Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

time_stated_uk

  1. Ƴan Najeriya 30,000 na neman diyya kan matsalar malalar mai

    Shell

    Alƙalai a Kotun Ƙolin London sun soma sauraron ƙarar da za ta tantance ko kusan ƴan Najeriya 30,000 suna iya neman diyya daga babban kamfanin mai na Shell saboda irin ɓarnar da malalar mai ya yi musu a 2011.

    Al'ummar yankunan da ke gaɓar ruwa a jihohin Bayelsa da Delta sun ce filayensu sun lalace matuƙa sanadiyyar malalar man.

    Wani hukunci da kotun ɗaukaka ƙara a London ta yanke tun farko ya ce an ɗauki lokaci mai tsawo wajen shigar da ƙarar tun bayan afkuwar lamarin.

    A ƙarƙashin dokokin Ingila, mai ƙara na iya neman diyya kan ɓarnar da aka yi wa dukiyarsa amma kar ya wuce shekara shida da faruwar ɓarnar.

    Kimanin gangar mai 40,000 ne ya malale a cikin teku abin da ya sa ya zama malalar mai mafi girma da aka taba samu a Najeriya.

    Al'ummar sun yi iƙirarin cewa lamarin na ci gaba da haifar musu da ɓarna ga filayensu da kuma ruwan shansu a don haka ya kamata a ƙyale su nemi diyya.

  2. EFCC ta kama mutum 23 da ake zargi da damfara ta intanet

    EFCC

    Jami'an hukumar EFCC mai yaƙi da yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon ƙasa sun damƙe mutum 23 da ake zargi da damfara ta intanet.

    A saƙon da EFCCC ta wallafa a shafinta na Tuwita, an kama mutanen ne a jihar Enugu bayan bayanan sirri da aka samu.

    Jami'an sun kuma gano wasu motoci shida na ƙasaita ƙirar Benz da Toyota da Lexus a hannunsu.

    Sauran kayayyakin da aka gano sun haɗa da wayoyin hannu guda 43 da kwamfutoci 11.

    Hukumar ta ce za ta tisa ƙeyar mutanen zuwa kotu da zarar an kammala bincike.

    View more on twitter
  3. Gawuna ya yi wa Abba Gida-Gida fatan alheri a mulkin Kano

    ...

    Mataimakin gwamnan Kano kuma ɗan takarar jam'iyyar APC a zaɓen gwamnan jihar, Nasir Yusuf Gawuna ya yi wa zaɓaɓɓen gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf addu’ar samun nasara a mulkinsa tare da yi wa kansa da magoya bayan jam’iyyar APC fatan ɗaukar kaddara.

    Gawuna ya bayyana hakan ne a cikin wani saƙon murya da aka naɗa, wadda mai taimaka masa kan harkar yaɗa labarai, Hassan Musa Fagge ya aiko wa BBC.

    Matakin na zuwa ne jim kaɗan bayan Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC) ta bai wa Abba Gida-Gida takardar shaidar cin zaɓen gwamna a ranar Laraba.

    A cikin saƙon, Nasir Gawuna ya ce “shi(Abba) wanda Allah Ya bai wa, Allah Ya sa ya zama shugaba nagari, mai adalci ga kowa.”

    Ya ƙara da cewa “Mu kuma Allah Ya sa mu zama masu biyayya ga shugabanci da kuma bin doka.”

    Gwuna ya buƙaci magoya bayanasa su ƙara haƙuri tare da addu’ar ɗaukan kadara a rashin nasarar da jam’iyyar ta yi a zaɓen gwamna na shekarar 2023.

    A ranar 20 ga watan Mayu ne, INEC ta bayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kano bayan zaɓen da aka yi ranar 18 ga watan na Mayu.

    Babban jami'in tattara sakamakon zaɓen gwamnan Kano Farfesa Ahmad Doko Ibrahim ya ce Abba Kabir ya samu ƙuri'u 1,019,602, yayin da Nasiru Gawuna ya samu ƙuri'u 890,705.

    Sai dai jam'iyyar APC ta ce ba ta yarda da sakamakon ba, kuma ta buƙaci INEC ta sake nazari kan zaɓen.

  4. Amurka ta ƙwace $53m daga hannun Diezani bayan kama ta da laifi

    Dieziani

    Ma'aikatar shari'a ta Amurka ta cimma matsaya kan wasu shari'u biyu da suka buƙaci ƙwace wasu manyan kadarori na alfarma da aka samar da su a ƙasar ta hanyar laifukan almundahanar kuɗaɗe.

