Sarki da Sarauniya sun leƙo ta baranda
Ɗaya daga cikin lokuta na tarihi shi ne lekowar Sarki da Sarauniya daga saman Baranda.
Wannan shafi ne da ke kawo muku ƙayatattun abubuwan da ke faruwa a wurin naɗin Sarki Charles III, kai-tsaye daga birnin Landan
Haruna Kakangi and Buhari Muhammad Fagge
Ɗaya daga cikin lokuta na tarihi shi ne lekowar Sarki da Sarauniya daga saman Baranda.
Asalin hoton, Reuters
Sama da sojoji dubu huɗu n suka takarawar gani a faretin da aka yi a yau a fadar Buckingham.
Sarki da Sarauniya sun fito gefen matattakala da ke sama suna kallon yadda ake take ƙasa.
Sun sha shewa daga wajen rundunoni daban-daban na dakaru.
Asalin hoton, Reuters
Yanzu da Sarki da Sarauniya suka isa fadar Buckingham, bari mu yi duba kan tafiyar tasu daga Westminster Abbey:
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Getty Images
Kambin da aka saka wa Sarki Charles III a yau domin naɗin sarautarsa a matsayin sarkin Ingila ya kai shekara 360 da ƙirƙira.
Kambin wanda ake yi wa laƙabi da Kambin Sarki Edward, an samar da shi a shekarar 1661 kuma Sarauniya Elizabeth II ce ta ƙarshe da ta saka shi shekara 70 da suka wuce.
Sarki Charles III ne basarake na bakwai da ya saka shi a tarihi kuma shi ma ba zai sake saka shi ba a rayuwarsa.
Ana saka kambin ne sau ɗaya - a lokacin bikin naɗin sarauta.
An kaɗa ƙaraurawar Westminster Abbey yayin da Sarki Charles III yake barin cikin ginin.
Asalin hoton, Getty Images
Archbishop na Canterbury ne ya jagoranci addu'ar neman dacewa.
Muna ci gaba da taya murna yayin da muke kawo muku hotunan Sarauniya Camilla da aka sa wa kanbi.
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Reuters
An ci gaba da kiɗa, kuma an ci gaba da gudanar da biki a ciki da wajen Westminster Abbey.
Dakarun Atilare na Sarki sun harba bindiga, waɗanda suka tsaya a wajen inda ake fareti, wasu kuma a gadar Landan wato Tower of London.
An buga bindiga 13 lokaci guda, a wurare daban-daban a Birtaniya ciki har da Edinburgh da Cardiff da kuma Belfast
Asalin hoton, Reuters
Ana ci gaba da waƙar taya murna ga sarki - mu kuma za mu ci gaba da kawo muku hotunan yadda lamura ke ci gaba da gudana.
Ga lokacin da aka naɗa Sarki Charles III.
Za ka iya ganin kambin St Edward a kusa, bayan an sanya shi a kan Sarki.
An haɗa shi da dutsen gwall 22, kambun mai shekara 360 ya fi tsayin senti mita 30, kuma nauyinsa ya kai kigiram 2.23.
Asalin hoton, Getty Images
Sarki Charles III ya ce bai zama sarki domin mutane su riƙa yi masa bauta ba, ya zo ne domin ya yi wa al'umma bauta.
Manyan mutane daga faɗin duniya sun samu wuraren zama a Cocin Westminster Abbey da ke birnin Landan domin kallon yadda za a naɗa Sarki Charles III.
Firaministan Birtaniya Rishi Sunak da sauran tsofaffin Firaiministocin ƙasar bakwai sun taru.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da matar Shugaban Amurka Jill Biden duka sun halarci wurin.
Wannan ne lokacin da ake jira.
Sarki Charles na sanye da alkyabba ta ƙasaita, wadda ta sha ado na alfarma.
Daga can ciki riga ce ta saurauta mai launin kunkumadi.
Samanta kuma akwai doguwar riga har ƙasa mai launin ruwan bunu, an yi wa gefenta ado da ruwan zinare tun daga sama har ƙasa, sannan aka zagaye ta da kwalliyar zinare.
Sai daga sama an yafa mata wani yadi mai kauri mai kama da alhariri, mai launin ruwan madara da ɗigo-ɗigon launin bunu da zinare.
Ya kuma rataya wani abu mai kama da zinare wanda ya sauko zuwa ƙirjinsa ya zagaya ta bayan wuyansa.
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Reuters
Sarki da Sarauniya sun isa cocin Westminster Abbey, inda a nan ne za a naɗa shi tare da ɗora masa kambi na tarihi mai ɗauke da zinare da lu'u lu'u da sauran duwatsu masu daraja da ƙasaita.
Wannan rana ce mai ɗinbin tarihi ga Sarki Charles da masarautar Birtaniya!
Asalin hoton, Reuters
Yarima William shi ne babban ɗan Sarki Charles III, wanda ya haifa tare da marigayi Diana.
Shi ne mai jiran gadon sarauta, kuma ɗaya daga cikin waɗanda al'umma ke nuna wa tsantsar soyayya a cikin iyalin masarauta.
Asalin hoton, EPA
Wannan ita ce gimbiya Anne, ƴa ga marigayiya Sarauniya Elizabeth II kuma ƙanwar Sarki Charles III da ake naɗawa a yau.
Ta kasance kusan a ko da yaushe tare da mahaifiyarta marigayiya Sarauniya Elzabeth II kafin rasuwarta.
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, PA Media
Asalin hoton, PA Media
Asalin hoton, Reuters
Da alama yarima Harry ya shigo cikin farin ciki da raha.
Shi Harry ɗa ne ga Sarki Charles III da ake naɗawa, kuma ƙani ne ga yarima William mai jiran gadon sarauta.
Sai dai Harry ya ajiye ayyukansa na masarauta a shekarun da suka gabata bayan saɓani da ya samu da ƴan uwansa na gidan sarauta.
Hakan ta faru ne bayan aurensa da Meghan Markle, wata ba'amurkiya.
Lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce sosai kuma har yanzu ana ci gaba da surutai daban-daban kan lamarin.
Asalin hoton, EPA
Asalin hoton, Reuters
Mutane sun ɓarke da sowa a lokacin da suka tsinkayi keken ƙasaita na masarautar Birtaniya ɗauke da Sarki Charles III da sarauniya Camilla.