Kotu ce za ta raba ni da INEC - Obi

Hoton Peter Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa na Najeriya a ɗaya daga cikin manyan jam’iyyun hamayya, Labour Party, Peter Obi ya ce shi ne ya ci zaɓen da aka yi ranar 25 ga watan Fabarairu 2023.

A cewarsa zai bi duk wani matakin shari’a domin ya ƙwato nasararsa.

Mista Obi ya ce wannan ne karon farko da ya fito duniya yake magana tun bayan kada kuri’ar da ya yi a zaɓen, saboda haka ya ce duk wani sako ko magana da aka danganta da shi a baya ba shi ya fada ba.

"Mun ci zaɓen kuma za mu tabbatar wa da 'yan Najeriya hakan," in ji Obi.

Ɗan takarar na jam'iyyar Labour ya ce har yanzu yana nan a kan bakansa na burin samar da sabuwar Najeriya.

Sannan ya yi kira ga dukkanin 'yan ƙasar da kada su gajiya kuma kada su karaya, su tabbatar sun je sun shiga an dama da su a zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisar dokokin jihohi da za a yi ranar 11 ga watan Maris.

Mista Obi ya ce ba wata haɗaka da yake yi da wata jam'iyya a yanzu amma yana tare da dukkanin 'yan Najeriya da ransu ya ɓaci kuma suka damu kan yadda sakamakon zaɓen ya kasance.

Ɗan takarar jam'iyya mai mulki, APC, wato Bola Ahmed Tinubu, shi ne ya yi nasara a zaɓen shugaban ƙasar inda ya samu ƙuri'a miliyan 8.79, wato kashi 37 cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa.

Sai Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP wanda ya zo na biyu, da ƙuri'a 6,984,520, wato kashi 29.07 cikin ɗari.

Yayin da Peter Obi ya zo na uku da ƙuri'a 6,101,533, wato kashi 25.4 cikin ɗari.

Ƙasar mafi ƙarfin tattalin arziƙi a Afirka, tana da al'ummar da ta zarta miliyan 200.

A ranar Laraba bayan da hukumar zaɓen ƙasar ta damka wa Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima takardar shedar zaɓensu, Jagaban ya bayyana cewa an yi zaɓen cikin gaskiya da adalci da kuma inganci.

Ya ce matsalolin da aka bayar da rahotonninsu waɗanda suka janyo ce-ce-ku-ce da kin amincewar ba su shafi sakamakon zaɓen ba na gaba ɗaya.

Mista Obi yana da ja a kan alkaluman da INEC ta nuna na cewa an samu ƙarancin mutane a zaben, a lokacin da yake ganin an samu tururuwar mutanen da ba a taba gani ba ta masu rijistar zabe.

INEC ta ce jumullar ƙuri’un da aka kada ƙasa da miliyan 25 ne, daga cikin mutane miliyan 87 da suke da katin shedar zaɓe, wadanda kuma suka cancanta yin zaɓen.

Inda aka nuna cewa kashi 29 cikin ɗari ne na waɗanda suka cancanta kada ƙuriar suka yi zaɓen.

Najeriya tana da daɗaɗɗen tarihi na rikicin siyasa, to amma a iya cewa yanayin ƙasar zuwa yanzu bayan bayyana sakamakon, ba wata fargaba sosai.

An ƙalubalanci sakamakon zaɓukan shugaban ƙasa na Najeriyar da aka yi a baya, a kotuna to amma babu wanda 'yan hamayya suka taɓa samun nasara a gaban shari'a.