    Wasu takardu daga ma'aikatar shari'ar ƙasar sun nuna cewa batun ya shafi tsohuwar ministar albarkatun man fetur ta Najeriya Diezani Alison-Madueke da wasu abokan kasuwancinta biyu Kolawole Akanni Aluko da Olajide Omokore.

    Da wannan mataki a yanzu ma'aikatar shari'ar ƙasar ta ce ta ƙwace kuɗin da ya kai dala miliyan 53.1, ƙimar kuɗin kadarorin idan aka sayar da su.

    Takardun kotun sun nuna cewa daga shekarar 2011 zuwa 2015 Diezani wadda a lokacin take ministar man fetur a Najeriya ta karɓi cin hanci daga abokan kasuwancinta.

    Wadda ita kuma Diezani ta riƙa bai wa kamfanoninsu manyan kwangilolin man fetur.

    Ma'aikatar shari'ar Amurkan ta ce an yi amfani da kuɗaden da aka biya a matsayin cin hancin da yawansu ya kai sama da dala miliyan 100, wajen sayan manyan kadarori a Amurka, ciki har da rukunin gidaje a California da New York da kuma Galactica Star.

  5. Sabon zaɓaɓɓen gwamnan Taraba ya karɓi takardar shaida

    Agbu Kefas

    Sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Taraba Agbu Kefas ya karɓi takardar shaidar cin zaɓe a ofishin hukumar zaɓen ƙasar da ke jihar.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Agbu Kefas ya ce yana gode wa al'ummar jihar bisa zaɓarsa da suka yi a matsayin sabon gwamnan jihar.

    Agbu Kefas

    Hukumar zaɓen ƙasar ce dai ta ayyana Agbu Kefas na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashen zaben gwamnan jihar da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris

  6. Saudiyya ta ƙwace tan biyar na naman kaji da ya lalace

    naman kaji

    Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Saudiyya (SFDA) ta ƙwace tan biyar na naman kajin da ya lallace a wani gidan ajiye kayyakin abinci da ke birnin Riyadh.

    Hukumar ta tabbatar da cewa gidan ajiyar kayan abincin ya saɓa wa ƙa'idoji masu yaw, cikin har da yin ƙarya sayar da kayayyakin da suka lalace, inda ake sake wa naman kajin mazubi tare da sanya musu sabbin kwanan watan lalacewa.

    Haka kuma hukumar ta ce gidan ajiyar ya saɓa wa dokokin lafiya, da amfani da ma'aikatan da ba su da takardun shaidar karatun lafiya.

    SFDA ta kuma rufe gidan ajiyar tare da lalata duk kayyakin da ta ƙwace.

    Hukumar ta ce ta gudanar da wannan aiki ne tare da hadin gwiwwar hukumar gudanarwar birnin Riyadh da ma'aikatar kasuwanci da ma'aikatar walwala da ci gaba jama'a da hukumar zakka da haraji ta ƙasar tare kuma da hukumar fasa ƙwauri ta ƙasar.

    Haka kuma hukumar ta yi kira ga kwastomomi da su kai rahoton duk wani shago ko kamfanin da ya sayar musu da kayayyakin da suka lalace.

  7. Indiya na murnar haihuwar damisar Namibiya

    s

    Damisar da aka sauya wa matsuguni daga Namibiya zuwa Indiya a shekarar da ta gabata, ta haifi 'ya'ya huɗu.

    Karon farko da wata damisa ta haifi 'ya'ya hudu a Indiya, kamar yadda ministan muhallin ƙasar Bhupendar Yadav ya bayana.

    Mista Yadav - wanda ya wallafa hotunan 'ya'yan damisar a shafinsa na twitter - ya bayyana lamarin a matsayin wani abu na tarihi a harkokin gandun dajin ƙasar.

    View more on twitter

    Nau'in damisar yankin Asia sun ɓace a ƙasar Indiya tun gwamman shekaru da suka gabata.

    A shekarar da ta gabata gwamnatin Indiya ta saki wasu damisa takwas nau'in Afirka a gandun dajin Madhya Pradesh a wani ɓangare na sake bunƙasa yaɗuwar manyan dabbobin.

    Inda aka killace asu daga cikinsu cikin tsauraran matakan tsaro, to amma a farkon wannan shekara ɗaya daga cikinsu ta mutu sakamakon jinya da ta yi.

  8. 'Yan fashi sun fasa kabarin wani zabaya don sace sassan jikin gawarsa

    gawa

    Wasu mutane sun fasa kankaren da aka binne kabari domin sace sassan jikin gawar wani zabaya a lardin Tete da ke yammacin ƙasar Mozambique.

