sojoji da yunƙurin juyin mulki

    BBC

    Shugaban jami'an rundunar kai ɗaukin gaggawa don tallafawa ayyukan tsaro ta masu kayan sarki a Sudan, Janar Mohamed Hamdan Dagalo, ya yi iƙirarin cewa an tilasta wa mayaƙansa yin artabu da sojoji ne don murƙushe wani yunƙurin juyin mulki.

    A wata zantawar wayar tarho da gidan talbijin na Al-Jazeera, Janar Dagalo ya ce mayaƙansa za su ci gaba da faɗa har sai sun ƙwace dukkan sansanonin soji.

    Ya bayyana babban hafsan sojojin Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan a matsayin wani mai laifi kuma ya zargi sojoji da aiwatar da wani makirci - da magoya bayan hamɓararren shugaban kama-karya na Sudan Omar al-Bashir, da aka kifar da gwamnatinsa a wani juyin mulki cikin shekara ta 2021 - suka kitsa.

  13. Saudiyya ta nuna damuwa kan ɓarkewar faɗa a Sudan

    Yariman Saudiyya

    Ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya, ta nuna damuwa matuka kan faɗan da ya ɓarke a Khartoum, babban birnin Sudan wanda kuma ke ci gaba da yaɗuwa zuwa sassan ƙasar.

    Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar, ta yi kira ga ɓangarorin da ke rikici da su zauna kan teburin tattaunawa maimakon tayar da tarzoma, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

  14. An tsinci gawar wani almajiri a Jigawa babu ido

    .

    Rundunar ƴan sanda a jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wani almajiri ɗan shekara 16 bayan an tsinci gawarsa a wani daji kusa da ƙaramar hukumar Kiyawa da ke jihar.

    A cikin wata sanarwa mai magana da yawun ƴan sandan jihar DSP Lawal Shiisu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an cire ɗaya daga cikin idanun almajirin.

    Shiisu ya ce Malamin marigayin, Malam Mustafa da ke garin Shuwarin, shi ya kai wa jami'an tsaro rahoto kan lamarin da ya faru.

    DSP Shiisu, ya ce Malamin ya kai korafin cewa ɗaya daga cikin ɗalibansa mai suna Yusufa Mustapha ɗan shekara 16, ya shiga daji don neman itace da misalin ƙarfe 8 na safe, wanda kuma daga nan ne ba su ji ɗuriyarsa ba sai dai ganin gawarsa.

  15. An cinna wuta a kusa da filin jirgin sama na Khartoum

    BBC
    Image caption: Unguwar da ke daf da filin jirgin sama na Khartoum ta turnuƙe da hayaƙi
    B
    Image caption: Mutane sun gudu sun ɓuya domin ba su san me zai je ya dawo ba
    BBC
    Image caption: Tituna babu kowa, mutane ɗauke da makamai kawai ake gani ko'ina
    BBC
    Image caption: Ana iya ganin mutane jefi-jefi a wasu yankuna na babban birnin
  16. Birtaniya ta umarci ƴan ƙasarta a Sudan da su zauna a gida

    Rishi Sunak

    Ofishin jakadancin Birtaniya a Sudan ta umarci ƴan ƙasarta da su zauna a gida bayan rikicin da ya ɓarke a ƙasar.

    Sanarwar da ofishin ya fitar, ta ce jami'ai na ci gaba da sa ido kan lamarin da ke faruwa a Khartoum da wasu sassan Sudan, inda ake ci gaba da artabu da sojoji.

    Ofishin ya kuma bukaci dukkan ƴan ƙasarta da ke Sudan da su guji fita waje, har sai sun ji wata sanarwa daga jami'a.

  17. An yi wa wakilin BBC duka tare da tsare shi a Khartoum

    B

    Sojojin Sudan sun kama wakilin BBC na shashen Larabci da ke Khartoum Mohamed Mohamed Othman, sun yi masa duka.

    Sojojin sun tsare shi ne a lokacin da yake cikin motarsa a Omdurman a kan hanyarsa ta zuwa wajen aiki a Khartoum.

    Sojojin sun karɓi motar tare da tukawa, inda suka kai shi hedikwatar sojoji da ke Omdurman.

    Yayin da yake yi musu bayanin dalilin fitowarsa, ya shaida masu cewa zai je ofis ɗinsa ne da ke Khartoum, dajin cewa ma'aikacin BBC ne wani ya dake shi a keya.

  18. Labarai da dumi-dumiMutum biyu sun mutu bayan harba harsashi kan jirgin sama a Khartoum

    Rahotanni sun bayyana cewa mutane biyu ne suka mutu a lokacin da wani harsashi ya faɗa kan wani jirgin fasinja a filin jirgin saman Khartoum.

    Jiragen saman dai na komawa ƙasashensu na asali maimakon yunkurin sauka a babban birnin ƙasar Sudan, inda jirage daga Saudiyya ke jujjuyawa a minti na karshe, kamar yadda bayanai suka nuna.

  19. Su wane ne jami'an ɗaukin gaggawa masu tallafawa tsaro a Sudan?

    Rapid Support Forces

    Rundunar kai ɗaukin gaggawa don tallafawa tsaro (RSF) wadda ta yi ƙaurin suna a Sudan, ta daɗe a cikin wannan dambarwa, wadda ake yi kan shirin miƙa mulki hannun gwamnatin farar hula.

    Rundunar wadda ke ƙarƙashin jagorancin Janar Mohamed Hamdan Dagalo - wanda shi ne kamar yake riƙe da muƙamin mataimakin shugaban ƙasa - an sha zargin ta da ayyukan keta 'yancin ɗan'adam.

    Cikin zarge-zargen kuma har da kashe masu zanga-zanga a ƙalla 120 a watan Yunin 2019, lokacin da cincirindon masu maci suna gudanar da zaman dirshen a hedkwatar sojojin ƙasa ta Sudan.

    An kafa rundunar kai ɗaukin gaggawa ta RSF ne a 2013, akasari da mayaƙan rundunar sojin sa-kai ta Janjaweed wadda cike da ayyukan rashin imani ta murƙushe 'yan tawaye a Darfur

    A 2015, wasu dakarun rundunar 40,000 suka shiga ayyukan soja na shiga tsakani da Saudiyya ta jagoranta a Yemen

    An kuma taɓa aika mayaƙan rundunar ta RSF zuwa Libya.

    A ƙoƙarin aiwatar da shirin miƙa mulki hannun farar hula cikin sauƙi, an ɓullo da wani shiri kuma na fara shigar da mayaƙan RSF cikin rundunar sojojin Sudan.

    Sai dai dambarwa tsakanin Janar Dagolo da kuma shugaban dakarun sojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan, game da lokacin da za a canza rundunar da kuma wanda zai shugabanci sabuwar rundunar da haɗe, sun sa an kasa samun ci gaba.

    Irin wannan zaman ɗar-ɗar ne ya fantsama, ya zama rikicin da ya ɓarke tsakanin ɓangarorin biyu kamar yadda aka fara gani da safiyar yau.