    Akan yi amfani da sassan jikin zabaya a ƙasar domin ayyukan tsafi.

    'Yan sanda sun ce sun tsaurara bincike a gundumar Moatize da ke lardin Tete domin kama waɗanda ake zargi da aikata laifin.

    A kwanan nan ne dai aka binne gawar zabayan mai shekara 50 a wani ƙauye da ke kusa da kan iyakar ƙasar da Malawi

    'Yan uwan mamacin sun yi amfani da sumunti wajen binne gawar don kauce wa ɓarayin kaburburan.

    Mai fafutikar kare haƙƙin zabaya a ƙasar, Remane Madane ya yi Allah wadai da lamarin, da ya kira da 'fashi'.

    Zabaya da dama a ƙasashen Afirka ciki har da Malawi da Mozambique da Tanzania na fuskantar barazanar kisa daga masu tsafi.

  9. Zimbabwe ta nemi taimakon dabarun aiki a wajen sojin saman Najeriya

    Sojojin sama

    Babban kwamandan sojin sama na Zimbabwe, Air Marshal Elson Moyo ya bayyana buƙatar ƙasarsa na neman tallafin dabarun aiki daga rundunar sojin saman Najeriya.

    Moyo ya bayyana buƙatar ne a lokacin da ya ziyarci babban hafsan sojin saman Najeriya Air Marshal Oladayo Amao, a shalkwatar rundunar sojin saman Najeriya da ke Abuja babban birnin ƙasar.

    Daraktan sashen hulda da jama'a da yaɗa labarai na rundunar Air Commodore Ayodele Famuyiwa, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

    Babban kwamandan sojin saman Zimbabwe ya buƙaci tallafin rundunar sojin saman Najeriyar a ɓangarorin da suka shafi bincike da ci gaba, da fannin fasahar jiragen yaƙi da gudanarwa da yadda za a yi aiki da jiragen yaƙin ƙirar F7 da Mi-35.

    Moyo ya ce ɓangarorin da ƙasarsa ke neman taimakon Najeriyar, ɓangarori ne da rundunonin sojin saman ƙasashen biyu duka ke amfani da su, musamman jiragen yaƙin da ƙasashen biyu ke amfani da su.

    Ya ce a cikin ɗan takaitaccen lokaci rundunar sojin saman Najeriya ta samu gagarumin ci gaba wajen gina kanta da amfani da dabarun cikin gida.

    A yayin da yake jawabi a nasa ɓangaren, babban hafsan sojin sama na Najeriya Air Marshal Oladayo Amao, ya ce rundunar a shirye take domin ƙulla ƙawancen da zai amfanar da juna tsakaninta da takwararta ta Zimbabwe.

    Amao ya ce a yanzu haka rundunar sojin saman Najeriya ta ƙulla ƙawance da ƙasashe da dama a nahiyar Afirka da ma wajenta, yana mai cewa a kodayaUshe rundunar a shirye take domin taimaka wa ƙasashen da ke buƙatar taimakonta.

    Ya ƙara da cewa haɗin kai tsakanin rundunonin sojin ƙasashen Afirka zai taimaka wajen magance matsalolin tsaron da nahiyar ke fuskanta

  10. Ziyarar Kamala Harris: Zambiya ta gargaɗi masu zanga-zangar adawa da auren jinsi

    Zambiya

    Gwamnatin ƙasar Zambiya ta gargaɗi 'yan adawa da su guji gudanar da zanga-zangar adawa da auren jinsi a lokacin ziyarar mataimakiyar shugaban Amurka Kamal Haris zuwa ƙasar.

    Jam'iyyar adawar ƙasar na shirin gudanar da zanga-zangar ne gabanin wani taron bunƙasa dimokraɗiyya na duniya da za a yi a Lusaka babban birnin ƙasar.

    Kamala Haris za ta ziyarci ƙasar ranar Juma'a, an kuma tsara cewa za ta gabatar da jawabi a gaban taron, wanda haɗin gwiwar ƙasashen Zambiya da Amurka da Costa Rica da Netherland da koriya ta Kudu suka ɗauki nauyinsa.

    Fiye da 'yan majalisa 50 ne na jam'iyyar adawa suka yi zargin cewa an shirya taron ne da nufin turtasa zartar da 'yancin auren jinsi a ƙasar.

    Ƙungiyar' 'Amnesty International Zambia' ta yi kira ga gwamnatin ƙasar da ta ɗauki mataki mai ƙarfi don goyon bayan 'yancin auren jinsi da kuma tabbatar da cewa zanga-zangar ba ta haifar wa taron tsaiko ba.

    Ministan tsaron ƙasar Jack Mwiimbu ya ce hukumomin ƙasar ba za su bari a karya doka a lokacin taron ba.

    Shugaban ƙasar Hakainde Hichilema ya yi kira da a kwantar da hankula tare da zama teburin tattaunawa game da barazanar zanga-zangar.

    “Mun fahimci damuwar 'yan adawa da sauran masu ruwa da tsaki, kuma a shirye muke mu zauna don tattauna yadda za mu warware wannan matsala'', in ji shugaba Hichilema.

    A farkon wannan wata shugaban ƙasar ya alƙawarta ci gaba da aiki da dokokin ƙasar da suka haramta auren jinsi.

    To sai dai 'yan adawar sun ƙaryata wannan iƙirari nasa, suna masu cewa gwamnatinsa na goyon bayan auren jinsi.

    Kamala Haris za ta ziyarci Tanzaniya ranar Laraba, kafin ta wuce zambiya a ranar Juma'a a wani rangadi da take a yi a nahiyar Afirka.

  11. Buhari ya rantsar da sabon shugaban hukumar kula da aikin 'yan sanda

    Solomon Arase

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da tsohon Sifeton 'yan sandan ƙasar Solomon Arase mai ritaya a matsayin sabon shugaban hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta ƙasar.

    Sabon shugaban ya sha rantsuwar kama aiki ne ranar Laraba a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja, gabanin fara taron majalisar zartarwa ta ƙasar.

    Watanni biyu da suka gabata ne dai majalisar dattawan ƙasar ta amince da shi a matsayin shugaban hukumar.

    Solomon Arase wanda ya yi ritaya daga aikin ɗan sanda a shekarar 2016, ya yi aiki a sassa daban-daban na rundunar 'yan sandan ƙasar, kafin daga bisani ya zama babban sifeton 'yan sandan ƙasar a shekarar 2015.

  12. INEC ta bai wa Abba Kabir shaidar lashe zaɓen gwamnan Kano

    Abba Kabir Yusuf
    Image caption: Abba Kabir Yusuf

    Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta a Najeriya ta miƙa wa Abba Kabir Yusuf shaidar lashe zaɓen gwamnan jihar Kano.

    Abba Kabir, wanda ya yi nasara zaɓen gwamnan da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, ya samu ƙuri'u 1,019,602, yayin da Nasiru Gawuna na jam'iyyar APC ya samu ƙuri'u 890,705.

  13. Faransa ta ce tsohon shugaban Tarayyar Soviet ya aikata kisan kiyashi

    Majalisar dokokin Faransa ta amince da gagarumin rinjaye cewa tsohon shugaban rusasshiyar Tarayyar Soviet Joseph Stalin ya aikata kisan kiyashi

    Faransa ta amince da cewa an jefa miliyoyin 'yan Ukraine cikin tsananin yunwa a shekarun 1930.

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ya yi maraba da ƙuri'ar da aka kaɗan wadda ya kira ta a matsayin babban abin tarihi.

    Gwamnatin Ukraine dai na ganin an shiga cikin tsananin yunwa a shekarun 1932 zuwa 1933 ne saboda ƙwace hatsin da aka yi a ƙarƙashin mulkin Stalin.

    Mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine a yanzu, ta sa ƙasar jan hankalin ƙasashen Turai akan su yarda cewa wannan jefa ƙasar cikin halin yunwar babban laifi ne.

  14. Zulum zai gina ƙauyuka uku don tsugunar da 'yan gudun hijira 20,000

    Zulum

    Gwamnamn jihar Bornon Babagana Umara Zulum ya bayyana shirin sake gina wasu ƙauyuka uku domin sake tsugunar da 'yan gudun hijirar da mayaƙan Boko Haram suka raba da muhallansu.

    Fiye da mutum 20,000 ne boko haram ta rana da muhallansu a jihohin Borno da Yobe da adamawa, waɗanda wasunsu ke zaune a makwabtan ƙasashen Nijar da kamaru da Chadi.

    A wani saƙo da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Tuwita ya ce tun shekarar 2014 ne mayaƙan Boko Haram ta raba mutanen da muhallansu.

    View more on twitter

    Zulum ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da kwamitin maido da 'yan gudun hijirar da ke ƙasashen waje a Abuja babban birnin ƙasar.

    Gwaman Zulum shi ne mataimakin kwamitin shugaban ƙasa na maido da 'yan gudun hijirar ƙasar da ke zaune a ƙasashen waje , tare da sauya tunanin mutanen da da Boko Haram ta sako.

    Inda mataimakin shugaban ƙasa farfesa Yemi Osinbajo ke zaman shugaban kwamitin.

    Gwamna Zulum ya ce shugaba Buhari ya amince da bai wa kwamitin naira biliyan 15, yayin da gwamnatin jihar Borno ke shirin sake gina ƙauyuka uku don tsugunar da 'yan gudun hijirar.

  15. Fasinjojin jirgin ƙasan Abuja - Kaduna da aka sace ba su gama karɓar kayansu ba

    hh

    Ma'aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta jihar Kaduna a Najeriya ta ce har yanzu akwai kayayyakin fasinjojin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna - da aka sace shekara guda da ta gabata - a ma'aikatar.

    A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Twiter ta ce bayan aukuwar harin a shekarar da ta gabata, ma'aikatar ta ɗauko jakankunan fasinjojin bayan da jami'anta suka hallara wurin da lamarin ya faru.

    To sai dai a cewarta har yanzu akwai jakankuna 16 da ke hannunta, ba tare da an karɓe su ba.

    A ranar 28 ga watan Maris na shekarar 2022 ne dai wasu mahara suka tare jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna, bayan da suka lalata hanyar jirgin da abin fashewa.

    Sannan kuma suka sace fasinjoji masu yawa tare da yin garkuwa da su.

    Fasinjojin dai sun kwashe kimanin watanni a hannun 'yan bindigar, inda suka riƙa sako fasinjojin rukuni-rukuni.

    Sun dai saki rukunin ƙarshe na fasinjojin da ya ƙunshin mutum 23 a farkon watan Oktoban 2022.

  16. Guatemala ta ɗora alhakin mutuwar 'yan ci-rani a kan masu safarar mutane

    Ministan harkokin wajen Guatemala, Mario Bucaro, ya ɗora alhakin mutuwar 'yanci rani akalla 40 a cibiyar da ake tsare su a Mexico akan masu safarar mutane.

    Yawancin wadanda suka mutum 'yan ƙasar Guatemala ne.

    Mista Bucaro, ya ce dole a ɗora alhakin abin da ya faru a kan masu safarar mutane saboda rawar da suke takawa wajen ƙoƙarin satar shigar da 'yanci rani cikin Amurka ba bisa ƙa'ida ba.

    Kafar yada labaran Mexico ta nuna wasu hotuna inda aka ga wasu masu gadi biyu sun guje wa wata gobara da ta tashi ba tare da bude kofofin dakunan da ake tsare da 'yanci ranin ba.

  17. Cutar Lassa ta kashe mutum 142 cikin wata uku - NCDC

    Lassa fever

    Cibiyar Daƙile Cutuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya NCDC ta ce a cikin ƙasa da wata uku an samu mutane 784 da aka tabbatar da cewa sun kamu da cutar zazzaɓin Lassa inda mutum 142 suka mutu a faɗin jihohin ƙasar 23.

    A wani saƙo da cibiyar NCDC ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce an samu waɗanda suka kamu da cutar ne daga 1 ga watan Janairu zuwa yanzu.

    NCDC ta ce an samu yawaitar ɓullar cutar ne a jihohin Edo da Ondo da Ebonyi da Bauchi da Taraba da Benue da Rivers da Plateau da Nasarawa.

    Haka kuma cibiyar ta ce an samu aƙalla mutum ɗaya da ke ɗauke da cutar a cikin jihohin ƙasar 23.

    NCDC ta ce kashi 71 na sabbin mutanen da suka kamu da cutar an same su ne a jihohin Ondo da Edo da Bauchi, yayin da aka samu kashin 29 a sauran jihohin ƙasar shida.

    Cutar Lassa wata ƙwayar cuta ce ta 'Virus', mai haddasa tsananin zazzaɓi da ɓullar jini a jikin wanda ya kamu ta ita, wanda ake kira a Turance - 'viral heamorraghic fever'.

    A wasu lokuta cutar kan zo da wasu alamomi kamar mura da mashako da samun matsalar numfashi.

    Asalin cutar ana samunta ne daga wasu nau'in ɓeraye da ake kira 'multimammet rats' a Turance.

  18. Assalamu alaikum

    Masu binmu a wannan shafi barkan mu da safiyar wannan rana ta Laraba.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin ci gaba da kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Ku leƙa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.